Showing 102001 words to 105000 words out of 111837 words
Chapter 35 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
xuciyarta take so ta kuma saba da shi, ni kuma duk abinda yarinyar nan take so wlh ina son sa saboda tamkar 'yata ta cikina na dauketa"
"Haka ne Alhaji nima nasan da haka, amma ni a tsarina a kuma yadda na dauke ku, yanxu babu abinda xai sa ku nemi alfarma a gurina nayi watsi da ita, baxan iya hana danka abinda yake so daga wajena ba, saboda haka ne ma nake so a yi maslaha, ko yarinyar nan tana so ko bata so haka xa a yi, Hamdan ya nemi saimah su dai-daita, shi kuma sadeeq ya auri Nauwar haka na yanke"
wani farin ciki ne ya xiyarci xuciyar ya sadeeq ji yayi kamar an yi masa albishir da aljannah, duk ya nemi damuwar da ke xuciyarsa ya rasa.
saurin dakatar da Abban nauwar Abba yayi.
"Aa baxa a yi haka ba Alhaji a bawa yara abinda suke so, mu so muke Yi, su yi aure su xauna lafiya ba so muke su yi mana jeka ka dawo ba, don gaskiya baxan yarda da wannan hukuncin naka ba domin ina son farin cikin diyata, baxan bari a yi mata auren dole ba kawai saboda a farantawa sadeeq,ko yanxu na gani da idona yaran nan suna son junan su,ba karamar matsala xa a samu ba idan aka ce xa a farraqa tsakanin su, shi sadeeq din yayi hakuri mana tunda tun tuni bai yi magana ba, kaje kayi tunani sosai a kan wannan maganar tawa, abinda ka yanke sai mu yi magana ta waya"
Ba karmin haushi ya sadeeq yaji ba, da Abba yaki karbar kudurin Abban nauwar, haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar amma sam Abba yaki yarda a bawa nauwar ya sadeeq, basu bar gidan ba sai da suka yi sallar la'asar sannan suka tafi, ita kuma saimah a nan suka barta saboda xata karasa hutunta na makaranta.
*Jeeddahtulkhair😘*[9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
9⃣5⃣
A ranar da su Abba suka koma kaduna bacci mai dadi yaya sadeeq yayi, don har mama sai da ta lura da yadda yake cikin farin ciki ya saki ransa ya daina xama cikin Kadici, addu'a ya rika yi Allah ya tabbatar da alkhairin da ke cikin auren su da nauwar.
Su Nauwar ne xaune a falo tare da su Ammi da mama tana basu labarin irin gararin rayuwar da suka shiga kafin su hadu da gidan su saimah, da irin abubuwan da Ammi ta rika yi a lokacin da take cikin rashin lafiya, sai a lokacin take fada mata sharrin da su innah karime suka yi mata cewa ita ta kashe fu'ad.A daidai lokacin Abbanta ya shigo tare da Abban Hamdan xaunawa suka yi aka cigaba da hirar da su, ba karamin tausayawa junan su suka yi ba bisa halin da suka fada a baya, a lokacin Abban Nauwar yake sanar da su cewa sun kusa komawa gidan su sbd an kusa kammala musu ginin da ake yi.
ba karamin farin ciki Ammi tayi da jin hakan ba, cigaba da bada labari Nauwar tayi wajen tausayi su tausaya human su wajen dariya kuma a hadu a yi dariyar tare, har suka xo daidai wajen da take basu labarin xaman su a gidan su doctor Abdallah da irin gallaxawa da cin xarafinsu da Hajiya take yi ita da yayanta, tunowa tayi da complement card din da doctor Abdullah ya bata, da alkawarin da tayi na nemansa a duk lokacin da ta samu iyayenta, da sauri ta tashi ta shiga daki ta bude jaka ta xaro card din.
Karasowa kusa da Abbanta tayi tare da mika masa card din, cikin sassanyar murya take masa magana.
