Layi-layi Kaaka ta bi tana kuka tana cewa;
"Ya ku ƴan uwana mutanen Yankin Tudu ku fito ga jikata Naila ta dawo daga Ƙasar Abyad, ku fito ku ganta Mutanen Yankin Tudu"
Kafin ka ce me, dangin Mahaifin Naila, da mutanen gari daga kowani ɓangare sun cika Gidan. Kowannensu idan ya yi dariya sai dai kaga haƙoransa ya cika masa fuska saboda rama. Maza da mata haka suka cika Gidan Kaka.
Da Naila ya kalli fuskokinsu da yadda suke dariyar da yake nuna irin farin cikin da suke ji sai ta fashe da Kuka.
Suma da yawansu sai suka saka kuka suna zayyanomata labarin irin talaucin da suke ciki.
Tsabar da ta taho da shi a take ya ƙare wa su ma basu samu ba. Bayan kowa ya watse Mahaifiyar Kabeer da ta kasa tafiya ta matso kusa da Kaka, da ƙaramin murya take roƙon ita bata samu ba su taimaka mata, da Naila ta kalleta ta tuna da ɗanta Kabeer ɗaya fita Zakka a ƴaƴansu saboda zafin naima sai ta fashe da kuka, da sauri ta miƙe shiga Ɗakin Kaaka na ɗauko kuɗi ta bata.
A wannan dare kwanan labari Naila sukayi da Kaka cikin kuka mai taɓa zuciya.
Da ƙarfin gwiwar Kaaka dana Yasar Naila ta yanke shawarar ƙin zuwa Gidan su Sufyan idan ya ji haushi ya bata takardarta ta.
★washe gari labarin dawowar Naila da shirye-shiryen shagalin bikin Sufyan da ƙin zuwan Naila gaishe da Mutanen Masarautar Yankin Tudu ya bazu ko ina, har kunnen Hindu mahaifiyar Sufyan da Kakansa Jalal.
Ƙura ba taƙara tashi ba, sai da Naila ta ɗebi dubban mutane Yankin suka shiga Kasuwar Maƙotan Yankinsu abisa shawarar Kaaka suka siyo ɗayyan abinci a farashi mai rahusa. Aka fara rabawa Talakawan Yankin.
A wannan rana sai da hankalin duk wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu ya tashi, domin ɗabi'ar da Naila ta tsiro da shi ɗabi'un Zuri'ar Marigayi Sarki Musa ne. Labari bai tsaya a iya Yakin Tudu ba har kunnen Sarki Hammam, Sufyan da Ɗayyib da suke can Birnin Abyad suna shirye-shiryen tahowa.
Sufyan kishine ya kamashi, shi kuma Ɗayyib da yake komai nasa a lissafe yake tafiya, a take ya alaƙanta kalan taimakon da Naila ta da mamallakin Companyn Dhahab da ɗansa yake aiki, kenan dole akwai ɓoyayyen dalilin da yasa aka ɗauki Sufyan aiki kai tsaye, saboda ko maƙaho a Yankin Tudu yasan irin taimakon da akace Naila ta yi yasan irin na jinin Marigayi Sarki Musa ne. Domin su ne suke taimako da gumin su, su kuma kawowa mutanen Yankin su cigaba da ƙwaƙwalwar su.
Lokacin da labari ya riskesu su na Airport, don haka suka matsu su iso ayi shagalin biki agama su kawo ƙarshen komai.
A can Yankin Tudu wajensu Naila
Ba bu tsangwama babu nuna waccen nawa ne, wannan ba nawa bane, Naila ta bada umarnin su kasafta abincin a tsakaninsu.
kuka da addu'o'in Tsofaffi, Maza da mata, Matasa, da Yara ne yake ta tashi tare da kabbarorin su ta ko ina.
Maimakon sanya idon da bindiddigin auren Sufyan sai Mutanen Yankin suka mayar da hankali wajen yiwa Naila addu'o'i da fatan nasara mai ɗorewa.
