x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 757

07 Oct 2025
cikin wankakkun uniform ɗinta, karkata keken ya yi ta hau.

Bayan sun isa Makaranta ya na sauketa ya juya batare da ya kalleta ba. Sai taji sam ba daɗi a ranta, kafin ta haɗu da ƙawayenta ta manta da komai.

NAILA;
A na tashinsu ta taho da gudu, nan ma Sulaim bai amsa mata gaisuwar da ya saba amsawa da gyaɗa kai ba, duk sai ta ƙarajin ba daɗi, jikinta ya yi sanyi.

Ya na sauketa ta fara lalubar jakarta, soyayyiyar Aya ta fito dashi mai yawa da ta siya kwandala biyu ta miƙamai. Bai karɓaba sai kallonta da ya tsaya yi.

"ga shi Yaya"

ta faɗa da tsoron yanayin fuskarsa. Murmushin yaƙe ya yi ya ce;
"Naila" da muryarsa mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji. kanta da ɗago dasauri ta na washe ƙananun haƙoranta kafin ta ce "na'am"
"Idan kina so na karɓa to ki faɗi sunana na ji" ya faɗa yana kallon fuskarta.

dariyar yaranta ta ƙyalkyale da shi, daɗi kamar ya sumar da ita, sai da ta tsagaita sannan ta ce. "Sulaim" ta ƙasara faɗa tana murmushi haɗe da rufe fuskarta. Shima murmushin fuskarsa ce ta faɗaɗa ya na kallon yadda take dariya kamar an bata aljanna. Hannunsa ya miƙamata, da sauri ta miƙamai Ayar ta na shigewa cikin Gidansu ranta fari fes saboda ya yi mata magana baki da baki, ba da kai ko hannu ba. Sannan ta matsu ta shiga gida ta basu labari.

Bayan ya zura Ayar da ta bashi a aljihun gaban rigarsa kasa tafiya ya yi sai da ya ɗan jima a zaune a kan kekensa kafin ya bar ƙofar Gidan...

ABDUH DHAHAB;
bai dawo gida ba, sai dare, Iyalin Mairam ba ta tambayarsa inda ya je, saboda tunda da ya daina kwana a ɗakinta take fushi.

SULAIM;
A daren ranar ma kasa runtsawa ya yi, saboda tunani da hasashen da bai san dalilin su ba. Ya na jin ƙewar Naila ba tare da yasan dalili ba ga fargaban dalilin da ya sa Mahaifinsa ya sayar da Tukwanen da zai fitar da su kasuwa washe gari ba tare da ya ƙera wa su ba.


Ƙarfe 2:00am ya ji alamar motsi, gefen Mahaifinsa da ya dawo kwana a ɗakinsa ya kalla ya ga alamar barcinsa ya yi nisa, miƙewa ya yi tsaye.

Wani ƙaramin ƙarfe mai tsini da kaifi ya ɗauka ya soke a gefen ƙugunsa, kafin ya fara takowa tsakar gidan a hankali.

Ya na ƙarasa fitowa tsakar gidan akayi masa yankar da ya sa shi buɗe dukka girman muryarsa a gefen kafaɗarsa na dama. Dole ya zube ƙasa zuciyarsa da gangar jikinsa na karɓar raɗaɗin azaba lokaci ɗaya.

"Au ashe iskanci ne dama ka iya magana?"

Wanda ya yankesan ya faɗa ya na sakin dariyar mugunta. Tsaf Sulaim ya ɗauki muryarsa duk da ba ya cikin nutsuwarsa.

"Zan Barka a raye matsawar ka faɗamin ina Mahaukacin Ubanka ya ke" wanda ya yankesan ya faɗa yana ɗagoshi.

Shiru Sulaim ya yi ya na kallon fuskarsa dake sakeye cikin baƙin ƙyalle.

Ƙaramar wukar hannunsa yasa ya ƙara yankar gefen kunci Sulaim da ƙarfi haɗe da ƙara maimaita: " ina Mahaukacin Ubanka Abduh Dhahab ya ke, a ina ya zuba tarin dukiyar Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Turawan da su ka zo kwana uku da suka wuce? Su na ina!" A wannan karon Sulaim bai saki ƙara ba, sai zaburar dayayi ya soke shi da ƙarfen da ya soke a gefen ƙugunsa a dai-dai saman kafaɗarsa tunda ya na da tsahon ƙafa.

"yaushe Mahaifina ya gama girbar amfanin Irin da ya sha wahala da azabar shekarun shukawa, da har zakazo karɓan na ka kason!?" Sulaim ya tambayesa da sansanyar muryarsa da azaba ta sa ya ƙara yaushi.

