x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 737

07 Oct 2025
Sufyan da Sumaya su ka ƙarayi a Makaranta, shaƙuwa mai ƙarfin gaske ya ƙara shiga tsakaninsu. Kowannen su ya na jin ya yi dace da Abokin rayuwa dai-dai burinsa.

Kamar jiya ita ta koshi har bakin Layi.

NAILA; Bayan ta dawo kasa aikata komai ta yi, barcin ma da ya ɗauketa a zabure na miƙe saboda mummunar mafarkin da ta yi, wai ga Salman ya biyota zai ciremata harshe. A take wani irin tsoro da kaɗaici ya soma tsargata.

A haka Sufyan ya shigo ya same ta. Bai tantace muryata da kuka ya dusasar ba, balle kayan jikinta da batayi wanka balle ta sauya su, kuɗin da'aka biyata a wajen kitso ya tambaya bayan ya zauna.
Dama su na gefeta, don haka ta ɗauko ta miƙamai.
Da ƙarfi ya ce "Allah! Naila sannu da aiki, Naila idan na gama Karatu na samu aiki sai kinfi kowa jindaɗi, kuɗin da kika ba ni yau ma riga ɗaya kawai na siya da shi, haka na wuni da yunwa. Yanzu kinsan mai za'ayi zan ɗauki kuɗinnan na ƙarasa siyan kayan sawa kinga mun gama da wannan, ɗan abin ya rage kuma na riƙe kuɗin makaranta ko ya ya kika gani, ko da yake bari na tashi na je yanzu saboda gobe lecture 7:00am zan shiga." Ya ƙarasa faɗa ya na miƙewa.

Kafin Naila ta ahaɗiye hawayenta tuni Sufyan ya fice, ko tambayar dalilin da ya sa ban tayi girki ba baiyi ba.

Sufyan ya zaɓi zuwa ya siyo ba tare da jiran gari ya waye ba ne saboda Sumaya karta sa ran zai kuma siyamata wa su kayan.

Ko tsinke baiyi hikimar siyawa Naila ba tunda itama kayanta duk Abaya ne ma su arahar gaske ga adon da aka yi mai na saƙi sak na ƴan karkara. Chocolate kawai ya iya siya da Naila shima kuma sai da ya haɗa da na Sumaya.

Daɗin samun komai da sauƙi yasa yake ta murmushi shi kaɗai har ya dawo Gida.

Lokacin da Sufyan ya dawo Naila ta ga bai siyomata ko tsinke ba kasa shiru ta yi ta ce;

"Ba ka kyauta ba, tayaya zaka siyo kaya iya kai kaɗai bandani? " Da farko da zafinsa ya ɗago amma kome ya tuna sai ya fasa ya fara lallashita haɗe da tambayar abinda ya ke damunta. Da salon dabaru Sufyan ya kalamacata har ya yi nasarar tserewa daƙinsa bayan ya bata abinda ya siyomata.

Naila ta so ta ba shi labarin abinda ta gani amma gudun kar ya kira ya fesawa Mahaifiyarshi ya sa taja bakinta ta yi shiru.

Daga wannan ranar Sufyan ya ƙara zage damtse wajen yin ado da kaya kala-kala, da zarar ta samu kuɗi zai siyeta da daɗin baki ya karɓe, har Mahaifinsa ya sa ya tura Yaro a kaiwa Kaka waya suka gaisa Naila.
Ranar da Naila ta gaisa da Kaka bata runtsaba, saboda tanaso ta bata labarin abinda ta gani da wanda Sufyan yakemata amma babu hali domin zama Sufyan ya yi gadinta da sunan kallon talabijin.

A haka rayuwar ta miƙawa Naila da Sufyan, da kuɗin sana'ar kitsonta ya ke komai na Makaranta har ya yi wa Budurwarsa Sumaya hidima, duk Naila bata sani ba, da kuɗinta dai ya ƙara ƙawata living room ɗin su har da ɗakin kwanansa.
A ɓangarena Suturar sawa kuwa Naila bata da na arziƙi, idan tayi ƙorafi sai ya ce mezatayi da sutura ita da ba fita na ke yi ba, kitso kawai yake zuwa, shi dama kuma ba ya son idan zataje yiwa Mutane kitso ta yi kwalliya kar wani ya ƙwacemasa ita, shi ya fi son ya ganta ta yi ado da kayan da ta taho da shi saboda hakan na tunamai da Yankinsu.