A wannan rana Naila ta wuni cikin jindaɗi da soyayya daga ɓangaren Mahaifi harma da ɓangaren Mahaifiyarta da suka samu labari.
Kaf kuɗin da Naila ta ɗauki shekaru tana bautar yin kitso da wanda Bushra da Yasar suke bata ta tattara ta bayar aka siyi kayan Abinci, sai abinda ba'a rasa ba daya ragemata ta bari a jikinta, tana addu'ar Allah Ya kawo ninkinsu.
Barci mai cike da nutsuwa suka yi ita da Kakaa.
Ranar da su Ɗayyib suka sauka wanda ya yi dai-dai da ranar cin kasuwar Zinare Naila da Mutanen Yankin sukayi shawara sukayi shawarar rushe Gidan Game ɗin Ɗayyib, da suma ƙiris suke jira har da matasan da suka ƙara ganin mutuncinta saboda abincin da rabawa Iyayensu, tsanar Ɗayyib ya yi kane kane a zuciyarsu.
Bayan gama cin Kasuwa kowa ya addana abinda ya samu suka taru suka rushe ƙaton wajen da Ɗayyib ya kewaye da langlanga.
Sannan Mazansu da Matansu sukayi tattaki har ƙofar Gidan Sarki Hammam da saukarsu kenan sukayi ƙorafin basason Gidan Game da Gidan Rawa lalata masu Yanki yake yi!.
Kayan Game ɗin cikin wajen da suka rusa babu wanda ya taɓa ko ɗaya, Matasa majiya ƙarfi ne suka Tattaro suka zuɓe a ƙofar Masarautar Sarki Hammam.
Da yake bikin Sufyan suke burin suyi hankali kwance sai Sarki Hammam ya fito ya basu haƙuri.
Ɗayyib mutuwa ne kawai baiyi ba. Jalal Mahaifinsa da muƙarabansa a ranar suka shirya taro a kan Naila saboda sun samu labarin ita ta kitsa komai, tare da bawa Sufyan umarnin sakinta da gaggawa, da shawarar kama Naila da Kakarta suka fara yankewa sai dai hakan zai tunzura mutanen Yankin da dama can a gajiye suke ayi tashin hankalin da ba sa so, shine suka yanke shawarar Sufyan ya saki Naila.
Hukuncin su Jalal gagarumin rigima ya tayar domin Hindu a take ta nuna Sumaya ba ta yimata ba idan kuma Sufyan ya sakeni sai ta tsinemai.
Sumaya dake lulluɓe cikin mayafi bata fuskanci duk abinda yake faruwa ba, ita da ƴan uwanta sai zare ido sukeyi.
Jalal ne ya daki ƙasa kai tsaye ya ce ƙaryar Hindu ya na so kafin rufuwar mintuna Talatin takarkar Sakin Naila ya isa ga ahalinta.
GIDAN KAKA
Sarki Tsafin Yankin Tudu da su Jalal suka butulcewa saboda ɗaukakar da Sufyan ya samu ne yasa Maza majiya ƙarfi masu ƙarfin tsafi a Jikinsu su yi gadin kaf faɗin kewayen Gidan Kaka saboda Naila.
A ɓangaren Matasan Yankin suma ƙofar Gidan Kaka suka mayar majalisar su har da abin shiffiɗar kwanciyar su saboda tsaron kar a biyoni cikin dare, Ni ma kuma ban gajiyaba wajen ambaton Ubangijin halittu.
NAILA; bayan ta huta suka ƙarayin waya da Yasar ya kuma ƙaramata ƙarfin gwiwar kar ta gajiya nasara na nan tafe In sha Allahu kafin dawowarta.
Da bayin Gidan Sarki Hammam Mata ta ɓangaren Jalal suka isar da saƙon Jalal na sakin Naila a gidan Kaka da rufa ido ɗaya a cikinsu da dama don abinda aka turota da ragowar kenan ta ɗauke wayar Naila.
