x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 744

07 Oct 2025
godiya akan shawarar da ya ba ta. Wa su addu'o'in yaƙara bata, domin yasan duk daran daɗewa su Jalal za su samu labari warkewar Naila, duk da ba lallai Sufyan ya ba su labarin yardar da maganin da ya yi ba.

SUFYAN; bayan ya fito daga gidan Kaka daidaita tafiyarsa ya yi kamar komai bai faru ba. Bayan ya kai gida ɓangarensa ya wuce ya yi wanka ya yi Breakfast dukka ransa ba daɗi da abinda Kaka tayi mai lokaci zuwa lokaci sai ya saki tsaki, a haka ya koma barci Bayan ya yi wayar sirri da Sumaya.

WAIWAYE
Sufyan lokacin da ya bar Yankin Tudu da Sumaya abisa umarnin Mahaifansa na idan sunje Birnin Abyad ya saketa, su na isa Birnin Abyad maimakon ya cika umarninu kai tsaye masauki ya wuce da Sumaya ƴan uwanta kuma suka wuce Gida.

Bayan sun nutsu sunci abinci sunyi wanka da Maganganu ma su daɗi yake ta lallashinta tare da nunamata duk wasu abubuwa da suke faruwa akwai dalili ba wai laifin Mahaifansa ba ne har da ce mata;

"Mahaifina mutumin ƙwarai ne mai sauƙin kai, amma rashin fahimta da butulcin mutanen Yankina yasa suke ganinsa kamar azzalumin da ya hana Yankinsu cigaba. Mahaifiyata Macece mafaɗaciya amma da zarar kun saba ta sauko daga fushin sakin Naila da na yi zata fara sonki, fushinta na wani lokaci ne, kuma Ni bazan taɓa son Naila ba, saboda mutumin da na fi tsana a rayuwarta take so har yanzu, da hotonsa take yawo, kuma akansa ta zaɓi bijiremin. Saboda haka nake roƙonki Sumaya ki kwantar da hankalinki ki bani haɗin kai"

A kaf maganganunsa ba bu wanda Sumaya ta fahimta tunda ya ambaci ba ya son Naila ne saboda tana yawo da hoton maƙiyinsa. Cikin kasa danne kishin Naila da ya yunƙuromata ta ce;
"Kenan da ba don tanason wanda ka tsana ba, ka na sonta kenan? Dama can itace bata sonka kakeyimin ƙarya? Sufyan banajin aurenmu zai kai labari saboda kowa naka ba ya sona, hatta Mahaifinka ƙiri-ƙiri na hango tsanata a cikin idanunsa. Tun kafin komai na mu yayi nisa kawai ka sauwaƙemin."

Sufyan murmushi ya saki yana kallonta, tayaya zai sha dukka wannan Yankar daga mahaifinsa kuma ya ɓata shekaru yana kashe mata kuɗinsa da na Naila ta ce haka kawai zata suɓucemai shi ba zai moreta ba? Su kansu Mahaifansa da zai bayyana musu bautar da ya yi mata da basu ba shi umarnin sakinta ba. Sai da ya numfasa sannan ya fara yaudararta da yaudararrun kalamansa da rabi da kwantansa duk ƙaryane, saboda yasan har abada Iyayensa ba za su taɓa sonta ba, amma shi kam bazai yi gangancin sakinta da wuri ba, sai ya samu wacce ta kwanmai ko Naila ta dawo hannunsa kamar yadda suka tsara.

Da dare ya yi,
Sumaya da yake gwanace wajen son duniya tana ganin Sufyan ya fita ya dawo da lodin Siyayya ta fara sakin ranta, sannan ya kuma cewa ta biyosa Babban Birnin Abyad idan taji batason zama da shi yayimata alƙawarin sakinta, babu ja ta amince.

★washe gari suka je har Gidan Iyayenta ta yi musu bankwana.

Muguntar Sufyan yasa ya biya tsohon Gidan su ko zai samu mukullin sashen Naila kafin su tafi, ga mamakinsa hanasa shiga Gidan akayi gaba ɗaya, haka ya dawo suka ɗauki hanyar Babban Birnin Abyad ransa a ƙuntace.

Kyan matsugunin Sufyan na Babban Birnin Abyad ba ƙaramin tafiya da imanin Sumaya ya yi ba, a take ta manta irin ƙiyayya da wahalar da ta sha a Yankin Tudu. Tana jin ko Iyayen Sufyan ba su isa su rabasu ba.