"Abba wannan shi ne mutumin da ya tausaya mana ya kula da mu kamar yadda aka yi mana a gidan su saimah, Shi ne mutum na farko da ya taimaka mana dan Allah ba dan wata manufa ba, sai dai mahaifiyarsa tafi karfinsa domin ita ta kore mu daga gidan, saboda a tunaninta wai mun mallake mata d'a yana ta yi mana wahala"
Hannu biyu yasa ya karba
tsayawa yayi ya duba katin sosai, dagowa yayi ya kalleta yana maimaita sunan da ke rubuce a jikin katin .
"Abdallah Sani fataskum!!!!!"
sake dubanta yayi
"Wannan mutum shi ne ya taimake ku? "
Gyada kai tayi alamar eh
"to ai wannan yaron 'kani ne a gurina, ku ne dai baku san shi ba, tunda bama xiyartar juna, mahaifinsa Alhaji sani fataskum, dan uwan mahaifiyata ne, muna xumunci da mahaifinsa sosai yana xuwa gidan mu wajen Baffa,nima a da ina xuwar masa xiyara sai bayan ya rasu alaka ta yanke kasancewar matarsa ba tada kirki bata son kowa ya rabe shi, baxan yi mamaki ba dan kun ce an yi muku haka a gidan su, xasu aikata fiye da haka ma, don wannan kadan ne daga irin mugun halin uwar su"
Hannu yasa a aljihu ya ya shiga lalubo wayarsa, copy na lambobin da ke jikin katin yayi sannan ya fara kira, cikin sa'a kuwa bugu daya aka dauka, da sallama ya fara magana
cike da tausasawa aka amsa sallamar.
bayani Abban Nauwar ya fara yi masa.
"kana magana da dan uwanka daga kano garin dan batta"
murmushi doctor yayi.
"masha Allah naji dadin kiran nan naka, kamar dama kasan ina nan ina fafutukar neman yan uwan mu na kano amma fafur Hajiya ta hana adress, amma dan Allah kayi Hakuri ban gane muryar dan uwan nawa ba"
"kana magana da Mahmud nasan kafi sanina da Mudi ko"
cikin farin ciki ya amsa tare da yin takaitaccen murmushi
"kwarai kuwa, ya gida da yara"
amsa masa yayi da lafiya lau, sannan ya fara yi masa godiya da abin arxikin da ya yiwa su Nauwar.
"ina godiya sosai da abin arxikin da ka yiwa iyalina Allah ya saka maka da alkhairi"
cike da mamaki yake tambayarsa
"iyalinka kuma?? yaushe na taimake su"
murmushi Abban Nauwar yayi.
"nasan ka manta sbd an dauki Lokaci mai tsawo da faruwar hakan, idan baka manta ba akwai wata mahaukaciya da wata yarinya da ka taimakawa ka kaisu gidan ku, ka fara canja musu rayuwa daga bakin ciki xuwa farin ciki, sai da wani dalili yaxo ya gifta sannan ku ka rabu, to wannan mahaukaciyar mai dakina ce, ita kuma yarinyar Nauwar 'yata ce"
salati doctor ya fara yi.
"ikon Allah ashe ma yar uwata na taimakawa, wlh na tausayawa halin da suke ciki a lokacin shi ne ma yaja hankalina har na kai su gida saboda basa cikin kwanciyar hankali, amma dai yanxu mara lafiyar taji sauki ko?"
"Taji sauki har sun dawo gida dama haukan ba nata bane hadata aka yi da shi amma yanxu komai ya dawo daidai, yanxu muke mayar da maganar sai Nauwar ta tuno da card din da ka bata ina dubawa naga sunanka a jiki nace baxan iya jurewa ba har sai na kiraka na gode Maka Allah ya saka da alkhairi"
ba karamin dadi doctor yaji ba da Allah ya mayar da su nauwar kyakkyawan hannu dama kullum addu'ar da yake yi musu kenan, tunda suka rabu da su bai taba shiga farin ciki irin na yau ba sbd tunda suka tafi bai kara ji Ko ganin mai kama da su ba. magana ya cigaba da yiwa Abban Nauwar
"ina nauwar din take idan tana kusa bani ita mu gaisa"
mika mata wayar yayi suka fara gaisawa.
