x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 29 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 84001 words
  • 87000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 752

07 Oct 2025
ɗakinta ta wuce har da kullo ƙofar ɗakin da mukulli gudun kar wani ya shigo ya ga kuɗin data samu, Surprise take son yi musu.

Kafin ta shiga wanka sai da ta ɗan yaga takardar da aka lulluɓe kuɗin da shi taga Dagaske dai kuɗaɗe ba ɗan kaɗan ba.

Dariya ta saki har da tsalle tana juyi. A ɗan hanzarce ta wuce Washroom tana juyi har da juya idanuwanta.

Bayan ta fito daga washroom, kimtsawa tayi cikin kayan shan iska, da murmushi ta juyo don ɗaukar kuɗin ta fita da su ta nunawa Ummee da Barirah su ga irin Babban kamun da tayi, tana waiwayo inda ta ajjiye kuɗin sai ta ga wayam babu kuɗin babu dalilin sa..

kuyimin afuwa da guntun paji uzurine ya riƙeni, Na gode🙏🏻
[9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

16


SIMBI;

Dukka idanuwanta ta zaro tana dafe saitin zuciyarta da yake tsananin bugu.

"Wanene ya shigomin ɗaki?" Ta tamabayi kanta tana kallon inda ta ajjiye mukullin ɗakin. Yananan yadda ta ajjiyeshi.

Cikin sanɗa ta nufi ƙofar, ta murɗa a hankali, tana murɗawa ta ji shi a kulle alamar ba'a buɗe ba. Da sanɗa taƙarasa kusa da mukullin ƙofar tayi wuf ta ɗauke, hannuwanta na rawa ta zura ɗan mukullin, tana buɗewa ta fito a guje ta nufi hanyar ɗakin Ummeensu tana ƙwala Ihu kiran sunanta.

A ɓangaren Ummu Malik daƙyar ta iya samun waje ta zauna, tunda Sulaim ya kirata da kansa ya sanar da ita naɗar duk wani motsin Simbi ko kalamanta, yana zargin ansamu matsala, kuma karta kirata ta bari har sai ta dawo.

Abunka da zuciyar Uwa sai ta kasa sukuni, tana tunanin mai Simbi ta aikata da har zaisa Sulaim ya kirata a karon farko a rayuwarsu, tasan koma menene baƙaramin abu bane.

Da ta ga tunanin zai yi mata yawa sai ta ɗoro alola ta tayar da Sallar nafila tun da lokacin ƙarfe 9:40 ne na safiya.
Ba ta jima da idarwa ta ji ihu, kamar na Simbi.

"Yaushe Simbi ta dawo gidannan bansaniba?" Ta tambayi kanta asarari tana miƙewa, bayan ta saita wayarta ta ajjiye a gefe.

A bakin ƙofa suka ci karo da Simbi tana zare idanuwa.

"Simbi! Lafiyarki kuwa? Wannan ihun naki ai sai ya firgita mutum" Ummu Malik taƙarasa faɗa tana kamota zuwa jikinta.

Da rawar murya Simbi ta ce;
"Ummee kuɗi saurayina ya bani, daga ajjiyesa akan gado na shiga washroom, ina fitowa naga babu kuɗin kuma wallahi na kulle ɗakin da hannuna"

Da alamar tambaya Ummu Malik ta ce;
"Saurayi kuma? Yaushe kikayi Saurayin da yake baki kuɗi bansani ba Simbi? Kina son ki fusata Yayanku ko?"

Kai Simbi ta girgiza. Babu wani nutsuwa a tattare da ita take bawa Ummeenta labarin yadda suka haɗu da Ɗayyib.

Da mamaki da tsoro Ummu Malik ta ce;

"Ai Companyn masarrafin Shinkafar D&J da ke Birnin Abyad na Mahaifin Bushra ne, anya ba Ɗan damfara ko Aljani kika haɗu da shi ba Simbi????

Sai a lokacin ta gano ina Sulaim ya dosa, ashe baƙaramin matsalane yake ƙoƙarin kunna musu kai ba.

