Bushra ba ta ta cewa Naila komai ba sai ɗan danne-dannen da ta yi a waya.
kamar daga sama Naila ta ji Bushra ta ce;
"Idan yau ace Mairam Matar Mahaifin Sulaim kuma ƴar Uwar mahaifiyarki da Mahaifiyarki ta rasa ranta wajen hidimtamata amma tabi umarnin iyayenta ta gudu ta barki duk da tasan zakisha wahala, kika ganta cikin daular da take da damar nemanki ta taimaka miki amma batayi ba yaya zaki ji?"
Kanta Naila ta ɗago dakyau hawayen tuna irin mutuwar azabar da Mahaifiyarta tayi na zubowa ƙuncinta, cikin dakiya da kyakkyawar fata ga kowa ta ce; "wataƙila tana da dalili, ina kyautatamata zato a duk inda take, idan da rai da rabo wata rana Allah zai ƙaddara saduwarmu, amma gareni na yafe mata duniya da Lahira." Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka.
Rungumeta Bushra ta yi cikin ƙosawa ta ce;
"Yaushe zaki daina barin hawayenki suna zuba Naila? dole duk wani matakin nasara na tare da ƙalubale, Karki bari yawan kukanki yazama lagonki a wajen maƙiyanki"
Kai Naila take girgizawa. A haka Bushra tayi ta lallashinta har ta yi shiru. Kafin ta bar Gidan sai da ta bata kuɗi masu yawa tace ta ɓoye zata ƙara dawowa kafin ta wuce Babban Birnin Abyad.
SUFYAN; Kuɗin Naima da yake tarawa kaf ya kwashe sukayi ƙwarya-ƙwaryar walima shida iyayen Sumaya da ƙawayenta, tare da alƙawarin da zarar yaje Babban Birnin Abyad ya samu yadda yake so shirye-shiryen auren su da Sumaya zai kankama.
Sai dare sosai ya dawo Gida.
★washe gari ma da sassafe ya bar gida. Duk Naila ba ta damu ba, ta bar shige da ficen nasa a matsayin shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad.
Ranar da jirginsu zai tashi a bakin Bushra da zo gidan Naila ta ji labari, sai dai bata nunamata batasaniba.
Bushra ta yiwa Naila kyautar kuɗi masu yawan gaske ta kuma yimata alƙawarin zata zana jarabawar share fagen shiga jami'a da taimakon Yasar. Da ta tashi tafiya waya mai kyau da tsada ta bata ta ce ta ɓoye kar ta bari Sufyan ya gani.
Naila bata fahimci tsanarta ya yi nisa a zuciyar Sufyan kuma har abadan bazai taɓa ƙaunarta ba, sai da taga dare ya yi babu Sufyan ko da ta kira Yasar da wayar da Bushra ta bata da lambobin su a ciki, a nan takejin labarin ashe Sufyan tun da yamma jirginsu ya tashi. Ta yi kuka mai raɗaɗi da ciwon da bansan iyakarsa ba bayan sunyi sallama da Yasar, kafin ta haƙura ta kulle kanta a ɗaki.
Tafiyar Bushra da Sufyan ne yasa Yasar dawowa ɓangarensa tare da ƙaramar ƙanwarsu da zamu zasu jarabawa tare sai dai Naila ta girmeta amma ta fi Naila girman jiki.
Naila ta ji daɗin dawowar Yasar da ƙanwarsa, da kai tsaye ɓangarenta ya turota don tayata kwana.
A take Naila ta saki ranta domin fuskantar sabuwar rayuwata.
SUFYAN; kafin tafiyar Babban Birnin Abyad tunda sassafe Naila tana barci ya ɗauki iya ƴan kayan da zai ɗauka ya bar gidan, a Makarantar suka wuni da Sumaya tana kukan zatayi ƙewarsa. Gudun lalacewar komai yasa bai barta ta rakasa airport ba kamar yadda ta buƙata.
Tare da Bushra suka hau jirgi..
Bayan sun isa filin jirgin Babban Birnin Abyad mota daban-daban suka hau da Bushra baima ƙara ganinta ba, kamar ba tare suka taho ba. Ma'aikacin Company ya kira kamar yadda Yasar da ya kira ya yi mai bayani haɗe da turomai Number.
Kamfanin Dhahab bai ƙarasa c
Tsakiyar Babban Birnin Abyad ba kuma anan inda Company ya ke anan staff quarters ɗinsu yake.