Su Naila ba su ankara ba sai bayan tafiyarsu.
A daren Ɗayyib ya yi duk wani bincike shida Sufyan da ƙwararren masanin na'ura mai ƙwaƙwalwa a Masarautar amma basu ga alama ɗaya daya haɗa Naila da Ma'aikatar su Sufyan ba. Cikin ɗacin hali Sufyan ya farfasa wayar ya cire layin ya karya.
★washe gari layi-layi fadawan Sarki Hammam suka bi suna gayyatar mutanen Yankin filin wasannin ƙarshen mako don gudanar da shagalin bikin Sufyan.
★
Ranar da ya kama shagalin bikin Sufyan da Sumaya. Sufyan ya yi ado na kece raini duk da ba haka yaso ba Naila ta ɓatamai komai.
Sarakuna daga Yanki-Yanki ƴan kasuwa da ƴan siyasa, su aka warewa waje na alfarma har da wajen da GM ɗin Sufyan da sukayi waya suna kan hanya zai zauna.
A cikin Dattawan da suka je gudun abinda zai biyo baya har da Mahaifin Kabeer da ya tsufa ya yanƙwane saboda wahala.
Lokacin da taro ya yi taro motocin Ɗayyin da Sufyan ya sabunta suka tafi taro GM ɗin Companyn sarrafa shinkafa ta Dhabah.
Isowarsa Motar da Gm yake ciki da saukarsa daga Mota duk akan idanuwan Mahaifin Kabeer.
Dark blue suit mai nauyin kuɗin gasken daya kwantawa farin fatarsa da kakkaurar jikinsa ya sanya. Gashin kansa dake amsar gyara na kwance luf. Lokacin da ya fara takawa, Mahaifin Kabeer da yunwa tasa ya ranƙwafa ya yanko wajen da aka hanasu ƙetarawa saboda su talakawa ne da gudu. Cikin ihun da ya haɗe da kuka ya ke faɗin;
"Ashe Malik zai cikamin alƙawarin da ya ɗaukarmin! sai dai ya shammceni, da na san irin wannan alfaharin yake nufi da na tattara masa dukka Ƴayana ya tafi da su.
kabeer Ɗana ashe da gaske zaka dawo garemu bayan mun cire rai, lallai Allah Abun godiya ne."
Cak Kabeer ya tsaya haɗe da buɗe dukka hannayensa da ke fitar da wani irin ƙamshi. Cikin soyayyar Uba da Ɗa kabeer ya rungume Mahaifinsa.
Babu wanda bai miƙe ba, babu kuma wanda bai razana ba daga waɗanda suka san Kabeer har waɗan da basu sanshi ba.
Da wani irin fushi Ɗayyib yake taka ƙasa kamar zai hudasa, gaban Sufyan da shi ma yake tsaye kamar mutum mutumi ya tsaya ya na kai hannunsa saitin ƙugun wandonsa.
Da zafin zuciyar azabar dake neman halakasa tashi ɗaya ya ce;
" Lallai ban haifo ɗa ba sai soko kaicona! Nasan Malik ya ɗauke Kabeer ya inganta masa rayuwarsa da turomana shi a irin wannan lokacin domin ya nuna mana iyakar mu, kuma ya yi nasara.
Amma idan har Malik zai mallaki dukiyar da zai sauya rayuwar Kabeer, Kabeer kuma ya sauya taka kai kuma ka sauya namu to tabbas su na da Ubangida, Uban gidan da ya kamata ace kasani tuntuni, amma sai gashi ko Kabeer ɗin ma baka sani ba Balle kuma Ubangidan su, daga yanzu har zuwa ajalinka ba zan taɓa yafe maka ba Sufyan har sai ka gano min wanene DHAHAB 🔥?????