Hannunta da yake rawa tasa ta janyo wayarta, duk bayanin da Simbi take koromata sam ba ta fahimta har sai da tabbatar saƙon Muryar Simbi data naɗa ya isa ga Sulaim....



SUFYAN;

A ɓangaren Sufyan tun bayan samun saƙon Malik ya ke cikin farin ciki, ƙuncin da yake fama da shi kwana da kwanaki sai ya kau, hankalinsa ya mayar kan kammala ayyukan da suka ragemai bai ƙarasa ba.

Ba su taɓa haɗuwa da Kabeer sun yi gaisuwar dake nuna sanayya ko abota a tsakaninsu shekarun baya ba. A matsayin Ubangidansa kullum yake gaishe da Kabeer.

Bayan sati ɗaya, yana zaune a office kiran Kabeer ya shigo ta wayan ofishinsa. Bayan ya ɗaga Kabeer ya shaidamai yana nemansa idan ya gama abinda yake yi.

Sufyan ji yayi gabaki ɗaya aikin da yake yi a lokacin ya fitarmai daga rai, burinsa kawai ya ji, wani babban daliline zai sa Kabeer ya nemesa a irin wannan lokacin.

Bayason Kabeer ya yi zargin wani abun ko nuna zumuɗinsa kan kiran da ya yi mai, wannan dalilin yasa ya danni zuciyarsa yaƙara Minti Talatin kafin ya miƙe.

A gaggawace ya nufi ofishin Kabeer da ya jima da sani, amma bai taɓa samun damar shiga ba.

A ɓangaren Kabeer
Babu kowa a ofishinsa sai shi ɗaya yana danna wayarsa. Naiman izinin shigowar Sufyan ne yasa shi ajjiye wayar a gefe yana ba shi izinin shigowa.

Kamar yadda suka saba gaisawa haka suka gaisa bayan Sufyan ya zauna a kujerar da ke fuskantar na Kabeer.

Gyaran murya Kabeer ya yi sannan ya ce;

"Jiya na haɗu da Mahaifinka Ɗayyib amma shi bai ganni ba, ina tunanin zai iya riskarka a kowani yanayi, kuma ina gudun abinda zai biyo baya, mai zai hana ka dawo wajenmu da zama, kafin saƙon ganinsa dana tura ya isa ga Sir Malik".

Tun lokacin da Kabeer ya ce ya haɗu da Mahaifinsa, Sufyan ya sunkuyar da kansa ƙasa

Cikin kuka Sufyan da yake ganin kamar gashi ga ajalinsa ya ce;

"Idan har ya samu ƙwarin gwiwar isowa Babban Birnin Abyad menene ya ragemin Kabeer, Gara na tsaya ya kasheni duk guje-gujena wata rana zai riskeni ya kasheni, Kabeer tsoro nake ji"

Tasowa Kabeer ya yi ya matso kusa da shi yana lallashinsa...

NAILA;

A ɓangaren Naila har ta gama mitarta ta shige Ɗakinta Kaka bata tanka mata ba.

Kasa jurewa tayi bayan ta shiga ɗaki, ta ƙara neman layin Sulaim amma ba'a ɗaga ba. Jifa ta yi da wayar tana hura siririn hancinta.

A ganinta zaƙewar Sulaim ya yi yawa, tayaya zaisata ta guji Simbi alhali shi yana tare da Yayanta dare da rana ta waya? So yake yi ita tayi baƙin jini kenan?.. ta tambayi kanta.

Babu kalar tambayar da Naila bata yiwa kanta ba kafin ɓarawon barci ya sace ta.

Ba ta farka ba, sai gab da Magriba shima Kaka ce ta tasheta.

Bata jima da yin wanka ba aka kira Sallar magriba a masallacin Dhahab. Dama tayi alolarta bayan ta yi wanka.

A ɗakinta tayi sallah saɓanin daa da takeyi a ɗakin Kaka.