Bayan kwana biyu da zuwansu Babban Birnin Abyad.
A zahirin gaskiya yanayin yadda yake yiwa Naila gadara da abinda yaga dama wajen sauke buƙatarsa sam ba iri ɗaya bane da na Sumaya, ƙiri-ƙiri take nuna ita batason wannan ita bazata iya wannan ba.

Wannan dalilin yasa ya ƙara karɓar shawarar Iyayensa hannu bibbiyu, Naila tamkar baiwa take sai yadda ya ga dama zai yi da ita, ta ƙiyi kuma jikinta ya gayamata tunda bata da gatan kowa dalilin dawowarsa Yankin Tudu kenan.

DAWOWAR LABARI
★washe gari Ɗayyib ya tura wakilansa kan komen Naila ta hanyar Yayyan Mahaifinta da suka yaudara da kuɗi a baya.

Da ƙarfin gwiwarsu dukkansu suka haɗa bakin ba su yarda Naila ta komawa auren Sufyan ba har sai ta samu sauƙi, kuma ko ta samu sauƙi sai sun ji ta bakinta idan ta amince. Idan kuma har da gaske Sufyan magani zai nema mata kamar yadda suka faɗa to yafara naima mata kafin ta koma Gidansa.

Martanin Yayyan Mahaifin Naila akan komenta gidan Sufyan mummunar labari ne a wajen Ɗayyib, Jalal, Hindu da Sufyan kanshi.
A wannan dare dukkasu sukayi tafiyar Sirri zuwa Yankinsu Hindu, suka bawa Malamin duban Hindu kuɗi maiyawa ya ƙara tura mugayen aljanun da zasu addabi Naila ta ji kamar zata mutu har sai ahalinta sun sallama sun amince da komenta.

SARTAJ WANDA YA CIYAR DA NAILA GUBA
Fitar su Ɗayyib da rashin dawowarsu da wuri ne, yasa Sartaj gajiya da zaman jiransu kan gulmar da ya kawo musu; na ga Naila can an shirya kaita Birnin Abyad gobe da sassafe neman magani.

Da ya ga dai bazai samu ganin su ba, haƙura ya yi ya nufo gida..

Ya na ɗanyi nesa da Masarautar Sarki Hammam, MALIK da ya sauko daga mota ya bayyana a gabansa gaba ɗayansa....
Bayyanar fuskar Malik ga duk wani ɗan Yankin Tudu, babban abun fargaba ne. Saboda ba ya zuwa ya tafi bai bar shaida ba.

Sartaj mummunar gani ya yiwa Malik saboda bai sakaya fuskarsa da hutu ya yi kamu mai kyau ba, a zallarsa ya fitomai.

Fararen idanuwansa masu tsananin haske da girma Malik ya zubawa ƙafafuwan Sartaj da suketa rawa kamar an jona mu su shocking.

Da zafin takunsa ya ke tunkaro Sartaj da gumi ke tsiyayowa tun daga cikin gashin kaa, har cikin suɗaɗɗen takalminsa.

Da sauri Sartaj ya yunƙura zai gudu, fitsari da bayan gida na zuwarmai lokaci ɗaya.

Munfashi Malik ya sauke kafin ya taka sawun da ya basa damar cafkar Sartaj.
Guri ɗaya ya tsayar da fuskar Sartaj yana kallonsa shima ya na kallonsa. A hankali Malik ya ɗage girarsa ɗaya ya ce;

"kasanni?"

"Ni dai ina neman afuwa, wallahi na daina" Sartaj ya faɗa daƙyar muryarsa na karkarwa.

"Na ce kasanni?" Malik ya ƙara tambayarsa kamar bai ji abinda ya ce ba.

"Na sanka! Au wallahi bansan ka ba" Sartaj ya faɗa a ruɗe.

"Tabbas ba ka sanni ba, domin da ka sanni da bakayi abinda ka yi ba" Malik yaƙarasa faɗa yana kai hannunsa bayan wandonsa.

"Au na tuna, na sanka wallahi! kuskure ne daga yau na daina, na daina kai gulmar kowa kuma ba zan ƙara cutar da kowa ba, Dan Allah ka yafemin wallahi sharrin shaiɗan ne."

Yana ƙoƙarin ƙarayin magana Malik ya kwantar da shi ƙasa ya na cewa;

"Bayyanata a Yankin Tudu na mutane ne ma su kafiya irinka, ba na zuwarwa laifi ɗaya sai sun taru. Idan na barka gobe sharrin shaiɗan zai sa ka ƙara kai musu wani rahoton, ba tare ka tuna da kashedina ba amma idan na bar maka shaida Fa??"

