x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 731

07 Oct 2025
PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥




NAFISA ALIYU SASAAL




Page 25


A kaikace yake kallonta, irin kallon da batasan yadda zata fassarashi ba.

A kan idanunta Driver ya tashi mota, duk da haka Mutumin yana kallonta kamar wanda bai Santa ba amma yake tunanin a ina ya taɓa ganinta

Tana ji tana gani mutumin da take kyautata zaton Malik ne ya yi tafiyarsa.

Tafiyarsa ba tare da ya buɗe baki ya cemata komai ba ya yi matuƙar sosa zuciyarta, har ya sata ta fara tunanin to maiyasa take bibiyar duk wani wanda abu ya taɓa haɗasa da Sulaim? mai take so su sanar da ita? Kenan batsyi imani da ƙaddara ba. Ko so take yi su cemata Sulaim yana raye? To idan ma Sulaim ɗin ma ya na raye cewa ya yi damacan ya na sonta ko zai iya aurenta? Maiyasa bazata rungumi maraicinta ta rufawa kanta asiri ba kamar yadda Allah Ya rufamata. Abinda da ya yi Sufyan shi ya yi Sulaim saboda daga tsatso ɗaya suka fito sai dai banbancin ra'ayi da ɗabi'a.

Jikina a sanyaya ta koma wajen Kaka, har suka dawo Gida bata saki ranta ba. Tun Kaka tana lallashinta da tambayar abinda ya ke damunta har ta gaji ta shareta.

Naila Sanyawa zuciyarta lallai sai ta manta Sulaim da duk wani abu daya dangacesa ne, ta fuskanci abinda zai kawowa Yankinta cigaba ne ya sanyamin zazzaɓi mai zafin gaske.

★Da Asubahi ta yi ko miƙewa da kyau bata iya yi saboda ciwon kai.
Kaka hankalinta ne ya tashi, cikin kuka takeyimata faɗar idan zaman Birnin Abyad ɗin ne banaso to na tattara su koma Yankin Tudu, su ƙarasa kasheta tunda ba zan kwantar da hankalina ba.

Da sassafe ta kira Yasar tana mitar ƙuncin da da Naila ta kwana da shi, yanzu gashi ta tashi da zazzaɓi.
Naila tana jin Yasar ya na tausarta Kaka tana ƙara haƙiƙancewa ya zo ya tambayeta idan zaman Birnin Abyad ɗin ne bataso sai su tattara su koma Yankin Tudu.

Ba su yi hour biyu da yin waya da Yasar ba, sabon Drivern da'aka Ma'aikatarsa ta ajjiye masa ya kawo shi gidansu.

Kaka ta na ganinsa ta miƙe zubur tana cewa;

"Ni bani da zaɓi, tunda bata tausayin kanta, tafison na mutu ina ƙunsar baƙin ciki, kuma daga yau Ni dai ba bu ruwana da ita" murmushi Yasar ya yi yana gaisheta, daƙyar ta haƙura da mitarta ta amsa gaisuwarsa kafin ta bar ɗakin.

Kafin Naila ta gaishe da Yasar ya katseta da ambaton sunanta
"Naila"

A hankali na ce "na'am"

"Menene alaƙarki da su Malik Dhahab? domin tun jiya ina sane da sauyin yanayinki, baki taɓa ɓoyemin komai ba amma jiya kin ɓoyemin Naila, menene gaskiya? " Yasar ya ƙarasa faɗa yana kallonta.

Haɗin sunan Malik da Dhahab shine abinda ya ƙara tsananta ciwon kan Naila lokaci ɗaya, kenan dai da gaske Malik ɗin Yankin Tudu mai gutsirewa mutane harshe ta gani, to ko dai da harshen mutanen dayake gutsirewa ya yi kuɗi har ya koma Malik Dhahab? Tunda a sanin da ra yi musu a shekarun baya talakawa ne fitik.