Ɗayyib ya ƙarasa faɗa yana yankar ƙuncin Sufyan da wuƙar da ya zaro a ƙugunsa, a take jinin kumatun Sufyan ya yi tsartuwar da ya fallatsa har saman fuskar Ɗayyib....✍🏻
Barka da Jumu'a.
[7/27, 9:52 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Page 21
Sufyan kansa ya sunkuyar ƙasa, raɗaɗin yankar da Mahaifinsa ya yi mai a kunci da yankar da Kabeer ya yi masa a zuci na naiman zautar da shi. Shi da kansa kunyar kansa yake ji, baƙin ciki mai girma na da ɗa mamaye zuciyarsa.
Ɗayyib da ya juya ya kalli irin gyaran da Masautar Yankin ya samu da dukiyar da kai tsaye za'a kirasa da na Malik da irin manyan mutanen da ya ɓata dukiya ya gayyata saboda Kabeer kawai, sai ya ƙara juyowa. Da wani irin fushin mai girma yake yankar Sufyan ta ko ina yana maimaita
"Ko Marigayi Sarki Musa zai dawo duniya a raye ba zan yimasa irin wannan hidimar ba na rantse da Sarki Allah! Sufyan ka cuceni! Ka cuceni!!"
Daƙyar aka ƙwace Sufyan da ya yi kacha-kacha da jini a hannun Ɗayyib da ya zama kamar Mahaukaci.
Mutanen Jalal ne suka ja Ɗayyib cikin Gida, shi kuma Sufyan aka wuce da shi Asibiti yana ihun azaba kafin ya sume.
Sarki Hammam a take ya bayarda umarnin a rufe iyakar Yankin Tudu, kuma a turo masa Kabeer cikin Iyayensa da gaggawa.
Da ƙananun gulmammaki taron shagalin bikin Sufyan ya watse maimakon yabo da ya ci burin yasamu a wajen Mutane.
Kamar yadda Sarki Hammam ya bada umarni haka akayi sai dai babu Kabeer babu Iyayensa. Da gaggawa Sarki Hammam ya ƙara bayarda umarnin abi duk Yankin da yayyen Kabeer mata suke aure a kamo su. Sai dai suma duk basanan acewar Surukansu sun bar Gida da sunan zuwa shagalin bikin Ɗan shugaban kasuwar zinaren Yankinsu tare da rakiyar Mazajen su da Ƴaƴan su.
Babu inda ba su bincika ba amma babu Kabeer babu ahalinsa. Dagaske dai Kabeer ya gudu da dukka ahalinsa.
Ɗayyib da labarin ɓacewar Kabeer da ahalinsa ya riskesa Ihu ya kurma haɗe da ɗaura ɗamarar binciko Kabeer da ahalinsa a duk inda suke. Fadawan Sarki Hammam majiya ƙarfi Jalal ya bawa umarnin tare Ɗayyib daga barin Masarautar, ya na fizgewa suna tarosa, daƙyar suka danneshi aka nemo likita ya yi mai allurar barci.
WAIWAYE
Da Malik ya ɗauko Kabeer daga gidansu a sirrince ya fitar da shi iyakar Yankin Tudu sukabi Jirgin samansu zuwa ƙasar Abyad.
Daga wannan rana Malik baiyi ƙasa a gwiwa ba sai da Kabeer ya zama abinda zai sosai zuciyar Ɗayyib da shi. Ya na shirin ɗauko Iyayen Kabeer, bikin Sufyan ya Kunno Kai, don haka suka turasa bayan sun shirya yadda zai taho da Iyayensa da zarar taro ya hargitse.
A zahirin gaskiya Kabeer shugaban Sufyan ne a wajen aiki amma ba shi ne GM ba, Uzair da Naila ta taɓa ganin mai tsananin kama da Salman ne GM.
DAWOWAR LABARI
Lokacin da Ɗayyib ya fara yiwa Sufyan magana, Kabeer ya sulale da Mahaifansa har da ƴan uwansa suka bar Yankin, dama kuma tuni motocin ɗaukar su Kabeer yana Yankin amma saboda taron mutane yasa babu wanda ya ankara.