A kwana a tashi Ruwaida ta fuskanci Sufyan cutar Naila yake yi domin kuwa duk ta rame tayi duhu saboda ƙewa da damuwa. Shawarar Naila ta fara ɓoye kuɗinta Ruwaida taba ta, idan sun taru za ta rakata ta siyi suturun sawa, idan Sufyan ya tambayeta ina ta samo ta ce ita ta siyamata da kuɗinta.

Bayan kwana biyu
Sufyan ya jera kwanaki uku ya na tambayar Naila kuɗi sai ta ce babu, da ya ga dai dagaske ta ke babu kuma aljihunsa ya yi ƙasa sai titsiyeta da tambayoyi, ƙarshe tana Madafi tana girki ya shiga ɗakinta ya bincike har sai da ya samu kuɗin da take ɓoyewa. Ta na tsaye ya shigo Madafi da kuɗin a hannunshi kafin ta yi magana ya kwasheta da mari cikin zafin rai yake masifar yasan Ruwaida ce take zugata, wallahi ta ci darajar itace take naimomata customers da sai ya ci mutuncinta ya wulaƙantata.

Sufyan ya yi tunanin ganin sauyi ko wani gagarumin ɓaci rai a saman fuskar Naila, amma sai ya ga akasin haka kamar baiyimata komai ba, cikin neman magana ya ce
"gaba zakiyi da ni saboda nayi miki faɗa ko,? to wai Naila saboda wa nakeyin wannan karatunnan? Saboda ke nake da ƴaƴan da zamu haifa, Naila saboda tsoron kar mu zo mu tara ƴaƴa babu kuɗin kula da su yasa kikaga na daure har yau ban kusanceki ba, duk wannan bai sa ki tausayamin ba haba Naila sai a fara zugaki ki na ɓoyemin samunki."

Murmushin mai ciwo Naila ta yi ta kalli fuskarshi ta ce;

"matacce ai ba shi da ran yin rigima da rayayye, idan kuma kasan yau ai ba kasan gobe ba, dalilin baiwar kitson da Allah Ya bani yasa ku ka kawoni Birnin Abyad, ga shi kana mora har ka na da ƙarfin halin yin iko da shi. Ba ni da ƙarfin yi ma iyaka amma lokaci zai yi maka a yanayin da baka taɓa tsammani ba"....✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c