"Naila kinyi shiru, ko dai da gaske Yankin Tudu kikeson ku koma kamar yadda Kaka ta faÉ—a?" Yasar da ya gaji da dakon jiran amsarta ya tambaya.

Kanta ta girgiza sannan ta fara magana muryata a sanyaye;

"Nasan Malik a Yankinmu shekarun masu yawa baya, ina bibiyarsa ne domin na tambayesa ina Sulaim da gaske wuta ta ƙoneshi ya mutu, sai dai ƙiri-ƙiri Malik ya nuna bai Sanni ba bai ma taɓa gani na ba, wannan ne ya yi min ciwo har ma tashi da zazzaɓi."

Da mamaki Yasar ya ce;

"Anya kuwa Naila kinsan wanene Malik? Su Malik fa asalin ƴan ƙasar Abyad ne, domin da harshen da mafi rinjaye kuma mafi wahala na ƙasar Abyad dukka ahalin Gidan su ke amfani, yare ne mai wuyar koya a wajen bare, ko dai kama yake yi miki da waccen Malik ɗin?"

Tasan dama ba lallai ya yarda da ita ba, don haka kai tsaye ta karɓi yardar Malik kama yake yimata da waccen Malik ɗin.

Nasiha Yasar ya yimata tare da tunamata yaƙinin da mutanen Yankinta suke da shi a kanta, don haka na mayar da kai tayi karatu bakin iyawarta.

Kamar zata iya cire komai a ranta ta amsawa Yasar da "to" haÉ—e da yimasa godiya.

Ya na É—an jima a Gidan kafin a mayar da shi gida.
Bayan tafiyarsa dalla-dalla Naila ta zauna ta warwarewa Kaka komai. Kaka tsohuwace mai saurin fahimta da sauƙin hali bata da birkicewar wa su tsofaffin.

Cikin hikima ta nusantar da Naila, ko da ace Sulaim yana raye ba Mijin aurenta ba ne, ta tsaya a iya matsayinta ta kuma tsaya tsayin daka wajen manta baya ta fuskanci gaba, kar ta manta haɗakar kuɗin Mutanen Yankin Kakanta, da na Mutanen Yankin Tudu ne ya kawosu Birnin Abyad ba domin komai ba sai don ta yi karatu, saboda daga gareta suke sakaran samun canji, kar ta bari tunanin wanda da zai samu damar ƙara dawowa duniya bata kai matsayin da zai sota ba ya lalatamata tunaninsa har ta kasa zama abinda mutanen Yankinta suke yi min fata.

Sufyan da bai gaji arziƙiba, bai kuma gaji sarauta ba ya gujeta balle Sulaim da ya gaji Sarauta gaba da baya tare da tarin arziƙine zai so ta, Karta kuma wahalar da kanta wajen tunanin Sulaim yana raye ko baya raye, ta ƙaddarawa ranta ya mutu, ba kuma zai ƙara dawowa ba har abada!

Maganganun Kaka gaskiya ne, amma É—aukarsu ga Naila a lokaci É—aya abune mai kamar wuya, amma tasawa ranta zatayi iyakar iyawata don ganin ta fidda mutanen Yankinta kunya.

Kwanaki bayannan, ta fara bin gidajen Customominta, ta kuwa yi sa'a hannu bibbiyu suka karɓeta har ta samu kitsa kan wasu, A ranar da kuɗi masu nauyi ta dawo gida.

Daga wannan rana Naila ta ƙara himma akan sana'arta, har zuwa lokacin da ranar komawarta Makaranta ya yi.

Yasar ne yayimata siyayyar komai. Shi da Kaka da ƙannensa ne sukayi mata rakiya har Makaranta.

Kasantuwar Naila a Jami'ar ƴaƴan masu wadatar Birnin Abyad bai sa ta kai kanta matsayi da su ba, kitsonta takeyi ido rufe, kuɗi kuwa kamar anayimata yayyafin su, domin wasunsu biyan fariya da isa sukeyimata ita kuma na karɓa hannu bibbiyu tana godiya.

