shi yayi mai faɗan yana so ne ya kashe kanshi? Ko wani abun ake yi mai a Asibitin da yake sashi yawan fargaba?
Hannu likita Sufyan ya kamo yana kuka yana bashi labarin su Malik ne suke basa tsoro. A wannan ranar daƙyar Sufyan ya nutsu ya kwantar da hankalinsa tunda likita ya yi masa alƙawarin su Malik ba zasu ƙara dawowa ba.
Da yammaci ya dannawa Mahaifiyarsa kira, bayan Sumaya ta tafi Gida ta ɗan huta.
Kamar tayi shekaru tana jinya haka Sufyan ya tsinkayi Muryar Mahaifiyarsa. Saitin zuciyarsa da bugunsa yake fita da ƙarfi ya dafe ya ce;
"Menene yake damunki Ummeena? Kwanana biyar bani da lafiya babu wanda ya nemeni a cikinku, ashe idan ba buƙatar kuɗi ba, ba ni da wani amfani a gareku"
Murmushi tayi kafin ta ce;
"Sufyan ɗana na fika shiga halin jinya, domin ciwona ba irin naka bane" gyara zama Sufyan ya yi yana yi mata sannu cikin tausayawa. Kamar daga sama ya ji tace;
"Ina ka jefar da makarin sirihin jikin Naila Sufyan?" Kame-kame ya farayi, sauƙin dole na zuwarmasa lokaci ɗaya.
Murmushi taƙarayi ta ce;
"Sufyan! Malik zai iya riskarka a koda yaushe, amma kafin na baka labari, inaso duk halin da kake ciki karka ɗara kwana biyu baka isa Birnin Abyad wajen Naila ba, duk iya yadda za kayi karka bar Naila ta isa Babban Birnin Abyad ba tare da ta amincewa komen aurenku ba, ko kwanciya ne kayi a ƙasa ka roƙi yafiyarsu, domin Naila itace Makamin tsirarka daga su Malik albarkacin matsayin da take da shi a Dhabah. Karkayi watsi da umarnina kamar yadda kayi watsi da shi ka cigaba da zama da Sumaya, idan ka isa Birnin Abyad duk abinda ka riska ka yi gaggawar kirana domin na baka wasiyyata ta ƙarshe." Tana gama faɗa ta datse kiranta.
Shi dai Sufyan bai san abinda ya samesa bayan katse wayar Mahaifiyarsa ba, sai da ya wayi gari yaga Sumaya tsaye a kansa tana kuka..
Daƙyar Sufyan ya daure ya ƙara kwana ɗaya a Asibiti. A gaggauce ya sanar da Sumaya ta shirya kayanta, a kwai aikin da zaiyi a Birnin Abyad.
NAILA
Suna zaune da Kaka kiran Amira Customarta ya shigo wayarta. Domin Kaka taji komai a sarari ta saka Muryar Amira bayan ta ɗaga.
Bayan sun Gaisa cikin zumuɗi take sanar da Naila kitsonta ya yi matuƙar jan ra'ayinsu kuma sunyi alƙawarin biyanta kuɗi masu nauyin gaske. Amma zatayi kwana biyu acan tana yi musu, sannan tayi mata bayanin tace musu tana da Kaka, sun ce zasu turo tikiti da komai mu taho tare.
Kallon Kaka Naila tayi tana jiran umarninta.
A hankali ta ɗaga kai alamar ta amince!!!!.....😄
Shin Sufyan zai riski Naila.???
🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Page 27
Bayan sun yi sallama Naila ta katse wayar, rungume kaka ta yi, ta sumbaci ƙuncinta tana dariya. Kai Kaka ta girgiza jikinta a sanyaye.
Kamar Naila bata lura da sanyi da jikin Kaka ya yi ba ta ɗauko waya ina kiran layin Yasar.
Da tsananin farin ciki Naila ta basa labari.
"Alhamdulillah!" ya furta da daukakkiyar sauti kafin yafara tsokanarta da "Finally yokel sister ta zata leƙa Babban Birnin Abyad, har na hango idanuwanki wallahi" Kaka da ke sauraronsu dariya tasa haɗe da sakin ajjiyar zuciya.
Da tsokana Naila suka ƙare waya da Yasar.
Da yammaci Kaka Mallam ta kira, ta yi tsammanin zai soki zuwansu Babban Birnin Abyad amma sai taji ya furta "Alhamdulillah" ƙwarin gwiwa da addu'o'in tsari kala-kala ya ƙara bata domin acewarsa; abinda zaiyi sanadin zuwan Naila Babban Birnin Abyad ya daɗe ya na jira kuma gashi Allah ya kawo.