Azabar ficewar ƙafar Sartaj ɗaya ne yasa ya shi sakin ihun da ya karaɗe Yankin.

Kafin fitowar Fadawan Sarki Hammam babu Malik ya shige Mota ya bar wajen, sai Sartaj da ke kwance cikin jini da ƙafarsa ɗaya da aka yanke rungume a hannunsa, kamar yadda Malik ya maƙalamai a tsakanin Hannuwansa.
Ihu su ma suka kurma.

Tuni mutane suka fara firfito daga Gidajensu.

Duk da Sartaj ya ba wa Mutanen Yankin Tudu tausayi hakan bai hanasu murmusa a ɓoye ba, acewar su sakayyar abinda ya yiwa Naila ne.




NAILA; A wannan dare tasha azaba irin wanda bantaɓa ji ba, Kaka tana kanta, da ƙarfin gwiwa tare yaƙinin samun sauƙi daga wajen Ubangiji take tofamata addu'o'i wasu ta tofa a ruwa ta shafa mata. Bayan wani lokaci barci ya ɗauke Naila.

Hannunta Kaka ta ɗaga sama tana ce wa;

"Ya Ubangiji! da wanda ya ke zuwa ya biya kuɗi a sanyawa Naila ciwo, da wanda yake turo ciwon, da shi kanshi jinnun da yake assasa ciwon duk Kaine Ubangijinsu Ya Allah! Ya Allah kayimin maganinsu da gaggawa Don ƙarfin Mulkinka, Ka sauƙaƙamin tafiya da ita Ya Allah."

Itama Kaka a kusa da Naila barci ya ɗauketa

★ washe gari da asuba Driver ya iso ƙofar Gidansu Naila, kafatanin mutanen Yankin da suka san da tafiyar duk sun hallara a ƙofar Gidansu, duk suna kuka da addu'o'i kala-kala ɗauke a bakunansu.

Ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungume Naila, suna sumbatar ƙuncinta, Naila ta zaune a Mota tayi laƙwas Hannuna a cikin na Kaka, Yayyan Mahaifin Naila suna kuka suma suka rungumeta, Naila dai bata iya kuka sai kai da take ɗaga musu.

Suna yunƙurin tafiya Kakannin Naila na wajen uwa suka iso da mutanensu, kalaman su ga Naila na ƙarfin gwiwa ne, tare da tarin yaƙini a kanta.

Da haka Motar Naila ta fara tafiya kaka tana kuka Naila itama sai a lokacin hawaye ya zubomata tana ɗagamusu kai, Mutanen Yankin Tudu suna kuka su na kuka suka rabu.

Misalin ƙarfe Takwas na safiya suka isa Iyakar Yankin Tudu da wajen hawa motar Ƙasar Abyad.

Driver shi ya taimaka musu har motar su ta tashi, shima da yaga Motarsu ta fara tafiya hawayensa ya sharce yana ɗago mu su hannu...🥹[7/30, 8:44 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥



N. A. S




Page 24

SARTAJ
★washe gari yana farfaɗowa daga dogon sumar azabar da ya yi da ihun kiran Malik yafara yana roƙo da magiya.

A surutan Sartaj da aka sanarwa su Ɗayyib da su kayi dawowar cikin dare suka fuskanci Malik yana bibiyarsu, irin bibiyar da basu san ta hanyar da zasu toshesa ba. Kuma sun kasa gano wane yake kai masa rahoto.

Mutanen Yankin da suka ji ai aikin Malik ne ya yankewa Sartaj ƙafa, tsoron gulmar kowa da cin amanar junansu ne ya ƙara shigarsu. Tunda ga shi an yankewa Sartaj ƙafar da yake zaryar kaiwa su Ɗayyib gulma dashi.

"Amma mai yasa Malik bai taimaki Naila ba, ko bai san halin da take ciki ba ne??????" Tambayoyin da suke ta yiwa junansu kenan.

Duk nacin da akayi Sartaj ya buɗe baki ya faɗi ina yaga Malik har ya yanke mai ƙafa, ƙin yin magana ya yi.

Washe gari da su Ɗayyib suka zo dubasa ihu ya kurma yana rufe fuskarsa, alamun bayason ganinsu. Har suka bar ɗakin bai buɗe fuskarsa ba.

Har Sartaj ya warke ba ya iya yin gulmar kowa, balle ya ambaci sunan Malik, gani yake yi kamar idan ya ambaci sunansa zai bayyana a gabansa.

Ranar da su Ɗayyib suka yanke shawarar neman mafita akan Sartaj a Fadar Sarki Hammam gudun tonuwar asirinsu washe gari aka nemesa aka rasa shi da tsohuwar Mahaifiyarsa.