Watanta É—aya a Makaranta ta dawo tayi weekend tare da Kaka, sannan da bata ajjiyar kuÉ—in kitson da ta samu ta dinga tara musu.

SUFYAN.
Babu abinda ya sauya tsakaninsa da Sumaya, yawan ƙorafi, batason wannan, ita wannan take so da dai sauransu. Rashin mafita yasa Sufyan yake lallaɓawa, kuɗi kuma idan ya samu na su Ɗayyib ne. Sumaya sai dai ta samu ɗan abinda ba'a rasa ba.

Wata rana taro ya kai Sufyan Companyn Dhahab da suke ƙera Tukwane. Lafiya qalau suka gama taro ya fito, a hanyarsa ta fitowa ya ga mutumin da ya zo Yankinsu a matsayin Kabeer saboda shi dai ya kasa yarda da gaske Kabeer ne. Basarwa ya yi, ya nufi Motarsa. Har ya shiga Mota ya tuna ya manta tabaransa a teburin da ya zauna. Da ɗan zafin nama ya juya saboda aikin dayake jiransa a office.

Baya ya dawo yana matse idanuwansa da suka farayimai yaji. Masu tsananin kamanceceniya da Malik, Salman, Kabeer ya gani a waje ɗaya. Ƙara buɗe idanuwansa ya yi gaba ɗaya yana zaresu. Babu wanda ya kallesa a cikinsu har su ka gama gaisawa suka tafi sai wanda yake tsananin kama da Malik ne ya rage a tsaye yana duba wayarsa.

Sufyan bai motsa ba sai gumin dayake tsiyayomai, yana cikin wannan halin Maigidanshi Baturen da suka zo tare ya fito daga ɗakin taron, da sauri ya ƙaraso kusa da shi yaja hannunsa har gaban wanda yake kallo.

A gabatarwa da Baturen yake yi Sufyan ya ji ya ambaci Malik Dhahab shugaban Companyn Tukunyar Dhahab na ƙasar Abyad. Malik baya kallon fuskar mutum sai cikin idanuwansa, kamar yadda ya koya daga iyayen Gidansa, don haka kai tsaye cikin idanun Sufyan da suka fara canza kala yake kallo

Tafin hannun Malik mai girma da faɗi ya miƙawa Sufyan, shima Sufyan ƙasa ya yi da kansa kafin ya ɗago hannunsa da ya jiƙe da gumi tare da yimai nauyi ya miƙawa Malik bayan ya laso laɓbansa don ya tabbatar da harshesa ya na bakinsa bai fita ba.

Haɗuwar tafukan hannuwansu waje ɗaya yasa Sufyan ya ɗan ɗago kansa a hankali don satar kallon fuskar Malik, charaf idanuwansa suka faɗa cikin nashi, kafin ya sunkuyar da kansa ƙasa Malik ya ce; "Sufyan Ɗayyib Jalal right?"
Ambaton sunansa da salon da yasan dole sai wanda ya sanshi a Yankin Tudu ne zai iya faɗa da kuma Muryar da ya tabbatar masa da dagaske Malik ne a gabansa yasa idanuwansa juyewa numfashinshi ya ɗauke nan take ya zube ƙasa.

NAILA.

A makaranta ta haɗu da ƙawa ƴar masu arziƙin da take biyanta kuɗin kitso mai nauyi, da style kala-kala take zuwa a wayarta ta yi mata sak irin wanda ta kawo. wannan dalilin yasa suke ɗasawa da ita har sukan yi hirar da ya shafi Kaka da Yankinsu da ita.