🔥ZINARE🔥

( ```The Gripping family saga with high Caliber)

```
SASAAL


14

Sufyan sak ya yi a tsaye har Naila ta gama magana ya kasa ce mata komai, har na ɓacewa ganinsa.
Bayan tafiyarta kafaɗarsa ya ɗaga
A ganinsa mai zai jiyewa takaici? kuɗi ne dai dole ya karɓesu saboda da su ya dogara.

NAILA
★washe gari kamar ko yaushe bata koma barci ba, sai da ta gama Breakfast.

Ko da koma barci ta farka misalin tara na safe, ta fito Parlo a yadda ta jera abincin haka na samesa Sufyan bai ci ba. Tasan ya yi hakane saboda kuɗaɗents da ya karɓe, a karon farko hawayen takaicinsa su ka zubomata, bata tsawaita zubda hawayenta ba, bata kuma hana cikina abinci ba. Bayan ta ci na ƙoshi na fito harabar Gidan shan iska.

Yasar ta hango ya na yunƙurin fitowa, da farko ta yi niyyar guduwa saboda ba ta son haɗuwarsu, amma da na tuna taimakon da ya yi msta ranar da accident ɗin sashen Ruwaida ya faru sai ta jirkirta.

Yasar manazarcin halayyar Ɗan adam ne, kuma likita a babban Asibitin Birnin Abyad. Gaishesa kawai ta yi ta matsar da kanta gefe.

Matsowarsa kusa da ita ya sa ta juyo tana zare ido.

Yadda ta zare ido na ne ya sa shu saki dariya ya na shafa tarin sumar kanshi da ya tattara wajen ɗaya ya ɗaure kamar Mace.

Ba bu zato ta ji ya ce;

"Maimakon zama haka mai zai hana Mijinki ya naima miki gurbin karatu a jami'ar su, idan ma ba shi da hali ki naimi izininsa ni zan biya miki Fisabilillah."

kalamansa sun wanke dattin da ya jima danƙare a cikin ƙwaƙwalwar Naila na tsahon lokaci, maganarsa abun dubawa ne a gareta, kuma shawara ne mai kyau amma tuna Sufyan ya sa ta ce;

"mijina ba zai yarjemin ba" ta faɗa da murya da ya bayyana rauninta.

Yasar ya kai wa su daƙiƙu ya na kallonta kafin ya murmusa da cewa;

"idan Mijinki ya na da sauƙin kishin da zai barki zuwa Gidajen da maza da mata su ke rayuwa, kamar Campus ɗin su Ruwaida kiyiwa Ɗalibai kitso, to babu dalilin da zai sa ya hanaki naiman ilimi. Menene amfanin neman da ba zamu gina gobenmu da shi ba?"

Kamar talabijin haka Naila ta zubawa fuskar Yasar mai tsananin haske da kyau ido, ba haskensa da kyansa ta ke kallo ba, gaskiyar da ya faɗa take gani a saman fuskarsa.

YASAR Duk da ya san Naila ta gamsu ɗari bisa ɗari kuma ta yarda da maganarsa amma tana kwakwanton naiman mafita sai ya ƙara ce mata;

"ga hanya mafi sauƙin warwarewa kanki komai, ki fara naiman izininsa a kan na ce zan biyaki kuɗi mai yawa ki kitsamin kaina, ki ji mai zai ce, idan ya ce a'a sai ki san dabarabar da za kiyi ki tambayesa izinin naimar miki jami'a, idan kuma ya ce eh, kin samu hanyar da zaki tafi Jami'a cikin sauƙi, ki nutsu ki warware komai dalla-dalla za ki fahimce ni da kyau".

Cikin nauyin baki Naila ta yi mai godia. Har ya ɓacewa ganinta bata daina kallon hanyar da yabi ba.

Yinin ranar a tunani ta ƙaresa domin ta kasa yarda Sufyan ba ya kishinta, shi da ya ce kishin ta ne ya ke hanashi siyamata kaya kar wa su, su ga kyanta, duk da tasan ba ya sonta sosai kamar kuɗin da na ke samu, amma ta yarda da zancensa.
Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa ta miƙe ta ƙarayin wanka, kayan dai da ta taho da su daga Yankinmu ta saka, duk sun ƙode sun jeme.

SUFYAN; Sufyan kayan ciye-ciye da ice cream kala-kala ya siya mu su shi da Sumaya, har sun dawo sunyi lecture ya tuna rashin siyawa Naila kaya zai ƙara tunzura ta, har ta ɓullo da wata dabarar tara kuɗin a inda ba zai gani ba balle ya ƙwata, musamman wajen Ruwaida, kuma siya mata kayan zai kawar da tunanin ba ya sonta ba ya son farin cikinta a ranta. Bai naimi rakiyar Sumaya ba ya tafi, kusan rabin kuɗin da ya ɗaukemata ya siyamata kaya da su ba dan ransa ya so ba.