Ɓatan Sartaj da mahaifiyarsa ya yi matuƙar tayar da hankali Mutanen Daular Sarki Hammam, sama da yadda labarin tafiyar Naila da Kakarta Birnin Abyad ya tashi hankalin su, domin sun san ko su Naila sunje dole su dawo, saboda maganin matsalarta ya na wajensu. Saɓanin talakawan Yankin da suke ganin Sartaj ya gudune saboda abun kunyar da ya aikata.

A karon farko aka fara saka jami'ai a duk wani hanyar da zai kai mutum cikin Yankin Tudu domin kawo ƙarshen Malik, shima Sufyan cikin gaggawa ya shirya komawa, saboda ɓacewar maganin da yasan dole idan ya cigaba da zama za'a tambayesa ya na ina? da kuma gudun kar ɓarna Malik ta ratsa da shi, domin zuwa lokacin ya fuskanci a kwai wasu manyan sirrikan da bai san da su ba...

NAILA
Allah Ya amshi addu'ar Kaka. A tafiyar kwanakin da suka yi, ciwon Naila ya na yawan tashi, amma da zarar ya tashi Kaka za ta rungumeta ta yi ta tofamata addu'o'i har sai jikinta ya yi yaushi barci mai nauyi ya ɗauketa

BIRNIN ABYAD

Da taimakon Allah suka isa Birnin Abyad. Kaka ta zuba ƙauyanci wasu lokutan garin Kallon Mutane har tuntuɓe takeyi.

Da ɗan ƙarfin da Naila take ji, take yi mata raɗar motar da zasu hau a kunne. Da hannu kaka take kwatanta mu su komai tunda batajin turanci, kuma batajin asalin yaren ƙasar. Kamar ko da yaushe idanun Naila maƙale a hanyar Babban Birnin Abyad, ƙewar Bushra da Yasar na bijiromin, suka wuce hanyar.

Gidansu Naila ba ƙaramin burge Kaka ya yi ba.
Ba ta hutu ba bayan sunyi salla ta fara gyara ko ina na sashen.
Da taimakon Kaka bayan ta gama gyare-gyarenta Naila tayi wanka. A ranar Kaka ta farayimata amfani da maganin su Sufyan kamar yadda Mallam ya koya mata. Bayan wannan ta haɗa har addu'o'in da ya bata.

Da guzurin kayan abincin da suka taho da shi daga Yankin Tudu suka fara amfani, kafin Naila ji sauƙi su canza ƙudi su siyo wasu.

A cikin kwana uku sauƙi ya fara samuwa, Naila tana iyayin komai da kanta, har tayi Sallah a tsaye a kan ƙafafuwanta.

Kwana biyu bayan nan Naila ta shirya ita da Kaka suka tafi Gidan Iyayen Yasar domin jin halin da yake ciki.

Yasar ya na kwance babu lafiya tsohon watanni biyar kamar yadda Mahaifiyarsa ta faɗa musu bayan sun gama gaisawa, ta ce Accident ya yi a kan hanyarsa ta dawowa daga Babban Birnin Abyad. Ya na barci lokacin da su Naila suka isa, bai farka ba har sai da suka fara haramar tafiya.

Da mamaki yake kallonsu kamar bai ganesu ba, har sai da Naila ta gaisheshi ta faɗamai sunana sannan ya fahimci ita ce. Da zafin naman ɗan ƙarfin da yake ji ya gyara zamansa ya na faɗin

"Naila! Maiyasameki kika koma haka? Ciwo kakayi? Maiyasa baki dawo Makaranta ba? Na so zuwa har Yankin Tudu cigiyarki Saboda na kira wayarki bana samu wannan tsautayin ya afkamin ki gafarceni."

Kai Naila ta sunkuyar ƙasa tana Kuka.
Kaka ce ta basu labarin jinyar da Naila ta yi. Dukkansu sun tausayawa Naila har Iyayen Yasar da a baya suke gudunta. Sun ɗan jima a Gidan kafin su dawo Gida.

★washe gari sai ga siyayyar kayan abinci da kayan motsa baki kala-kala har da kayan sawar Kaka, da wayar amsa kira duk daga Gidansu Yasar. Su Naila sunyi farin ciki matuƙa tare da godiya mai tarin yawa.

A hankali a hankali jikin Naila ya fara murjewa saboda canjin cima, muhallahi da kuma lafiyar da take ƙara samu. Itama Kaka tsaf ta yi kyau, su na waya da mutanen Yankin Tudu lokaci zuwa lokaci da number da suka rubuto mata a jikin takarda.