Bayan ta idar gajeran saƙo ta turawa Sulaim tana tsimayin kiransa.

Tana zaune har aka kira Sallar ishsha'i amma Sulaim bai kira ba, zuciyarta babu daɗi ta miƙe ta tayar da Sallah.

A ɓangaren Kaka. Ta yi mamakin rashin fitowar Naila , amma da ta tuna ƙorafin Sulaim da ta wuni tanayi tun bayan dawowarta daga Makaranta ta gane dalilin maƙalewarta ta a ɗaki.

Dama sararin yin waya Kaka take nema, don haka ta kulle ɗakinta ta kira mutanen Yankin Tudu, don jin labarin abubuwan da suke wakana.

SULAIM;
A ɓangaren Sulaim tun lokacin da aka sanar da shi, Naila ta kafe dole sai sun tafi Makaranta tare da Simbi ya ce abi bayansu.

Sulaim ya samu labarin Saukar Simbi daga Motarsu Naila da murmushi akan fuskarta, sannan bayan ɗan daƙiƙu wata Mota ta tsaya a gefenta. Amma har wanda ya bi bayansu ya share mintuna kusan goma daga inda yake zaune cikin mutanen da suke hada-hadarsu bai ga kowa ya fito daga cikin Motar ba, sai Simbi da ya hango tana magana ita kaɗai bayan tagama amsa waya. Bayan ɗan wani lokaci, ya ga motar ta bar wajen ba tare da kowa ya fito daga ciki ba, bayan tafiyar Motar, Motar gida ya iso ya ɗaukarta...

Bayan Sulaim ya gama saurarar bayanin wanda ya tura,
Bayanin Drivern da take kai Naila Makaranta ya shiga ya duba.

"Simbi ta sauka ne dalilin manta takardun Makarantarta a gida kamar yadda ta ce" yana gama karantawa ya rintse idonunsa. Bai yi ƙasa a gwiwa ba a wannan tsakankanin ya kira Ummu Malik..

Duk kiran da Naila take yi bai san ma tanayi ba saboda kansa da ya ɗau zafi.

Ba shi da niyyar ramuwar gayya a cikin zuciyarsa, amma yana ganin idan bai motsa ba, babu abinda zai hana burin Jamil na shekaru aru-aru cika akansa, tunda yanzu shi kaɗaine ya rage sunyi nasarar kashe ragowar.

Abokanan Kasuwancinsa ya fara kira, su naimo mai Babban Islamic scholar kafin dare ya rufa.

Sallah ce kawai take tashinsa daga inda yake, tsabar kallon System idanuwansa har jaa sukayi.

Bayan Magriba da saƙon Malik ya riskesa na batun Sarkin Tsafin Yankin Tudu sai ya ƙara tabbatar da mai siffar Ɗayyib aka turo, domin yayi amfani da Simbi wajen rusa Dhahab tunda zuciyarta cike take da ƙyashi da hassada.

A wannan dare Sulaim ya shirya tafiya ƙasar Abyad.

Sai da ya yazo kwanciya sannan ya tuna kwata-kwata bai kira Naila ba tun wayar Asuba da sukayi.

Yana ɗauko wayarsa da suke waya da shi ya samu miss calls ɗinta rututu.
Ɗan murmushi ya yi, a zuciyarsa yana faɗin "Allah Ne kaɗai yasa kukan da zatayi da irin zagin da zansha a wajen Kaka"
Bayan ya danna kiranta ya jingine wayar yana jiran ɗagawarta..

NAILA;
A ɓangaren Naila kukan takaici tasaka, baa ta alaƙanta ƙin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi da komai ba, sai don ya nuna mata ita ɗin ba komai ba ce, amma har wani irin laifi zatayi mai da zata kirasa kusan sau talatin yaƙi ɗagawa?

Da lallashin Kaka ta ci abincin dare tana ci tana ƙorafin rashin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi, har ta gama mitarta kamar kullum Kaka bata tofa mata ba.