NAILA;
ɗaukemata waya da Bayin Gidan Sarki Hammam sukayi ya zama iyaka tsakaninta da Yasar, saboda tanan kawai yake iya sanin halin da take ciki. Lamarin ya sosa zuciyarta tare da ɗaga mata hankali sama da Sakin da Sufyan ya yi mata, domin ko bai saketa ba, dama tayi alƙawarin bazata ƙara iya rayuwar auren rashin ƴanci da shi ba.
Damuwar da ta shiga akan hanyar da zan ƙara samun Yasar ba ƙaramin tashin hankalin Kaka ya yi ba, cikin ƙarfin halin ɓoye ta ta damuwar take jaddamata ko da karo-karon ne zasu haɗamata kuɗin Mota ta koma Makaranta ita da ƴan uwan Mahaifinta dana Mahaifiyarta har ma da mutanen Yankin.
Wannan ƙarfin gwiwa da Kaka ta bawa Naila sai ya gusar da duk wani damuwa da fargaba da ke danƙare a cikin zuciyarta na fara walwala kamar kowa.
A haka suka kwashe kwanaki uku cikin gidajensu, ba tare da dogon zirga-zirga ba, abisa umarnin Sarki Hammam.
SUFYAN; yasha azaba irin azabar da bai san akwai irinsa ba, kullum cikin kuka yake tunda ya farfaɗo daga duniyar azabar da Mahaifinsa ya kaisa.
Sumaya ta na gefe itama tasha kuka idanuwanta duk sun koɗe, wahalar da bata taɓa tunanin zatasha ba har su gama rayuwar Aurensu da Sufyan shi take sha, idan zai yi fitsari da Toilet duk ita take taimaka mai gashi da raki kuma ita dama can ba saba aikin wahala ta yi ba.
Ga shi
Bayin ma da aka bari Maza ne masu gadinsu balle su taimaka mata.
Ƴan uwanta suma gaba ɗaya sun matsu su koma Birnin Abyad, danasanin rako Sumaya Yankin Tudu na damun zuciyarsu.
A ɓangaren Hindu bayan barinta Yankin Tudu zuwa Yankinsu, kai tsaye wajen Malaman dubanta ta wuce.
Tabbacin suka bata na; nasarar Sufyan da isarsa tsakiyar Babban Birnin Abyad da kuma samun ɗaukakarsa mai girman gaske ya na tare da Naila, babu abinda ya sauya.
Amma ita da Sufyan sun karya dokar da aka shimfiɗa musu tun farko. Na farko zaman Sufyan a Birnin Abyad saɓanin Babban Birnin Abyad da aka sharɗan ta musu, na biyu gaggawar Sufyan na yin Soyayya da Sumaya har da aurenta. Na uku sakin Naila da ya yi, shi ya ƙara wargaza komai.
Da rawar murya kuka Hindu take roƙon asama mata wata mafitar tun da wannan ya lalace.
Sihirin da za'a shayar da Naila ya bata na tsahon kwanaki uku ba tare da rarrabewar kwanaki ba. Zata dawwama a ciwon da babu magani, bayan tasha wahala Sufyan zai je da sunan taimakonta.
Idan har Iyayenta sun amincewa Sufyan ya samu damar ɗaukarta zuwa Masarautar su to ta dawo za'a bata maganin da zai karyar sihirin da sukayimata ta samu sauƙi, daga nan sabon shirin tunkurarsu Babban Birnin Abyad zai kankama da zafin da dole nasara ta tabbata. (Anya wannan nasarar zata tabbata🤔)
Da wannan ƙwarin gwiwar Hindu ta fara shirye-shiryen dawowa Yankin Tudu, bayan tayi kwanakin da ta ɗibarwa kanta.