Da ya dawo Makaranta da Kayan Ƙiri-ƙiri Sumaya ta nuna ƙishinta, ranar ko ƴar hirar da su ke yi a kan hanya ba su yi ba, bakinta a gaba take tuƙi, takaici da kishi na nuƙurƙusarta. Ko da ta sauke Sufyan kafin ya yi mata sallama ta figi mashin ɗin ta.
Jiki a sanyaye Sufyan ya shigo gida.

Da Sufyan ya shigo bai bawa Naila kayan da ya siyo ba, ɗakinsa ya wuce da kayan ransa fal kokwanton ko dai gobe ya kaiwa Sumaya, saboda bai ji daɗin yadda su ka rabu ba.

Jikinsa ba kuzari ya tsakuri abincin da ta girka, itama Naila tata fuskar sam ba fara'a. Bayan ta tabbatar ya huta ta sako masa hirar neman izininsa zata yiwa Yasar moƙocinsu kitso tare da bayyana masa irin kuɗin da ya ce zai ba ta. Ga mamakinta Sufyan ko alamar banbanci tsakanin jinsi Namiji da na Mace bai nuna ba yace ai neman kuɗi ne babu Matsala. Zuciyarta da jinina na gudana da sauri-da sauri ta tambayesa izinin komawa Makaranta, kai tsaye ya ce mata;

"ba ni da kuɗi, ko kuɗin da kike ba ni kike yiwa baƙin ciki Naila?" Muryarta ta na rawar kukan da ya tahomata tana ƙoƙarin dannewa ta ce;

"ance ba sai ka biya ba za'a samomin Scholarship" kamar an tsikaresa haka ya miƙe ya na masifa kamar zai taune harshensa. Sai da ta bari ya gama kumfar bakinsa, sannan ta miƙe haɗe da cewa;

"zuwa Makaranta da sunan naiman ilimi sai zama aji ɗaya da Maza, amma kowa da Mazauninsa, ba bu kuma tilas ɗin mu'amalantar juna, iskanci ne. Amma zuwa Gidan da Maza su ke rayuwa da sunan sana'a haɗe da kama kansu na kitsa saboda za su bani kuɗi mai yawa shi ba Iskanci ba ne Sana'a ce ko? Idan ka rayu a matsayin miji a gareni sannan ka zaɓi zaluntata da duƙushemin rayuwa wacce riba za ka samu Sufyan?"

Ƙasa ya yi da kansa, ganin ba shi da mafita sai ya fara lallashinta haɗe da garzayawa ɗakinsa a hanzarce ya kwaso kayan da ya siyo mata yake kokwanton ba ta. Kamar zai yi kuka haka yake magiyar gwadata ya ke yi kamar yadda akasarin Maza suke yaudarar Mata da sunan gwaji.

A cewarsa idan banda gwadata ya ke yi ta ya ya zai yarda ta yiwa Yasar kitso sai ka ce ba Musulmi ba, shi kansa Yasar ɗin ai ba mutumin ƙwarai ba ne, idan ban da haka ta yaya zai ce Matar aure ta yi mai kitso. Da ire-iren waɗannan kalaman ya so yaudarata.

Ba bu daɗin bakinsa ɗaya da ya samu gurbi a cikin zuciyar Naila, amma ta ji daɗin kayan da ya siyomata. Kamar komai ya wuce haka ta nunamai, domin ya ƙara shashantar da ita sai ya fara ragewa kanshi zafi kamar yadda ya saba.

Bayan ta koma daƙina kuka da ya sanyamsta ciwon kai ta yi, ba ta da wanda zats buɗewa zuciyarta ta zazzage masa dukka damuwarta sai dai tasha kukanta ita ɗaya a ɗaki.

★washe gari da Sufyan zai fita Makaranta Cikin dabara ya ke ja mata kunnen rage mu'amalantar Ruwaida idan ba haka ba zata kaita ta baro.
Abinda bai sani ba
Kalaman Ruwaida ga Naila ma su taushi ne haka zuciyarta da niyyarta dukkan ma su kyau ne a kan Naila, idan ma cuta ce Ruwaida ta rasa wacce zata cuta sai irin Naila.

Naila Ba ta ce mai kanzil ba har ya bar Gidan.

Da ga ranar ta ƙauracewa zaman harabar Gidan saboda Yasar, idan ka ganta a waje to Ruwaida ce ta haɗata da customer, ko kitso idan aka biyota Gida a living room ta ke zama su yi.

A hankali a hankali Naila ta fara rama mai busar da Mutum tambayar duniya idan Ruwaida ta yi mata sai na ce mata"ba komai".


Sufyan ya haramtamata gaisawa da Kaka kullum sai ya ce ya kira Ɗayyib Mahaifinsa ba ya samu.

A kwana a tashi cikin hikimar Ubangiji suka shekara ɗaya da rabi a Birnin Abyad.

A ɓangaren Sufyan ya canza ya ƙara haske ya yi kyau sak mazaunin Birnin Abyad, saɓanin Naila ta da ta bushe ta rame idan ta yi dariya sai haƙora su cikamata fuska.