Sulaim Bai gama sauke hannunsa da haɗiye yawun kalamansa ba ya ƙara yankarmai gefen kafaɗarsa na hagu haɗe da fesar da hucin haushin kalaman da Sulaim ɗin ya jefesa da shi. Shima Sulaim bai zube ƙasa gaba ɗaya ba sai ya da ya zaro ƙarfen da ya sokamai a kafaɗa ya ƙara kafamai a tsakiyar cinyarsa da dukka ƙarfin daya rage mai. Kusan lokaci ɗaya su ka zube ƙasa. Kowannen su ya na sauke numfarfashin azaba ga jinin da ya ke bin jikin kowanne su.

Kasa jurewa Matar Mahaifin Sulaim da ke laɓe ta yi ta fito ɗaga ɗakinta don tsaf ta haddace muryar wanda ya shigo musu gida.

Da kuka ta fito ta na ba shi haƙuri. Wanda ya yanki ya na ganin fitowarta ya miƙe da sauri kamar ba shi ba, saboda hasashen mallakar dukiyar Tukwanen Zinaren da Abduh Dhahab ya ɗauki tsahon shekaru ya na bautar tarawa ba tare da ya bari ko shi kansa ya mora ba.


Itama tambaya ya titsiyeta da shi ya na rintse idon azabar da ya ke ji, "a ina Abduh Dhahab ya ajjiye kuɗin Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Turawan da suka zo? kuma a ina ya ke ɓoye dukka dukiyarsa ki faɗamin na ƙyaleki a raye?" Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba, sai kallon bayansa da ya ga ta na yi. Bai kawo komai ba a ransa ya ɗauka halin da Sulaim yake ciki ta ke kallo.

Ganin bazata faɗa ba yasa ya kai mata hauri ta bugi bango da ɗaya ƙafarsa mai lafiya. Ya na juyowa inda ya bar Sulaim yaga ba bu shi a wajen. Kenan Abduh Dhahab yana gidan? maiyasa bai fara bincika ɗakunan Gidan ba tukunna?

"Abduh!!!!" ya faɗa da ɗan ƙarfi yana zare dukka girman idanuwansa da su ka yi jajir

Pito ya yi, abokannan rakiyarsa da suka maƙale suna jiran umarninsa suka shigo Gidan. Biyu zama su ka yi ɗauremasa ciwukan da Sulaim ya ji mai, bayan sun zare ƙarfen cinyarsa, ragowar kuma suka hau bincika gidan.

Sun samu Ɗakin Abduh Dhahab da duk amintakarsa da Mutum ba ya bari ya shiga, sun bincika amma babu ko sisi a ciki.
Hanyar da jinin Sulaim ya ɗiɗisa su ka dinga bi su na haskawa, har suka samu ta inda Abduh Dhahab da Sulaim suka bi suka bar gidan, ta ƙofar da ba su san da shi ba.

Zabura ya yi ya na haska ƙofar bayan da Abduh Dhahab ya bi har zuwa inda jinin ya tsaya. Dariya yaƙen azabar da ke nuƙurƙusarsa ya saki ya na kutsa kai cikin gidan bayan sun ɓalla ƙofar Moƙocinsa kuma Amininsa da suke kyautata zaton nan Abduh ya shiga.
Da matar gidan su ka ci karo tana salla a tsakar gida. Bai amsa tambayoyin da ta ke jero mu su na dalilin shigo mata gida kai tsaye ba ya ce:
"Sarah! Ina Mijinki ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗan shi? Asibiti ya kai shi, ko su na cikin Gidannan? kifaɗamin gaskiya ko na wulaƙantaki" ya ƙarasa faɗa ya na ƙare mata kallo ta hasken farin watan daya haske gidan.

Da sunan Ubangijin da take ambata ta yi jarumtar furta "Mallam ba ya gari, ya tafi Fansar Litattafai, Asibitin kuma sati ɗaya kenan ba a yi aiki a cikinsa ba"

dariya su ka bushe da shi don ko a ranar sun ga mijinta. Ƙasan Gidan ya haska ya na kai dubansa dai-dai wajen da Jinin da ya ɗiɗisa har zuwa inda ya tsaya.

Dai-dai inda Mallam ya ke ajjiye kekunan hawarsa har guda biyu jinin ya tsaya. Dariyar ƙeta ya sa kafin ya ce. "ashe Mallam mai Asibiti da zai fita da dukka kekunansa ya fita Fansar Litattafai kenan? Ki faɗa min wanene ya tuƙa ɗaya keken?" Kai ta girgiza haɗe da yin duk addu'ar dayazo bakinta.

