Showing 27001 words to 30000 words out of 111837 words

Chapter 10 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

ya kore mu sannan duk kayan aikin mu na gidan an 'kone mana, sun lalata mana asiri yanxu ya dawo hankalin sa, a cewar sa ma bai san muna gidan ba duk xaman da muka yi"




salati Habi ta fara yi
"Kai amma wad'annan mutane an yi masu kwasasshiyar albarka, sun cuce mu, yanxu ina muka ga kud'in komawa a 'kara yi mana wani abin, amma ya xama dole mu d'auki mataki, ni dai ko xan tafi tsirara sai na dawo da hankalin Mudi kaina, kuma sai Magaji ya koma birni, ke kuma sai ki nemi mafita idan xaki bayar da Akuyar ki a siyar to, idan kuma kina ganin baxa ki iya ba, sai na nemar wa 'ya'yana su kadai.


shiru Innah karime tayi tana naxarin maganar Habi, sai da aka d'auki lokaci mai tsawo sannan ta bata amsa
"sai na bayar uwar Audu in dai bu'kata xata biya"


kwanan su uku a 'Dan batta suka fara gane kuskuren su, duk yanayin su ya canja, saboda canji abincin da suke ci,da muhallin da suke rayuwa, wannan dalilin ya 'kara harxu'ka xuciyar su wajen baxama neman maganin da xasu mallake mahmoud da iyalansa.




A 6angaren Hamdan kuwa mahaifiyar sa ce, ta matsa masa a kan dole ne ya je gidan su Ajmal ya ganta, su kuma dai-dai ta a kan maganar auren su, danne xuciyar sa ya yi ya amsa bu'katar ta, don haka bai tsaya yin wata kwalliya mai kyau ba, yana fitowa ya had'u da maminsa, kallon shi tayi sama da 'kasa ta ga ba wani kwalliya yayi mai kyau ba, why are you wear this shabby shirt Hamdan?oya yi maxa ka canja ta,kafin raina ya 6aci, tafiya yayi ya canja wasu, sannan ya fito ta ganshi ta yaba da kwalliyar da yayi sannan ya fita ya d'au mota.


kai tsaye gidan su Nauwar ya isa, yau a waje ya tarar da su suna ta hira ita da fu'ad, yana yin parking ya fito ya tsaya, yana kallon su kamar mai tunani, yaran suna matu'kar burge shi sun sha'ku da junansu kamar tagwaye,Nauwar ce ta hango shi da gudu ta 'kara so inda yake xata rungume shi ya ja da baya.
murmushi yayi mata sannan ya fara mata magana.


"dearna kinga kin fara girma ki daina cewa xaki rungume ni, kin ji ko 'yar kanwata"


gyad'a kai tayi alamar eh,
"Yauwa yaya ina ta son dama na ganka fu'ad He's been gossiping about you"


Hamdan na jin haka ya matsa gurin da fu'ad yake ya ja kunnen sa, "Gulmana ka ke yi ko aboki, daga yau mun 6ata"


'Yar kara Hamdan ya saki "Allah yaya ba gulmarka nake yi ba, naga kwana biyu baka le'ko bane, shi ne na fad'a mata ko Magaji ka ke jin tsoro, shi yasa baka le'ko mu ba.
dundu ya sakar masa a baya,
"baka ji abokina mun yi fad'a daga yau" yana maganar yana 'yar dariya.
"kayi hakuri yayana na tuba"
"to naji ku wuce ku shirya xaku min rakiya wata 'yar unguwa"
gaba d'ayan su suka wuce suka fara shirin raka Hamdan, shi kuma ya shiga ciki don gaisawa da Ammin Nauwar.