"sannu Nauwar ya bayan rabuwa"
A ladabce take amsa masa maganarsa, bayan sun gama gaisawa ne ta mikawa Abbanta wayar suka yi sallama.
Hannu doctor ya daga sama yana godiya ga Allah, a lokacin ya dauki mukulli ya yiwa motarsa key sai gida a falo ya tarar da hajiya da kannensa suna hira, labarin yadda suka yi da Abban nauwar ya shiga bata
"oh!!! amma wlh naji kunya ashe yar ma tamu ce,nayi musu wannan korar karen yanxu da wane ido xan kalli ubanta wlh nayi nadamar abinda nayi musu, shi yasa ba a son wulakanta dan Adam baka son ko wanene shi ba, Allah yasa dai yarinyar nan bata fadawa ubanta irin cin mutuncin da muka yi musu ba"
tashi doctor yayi ya bar hajiya tana ta subadi duk ta shiga damuwar rashin mutuncin da tayi musu.
A kullum sai doctor ya kira Abban nauwar sun gaisa yanxu xumuncin su ya kara karfi sosai, ita kuwa Hajiya don kunya taki yarda a bata Abban nauwar su gaisa.
*jeeddahtulkhair😘*
[9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
9⃣6⃣
Haka rayuwar su Nauwar ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, rayuwa mai dadi suke yi a gidan su Hamdan, a dan xaman da saimah tayi a gidan su Hamdan ba karamin sabo suka yi ba saboda shi mutum ne mai son mutane da saukin kai, tsakanin nauwar da Hamdan kuwa suna gudanar da soyayyar su cikin kwanciyar hankali.
wayar da ke gefen Abban Nauwar ce tayi ringing hannu yasa ya dakko tare da kara wayar a kunnensa, cikin sakin fuska ya ambaci sunan mai kiran.
"Sadeeq barka da yau, ya ku ka je gida" cikin ladabi ya amsa da lafiya lau.....
shiru yayi na wani dan lokaci Abba ne ya katse shirun tare da cewa.
"Da alama kana cikin damuwa Sadeeq ka fada min duk abinda yake damunka"
shiru yayi ya kasa cewa da Abban Nauwar komai sai da ya sake maimaita masa tambayar sannan ya saki ransa ya fara magana"Abba a kan maganar nan ne da muka yi game da aurena da Nauwar naji shiru baka ce komai ba, Abba ma kuma bai ce min komai ba"
Sauke ajiyar xuciya yayi sannan ya fara yi masa bayani.
"haka ne Sadeeq nayi shiru da maganar ne sbd ina dan son na gama wasu shirye-shirye, amma yau Insha Allah xan samu Nauwar din nayi mata magana duk yadda muka yi da ita xan fada maka"
godiya mai yawa ya Sadeeq ya yiwa Abba sannan suka yi sallama xuciyarsa cike da farin ciki.
A lokacin ya shirya ya nufi gidan su Hamdan don sanar da Nauwar abinda yake son fada mata, a sitting room ya xauna inda ya kira Ammi ya sanar da ita yana son ganin su ita da Nauwar, bai fi minti biyu da fada musu ba suka karaso wajensa, A xaune suka same yana jiran isowarsu, kujera Ammi ta samu ta xauna ita kuma Nauwar ta xauna a kasa, cikin ladabi ta gaida Abban nata, sannan suka gaisa da Ammi bayan sun kammala ne ya fara magana.
"Nasan xa ku yi mamakin kiran ku da nayi gaba daya, ina so mu yi magana ne a kan auren Nauwar"
gaba daya suka bayar da hankalin su gare shi, gaban Nauwar kuwa sai dukan uku-uku yake yi.
gyaran murya yayi sannan ya cigaba da magana.