Naila ta yi tunanin lamarin zai zo mata da sauƙi bayan ta koma ɗaki ta manta komai ta kwanta tayi barcinta hankali kwance, amma sai ta ga lamarin ya gagareta.

Tana cikin jan tsaki kiransa ya shigo mata...
[9/5, 9:01 PM] Maman Amatullahi: Nafisat Aliyu Sasaal


Page 17


NAILA;
Hannunta yana rawa ta janyo wayarta, zaman hular kanta ta gyara saboda video call ne. Sai da ta ɓata fuska sannan ta ɗaga..

fuskar Sulaim ce ta bayyana yana kwance. Murya ciki-ciki Naila ta ce;

"Barka da dare"

Sulaim bai amsa mata ba ya ce;
"Kin jini shiru ko, aiki ne ya riƙeni ina fatan kina lafiya"

Sai da Naila ta marairaice fuskarta sannan ta ce;
"Nasan babu wani aikin da ya yi maka yawa kawai kaƙi ɗaga kirana ne, saboda munje Makaranta tare Simbi, ban san maiyasa kake son shafamin baƙin jini ba, bayan kai kullum kana tare da Yayanta"

A ɓangaren Sulaim lumshe idanuwansa ya yi yana saurararta
Har ta ɗisa aya bai ce mata komai ba.


Naila jin Sulaim ya yi shiru kamar ma baya kallonta sai ta fashe da kuka tana mitar ita fa ba wai aminta tayi da Simbi ba, kawai mutunci suke yi, a matsayinsu na ƴan Yanki ɗaya.

Sulaim dai bai ce mata komai ba, har sai da ta haƙura tayi shiru dan kanta sannan ya ce;

"Me kikeso Nailaa bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin?"

Da sauri Naila ta share hawayenta ta ce; "ka barni muyi zumunci Ni da Simbi"

Sulaim idonsa da sukayi ɗanyi jaa ya buɗe saɓanin daa da suke lumshe ya na kallon fuskarta, sun kai wajen minti ɗaya haka yana kallonta tana kallonsa sannan a hankali ya furta;
"Na barki Naila shikenan?"

Kai Naila ta ɗaga, alamar eh tana murmushi, "kamar sunana na ji ya kira" ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.

Maganarsa ce ta cire mata kwakwanton da take yi a cikin zuciyarta;
"Na gaji Naila da safe zan kira ki, anan Kahala yanzu dare ya raba"

Da rawar murya Naila ta ce.
"Maiyasa yau ka kiran sunana baka ce Sa'aadati ba, ko har yanzu fushi kake yi da ni"

Sai da Sulaim ya ɗanyi murmushi sannan ya ce;
"Na tambayeki me kike so bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin, kika ce na barki da Simbi. kuma na ce na barki, karki ƙarawa kanki damuwa, Allah Ya tashemu lafiya"

Da wani irin zare idanuwa kamar zasu faɗo ƙasa Naila take tambayarsa "ka barni? ka barni fa ka ce? to ai ban fahimci ka barni ba, kayimin bayani"

Babu bayanin komai Sulaim ya datse kiransa.

A ɗimauce Naila tafara kira layukan wayarsa amma yaƙi ɗagawa.

Batasan sau adadi nawa ba ta kira layukan wayarsa a wannan dare ba amma sam bai ɗaga ba.
Da dai ta fuskanci Dagaske bazai ɗaga kiranta ba Kuka ta rushe da shi tana dafe kanta.

A ɓangaren Kaka ƙarfin kukan Naila ne ya tasheta daga barcin da bata jima da farasa ba.
A ɗimauce ta nufo ɗakin, babu irin bugun da batayi ba amma Naila taƙi buɗewa.

Kaka masifa da mitar maza ta kashe kanta ta fara yi tana cigaba da bugun ƙofar. Amma Naila tayi biris da ita.

Har dare ya raba Kaka bata koma ɗakinta ba tana tsaye jikin ƙofar Naila tana lallashinta ta ɓude tunda tayi masifa da zage-zage bata buɗe mata ba.