Apartment ɗin da yasa Sufyan zubewa ƙasa yana yiwa Allah godiya aka kaishi. Ranar kwana ya yi bawa Sumaya labari haka su Ɗayyib da ya kira. Sam ya manta da Naila.
Kan Sufyan bai ƙara kwancewa ba sai da aka kaishi Office ɗin da ake ce nashi ne.
Duk da Sufyan yana da son banza da kwaɗayin son tara abin duniya sai da ya tsorata ba kaɗan ba. Tayaya ya samu matsayin da ko da dukka karatunsa ya kammala ba zai samu ba? anya Bushra da Yasar da Naila ba haɗa baki sukayi domin a siyar dashi ba tunda yana cinyemata kuɗin kitso? Hannunsa na karkarwa ya lalubo wayarsa😂.
🔥
SASAAL
18
Duk number wanda ya kira ba ya samu hatta number Bushra da bai ƙara gani ba a kashe yake. A take nadamar rashin siyawa Naila waya ya lulluɓesa, da yanzu ita zai kira yayiwa barazana tunda yasan matsoraciyace.
Fatar hannunsa, takalmin ƙafarsa da kayan jikinsa ya kalla, ya ƙara kallon ofishin bai san sanda ya fashe da kuka ba. Sam Chemistry bai haɗu ba dole akwai manufa. Cikin kuka yake ƙara zagaye ofishin har da Bedroom da washroom.
Lokacin da ya gama ƙarewa komai na ofishin kallo sai ya ƙara sakin kuka, hannunsa na tsuma ya ƙara lalubo wayarsa a karo na biyu ya dannawa mahaifinsa kira, saboda daa baiyi niyyar kiransu ba kar ya ɗaga musu hankali.
Duk son duniyar Sufyan a bayan Hindu Mahaifiyarsa yake haka itama duk son duniyarta a bayan Ɗayyib suke, domin shi bashi da tsoro akan duk wani abu daya kafawa ƙahon zuƙa.
Sufyan cikin kuka yake bawa Ɗayyib labari. Maimakon ya ji tashin hankali a muryarsa sai ya ji ya saki ƙaramin dariya.
Da ƙwarin gwiwa ya ce;
"Naila bata da muguwar zuciyar sayar da kurwarka Sufyan"
Kai Sufyan ya girgiza idanuwansa ƙyam akan kujerar alfarmar da yake a matsayin mazauninsa.
"Baaba bazaka fahimta ba, ba su kirani interview ba balle na tantance ƙwarewa ta ce yasa suka bani wannan ofishin, babu wani abu daga neman aiki sai shiga ofishi, tun daga ranar da na sauka ko Bushra banƙara gani ba, Baaba ni dai kawai haƙura zanyi da aikin nan"
Da zafin muryar da zai nutsar da Sufyan kar yaja musu asara Ɗayyib ya ce;
"Ka kwantar da hankali ka, duk na sa Ubangidana ya bincikamin komai, kana tunanin rayuwar kara zube kakeyi a Birnin Abyad? Har soyayyarku da Sumaya na sani, da bushashar da kakeyi da Kuɗin sana'ar Naila, dama abinda muka turaka kayi kenan?
To ka buɗe kunnuwanka dakyau ka saurareni. Ka mayar da hankali kan aikinka domin fansar dukiyar da Mahaifiyarka da ni kaina muka sadaukar akanka ba ka zauna yin shirme ba. Inaso ka tara kuɗi Ubangidana yaƙara bincikamin komai a kan ma'aikatarku domin sanin muhimman abubuwa akan mai kuɗi sai da kuɗi.
Yaya ma sunan ma'aikatar taku ka ce?"
Kafin Sufyan ya ɓude bakinsa da ya yimai nauyi saboda kalaman Mahaifinsa da suka sanyaya mai jiki, an buɗe ƙofar ba tare da naiman izini ba. A gigice ya katse kiran.
Rashin nutsuwar da yake ciki da kuma rashin sanin matsayin da aka bashi yasa bai tuhumi wanda ya shigo maiyasa bai naimi izini ba.
Ɗayyib bai haƙura ba ya cigaba da kira Sufyan a ɗan gajarce ya ɗaga ya ce ya bari idan yaje Gida zasuyi waya.
Cikin ƙwarewa bayan sun Gaisa da wanda ya shigo yake koyawa Sufyan yadda zai gudanar da aikinsa.
Fara'ar fuskar Baturen da yadda yake nunamai yadda zai gudanar da aikinsa ne yasa Sufyan ya ɗan saki jiki.