Kafatanin kuɗin da Naila take tarawa A banki ta turawa account ɗin mutanen Yankin Tudu.
Kafin dare ya yi kiraye-kirayen su sai shigowa yake yi, abun dariyar duk da wayan mutum biyu ake wayan, talauci ya hana da yawansu mallakar wayoyin hannu.
Kaka bakinta kamar zai yage, banda "Ameen Ya Allah! Ameen thumma Ameen!" Babu abinda take maimatawa. Ba su daina kira suna Godiya da addu'o'i ba har sai da chajin wayar ya ƙare.
A jiyar zuciya Kaka ta sauke, lokaci zuwa lokaci sai ta saki murmushin farin ciki. Kusa da ita Naila ta matso taa zauna ta ce ;
"ya ya zakiji idan akace mutanen Yankin mu, sun samu farin cikin da ya fi wannan?"
"Zan ji daɗi Naila sama da wanda na ji a yanzu" Kaka ta faɗa da murmushi kwance a saman fuskarta.
"To ki saki ranki mu shiga Babban Birnin Abyad, In Shaa Allah ba zamu dawo ba sai da nasarar da zai kawowa Yankinmu gagarumin sauyi." Murmushi suka sakarwa juna.
Da yake Yasar ya zo hutun ƙarshen Mako Gida, ziyarar bazata shi da ƴan gidansu suka kai Gidansu Naila don tayata murna.
Kaka baki ta saki da ta ji abinda ya kawosu kafin da kwashe da dariya ta na cewa "wai ni kuyimin bayani wani irin arziƙi Naila zata samo a wannan Babban Birnin Abyad ɗin da kowa yake farin ciki, kar fa muje a siyar da mu" Dariya Yasar da Iyayensa suka kwashe da shi, ƙannensa da suka saba wasa da dariya su na tsokanarta.
Cikin raha Yasar yake bawa Kaka labarin da zarar ta shiga Babban Birnin Abyad zatasan ko wanda ya yi wanke-wanken rana ɗaya dole ya fito da kuɗi mai tsoka.
Ana raha da wasa mukayi Dinner da su Yasar.
Sai dare sosai suka tafi Gida.
★washe gari su Naila suka fara kimtsa kayan da zasuyi tafiya da shi, amma har lokacin abinda yake bawa Naila mamaki shine tayaya za'ace zuwansu na kwana biyu ne zai warware ƙullin shekaru aru-arun da ko Kakanta ba haifa ba lokacin, ko dai ta Kaka kashesu za'ayi.
★washe gari daya kamar ranar tafiyarsu, tsaf Naila ta shirya cikin baƙin Abaya haka Kaka irin Abaya ɗaya suka sanya na Company ɗaya.
Har Gida ƙanin Yasar ya zo ya ɗaukesu saboda tare zasu wuce da Yasar don haka sai sun fara biyawa Gidansu tukunna
A dai-dai lokacin da Motarsu Naila ta gifta ta hangi Sufyan A cikin Motar da take kyautata zaton Taxi ne. Mamakin abinda ya kawoshi ta yi cikin daƙiƙu kafin na tattara lamarinsa na watsar tana danna wayarta.
SUFYAN.
Ƙwallane ya tararwa manyan idanuwansa da suka ƙara zama farare ƙal lokacin da mai gadi ya tabbatar masa da su Naila sun fita yanzunan ita da Kakarta. Yasan kuma ba Makaranta ta je ba, domin can ya fara biyawa akace sunyi hutu, a hankali ya nemi waje ya zauna ya zaro wayarsa. Bugu ɗaya Hindu ta ɗauka.
Ko sallamarsa Hindu bata amsa ba ta ce;
"Ka riski Naila?"
Jiki a sanyaye ya ce; " a'a"
Kuka ta saki na tsayin mintuna shida kafin ta ɗora da;
"Son zuciya shine mafarin halakata, bayan tafiyarka muka gano ka yardar da maganin makarin asirin jikin Naila a gidansu kamar yadda Malamin Yankinmu ya sanar mana, maimakon Jalal da Mahaifinka su ga laifinka, sai suka juye laifin akaina, acewarsu duk nina tsiro musu da wannan musibar, sun tisani a gaba da asiri kala-kala kullum cikin ciwo nake, na je wajen Mahaifiyata Ɗayyib ya zugeta ta koroni.