Ta ƙara samun customers wa su ta je Gida tayi musu wa su kuma su biyota Gida, duk tarin kuɗin da take samu Sufyan ne yake kwashewa domin akwai ranar da ta ɓoye kuɗi a wajen Ruwaida, har ya titsiyeta da tambaya.

Bata ɓoye masa su na wajen Ruwaida ba, a ranar sai da ya yi mata dukkan da ya hanata motsi. Bayan ya fita Makaranta ya kira Mahaifinsa ya yi mai bayani. A take shima ya sanar da Uban Gidansa, washe gari jami'an tsaro mata suka zo har Gidan su ka jawa Ruwaida kunne haɗe da karɓe kuɗin da na ke tarawa, bayannan su ka yi mata tsakani da ni.

Ruwaida ta na tsoron abinda zai taɓa karatunta. Ba tare da ta nemi ƙara ganin Naila ko tambaya ta sane abinda aka yi mata ko ba na sane ba, ta tattara Kayanta ta tashi bar Gidan, sai ma su kwashe kayanta kawai Naila ta gani.

Tun da ga lokacin sai Naila ta ƙara zama kamar sha-sha-sha. Ga shi Yasar tun da ya ya bata shawara na yi watsi da shi har take gudun haɗuwa da shi ya tattara lamarinta ya watsar ko haɗuwa sukayi ta gaishesa daƙyar ya ke amsawa. Yasar bai ƙara tsanar Naila ba sai da ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Sufyan da Ruwaida. Daga wannan ranar ko gaishesa Naila ta yi baya amsawa.

Abubuwan da su ka faru da Naila sun sa ta yi losing hope, sai ta ke ganin sakarwa Sufyan komai ya yi iyakacin zaluncin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwata shi kawai ya fiyemata sauƙi.

Da ga wannan dukan farkon da Sufyan ya yimata ya mayar da ita kamar jaka, akan abu ƙalilan sai ya zaneta, ɗai-ɗaikun ranaku ne baya kai hannunsa jikinta, ga dabaru da ya ɓullo da shi, haka zai sakamata videon tsaraicin wa su ya ce ta nutsu na kalla irinsa zata yimai. Da farko gardamar bazan yi ba ta yi mai, ai kuwa ya kamata ya yi mata dukan tsiya, abisa tilas ɗin rashin zaɓi ta fara bin umarnin Sufyan.

A haka su ka ƙara shafe shekara ɗaya cikin uƙuba da tsanani, ba ta gaisawa da Kaka, ba ta da abokin hira, domin wacce ta tare a ɓangaren Ruwaida sai da Yasar ya ja mata kunnen kar ta kuskura ta kula Naila idan ba haka ba zan ƙulla mata sharrin da Allah ne Kaɗai zai wanke ta.

Da kuɗin guminta Sufyan ya ke rayuwa, da kuɗin guminta ya ke tari a Bankin da Ubangidan mahaifinsa ya yi mai jagora ya buɗe, da kuma kuɗin guminta ya ke yiwa budurwasa Sumaya siyayya. Ita kuma ko cikakken Suturar sawa ba ta da shi, idan ta yi dariya tsananin munin ta sai ya bayyana saboda rashin namar fuska har wani yamushewa fatatar ta yi. Sufyan ma ya kance ba ta da abinda zai mora a jikinta duk ta rame sai ƙasusuwan da zasu jimai ciwo, da wannan yake fakewa sai dai ya tuɓe ya yi ta umartata tana yimai abinda zai gamsar da shi.

A ɓangaren Sumaya da Sufyan soyayyar su kullum ƙara armashi ya ke yi saboda basa ɓoyewa junansu komai sai na ɓangaren da ya shafi sirrin su, Sumaya ko sunan Naila bata son ji a bakin Sufyan wannan dalilin ya sa baya yi mata hirar ta.

A yammacin wata asabar Naila ta shirya zuwa Gidan ƙawayen Ruwaida da ta taɓa kaita, domin ba ta muzantata a wajen kowa ba, dukka ƙawayenta waɗanda su ke kiranta ta yi musu kitso ba su daina ba, Ruwaida ce dai kawai ta ƙauracewa haɗuwa da ita.

Ta na fitowa na haɗu da Yasar, da ta gaishesa daƙyar ya amsa yana gyara zamansa a han ɗan tudun da ya ke zaune.

Naila bata yi nisa da Gidan su ba, ta hango lafiyayyen mota mai farin gilashin da mutum zai iya ganin na ciki, fuskar Salman ta gani kamar dai yadda ta gani a farkon zuwanta Birnin Abyad. Da gudu ta tunkari mota da ya ke tafiya a hankali ta na kuka haɗe da magana da iyakacin ƙarfin muryarta;

"Salman na san kai ne ka tsaya ka