*Jeeddahtulkhair*😘
08094136204
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


maijiddatijjaniadam@gmail.com




*β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†




3⃣1⃣






Hanyar gidan su Ajmal suka kama, wanda kuma kusa yake da gidan su Hamdan, yana xuwa aka bud'e masa gate ya shiga, 'kaninta ne ya hango Hamdan har 'kasa ya tsugunnah ya gaida shi, sannan ya yi masa jagora har wajen da xa su yi xance da yayar shi.
cikin gida ya shiga ya sanar mata da xuwan Hamdan, saboda ko number wayar ta ba shi da ita. kanta sai rawa yake yi ita da mamanta, abinci na musamman aka girka masa, sannan aka bawa yaron ya kai musu, nan da nan she had her new gown on, ta hau gyaran fuska sai da ta kwashe kusan 1hour tana abu d'aya, har sai da Hamdan ya gaji da xama He is pacing up and down waiting, saboda baya jure zama da yawa.




wata siririyar murya suka ji tayi sallama, gaba d'ayan su suka mayar da kallon su gareta, tafe take tana rangwada har ta iso inda Hamdan yake, daf dashi ta xauna kamshin turarenta yana dukan hancin shi,su kuma su Nauwar suna gefe, wani irin d'inki ne mara fasali a jikinta,wanda sai da rabin breast d'inta suka bayyana a waje, d'an mayafi kawai ta yafa wanda ya tsaya iya wuyanta, Hannun shi ta kamo gami da rungume shi, saurin janye jikin shi yayi daga gare ta. tambayar shi tayi cikin sigar rashin jin dad'in abinda yayi mata.
" me yasa xaka janye jikinka ko baka son mu gaisa ne" tana maganar tana ya mutsa fuska


"irin wannan gaisuwar taki ba gaisuwa ce ta yara masu tarbiyya ba, don haka bana son ki 'kara min haka"
tashi yayi tsam ya bar mata wajen


kallon su Nauwar tayi ta yatsina fuska.


"Wad'annan yaran kuma daga ina? nasan dai ba 'ya'yan gidan ku ba ne, gaskiya xan fad'a maka ban so kana xuwar min da yara ko abokai, kai kad'ai nake son gani"


ranshi a had'e ya mayar mata da martanin maganarta
"yaran nan cousin's d'ina ne, mun sha'ku da su bama rabuwa, tare kika ganmu,haka xaki yi ha'kuri na ri'ka xuwa da su, kuma ni ba xance naxo ba, dama mami ce tace naxo mu gaisa saboda xumuncin mu ya 'kara 'karfi, ina fatan kin ji dad'in wannan xiyarar da na kawo miki.


mi'kewa tsaye yayi yana kallonta.
"to ni xan wuce ki gaida min da su Hajiyar"


bai tsaya jin amsar da xata bashi ba ya fice daga d'akin ya barta.
takaici ne ya mamaye xuciyarta,ta rasa ina xata sa kanta, a matsayin ta na budurwa mai ji da kanta, a ce Hamdan ya xo ya wula'kanta ta, duk 6ata lokacin da tayi wajen ganin tayi kwalliya don ta faranta masa amma duk hakan bai burge shi ba, cikin gida ta koma d'akinta ta bud'e ta shiga, kan gado ta fad'a tana ta xubar da hawaye, wayar ta ta d'auka ta kira 'kawarta Haseenah


cikin kuka take mata magana,
"my Hasee ki yi sauri kixo akwai matsala, dan Allah ki taimake ni kada kiyi delaying wajen xuwa ki ji matsalata"


"gani nan xuwa but ina Aminu kano teaching hospital naje duba mujaheed amma ki jira ni xan xo yanxu"


Ba a fi 5minutes ba Haseenah ta 'karaso gidan su Ajmal, tarar da ita tayi ta sha kuka har ta 'koshi,idanuwanta sun yi jawur, tambayar ta abinda ya sameta tayi.
ta kwashe labarin abinda ya faru tsakaninta da Hamdan, ta gaya mata.
kallon ta Haseenah tayi tana hararta.