Ko da Baturen ya fita sai da ya ƙara ƙarewa komai kallo yanajin alfahari da girman kansa na ƙaruwa a hankali. Murmushi ne ya kufcemai bayan ya sauke ajiyar zuciya wawtar dayaso tafkawa na dawomai.
Bayan Sufyan ya isa Gida ko cikakken hutun minti biyu bai yi ba, aka aiko mai da lafiyayyun kayan fita Office. Cikin isa yake gwada kowanne kanshi na ƙara girma.
Da yake Sufyan sha-sha-sha ne ko da ya nutsu maimakon ya kira Mahaifinsa sai ya kira Sumayya suka yi ta waya har barci ya ɗaukesa.
★sai washe gari da safe ya tuna da kiran Mahaifinsa, a gurguje ya kirasa suka gaisa sama-sama.
Irin motar da aka zo ɗaukarsa zuwa office ne yasa ya ji daɗi kamar ya kashe shi, cikin isa ya gyara kwalar rigarsa haɗe da motsa kafaɗunsa kafin ya shige.
Daga wannan rana aikin Sufyan da ya mayar da kai ya miƙa, cikin kwanaki ya ƙara gogewa ya fara ɗaukar hanyar zama Sufyan Dhahab ɗin da yake fata.
A computer yake ganin irin Tukwanen da Company Dhahab suke ƙerawa amma bai taɓa ganinsu ido da ido ba, domin ma'aikar da ake ƙera Tukwanen daban yake da na sarrafa shinkafa da yake aiki. Sai dai labarin Tukunyar da ya ke datsa jefi-jefi a wajen Abokanan aikinsa.
Hankalin Sufyan ya ƙara tsayuwa waje ɗaya bayan samun tabbacin Turawane manyan Company, ƴan asalin ƙasar Abyad tsirrai ne a ciki.
Cikin ɗumbin narasa, kwanciyar hankali, ƙaruwar soyayyarsa da Sumaya, manta Naila gaba ɗayanta, rayuwar Sufyan ya miƙa.
BUSHRA; tun ranar da ta sauka a Babban Birnin Abyad bata samu nutsuwa ba sai da ta tattara ta bar ƙasar gaba ɗaya. Saboda har lokacin bata cire ran samun kira daga Malik ba. Lokacin da taje Dhahab ma a tsaitsaye suka gaisa da Simbi Uzair ya dawo da ita Gida. Daga wannan rana ta ƙauracewa ƙasar Abyad gaba ɗaya, sai saƙon kuɗi da take aikawa Yasar ya bawa Naila.
NAILA; Duk da ta saki jikinta a wasu lokutan tanajin ranta babu daɗi, tanaason magana da Kaaka amma bata da hanyar samunta.
Tana cikin wannan yanayin ta zana jarabawar share fagen shiga jami'a ita da ƙanwar Yasar. Har lokacin babu kira daga Sufyan, kuma bai zoba, ko Yasar ya daina kira a waya.
Kwanaki biyu da gama zana jarabawar su aka kira Yasar Interview a Dhahab Babban Birnin Abyad.
Rai babu daɗi Yasar ya fara shirin tafiya Babban Birnin Abyad. Bazata taɓa manta alkhairin da ya yimata ba, da abubuwa dayawa da bazan taɓa iya mantawa da su ba, ya yi mata alƙawarin zaman ƙanwarsa a tare da ita.
Sai dai da yaje yiwa Iyayensa sallama ƙememe suka nuna ba su amince ƴar su ta zauna a inda babu mafaɗi ba, da yake Naila ta rakasa domin dawowa tare da ƙanwarsa a gabanta suka dinga sakin maganganu marasa daɗi da nuna ita ɗin ba wata abar aji tausayi ba ce. Bata yi kuka ba, ba kuma taga laifinsu ba amma ta ɗan ji haushinsu tunda ko ba komai ai sai su yi tunanin suma tasu ɗiyar zata iya tsintar rayuwarta a cikin kwatankwacin irin wanda ta riski na ta a ciki.
Har suka dawo Gida haƙuri Yasar yake bata, ta na ta nunamai babu komai.
A washe garin ranar da ya rage saura kwana ɗaya Yasar ya tafi Babban Birnin Abyad ya kai Naila ya buɗemata asusun ajiyar kuɗi a Babban bankin Birnin Abyad, tare da siyayyan kayan abinci da kayan maƙulashe kala-kala.