"Wallahi kinji na rantse idan baki faɗamin gaskiya ba zan ƙona gidanan da ke da ƴaƴanki gaba ɗaya." kuka tasa ta na roƙonsa da magiya kala-kala.

Ganin ta na ɓata mu su lokaci ya sa ya ce a ƙona Gidan tunda taurin kai ne da ita. Ta na jin haka ta ce Abduh Dhahab ya zo da Ɗan shi amma sun tafi Asibiti. Dasauri ya ce: "ya zo da kuɗi?"

"Bansaniba amma dai yazo da buhu mai girma da abu a cik.." bai bari taƙarasa ba, su ka bar Gidan.

Ko da sukaje Asibitin Mallam, ba bu Abduh Dhahab da Sulaim kuma ba bu ko sisi sai Mallam da su ka samu yana ƙoƙarin dawowa Gida.

"A wani ɗakin ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗanshi da kuma dukiyar da ya ƙullo a buhu?" Suka tambayi Mallam.

Shiru Mallam ya yi kamar kurma. Sunfi minti 15 su na ta tambayarsa kafin ya basu amsar Abduh Dhahab yana cikin Asibitin da dukiyarshi.

"A wani sashe na Asibitin? kuma a wani ɗaki?" Su ka ƙara tambayarsa Tunda Asibitin ba laifi ya na da girma. Shiru ya yi yaƙi ba su amsa kuma ba bu inda ba su duba ba babu Abduh Dhahab kuma sun kasa gano shaidar ɗakin da zasu sameshi ga dai keken Mallam daya tuƙo a gefe jini duk ya ɓatashi. Kuma Mallam ya kafe Abduh Dhahab na cikin Asibitin da ɗanshi da dukiyarshi. Ganin kamar raina mu su hankali haɗe da son tona mu su asiri ya ke yi. Sai suka turashi cikin Asibitin su ka kulle.

A can gidan Mallam
Suna fita Matarsa ta tattara ƴaƴanta su ka nausa hanyar Yankinsu a cikin daren kamar yanda Mallam ya umarceta kafin ya zo ya samesu.

Bayan sun tura Mallam cikin Asibitin sun kulle, wuta suka saka, sannan suka ƙara dawowa gidan Abduh Dhahab suka yiwa Matarsa kashedi mai zafin da ya kai ga guntule mata ƴan yatsu biyu, tare da yashe duk wasu dukiya da suka samu a ɗakinta na tarin kuɗin la'adar da Abduh yake biyanta idan ta tayasu aiki.

★washe gari labarin gobarar Asibitin Mallam ya karaɗe Yankin, Da farko ba'a fahimci gawar su waye a ciki ba, sai da Surikin Mallam ya biyo jin ba'asi bayan isar Matar Mallam Yankinsu anan ya tarar da mummunar labari, ya kuma tabbatarwa da Mutanen Yankin su Mallam ne suka ƙone, da iyakacin hujjar da ƴarsa ta bashi.


Duk da a kwai waɗanda suka ɗan ji abinda ya faru a cikin daren, amma sukayi shiru su ka ƙi magana, kowa ya ja bakinsa ya tsuke, tunda matar Abduh Dhahab bata farfaɗo ba, tun cikin daren zuwa wayewar gari balle ta faɗi sunan waɗanna su ka aikata a ɗauki mataki a kansu, kamar yanda Sarki Hammam ya bayar da shela.

Gawar Mutum huɗun da aka zaro sun ƙone ƙurumus bakyan gani don babu fuskar wanda aka gane balle a banbance. Ɗayyib ya na kwance lulluɓe cikin abin rufa sai kuka da ihu ya ke yi jikinsa ya na rawa, haɗe da sabbatun su fito masa da Abokinsa Abduh Dhahab, wallahi bai yarda Abduh Dhahab ya mutu ba, wanene ya kashemasa Abduh Dhahab Aminin ƙwarai?


0


09132403788
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥



SASAAL




03

A fadar Sarkin Hammam aka sallaci gawarwakin da Sarki Hammam da kansa ya jagoranta. Kafatanin Mazan Yankin ne sukayiwa gawarwakin rakiya izuwa makwancin su. Kafin dawowar su Dangin Mahaifin Mairam (matar Abduh Dhahab) sun zo sun ɗauketa saboda gudun abinda zai biyo baya, haka Malik maiyiwa Abduh Dhahab hidimar shara duk safiya shima ana dawowa da ga kai su Abduh makwanci aka nemesu aka rasa shi da Iyayensa.