Sufyan mafita ɗaya ya ragemaka, ka koma bakin aikinta ka riƙi aikinka da gaskiya da amana, amma a kowani yanayi ka ji tsoron Allah kuma kaji tsoron Malik, domin baya ganinka ba kuma ya tare dakai amma ka sani yana saurararka a duk inda kake a Babban Birnin Abyad kamar yadda malamin duba ya sanarmin, a yanzu amfaninka a wajen Ɗayyib shine ka bincikomai su wanene DHAHAB? banda wannan baka da wani amfani a gareshi, su kuma su Malik suna tare da kai ne domin ganin iya gudun ruwan Jalal, kamar taku ɗaya haka kake da mutuwarka Sufyan a tsakanin Ɗayyib da su Malik, amma abinda na faɗawa Ɗayyib ya hukuntani shine wanɗanda suka ƙirƙiri sabon Dhahab ba abokanan yaƙar su ba ne, saboda suna da damar shafe Yankin Tudu da mutanen cikinta, domin ko kai kanka da kake cikin Daularsu har yanzu mai asalin Dhahab ɗin bai san dakai ba, wataƙila da ya sani da tuni ka jima da ruɓe a cikin ƙarƙashin ƙasa. Ina gayamaka dukka wannan ne domin kayi takatsantsan kamar yadda malamin duba ya sanar da ni, ina nadama Sufyan, ka yafemin. Ba lallai mu sake magana makamanciyar wannan da kai ba, ba kuma lallai ka dawo ka riskeni a raye ba, amma Allah Ne shaida bani da masaniyar komai a kan kisan su Abduh da ahalinsa." Ɗif wayar Hindu ya katse kamar dai waccen ranar.
Wayar Sufyan ya bi da kallo yana zare idanuwansa da suka koma jajaye cikin ƙarajin da ya tashi dukka jijiyoyin wuyarsa da goshinsa ya na furta "Ummee! Ummee!! Ummee!!!" A lokaci ɗaya yana ƙara kiran layinta da baya shiga kwata-kwata. Hankali a tashe Mai gadin gidansu Naila ya kiran layin agajin ƙasar. Kafin su iso Sufyan ya zube ƙasa idanuwansa a juye.
NAILA.
Wannan hanyar da take bi da kallo tsayin shekaru yau gashi zata tunkareshi da ƙarfin ikon Allah.
In Shaa Allah anan Free pages ɗin ZINARE ya tsaya. Ga waɗanda suka bibiya ba su da halin biya na gode da comments da addu'o'in ku, ga waɗanda suke da wadatar biya suma ina godiya mai tarin yawa Allah Ya bar zumunci.
Kuɗin motar zuwa Babban Birnin Abyad Naira 500 ne kacal, ta wannan account ɗin
Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182 tare da tura shaidar biya ta 09132403788,08138665117. Ga masu bibiya kuma ta Arewabooks sai su ɗora. In Shaa Allah zamu cigaba da Posting ranar Monday, 4, August, 2025 da misalin ƙarfe 8:00pm
Na gode🙏🏻
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
ZINARE.
2
BY
NAFISAT ALIYU SASAAL
CHAPTER 1;
*DOGON TARIHIN AHALI MAI ƊAUKAR HANKALI DA ƘARFIN ARZIƘI TARE DA DARAJA TA MUSAMMAN A BABBAN BIRNIN ABYAD*🔥🔥🔥
Page 1
SUFYAN
Hour biyu ya yi a kan Gadon Asibiti kafin ya farka.
Gefensa Iyayen Sumaya ne da ƴan uwanta . A can gefe kuma Sumaya ce a zaune itama idanuwanta sun kaɗa sunyi jajir alamun tasha kuka.
Guri ɗaya ya ƙurawa ido farkon zuwan Bushra da Yasar makarantarsu na dawomai;
"Bushra tayimin alƙawarin komawa Makaranta bayan na fara aiki a Babban Birnin Abyad, maiyasa ban ƙara ganinta ba?"
Wani sashe na zuciyarsa ya tambayi wani sashe.
Ƙasa-ƙasa Sufyan ya ce;
"Ni na wargatsa komai da kaina, ni na cuci kaina da kaina, son zuciyata ya sa na zaɓi Sumaya na wulaƙanta Naila. Kwaɗayin duniya da shagala yasa na manta batun komawata Makaranta na baje a Gida mai na'urar sanyaya ɗaki da Ofishi, yanzu gashi duk komai ya hargitse a cikin kwanaki ƙalilan, tayaya Malik yake iya saurarata bayan baya ganina, sannan kuma bai kasheni ba mai yake nufi da ni? Maiyasa ya yankewa Baffan Mahaifina Bashar harshe? Mai Mahaifina Ɗayyib yake nema da zuri'ar amininsa Abduh Dhahab dayake kukan rashinsa kullum? Menene suka jima suna ƙullawa tun zamanin kakannin-kakanni na? A kwai abubuwa dayawa da ya kamata ace na sani, amma son kyau irin nawa ya jagoranci mayar dani mai ƙaramin ƙwaƙwalwa da ƙaranci tunani. Kurakuraina a bayyane suke, amma ta yaya zan gyara su? Na ɗauki darasi mai girma, domin duk Namijin da yaba kyawunsa zai zama lagonsa to tabbas wata rana zai faɗa a komar danasani, saboda da shi Sumaya ta rijayeni har muka fara soyayya ba don tafi Naila kyan siffa ko na haliba sai don zuzuta kyawuna da take yawan yi.