"Kema dai kina da matsala Ajmal kin san da cewa, ko kin samu miji 'yan kungiyar mu baxa su ta6a yarda kiyi aure ba, banda ma tsabar da'ki'kanci irin naki mu da muke da hanyoyin biyawa kan mu bu'kata, ina ruwan ki da wani namiji, da har xai 6ata mik rai, ki ri'ka takaici da xubar da hawayen ki a kansa, tun wuri ki cire tunanin sa a ranki,tun kafin uwar gida taji labarin kina kula maxa"


shiru tayi tana kallon Haseenah, sannan ta share hawayenta ta fara yi mata magana.
"wlh my hasee na gaji da harkar nan, so nake yi nayi aure na tattara hankalina guri guda, saboda wannan hanyar da muka d'auka ba mai 6ullewa bace, shikenan haka xamu xauna shekarun mu suna nisa ba aure, ko don kada duniya ta xage mu ai gara mu yi auren mu mu huta"


A gurinki ne dai kike ganin bata 6ullewa,shekarar mu nawa muna yi, gamu nan ba abinda ya same mu, idan xaki cire xancen wani banxan namiji a ranki ki cire, idan kuma ba haka ba hawan jini ya kamaki"


"To naji 'kawata amma xan yi naxarin maganar ki don wlh ina son Hamdan,kuma muddin na aure shi na bar wannan harkar har abada ko kashe ni xa a yi, sai dai a kashe ni"


"To ai sai ki yi 'yar wahala"


Haseenah ce ta jawo Ajmal ta manna bakinta da nata, suka fara sa6awa Allah kamar yadda suka saba, Haseenah bata bar gidan su Ajmal ba sai bayan sallar magrib.


*******************


Hamdan na barin gidan su Ajmal, ya je ya mayar da su Nauwar gida, ran shi duk a 6ace yake, saboda ri'ke mishi hannun da ajmal tayi, idan da abinda ya tsana a rayuwar shi, bai wuce ta6a jikin matar da bata halatta a gare shi ba.


Nauwar ce ta tambaye shi
"yaya why are you frowning?
murmushin 'karfin hali ya yi
"ba komai kanwata"


"Allah ban yarda ba yaya ka fada min abinda aka yi maka,ko nice na 6ata maka rai"


He pursed his lips sannan yace mata
"ai ba kya laifi my dear, wannan mara tarbiyyar yarinyar ce ta 6ata min raina, ta xo tana min wani swaggering a gabana, hakan ma bai isheta ba sai da ta kama hannuna, gata da wulakanci, sannan ta saka wasu skimpy dress, ko gani take xata burgeni oho, dama ni tun farko na fad'awa mami baxan je ba, don naga tayi fushi ne kawai naje"


"Ai gara da kaje yaya nima ban so ka 6atawa mami rai"
"ai tunda naje na d'aya baxan je na biyu ba, na gama xuwa"


sallama suka yi shi kuma ya wuce gida


Wani ba'kin ciki ne ya mamaye xuciyar Nauwar, ta rasa me take ji game da Hamdan,son shi take yi, ko kuma kishin shi take yi a matsayinsa na d'an uwan ta, wajen Ammi suka shiga suka sanar da ita dawowar su.




*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




maijiddatijjaniAdam@gmail.com


*β™»EXCLUSIVWRITER'S FORUM*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*Yau shafin gaba d'aya naki ne uwar gida ran gida, gugan 'karfe sha gwagwarmaya, murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, kainuwa dashen Allah, Carbin 'kwai mai wuyar ja, uwar gida kuma Amarya a gidan BARRISTER HAJIYA RUKAYYA SANI, Allah ya barki da angonki Allah ya kara muku soyayya da 'kaunar juna, JEEDDAH tana yin ki, kuma ana tare irin mugun sosai d'in nan*🀝




3⃣2⃣






*A* haka Nauwar ta kwanta bacci xuciyarta cike da kishi gami da kewar Hamdan.


washe gari ma tun safe a d'aki ta wuni, Amminta ce ta lura da halin da take ciki,don haka ta yanke shawarar shiga gurin d'iyar tata don ta ji matsalarta,shiga d'akin da Nauwar take tayi, tarar da ita tayi ta had'a kai da gwiwa ta xuba uban tagumi.


"lafiyan ki Nauwar, me yake damun ki naga tun jiya babu walwala a tare da ke?"
"Babu komai Ammi ban jin dad'in jikina ne"


"Ayyah!! Allah ya baki lpy ki sha magani, ki shiga kitchen ki duba min idan stew d'in nan ya yi ki sauke"


"To Ammina"


tashi tayi ta d'auki maganin ta 6oye a hannunta saboda tasan cutar ta ba ta magani ba ce, kitchen d'in ta shiga ta fara aikin da Amminta ta sa ta, tunda ta shiga wani tunanin ya dad'a mamaye xuciyarta, yanxu a ce duk yadda take jin ya Hamdan a ranta da yadda ta sha'ku da shi, ashe baxai xama mallakinta ba,gurin wata xai je da niyyar aurenta, hawaye taji yana kwarara a kan Fuskarta.