A wannan ranar kasuwar da Abduh Dhahab ya sha gwagwarmaya shekaru kafin kafuwarsa na siyar da Tukwane ma su Taken Tukwanen ZINARE don cigaban Yankinsa ya yi faɗuwar tasa da ba'a taɓa tunani ba.

Domin duk wanda ya zo ya ji mutuwar Abduh Dhahab ba ya iya tsayawa ya ke juyawa inda ya fito. Dubban mutanen Yankin sun tafka asarar abincin siyarwa da su ka dafa da sauraran kayan amfanin da suka sarrafa don siyarwa baƙin da suke shigowa.

Anya mutuwar Abduh Dhahab bazai kawowa yankin su Talauci mai ƙarfi da koma baya ba kuwa? tunda ta nan suke samun kuɗin shiga ta hanyar abubuwan da suke sarrafawa su siyarwa Baƙin da su ke shigowa, ga kuɗin hayar masauƙin da suke samu da ga wajen baƙin da suke zuwa daga nesa. Dukka wannan ya rushe kenan? Tambayar da Mutanen Yankin suke ta yiwa kansu kenan..



NAILA
Ta fi minti Talatin a tsaye a harabar Gidan su Sulaim ta na jiran fitowarsa, bayan tasha kukan daya ɓata Kyakkyawar Fuskarta da hawaye da majina. Don ita bata yarda Sulaim ya mutu ba.
Daƙyar Babanta ya janyeta shima na shi ran na suya.

Da Surukin Mallam zai koma Yankinsu Sarki Hammam ya umarcesa ida anyi Ukun su Mallam ya kawo masa Sarah ya na son yi mata tambayoyi, tunda Matar Abduh bata hayyacinta. Da "to" Surukin Mallam ya amsa amma har cikin zuciyarsa bayajin Sarah ɗiyarsa zata ƙara taka Yankin..

Da yammacin ranar aka binne su Abduh Dhahab, sai gaba ɗaya mutanen Yankin suka koma zancen asarar da suka tafka, ba tare da sun ƙarabi takan abinda ya yi makasudin ajalin Abduh Dhahab da Ɗansa har ma da Mallam ba. Wannan lamari ya yi matuƙar sosa ran Dajjito Junaid.

Junaid ɗaya daga cikin Dattawan Yankin ne, kuma na hannun daman Sarki Hammam, ba shi alaƙar Jini ko na dangantaka da su Abduh Dhahab.

★washe gari Dattijo Junaid tattaki ya yi har Yankin su Sarah Matar Mallam. Ya sameta a mawuyacin hali mai ban tausayi, iyayenta sun karramashi tare da bashi abin sha don jiƙa maƙoshi. Tambayar duniya Sarah taƙi faɗar waɗanda suka zo gidanta neman Mallam, ƙarshe da Dajjito Junaid ya matsa mata kuka ta fashe da shi raɗaɗin kisan gillar da akayiwa Mijinta na cigaba da sukarta. Ta yaya zata faɗa bayan tasan za su bibiyeta.

Har Rana ta yi Dattijo Junaid bai bar Gidan su Sarah ba. A kan idonshi Iyayen Sarah da ita kanta da ƴaƴanta suka fito da kayayyakin su don yi balaguro tunda sun san dole a bibiyi ƴarsu gudun kar ta faɗi gaskiyar abinda ta sani.

Hawaye Dajjito Junaid ya share ya na bin bayan su. Cikin taushin harshe da amon dake bayyana irin raɗaɗin dayake ji a ƙasar zuciyarsa ya ce;

"Sarah tunda bazaki bani ƙarin haske akan abinda ya faru ba, ki taimaka ki faɗamin inda Mallam yake samun taimakon inganta babban Asibitin mu, da kuma Makarantun ƴaƴamu na roƙeƙi" ya ƙarasa faɗa yana haɗa fararen hannayensa waje ɗaya alamar roƙo. Tsayawa Sarah ta yi zuciyarta na karyewa tsananin tausayin Abduh Dhahab da Sulaim na bijiromata. Sai da ta tattaro dukka jarumtar daya bata damar shanye kukan dake neman cin ƙarfin maganganun da takeson faɗa sannan ta ce;

"Abduh Dhahab shi ne wanda ya gina makarantu da Asibitin daya bawa Mallam amana bayan ya roƙi Mallam ya yi mishi alfarmar kar ya bari kowa ya sani har sai idan shi ya buƙaci hakan da kanshi. Ya ƙare rayuwarsa da Ɗansa wajen bauta muku da son ganin cigaban Yankinku, amma duk da haka sai da kukayi sanadiyar ajalinshi. Tir! da wannan Yanki na ku" ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka haɗe da barin Dajjito Junaid tsaye da sakekken baki.