Gane lagona na son a cemin ina da kyau yasa bamayin hirar minti goma bata nanata baiwar kyan da Allah yayimin ba, tare da zuzutani, irin zuzutawar da tasan zai ɗimautarni, Ni kuma gareni hakan shine so, domin ni bandamu da na yabeta ba amma ita bata gajiyawa kamar karatun bita. Har a wasu lokutan ta kan cemin babu Namijin daya kaini kyau, maimakon na fahimci kalamanta a matsayin yabo, a matsayina na masoyinta sai na ɗauka dagaske Ni ɗin Namijine dana fi duk Mazan Abyad kyau, samun irina sai an tona"
babu wanda ya ji abinda Sufyan yake faɗa sai bakinsa da suka ga yanata motsi.
Sumaya da ta kasa jurewa ƙananun maganganun da yake yi da iya motsa laɓɓansa ta ce;
"Sufyan ka nutsu ka sawa zuciyarka salama, In Shaa Allah komai zai yi sauƙi banason wannan ƙananun surutan da kakeyi Kaji"
Kamar an mintsinesa ya miƙe.
"lafiya Sufyan?" Ta tambaya itama tana miƙewa
"Zan wuce bakin aikina, kwana ɗaya na tambaya" ya faɗa yana ƙoƙarin tattara Rigarsa.
Baijira ƙorafin da sukeyi ba, ya ɗora rigar saman shirt ɗinshi da aka ciremai ya kwashi wayoyinsa da Card ɗinsa ya bar ɗakin.
Da sauri Sumaya ta rufamai baya tana kiran sunansa.
NAILA;
A zahirin gaskiya ta so ace tafiyar Mota zasuyi domin ta kalli gagaruwan da suka fi kusa da Babban Birnin Abyad, amma haka ma bata ɓaci idan suna dawowa sai su biyo Mota.
Kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a Babban Birnin Abyad haka take jinta, Yasar sai dariya yakemata yana tsokanata da "ƴar ƙauye zata je Birni"
Ita da Kaka duk sai da sukaji tsoron hawa jirgi duk da ita Naima wannan ne karonta na biyu. Da sannu jirginsu ya ɗaga daga Birnin Abyad zuwa Babban Birnin Abyad.
Bayan sun sauka
A kwai banbanci mai girma tsakanin airport ɗin Birnin Abyad da na Babban Birnin Abyad.
Ɗan waiwayowa Yasar ya yi ya ce; "ki kirata idan babu nisa, sai nasa Drivern da zai zo ɗaukata ya fara saukeku kafin mu wuce"
"Okay Sir!" Naila ta ce tana saramai, dariya suka saki dukkansu har da Kaka.
Bugu ɗaya Amira ta ɗaga, jindaɗin Naila ta ce mata gata ta iso bayyana a cikin muryarta suka gaisa. Cikin zumuɗi Amira ta ce, zasu turo Driver idan kuma zata yya tarar Taxi to ta ce masa ya kawota DHAHAB.
Cire komai da Naila ta yi a ranta tun kafin tahowarsu dangane da Sulaim ne yasa batdamu da sunan da Amira ta ambata ba amma duk da haka sai da zuciyarta tayi bugun ɗakiƙu.
Bayanin Yasar zaisa Drivern da zai zo ɗaukarsa zai sa ya ɗaukesu tayiwa Amira basai sun turo Driver ko sun hau Taxi ba. Godiya Amira tayi tare da cewa ta kirata idan dun iso.
"ta ce Dhahab za'a kai mu" Naila ta faɗa bayan ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon Yasar
Murmushin fuskar Yasar ne ya ɗauke lokaci ɗaya.
"Dhahab? Dhahab fa kikace Naila? Ki ƙara kiranta ki ji ko jine bakiyi da kyau ba, domin bare baya shiga Dhahab kai tsaye"
Musu da haƙiƙancewa ba halinta bane don haka ba tare da tace komai ba ta ƙara dannawa Amira kira, a sarari ta saka wayar saboda Yasar yaji da kunnen sa.