"Nauwar"!!!!
taji an kira sunanta, da sauri ta juya.
Ammi ta gani tsaye tana salati.
"yanxu don Allah tunanin me kike yi da har kika bar miyar nan ta fara kamawa, kinsan dama tunanin xa kiyi kika kar6ar min aikina da sai ki barni nayi da kaina, 'kaurinta na jiyo na fito, ashe ma kina kitchen d'in kina aikin tunanin da kika saba ko?
"Allah ba tunani nake yi ba Ammi sha'afa nayi"


"kina son mayar da ni 'karamar yarinyar Nauwar, tunda na riga na haifeki ai babu abinda xaki 6oye min game da ke, nasan farin cikin ki, na kuma san damuwar ki, xo nan ki fad'a min abinda yake damunki"


'Daki suka shiga tayi tambayar duniya, ta'ki fad'a mata gaskiyar abinda yake damunta, sai haka ta kyaleta.


Su Innah karime ne xaune suke ta 'kullawa da kwancewa, game da yadda xa su yi, su koma birni su cigaba da rayuwa mai dad'i.


"Audu ne ya shigo wuyan shi rataye da fatanya, sallama ya yi sannan ya samu guri ya xauna.
gaishe da su innah karime yayi, sannan ya yi 'yar gyaran murya.




"Innah wai a ina aka kwana ne, game da zuwa gurin Bokan nan, idan fa muka yi shiru muka sa ido, abin nan xai yi ta mi'kawa ne, kin ga fa tun da ku ka dawo yaron nan bai xo da niyyar baku ha'kuri, ko nuna nadamar wula'kancin da yayi muku ba, a matsayin sa na jikanki.




"Hmm Audu kenan, Ai Mudi tuni ya dad'e da xama d'an kansa Audu, matar sa ta lalata shi, baya son yan uwan sa, ubansa ne kawai yake yake morar arxi'kinsa mu kuwa baya ta tamu, an ci gari da mu,an barmu da kuturun bawa, yanxu haka ma rashin kud'i ne ya hanani komawa wajen gobe da nisa, amma Allah yana warware min matsalar garin nan xan koma.
hannu Audu yasa a aljihu ya fara laluben 'yan canjin da suka rage masa


"yanxu haka akwai 'yan kud'ade a hannuna innah, xan ba ki,ki fara ajiye wa, saboda lamarin nan sai an shirya sosai, Bokan nan baya aiki a kan kud'ad'e kad'an".


wasu tsofaffin kud'ad'e ya mi'ka mata, wad'anda baxa su wuce naira d'ari biyu ba. da fara'arta ta mi'ka hannu ta kar6a, tana masa godiya.


A lokacin suka yanke shawarar siyar da kadarorin su, da 'yan kayayyakin da suka mallaka, don su ji dad'in yin asiri son ran su.


Hamdan ne sunkuye gaban mahaifiyar shi, ya kasa cewa komai,saboda fargabar da ta cika xuciyar shi, shirun da ya yi yawa ne,yasa maminsa ta fara yi masa magana.


"Wannan dunkufen da kayi,kamar me neman gafara na menene Hamdan?"


shiru yayi ya kasa bata amsa, saboda bai san da wace irin kalma xai yi amfani ba, wajen bayyana mata abinda yake ransa.


'kara tambayar shi tayi


"kai fa nake sauraro Hamdan"


"wlh ina fargabar fad'a miki abinda yake damuna ne mami, ban san da wace fuska xaki kalli abin ba"


"Fad'a min d'ana ai baxan so matsala na damuna ka, ka 'ki fad'a min ba, duk duniya kai kad'ai na mallaka a rayuwata, ta yaya xan so 6acin ranka,"


wannan maganar ita ce ta sanyayawa Hamdan rai, ya kuma ji 'karfin gwiwar sanar da ita abinda yake ransa.