Dattijo Junaid Tafiya yakeyi da iya ƙarfinsa amma sai yake ganin kamar baya sauri, burinsa ya isa Yankinsa ya ba su labarin da zai dawo da su hayyacinsu su binkico shaiɗanin dayayi sanadiyar rushewar Yankin su.

Da Yammaci Dattijo Junaid ya iso Yankinsu da labarin alkhairin Abduh Dhahab,
Ba bu wanda ya yarda da shi, sai ma cewa da suke yi;

"Abduh Dhahab ɗin da yake mayen kuɗi ne, zai yarda ya bautawa Yankinsu da dukiya mai yawa irin wannan? Kawai ƙage da rashin son zaman lafiya Dajjito Junaid yake son kawowa Yankin su" ire-iren maganganun da sukai tayi kenan har da masu kwashewa Dattijo Junaid albarka.

★Duk da haka Dajjito Junaid bai gajiya ba washe gari ya ƙara ɗaukar harama ya na shela layi-layi.

"Ya ku mutanen Yankin Tudu! Ina jiyemuku ranar nadamar da zakuyi nan gaba da kuma talauci mai raɗaɗi da azabar da zai iya riskarku matsawar kukayi butulci baku tsaya tsayin daka wajen ganin an binciko waɗanda suka kashe Abduh Dhahab da Iyalinsa ba, lallai sakayya mai raɗaɗi yana nan zuwa garemu, matsawar kuka yofintar da zance na. Haƙiƙa nan gaba kowa a cikinmu zai ɗanɗana kuɗarsa, Wannan wahalar nake jiyemana mutanen Yankina"

Leƙosa sukeyi wa sun su na dariya tare da yin Allah wadai da kalamansa, su na cewa;

"ai mu Abduh Dhahab ya cuta, tunda dama sihiri ya yi wa Kasuwar Zinaren da idan ya mutu Kasuwar da ya gina shima zai mutu baza mu moraba, tsabar mugunta da ya shiryamana har Tukwanensa ya kwashe kaf ya siyarwa da Turawa mu kuma ya barmu da tafka asara" har ya gama Shelarsa ya wuce Fadar Sarki Hammam babu wanda ya ƙullasa.

Da Dajjito Junaid ya yi magana a fada Sarki Hammam, ansamu waɗanda hankalin su ya karkata kan anya labarin da Dattijo Junaid ya zo dashi ba gaskiya ba ne ba kuwa? Haka a ɓangaren Sarki Hammam ɗari bisa ɗari ya yarda da zancen Dajjito Junaid har ya bada tabbacin ƙara zurfafa binciken waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin. Dama ya daɗe yana kokwanton waɗanda Mallam ya ce suke ɗaukar nauyin dukka ayyukan tun farkon buɗe Makarantun da Asibiti, da yanda ake biyan ma'aikatan jinya da malaman Makaranta albashi akan lokaci, da yanayin kulawar da ma'aikatan suke samu duk ba iri ɗaya bane da wanda suka samu gwamnati take ɗaukar nauyi.

Ragamar binciken komai Sarki Hammam ya miƙa a hannun Dattijo Junaid.

A wannan ranar da tsananin farin ciki Dajjito Junaid ya nufi Gida.
bai runtsa ba har sai da ya fara kamo bakin zaren abinda yake zargi.

A Yammacin wata Laraba ya shirya kaiwa Sarkin Hammam ziyara, don gabatar da shaidun da zai ƙara buɗe idon mutanen Yankin har su bashi goyon baya wanda ya yi dai-dai da cikar su Abduh Dhahab sati biyu a kaburburan su. Kafin ya buɗe gidanshi anrigasa buɗewa.

★washe gari, har rana ta fito Ba bu wanda yaji ɗuriyar Dajjito Junaid da Matarsa dama kuma Allah bai ba su haihuwa. Wannan dalilin ya sa aka ɓalla Gidan tunda ana da tabbacin su na ciki. Cikin jinin daya bushe aka samu Dattijo Junaid da wuƙa soke a gefen cikinsa, bakinsa ma jini duk a bushe ko da suka duba bakin anyanke mai harshe. Tsohuwar Matarshi kuwa tana Ɗaki a kulle tsoro da tashin hankali