Amira mai zuwa kitso wajen Naila da suka fi ɗasawa sun riga su Naila gama Exams. Ana saura kwana ɗaya zata tafi Gida ta zo da wani style ta ce Naila mata. Bayan mun gama take shaidawa Naila Babban Birnin Abyad zataje tsare-tsaren Bikin ƴar uwarta, wataƙila idan kitson ya yiwa ƙawayenta su zaɓeta ta zo tayi mu su, domin dalilin da yasa tace tayi mata irinsa kenan. Ko Kakarta ba zata amince ba?

Naila Tuna muradinta na son zuwa Babban Birnin Abyad yasa ta ji kamar ta amsata mata kai tsaye sai dai da ta tuna faÉ—an da Kaka tayimata akan Sulaim, sai tace bata ba, amma ta bari idan taje gida zata tambayeta idan ta amince zata sanar mata....
A akan haka suka rabu.


Shin Kaka zata amince kuwa??😄

🔥ZINARE🔥




SASAAL




Page 26


Har su Naila gama Exams bata daina tunanin tattaunawarsu na zuwa Babban Birnin Abyad da Amirka ba. Amma ta sawa ranta amincewar Kaka shi ne nata.

Ranar da ta koma gida
Da murna Kaka ta tarbeta bayan girki-girke ma su daÉ—i da ta shiryamata, sai da ta huta ta ci abinci, takasa sakowa Kaka zancen zuwanta Babban Birnin Abyad yin kitso saboda tsoron yadda Kaka zata fassara zancen take yi.

★har washe gari ta kasa yi mata zancen tafiyar, Sai Kaka da kanta ce ta kalleta cikin dariyar da ya haɗe da mamaki ta ce;
"Me kikeson faÉ—a kika kasa Naila? Tun jiya ina ankare da ke, karki ji nauyi ki faÉ—amin zan fahimceki kinji"
Murmushi ta yi tana murza goshinta, cikin kame-kame ta ke bata labari yadda sukayi da Smira.
Kaka kallon Naila takeyi maganganu Sarki tsafin Yankin Tudu lokacin da ya zo duba Naila na amsa kuwa a cikin kunnenta "Naila zata warke amma akwai jarabawar da ya fi wannan raɗaɗi a gaba, domin zata isa Babban Birnin Abyad, da ƙarfin ikon Allah! Amma daga lokacin ƙullin shekarun da aka kasa warwaresa zai fara warwarewa da kansa, arziƙin da Sufyan ya yi gajen haƙurin ya riskesa zai bayyana, wannan yana ɗaya daga cikin abinda Mahaifiyarsa take kwaɗaitar masa ya gaza fahimtarta, da ya yi haƙuri da zai zama wankakke abisa laifin da Kakannin-kakanninsa suka jima su na aikatawa aban ƙasa, ko da Naila ta warke ta koma Birnin Abyad, Birnin Abyad ba mazaunin Naila ba ne. Ba lallai ki yarda da maganganuna ba, amma daga ranar da sanadi ya kai Naila Babban Birnin Abyad, zaki gasgata batuna" furucin Sarkin Tsafin Yankin Tudu kenan lokacin da ya zo duba Naila, amma Kaka tayi watsi da zancensa acewarta; Boka Ɗan uwan shaɗai ne, don haka babu gaskiya a maganarsa..

Tuna wannan yasa Kaka a zafafe ta ce;
"Wallahi ban amince ba Naila, kinsan abinda kike faɗa kuwa? Babban Birnin Abyad har abada ba wajen zuwanki ba ne, karma ki ƙara tambayata don bazan lamince ba na gayamiki" Kaka taƙarasa faɗa cikin masifa! Tsabar masifa har rufe idanuwanta take yi kafin ta fashe da kuka.