Tabbacin can za'a kaisu da Amira ta bayar yasa Yasar shafa gefe da gefen fuskarsa haɗe da furzar da huci ya ce;
"Kin ce biki zasu yi ko?"
Da sauri Naila ta ce "eh"
Wayar Abokin aikinsa ya kira ya tambaya.
Ya shadamai bai san da wani biki ba, amma bari ya bincika sashen hadimai yaji. Domin yaji kamar ƙiƙishin-ƙishin ɗin amincewar Sir Malik akan wani biki da za'ayi a Ɓangaren.
Naila da Kaka dukkamsu shiru sukayi kowa da abinda yake saƙawa a ransa.
Burina ta isa Dhahab ta ga menene a ciki.
Kaka kuma mamaki takeyi saboda sunan da yayi mata kamanceceniya da na ahalin su Marigayi Abduh da kuma yadda Yasar sam bai nuna farin cikin inda zasu je ba kamar yadda ya nuna kafin tasowarsu.
Ko minti biyar ba'a rufaba aka ƙara kiran Yasar. Tabbacin shagalin Bikin ƴar ɗaya daga cikin masu dafa abincin ɓangaren Hadiman Dhahab aka bawa Yasar, kuma da izinin Sir Malik akeyin komai.
Tsaki Yasar ya saki, bawai baya son Naila taje bane tsoro yake ji kar wani abun ya samesu.
Bayani ya yi musu a can yake aiki shima, amma bai san da biki ba Gidan, ashe ɓangaren masu dafa abincin Hadiman Gidanne suke aurar da Ƴa.
Jakar daya so faɗuwa ta ƙanƙame.
Irin kuɗin da Amira ta ke kashewa a Makaranta da irin motocin da take hawa na faɗomata.
Bayan gama wannan tunanin a zuciyarta Naila ta ce;
"Hadimai kuma? Yanzu saboda kitson ƴaƴan Hadimai masu girki, girkin ma bana mutan Gidan ba a'a na Hadimai ƴan uwansu shine zasu gayyotoni tun daga Birnin Abyad har su biyamin kuɗin jirgi ni da Kakata? to ko dai suna nufin da kuɗin da zasu bayani muka hau jirgi? Wallahi bazai saɓu ba"
maganar Yasar ne ya katsemata zancen zucin da take yi.
"Da nasan Dhahab zakije da ban amincewa zuwanki Babban Birnin Abyad ba, wallahi tsoro nake ji, amma Allah Ya sa ku shiga lafiya ku fito lafiya"
Da sauri Naila ta amshe da;
"Ameen, Nima da sani banzo ba, tayaya zanzo yiwa ƴaƴan Hadimai masu yin girki Hadimai kitso tun daga Birnin Abyad, nawa suka ci nawa suka bayani, ni dai kam sun cuceni wallahi"
"In dai Hadiman Dhahab ne zasu iya biyanki kuɗi sama da hasashenki Naila"
Yasar ya faɗa ya na shigewa lafiyayyen Motar da ya zo ɗaukarsu. Lokaci zuwa lokaci sai ya ja tsaki har muka fita daga Airport gaba ɗaya.
TSAKIYAR BABBAN BIRNIN ABYAD
Naila ba ta yadda zata fasalta kyan Babban Birnin a zahiri ba, amma yana da kyau irin kyan da bata taɓa gani ba ko a talabijin, Gine-ginensu da komai nasu na alfarma ne. Mutanensu masu kyan gani ne sama da na Birnin Abyad, babu hayaniya da karamniyar abubuwan hawa duk masu tsada ne da kyan gani a ido, dai-dai da Motocin sufurinsu abin kallone.
Baki, hanci da ido Naila ta saki ta kallon komai tare da haddacewa don ta bayar da labari wata rana.
DHAHAB
A zuciyar Naila ta ce;
"Zan iya kiran Dhahab haɗaɗɗiyar Daula ko na ce wata duniya da wani Attajiri ya ƙirƙira a Babban Birnin Abyad"
A Gajaren Gate ɗin dayake bawa na wajen damar ganin rukunin Gidajen da aka yiwa gini na alfarma Motarsu ta dakata.
Jami'ai masu murɗaɗɗen fuska da jiki ne suke gaɗin ɗan gate ɗin da mutum zai iya haurawa a guje.
Wayarta Naila ta zaro ta kira Amira domin ta sanar da ita isowarsu.
Kafin Yasar ya sauka daga motar kanshi ya juyo bayan Naila ta gama waya, daga kujerar gaban da yake zaune zuwa saitin inda take.
A hankali yadda Kaka bazata ji sa da kyau ba ya ce;