★washe gari da sassafe Yasar ya fito zai tafi. Ta yi kuka irin kukan da ban san iyakarsa ba, sai take ji kamar ita kaɗaice a duniyarta, sai ta ke jin kamar ta bishi taga inane wannan Dhabah ɗin, su waye a ciki, tanaji a jikinta kamar ta san su, kamar tana da alaƙa da su. Cikin kuka ta ce idan ya je ya gaishemata da mutanen cikin Dhahab. Duk yadda Yasar yaso ya jure kasawa ya yi yasa kuka da haka suka rabu da Naila ba tare da sanin ranar da zasu ƙara ganin juna ba.
Naila bata taɓajin kaɗaicin da ta ji ba a kaf rayuwata irin ranar da Yasar ya bar Birnin Abyad. Ko ina yayimata shiru wa su lokutan sai ta ji kamar motsi a bayanta wa su lokutan kuma sai ta ji kamar ana kiran sunana. A wannan dare ta gane girman rahamar zama da mutum a waje ɗaya.
A haka wahalallen barci ya ɗauketa cike da mafarkai ma su ban tsoro.
A haka ta shafe kwana uku cikin kaɗaici duk da tana waya da Yasar jefi-jefi a rana.
Tun tana jin tsoro har ta haƙura ta sanyawa zuciyata dakiya.
Da sannu zuciyarta ta ƙeƙashe ta daina jin tsoron komai. Zata tashi da safe ta yi Breakfast ta ci na ƙoshi idan rana tayi ta tafi Gidan Customers ɗinta wa su kuma su biyota Gida. Idan Dare ya yi ta ɗauki kuɗi a cikin kuɗin sana'arta ta je nasha Ice cream a wajen da Yasar ya nunamata.
A haka rayuwata ta miƙa, jarabawarau ta fito tayi kyau. Da taimakon Abokin Yasar ta samu gurbi a jami'a mai zaman kanta na Birnin Abyad duk Bushra ce ta biya ta hanyar Yasar, shi kuma ya turawa amininsa.
Kuɗin siyayyar kayan abinci da abubuwan amfani Yasar ya turomata. Da ta rasa kalar godiyar da zanyi musu shi da Bushra kuka na sanya.
Duk da Bushra ta ƙauracewa waya da ita, ta ƙauracewa zuwa inda take domin ta jima da dawowa Babban Birnin Abyad amma saboda tana tsoron kar ta cigaba da zuwa wajen Naila asamu matsala, sai ta daina kiranta, ta daina zuwa wajenta ko ta shigo Birnin Abyad gudun kar ta ƙara saka Naila a cikin matsala.
Da taimakon Abokin Yasar Naila ta kammala komai na fara attending lectures
A ranar da ta fara zuwa Makaranta da yamma bayan sallar la'asar ta fita siyayyar abinda zatayi amfani dashi tunda a Hostel zata zauna saboda tazarar Makarantar da Gidansu.
Doguwar Riga mai taushi da faɗi taa sa ta naɗa mayafin da ya yiwa fuskarta da ya rage rama kyan gaske. Waya da card ɗin da zatayi siyayya dashi kawai ta ɗauka.
Wajen siyayya mafi girma a Birnin Abyad ta nufa saboda a can zata samu duk abinda take so.
Tun shigowarta ta hango Sufyan hannunsa sarƙafe da na Macen da bata sani ba (Sumaya).
Ya yi kyau irin kyan da yake buri, ya ƙara haske da ƙiba kamar ba Sufyan ba. Macen ce ta fara hangota kamar ta Santa, sai ta ƙara ƙanƙame hannun Sufyan cikin kishin da ya bayyana a saman fuskarta. Naila ba ta nuna ta gansu ba, ta fara ɗaukar abinda ya kawota.
Duk yadda Matashiyar da ke tare da Sufyan ta so janye hankalin daga ɓangaren da Naila take sai da ya waiwayo.
Da farko bai gane Naila ba sai daga baya. Hannun Sumaya ya saki da sauri ransa na suya, hassadar yadda ta canza har ta samun ƴanci da kuɗin yin siyayya a wajen da ya kawo Budurwarsa na cin zuciyarsa. Naila tana sane da tahowarsa kafin ya ƙaraso ta yi wuf ta nufi wajen biya. A kwai mutane a wajen don haka ya juya ya na ɗaukar komai a hanzarce don suyi su gama, bai damu da yadda Budurwartasa take ƙunci ba.
Lokacin da ya iso da jibgin kayan siyayyarsu lokacin Naila ta nufi ƙofar fita.