Birkicewar Kaka lokaci ɗaya da yadda take magana har da su fashewa da kuka ba ƙaramin tsoro abin ya bawa Naila ba, cikin haushin yadda ta hantare ta har da su kuka ta ce;

"Kaka kukan me kike yi, ni fa kawai shawararki na nema, bance dole sai na je ba, sannan ke kika ce na gayamiki kar na ji nauyin komai zaki fahimce ni, amma gashi akan kawai na faÉ—a miki gaskiya shine kike masifa har da su kuka, dama can dai haushina kike ji, daga dawowata zaki sanyani cikin damuwa, na fara ciwo kuma kiyimin sharrin Yankin Tudu nake son komawa, gaba É—aya kin canza Kaka." Tsit ta yi tana kamo hannun Naila. ÆŠan fizgewa Naila ta yi tana cewa;
" ki ƙyale ni Kaka, tunda kin fara jin haushina a ɓoye bansani ba, ni ma daga yau babu ruwana da ke"

Hawayenta ta share still ba ta saki hannun Naila ba, da sanyi jiki ta ce;
" to zauna na faÉ—a miki gaskiya ina fatan kema za ki fahimceni, ki janye batun zuwanki Babban Birnin Abyad"

Son labari irin Naila yasa ta zauna da sauri jikin su na gogar na juna.

Abinda Sarkin tsafin Yankin Tudu ya faÉ—a ta maimatamata sannan ta É—ora da;
" Naila bawai na gazgata maganganun sa bane ɗari bisa ɗari, amma a yanzu a jikina nake jin ko dukka maganganunsa ba su zama Gaskiya ba, to baza'a rasa gaskiya ko da yaya bane ciki, duba da yadda su Hindu suke fafutukar dole sai kin koma cikin rayuwar ɗansu, Naila inajin tsoron matsalar da zai ƙara kunnowa rayuwarmu kai a yanzu, ki gafarceni"

Da mamaki Naila ta kalli Kaka tana tattare girarta waje É—aya ta ce;
"Saboda iya wannan dalilin zaki haramtamin samun kuɗin da zai sauya rayuwar Yankina? Kinsan nawa za'a biyani Kaka?. Rayuwarmu bazai taɓa cigaba da tafiya a haka ba, dole sai da gwagwarmaya tare da ƙalubale Kaka, baƙin ciki da farin ciki basa dawwama a rayuwar Bawa, idan warware ƙullin ne zai zama cigaban Yankinmu mai zai hana mu tunkari warwaresa ko da hakan zaisa mu rasa rayukanmu, tun da dai dole zamu mutu wata rana. Kaka kiyi tunani tunda na ki tunanin yafi nawa zurfi, ba kuma zanyi yin kaina ba dole zan jira umarnin ki, amma Kaka ki tuna gina kanmu da Yankinmu wajibunne, saboda Yasar shine ƙarfin gwiwar zamanmu a Birnin Abyad, to idan ya mutu fa? ko ya gaji damu fa? Jira zamu yi tayi sai dai wani yayimana gwagwarmaya mu muji daɗi mu ba za muyi da Kanmu ba? Saboda muna tsoron mutuwa?
Kaka kiyi tunani a nutse, kuma karki ji shakkar sanar da ni duk abinda kika yanke, In Shaa Allah zan yi miki biyayya kin ji."
ta ƙarasa faɗa tana rungume kaka bayan na sumbaci goshinta.

Tun a lokacin bugun zuciyoyinsu ya sauya daga tsoro zuwa ƙarfin gwiwa.


SUFYAN
Da ya farka ya ganshi a gadon Asibiti baiyi mamaki ba.
Sumaya tana ganin ya farka ta ajjiye wayar hannunta tana matsowa kusa da shi, sannu take ta nanatamai tana kamo hannunsa. Laƙwas Sufyan ya yi. A hankali ya buɗe bakinsa ya zaro harshensa.

"Sumaya kina ganin harshena, yana cikin bakina?" Ya yi tambayar yana karkaÉ—a harshensa.