Gajiya Kaka tayi da tsayuwa da zama ta koma Ɗakinta, haushin kafiyar Naila na damun zuciyarta

★har washe gari da Safe Naila ƙin buɗe ƙofarta tayi, duk naci da magiyar da Kaka tayi mata bata buɗe ba, wannan dalilin yasa ta nufi Sashensu Simbi.

SIMBI
A ɓangaren Simbi daƙyar Umminsu ta kwantar mata da hankalin ta nutsu, amma gargaɗeta da ta kiyaye, kuma duk inda taga mutumin ta riƙe addu'a a bakinta karta ƙara kulashi ko da yayi mata magana.

Har dare ya yi Simbi bata wani saki jikinta ba. Rashin sukuni da yadda ta dawo shiru-shiru ne yasa Barirah bayan ta dawo daga wajen aiki ta ce tazo ta rakata su je Siyayya.

Ba don hankalin Ummu Malik ya kwantaba ta barsu suka fita.

A motar Barirah suka bar Gidan. Wajan Siyayyar kayan shafe-shafe suka shiga, Barirah tana gaba Simbi tana binta a baya.

Kamar ance Simbi ta waiwaya gefen hagunta ta hango Dee cikin shigar wasu kayan daban ba irin wanda ta gansa da shi da safe ba.

Ya yi matuƙar yimata kyau a ido, tuni addu'ar da Mahaifiyarta ta ce tayi idan ta gansa ya bar kanta, burinta hankalinsa yayo kanta ta bashi labarin kuɗinfa da ya bata aljanun gidansu da batasan da su ba sun ɗauke. Tana so kuma ta tambayesa maiyasa bai kirataba, ta manta tsarin data saka wayarta na idan bata da lambar mutum ko ya kira ba zai zo ba.

Maimakon Simbi tabi bayan Barirah sai tasha kwanar inda ta hango Dee.
Tana kuwa matsawa tayi sa'a Dee ya hangota.

A ɓangaren Dee da murmushi ya nufo Simbi da wani salon tafiya da zai ƙara siye zuciyarta.

Da Muryarsa mai daɗin daya siye zuciyarta ya ce;
"Barka da dare Gimbiyata Simbi"

Ido Simbi ta lumshe, tana ƙanƙame wayar hannunta saboda daɗi.

Murmushi Dee ya yi, kafin ya ƙara ce wa; "idan babu damuwa zamu iya tattaunawa daga waje" ya ƙarasa faɗa yana giftata ya nufi hanyar fita.

Kafaɗunta Simbi ta ɗage dukka biyu tana juya idanuwanta kafin tabi bayansa.

Tsayuwarsa Dee ya gyara lokacin da Simbi ta ƙaraso gefensa. Sai da yayi gyaran murya Sannan ya ce;
"Wai wanene ya kafa Unguwarku, kyansa ya birgeni."
Shiru Simbi tayi kamar bata wajen.
Dee kansa ya ɗan dafe ya ce;

" Ohh kiyi haƙuri naga kamar tamabayar bata yi miki daɗi ba, kyan Unguwar ne yasa na tambaya, amma kamar yanzu fuskarki tafi annuri Gimbiyata, da safe da muka haɗu kamar akwai abinda yake damunki ko kuma akwai wacce take son yi miki shishigi a cikin rayuwarki, kinsan ni ina da ƙwaƙwalwar saurin nazartar mutane, ko zan iya sanin wacece wannan, na taimakamiki da shawara ko wani abun?"

Simbi, Dee ya sosa mata inda yake yimata ƙaiƙaiya, duk da tana ganin kamar bai dace su tattauna irin wannan matsalar daga haɗuwarsu ba, sai dai a cikin zuciyarta ji takeyi kamar ana ingizata.

Zata yi magana kenan suka hango Barirah ta fito tana rarraba ido alamun ita take nema.