Bayan Naila ta samu sauƙi, Yasar da kansa ya jagoranceta har Makarantasu duk da baya iya tafiya sosai saboda karayar ƙafarsa da bai gama warkewa ba.

Naila bata samu matsalaba albarcin Yasar da kuma shaidun da suka gani da ido, saboda har lokacin akwai banbanci da yadda nake a baya kafin ta bar Birnin Abyad.

Da farin ciki Naila ta dawo Gida, itama Kaka daɗi ne ya kamata, tayi ta yiwa Yasar godiya tana samai albarka.

A cikin watanni biyun da Makarantarsu Naila suka ƙaramata a matsayin hutu, jikinta ya yi kyau kamar bata taɓa jinya ba. Da kanta ta kai Kaka sukayi siyayya kafin su wuce Gidansu Yasar.

Irin motocin da muka gani a harabar gidanne yasa Naila ta cewa Kaka su juya, domin jikinta ya na bata wakilai ne daga wajen aikinsa na Babban Birnin Abyad. Sam Kaka ta nuna bata san zanceba ba, a cewar ta; "mu ina ruwanmu da su? mu da ba wajensu muka zo ba."

A living room ɗin farko idanuwan Naila suka sauka a kan mutumin da ta ke gani tamkar Malik, duk da ya sanya tabaran rage hasken ranar da ya sakaye idanuwansa, ga kuma tarin ƙasumbar da ya bari a fuskarsa. Sai mace ɗaya da take zaune a kujera daban itama Naila ta kasa gane ina ta santa ina ta taɓa ganinta kuma da wa take yi mata kama.

Kamar yadda Naila take Kallonsu bayan ta gaishesu haka Macen da ba wani shekaru bane da ita ta ƙuramata ido.
Kaka tunda ta gaishesu ta nufi cikin Gidan wajen ƙannen Yasar da suke wasa da dariya.

Namijin ne ya fara miƙewa gaba ɗayansa yana miƙawa Yasar hannu. Miƙewarsa ya sa ya fito sak a Malik ɗin da Naila take zargi, kallon da ta yi masa shekarun baya a gidan Abduh Dhahab yana shara da safiya ya ƙara dawowa idanunta. Zumbur ta miƙe tana kallonsa kamar zata cinyesa, kafin ta ambaci sunansa mahaifiyar Yasar da take ganin girmansu a matsayin su na Manyan Iyayen Gidan ɗanta ta ja hannun Naila ta zaunar da ni a gefenta, a tunaninta ciwon jinnun da Kaka tace ta yi ne ya ƙara dawowa. Da harshen ƙasar Abyad take ba su haƙurin Naila ba ta da lafiya ne.

Macen ce ta amsa mata amma Namijin fita ya yi. Itama Macen miƙewa tayi Zinaren da ta yi ado da shi na walwali a kunnenta da wuyarta.

Har mota Mahaifiyar Yasar da Yasar suka yi musu rakiya, har lokacin Naila tama zaune kamar an dasata.

Bayan sun dawo Yasar yake tambayar Naila n
Ta san su ne? Naila yasan ko tayi masa bayani ba lallai ya yarda da ita ba don haka ta ce mai "a'a." Har suka bar gidan bata saki jikinta ba, duk Yasar yana ankare da ni.

Rashin walwala da yadda Makka take haɗe rai bayan sun koma Gida yasa Kaka ta ce ta zo ta rakata su siyo abu, Yasar ya bata kuɗi.

Waccen wajen Siyayyar da ta taɓa haɗuwa da Sufyan ta ce suje. Ƙananun kayan CK da Yasar yake yawan siyomata ta sanya sai malulluɓi mai girman da ta nannaɗe har rabin fuskata da shi gudun haɗuwa da Sufyan, ko Sumaya.

Bayan isarsu
Su na cikin siyayya idanuwanta suka faɗa kansa da jami'ai biyu a bayansa, wannan dai mutumin da na gani a Gidan su Yasar da rana ne.

Ya na fita ta rufamai baya da hanzari ba tare da ta saurari Kaka da ke tambayar "Naila ina zaki je?"

Yana ƙoƙarin zura gangar jikinsa a Mota Naila ta ƙaraso ɗan nesa da Motar da Gudu, cikin ɗan ɗaga murya ta ce "Malik, dan Allah idan kaine ka tsaya na roƙeƙa"...✍🏻

Duk mai son Ɗaukar Malik haya a Yankinsu tayimin DM saboda irin su Sartaj😂😂 I came in peace ☹️
[7/31, 10:04