Da mamaki Sumaya ta ce; "gashinan kana karkaɗawa, maiyasa zaka yimin irin wannan tambayar Baby, relax har yanzu zafin ciwon bai gama sakinka ba, bari na kira Likita" ta ƙarasa faɗa tana sakin hannunsa haɗe miƙewa ta bar ɗakin.
Ajiyar zuciya Sufyan ya sauke, sai dai kafin ya yi relax ɗin da Sumaya ta ce, asalin fuskar Malik da babu Tabarau babu komai sai ƙasumbar da shima an ragesa sosai saɓanin jiya da ya cikemai rabin fuska ya bayyana a ɗakin, mai kamannin Salman sak na biye da shi a baya.

Jikin Sufyan ne ya saki, tabon tsoron Malik da ya kwana da shi washe gari ya ɓace na dawowa sabo fil, idanuwansa ya kulle gam kamar mai barci.

Ido Malik ya lumshe kafin ya saki murmushin da sam bai masa kyau ba saboda bai saba ba, da iya ganin fuskarsa kaɗai zai iya kawar da Sufyan a doron ƙasa ta hanyar bugawar zuciyarsa. Amma Yaron tausayi yake bashi bai san komai ba sai abinda suka ɗorasa akai, ya jima da karantar Sufyan shi ba faɗan kawar da wani ne a gabansa ba, shi dai burinsa ya zama kyakkyawa ya tara kuɗi shima ya zama Dhahab ɗin kansa kamar yadda suke sauraran duk wa su hirarrakinsa ta offishinsa har ma da Gidan da yake kwana.

Da buɗaɗɗen muryarsa mai nauyin dake amsa amo da ya dace da kalar siffarsa Malik ya ce "sannu da Jiki Sufyan Ɗayyib Jalal, Allah Ya ƙara afuwa, ga colleague ɗina Uzair ku gaisa" ya ƙarasa faɗa yana nuna Uzair.

Sufyan daya kasa gaishesu da sunan ya na barci, kuka ya fasa idanuwansa a kulle, kansa a can gefe. Hannuwansa biyu ya haɗa waje ɗaya ya ɗagashi can sama dai-dai saitin su alamar roƙo. Tsabar kukan da yakeyi kafaɗunsa da ko ina nasa rawa yakeyi.
Malik miƙewa yayi zai fita saɓanin Uzair da ya tsaya kallon Sufyan da mamaki. Da taushin Muryar da sam baya kama da na Salman yake tambayarsa da yaren ƙasar Abyad

"maiyasa kake kuka?"

Damacan Sufyan ba wani sanin Murya Salman ya yi ba balle ya tantance.
Sufyan bai amsa ba still yaƙi kallon gefen da Malik ya bar Uzair a tsaye.

Sufyan na jin Muryar likita ya ɗan saki ajjiyar zuciya sai dai ƙara jin Muryar Malik a bayansa ya sa ya sume kansa ya karyo kamar zai faɗo daga kan gadon.

Hannun Malik Uzair ya ja suka fito waje.

Da fuskar tausayi Uzair yake tambayar Malik wanene Sufyan? Maiyasa yake jin tsoron da ya ke sashi sumewa idan ya gansu?

"Yankin Tudu, Babban ÆŠa namijin ÆŠayyib Jalal" Malik ya faÉ—a yana kallon Diamond Bracelet É—in hannunsa.
Wayar Uzair ne ya faÉ—i kasa a take gilashin baya da na gaba yayi kwatsa-kwatsa.

Dariyar muguntar da ba kasafai Malik ya fiye yi ba yasa ya na kama hannun Uzair da ya sanƙame a tsaye. Wayarsa ya sunkuya ya ɗaukarmai suka bar wajen.

Sufyan sai da ya yi kwana biyu yana fama da zazzafan zazzaɓi jininsa har hawa ya yi, baya iya ɗaga kiran kowa, da zarar ya ji motsin ƙofa gabansa yake faɗuwa, hankalinsa baya dawowa jikinsa har sai yaga wanda zai shigo.

Likita ne ya zaunar da