ƊAYYIB
Har sati ɗaya ya shuɗe idanuwan Ɗayyib ba su washe ba, baya iya magana saboda baƙin cikin da suka yi mai karo. Ko Asibiti yakasa zuwa duba Sufyan, itama Hindu tattare lamarinta ya yi ya watsar, burinsa ya samo ina Kabeer da Malik su ke, su bashi labarin wanene Uban gidansu.
Babban Malamin duba da suka musanya bayan faɗarsu da Sarkin Tsafin Yankin Tudu Jalal ya gayyato tun daga wata ƙasar domin fayyace musu abinda Ubangiji ne Masani akai.
"Ina su Malik da Kabeer suke? A wacce duniya suke rayuwa? Shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan. Wanene ko wacece asalin Uban gidansu? Waɗannan tambayoyin shi su Ɗayyib suke neman haske a kansu ido rufe.
Bayan sun gama korowa Malamin duba bayani.
A duban da ya yi
Abu ukun da suka tambaya bayyanannu ne amma na ukun saninsa sai Allah.
Na farko inda Malik da Kabeer suke da duniyar da suke rayuwa, na biyu kuma shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan,
Na ukun da ya kasa gonowa shine sanin asalin Uban gidan su.
Amma ya kuɗurce a ransa bazai gayamusu ba sai abinda zai faranta ransu su biyasa kuɗi mai tsoka, don haka ya gyara zama ya yace;
"Kabeer da Malik suna wani gari ne Daf da shiga Babban Birnin Abyad, kuma suna rayuwa ne kusa da Company da Sufyan yake aiki ba a cikin asalin ƙwaryar Babban Birnin Abyad ba.
Kabeer kuma ba shine Uban gidan Sufyan ba, a yadda dubana ya nunamin Kabeer ba shi baya aiki ma da Ma'akatar su Sufyan kawai rufa ido ya yi muku. Asalin Ubangidan Malik kuma Macece wacce ta taɓa zama a nan Yankin Tudu amma nakasa gano asalin wacece"
Da sauri Ɗayyib ya miƙe yana dariya, cikin yaƙini ya ce idan ba Nanaah Faɗima ba ( kakar Sulaim matar Ubaidu) to Aysha ce( matar Abduh Dhahab Mahaifiyar Sulaim). Da sauri malamin duba ya gyaɗa kai alamar gaskiya ne.
Kuɗi masu nauyin dake bayyana jindaɗinsu suka sauke mai. Da murmushin samun nasarar duƙunƙune sun da ya yi, ya saɓa jakarsa ta zallar fata ya yi musu sallama. A zahirin gaskiya Kabeer da Malik tabbas a kusa da Company Dhahab suke rayuwa, amma da gaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan yasan idan ya faɗi gaskiya a matsayinsa na babban malamin duban da suka ɗauko tun daga wata nahiyar ba zai samu kuɗi mai tsoka ba, batun Macece ko Namiji ne asalin Uban gidan su Malik ba shi da sanin komai akai, shima ya faɗa ne don ya faranta musu shima su faranta mai. Da mugun murmushi malamin duba ya hau motar da zai sadashi da iyakar Yankin Tudu da tumulin kuɗinsa a jaka.
Da gaggawa Ɗayyib da bai taɓa zuwa duba Sufyan ba ya ɗauki hanyar Asibiti, ɗauke da wayar Sufyan da ya jima a kashe.
Bai damu da halin da Sufyan yake ciki ba, ko yaya yanayin jikinsa yake ya naimi waje ya zauna.
Cikin sanyi murya Sufyan ya gaisheshi. Da sakin fuska ya amsa yana yi mai yaya jiki, ko kallon inda Sumaya take baiyi ba, balle ya yi mata godiyar hidimar da takeyi da ɗansu, sai ta basu guri zasuyi magana da ya faɗa a kausashe.
Jiki a sanyaye Sumaya ta bar Ɗakin nadamar auren Sufyan na mamaye ruhinta,