Dasauri Dee ya kamo hannun Simbi ya dunƙulamata wani ɗan kulli, sannan a gurguje ya ce

"Ko wacece ki sa mata a abinci zata koma inda ta fito ta bar muku Gidanku, amma baki faɗamin sunan wanda ya kafa Unguwarku ba"

Da harshenta da ya yi mata nauyi ta buɗe baki zata bashi amsa Barirah data hangota ta ƙwala kiran Sunanta.

Da saurin da ya bawa Simbi mamaki Dee ya shige tsakankanin Motocin dake wajen.

Ƙullin da ya damƙa mata ta riƙe da kyau.

Kafin Barirah ta ƙaraso tuni ta saita nutsuwar haɗe da zura ƙullin da Dee ya bata a ciki jaka.

A ɓangaren Ummu Malik, bayan fitarsu Simbi, baifi da mintuna goma ba, Malik ya kirata kar a bari kowa ya fita, ya kira Securities su datse Dhahab ba shiga ba fita.

Da fargaba take sanar da shi ai su Simbi da Barirah ba su jima da Fita ba, ihun salatin daya tashi hankalinta Malik ya saki, kafin ya ce takirasu kuma idan sun dawo babu shiga babu fita.

Ko da su Simbi suka dawo Simbi bata gayawa Mahaifiyarta ta haɗu da Dee ba.

Ummu Malik Kashedin da Malik ya ce ayi musu ta sanar musu jikinta a sanyaye.

Bayan Barirah da shiga ɗakinta bakinta ta turo aganinta kawai izzar Malik ɗin ne ya motsa banda haka, maiyasa zai ce ba shiga ba fita Sai kace ana wani tashin hankali, ko don kawai an ɗaukewa Simbi kuɗi shine zasu takurawa Mutane.

Ita ma Simbi ɗakinta shige ta kullo kanta ba tare da ta naimi jin ba'asin hukuncin Malik ba.

Ƙullin da Dee ya bata ta fito da shi tana kallo, zuciyarta na kitsa mata kawai ta sawa Naila ta tattara ta koma Yankin Tudu, Sulaim ya auri Barirah ko ya samo wata can daban, sai dai tayaya zata sa bayan Mahaifiyarta ta sanar da su ba fita ba shiga? Ɗakyar ɓarawon barci ya saceta.

★washe gari suna cikin yin kari Kaka ta shigo, tunda batasan sharaɗin da Malik ya zana ba, kuma Securities basu hanata zuwa ba.

Da magiya Kaka take yiwa Ummu Malik bayanin tanason Simbi ta biyota su lallaɓa Naila ta buɗe ƙofarta tun jiya ta kulle kanta taƙi fitowa.

A zuciyar Simbi Allah-Allah takeyi Mahaifiyarta ta amince.

Barirah kuwa tashi tayi tabar wajen tana taɓe baki.

Sai da Ummu Malik ta ɗan nisa sannan tace Simbi ta ɗauko Mayafinta su je, amma karta daɗe ta dawo da wuri.

Jikin Simbi har ɗan rawa yakeyi tabi bayan Kaka bayan ta soƙe ƙullin maganinta a ƙugu.

NAILA;
Kwana tayi kiran Sulaim, amma bai ɗaga ba, bayan Sallar Asubahi da ta ƙara kira sai ta ji wayar a kashe.

Tabbacin Kaka bazata tankawa matsalarta ba ne yasa tayi biris da ita taƙi buɗe mata ƙofa.

Bayan sallar Asuba da Kaka ta dawo tana ƙwanƙwasawa barci mai nauyi ya fara ɗaukarta .

Ko da ta farka ta fito bata ji motsin Kaka ba, bata damu ba.
Kitchen ta wuce ta haɗa ɗan shayin da zata iyasha.

Tana cikin shan shayin Kaka da Simbi suka shigo.

Sama-sama Naila ta amsa gaisuwarsu, tana cigaba da shan shayin dayake ƙona mata baki.

Ƙin tashi Simbi tayi ta koma Sashensu.
Guri ta naima kusa da Naila t