"Mami dama so nake na sanar da ke,don Allah don sonki da Annabi,a bar maganar aurena da Ajmal, wlh yarinyar sam bata dace da tsarin rayuwata ba, tarbiyyarta bata yi min ba, a jiya ma na 'kara tabbatar da hakan, ina xuwa ta mi'ka hannunta ta rungume ni, ni dai don Allah kiyi min rai, kada ki bari na aureta, kowane namiji burin sa ya samu mace ta gari, wacce 'ya'ya na gari xasu fita daga jikinta,yanxu idan na aureta yaya kike tunanin tarbiyyar yarana, nasan ke ma xa kiyi alfahari, idan na samu mace ta gari mai tarbiyya da addini, don Allah ki duba maganata da idon basira mamina"


ya 'karasa maganar yana kuka.


Numfashi mami ta sauke sannan ta fara magana
"na gamsu da maganganun ka Hamdan, nima nasan halin yarinyar wayewarta tayi yawa ta wuce misali, na amsa bu'katar mahaifiyarta ne, saboda kada taga na watsa mata 'kasa a ido, na yarda ka nemi duk yarinyar da kake so, amma da sharad'i,nan da sati biyu nake son ka xo min da magana mai kyau"


wani dad'i ne ya kama Hamdan,jinshi yake kamar wanda aka yi wa bushara da aljannah.


"Na gode, na gode mami, Allah ya saka da alkhairi Allah ya ja da ranki, insha Allah xan yi yadda kika ce"


tashi yayi ya shiga d'aki xuciyar sa cike da nishadi da farin ciki.










*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


maijiddatijjaniAdam@gmail.com




*β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*Sadaukar wa gareki MARIYA ABDULLAHI YAQUB (mariyar makkah) Amaryar gobe😜idan Allah ya so, Allah ya nuna min auren ki mu sha shagali*


*Asha rawa rawa,πŸ’ƒ mata a sha rawa, ku sha sha'aninku duniya ce, ku sha sha'aninku 'kawayena, yasin ina yinku 'yan Almajira fans, muna mugun tare*🀝






3⃣3⃣






Yana shiga d'akin ya tarar da wayar shi na ta faman ringing, hannu yasa ya d'auketa, ba'kuwar number ya gani,don haka ya yi wurgi da ita gefe guda, kasancewar baya d'aga number dai bai sani ba, harkokin gaban shi ya cigaba da yi, 'karar wayar ne ya hana shi cigaba da abinda yake yi, don haka ya mi'ka hannu ya d'auketa,15 missed calls ya gani, mamaki ne ya kama shi.
"Wanene yake ta kirana haka"?ya tambayi kan shi


yana shirin bin kiran ne aka sake kira, da hanxari yayi picking, ya kara wayar a kunnen shi


shiru yaji an yi ba tare da an ce komai ba, shi ma dai shirun yayi, da yaga ba a da niyyar cewa komai, shi ne yayi 'karfin halin yin magana.


"Hello"
wata murya yaji ta yi magana.


"ka taimaka min, ka tallafi marainiyar xuciyar da bata san komai ba sai soyayyarka,tun bayan rabuwar mu da kai, xuciyata ta shiga 'kunci gami da kewar rashinka, kai taimake ni ka dawo gareni,don Allah kada ka rabu da ni, duk yadda kake son na koma maka, xan yi biyayya a gareka, ka tallafawa rayuwata don Allah"
aka 'karasa maganar da kuka mai tsanani.


mamaki ne ya kama shi, ko a ina Ajmal ta samu number shi? rasa amsar da xai bata yayi, duk ta 'kulle masa tunani.


jin ya yi shiru ne,ta cigaba da yi masa magiya, tana kuka tana ro'kon shi ya yafe mata idan laifi tayi masa.


"Baki min komai ba, sai dai akwai banbanci mai yawa tsakanina da ke, bana son irin rayuwar ki sam yanayin halayyar ki bai min ba, kuma a gaskiya baxan iya xama da ke a matsayin uwar 'ya'yana ba,sai dai xamu cigaba da gaisawa a matsayinki na 'kanwata" kashe wayar ya yi ya 'kyaleta.


wani irin ihu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login