Yaso jirkintawa su gama biya amma ganin kamar hakan zai ɗauki lokaci har Naila ta ɓacemasa kawai sai ya miƙawa Sumaya card ya bi bayanta da sauri ba tare da tsayawa kallon ƙuntatacciyar fuskar Sumaya ba.
Ya na fitowa Naila tana shiga Taxi kafin ya shiga Mota tuni mai Taxi ya bar wajen.
Lafiyayyen motar da Company Dhahab suka siyamasa ya shige a hanzarce. Da speed ya bi bayansu kar su tsere mai, ganin sun ɗauki wani hanyar daban ba na gidan daya sani ba sai ya ji hassada na naiman kassarashi zuciyarsa na tiriri.
Naila suna isa gare ɗin Makarantarsu da ɗan hanzari ta sauko daga Taxi dama tun a ciki taa sallamesa.
Gate ɗin Makarantar nufa hankalinta a kwance duk da ta hango motar da na ke kyautata zaton na Sufyan ne.
ID ta nuna ta Securities su ka barta ta wuce.
Tana shiga ta ƙara shiga Motar da zai kai ta har bakin Hostel ɗinsu. Sai a lokacin ta saki ɗan dariyar da ya ƙaramata kyau tana hasaso irin ƙuncin da Sufyan zaiji domin tasan ko shi yafi kowa kuɗi baza'a barshi ya shigo ba, tunda bashi da Numbern wayar kowa kuma bai san kowa ba a Makarantar.
Sufyan sai ta nutsuwarsa ya yi bayan ya yi parking domin kai tsaye suka hanashi shiga kamar yadda ya so.
Ba irin bayanin da bai yi ba, babu kuma irin rantsuwar da baiyi ba shi Mijin Naila ne amma suka nuna su sam basu santa ba duk kwatancen da ya yi musu.
"shin yamasan a gaban wani University yake tsaye kuwa? Securities suka tambayeshi.
Sai a lokacin ya ɗaga kai yana kallon sunan da yake jiki saman Dogon Ginin ɓaro-ɓaro a take ya ji hassada na naiman kasheshi jirin baƙin ciki na naiman kai shi ƙasa. Sum-sum ya dawo wajen Motarsa yana jin muzanta a karon farko tun bayan tafiyarsa Babban Birnin Abyad.
Da ya shiga Mota kasa jurewa ya yi, ya fara dukan kujerun motar ya na surutai "Ni Naila zata yiwa taurin kai, har ta yarda su kawota jami'a irin wannan, wallahi! Wallahi!!! Wallahi!!! Sai nayi sanadiyyar barinta Birnin Abyad wayyo zuciyata zata fashe" ya ƙasara faɗa ya na dukan saitin zuciyarsa....✍🏻
[7/24, 9:20 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥
SASAAL
19
Sufyan ba wannan ne zuwansa Birnin Abyad na farko ba. Tun lokacin da aikinsa ya miƙa komai ya yi mai yadda yake so ya fara kawowa Sumaya ziyara.
Sumaya macece tasan kuma abinda Sufyan yake yiwa Iyalinsa ba daidai ba ne, a addini har ma da al'ada amma son kai da tsanin son zuciyar kutsa kai cikin abinda batasan mafarinsa ba yasa take ganin kamar Sufyan ma son Iyalinsa ya ke yi banda haka ya saketa mana kawai ita ya gabatar da ita a wajen Iyayensa suyi aurensu. Har layin tasha zuwa taga yaya Naila take..
Son zuciyar Sumaya kaɗan ne akan na Mahaifanta, domin su cewa su kayi bazasu ba shi Sumaya ba har sai ya saki Naila.
SUMAYA
Da Sufyan ya dammaƙa mata Card zuciyarta ce kawai bata haɗiya ba, kishi ya toshe komai nata gani take yi duk kuɗin da Sufyan yake ikirarin ba shi da shi Naila yake kashewa ba Iyayensa yake turawa ba kamar yadda ya faɗa. Saboda tun fara aikin Sufyan ranar ne kawai tasan ya yi mata siyayya ma su nauyin kuɗi, duk zuwa idan ya yi ƴan kuɗine yake rabawa Mahaifanta. Amma ga Matarsa nan tayi kyau tasa sutura na alfarma, saboda kishin ma kar wani ya ganta har rufa mata baya ya yi yana muzurai sai ka ce wani sakarai. To kenan yaudararta ya ke yi da ya ce ba ya zuwa wajen Naila?