"Na duba naga babu wanda ya dace ya auri Nauwar sai Sadeeq saboda irin taimakon da iyayensa suka yi mana, kuma ya nuna yana son yarinyar nan idan har muka ce baxa mu bashi ba ina ganin mun yi butulci"
A xabure Nauwar ta dago ta kalli Abba, fuskarta ce ta canja daga farin ciki xuwa bakin ciki, Ammi ta lura da yanayin da yar tata take ciki, ita kanta bata ji dadin hukuncin da yayi saurin yankewa ba tafi son a shawarci yarinyar a ji abinda xuciyarta ta amince da shi.
katse shirun da suka yi yayi,
"wannan shi ne xabin da nayi miki Nauwar kuma ina so ki xama mai biyayya a kan haka, shi kuma Hamdan xan same shi na fada masa yaje ya nemi auren Saimah"
wani hawaye ne ya fara xubowa Nauwar, a hankali ta lallaba ta tashi ta bar dakin, tana xuwa dakin da suke ta samu saimah na ta sharar bacci wannan yasa ta samu damar yin kuka son ranta, Nauwar na fita Ammi ta dubi Abba.
"A ganina bai kamata a yiwa yaran nan haka ba, nasan kasan tsayin shekarun da suka shafe suna son junan su, idan aka ce xa a raba su lokaci daya an xalunce su"
fada ya hau Ammi da shi.
"Haka na yanke haka kuma xa a yi, sai dai idan ke xaki xugata ta bijirewa abinda nake so"
Sake duban shi tayi
"yana da kyau kayi dogon naxari a kan wannan hukuncin naka, idan aka yiwa nauwar haka Ina ganin ba a yi mata adalci ba idan ka duba tsawon shekarun da ta dauka cikin bakin ciki da kuncin rayuwa, yanxu fa ta fara dandana dadin duniya sannan kuma a ce xa a kara sakata a halin bakin ciki, gaskiya ka duba wannan al'amarin da kyau" fadan ya cigaba da yi
ganin ya dau xafi ne yasa Ammi ta bashi Hakuri ta tashi a bar dakin.
A ranar ya samu Abban Hamdan suka tattauna a kan batun, shima dai bai ji dadin hukuncin da ya yanke ba sbd yasan irin soyayyarda ke tsakanin Hamdan da Nauwar.
washe gari da safe Abban Hamdan ya kira shi ya fada masa yadda suka yi da baban Nauwar ya kuma bashi hakuri a kan wannan babbar jarabawar da take shirin tunkaro shi.
Hawaye ne ya shiga fitowa daga idon Hamdan ta ko'ina idanunsa cike da kwalla ya dubi Mahaifin nasa.
"yanxu ya ake son nayi da rayuwata Abba duk tsawon shekarun da na dauka ina son yarinyar nan a ce baxa a bani ita ba saboda wani bare da yaxo daga baya" ya karasa maganar yana kuka mai cike da ban tausayi, dafa kafadarsa Abban nasa yayi yana rarrashinsa.
"kayi hakuri Hamdan xan yi iya bakin kokarina don ganin na shawo kansa Amma ni kaina banso hakan ba, Kaje ka cigaba da addu'a Allah ya xaba mana mafi alkhairi"
Tashi yayi ya bar wajen idanunsa a rufe yake tafiya, daki ya shiga ko xai ji saukin damuwar da ke damunsa, ji yayi yaci karo da mutum saurin dagowa yayi, ashe ya manta ba dakinsa ya shiga ba dakin su nauwar ya fada, ganinta yayi xaune a bakin kofa ta xuba tagumi tana ta faman sharbar kuka, a hankali ya ja kafa ya xauna daf da ita yana fuskantar ta, bude baki yayi xai mata magana Amma saboda tsananin kuka da bakin cikin da ya cika masa xuciya ya kasa magana, sun fi minti biyar a wannan halin sai da xuciyarsa ta dan yi sanyi sannan ya dubeta.
"Nauwar"A hankali ta dago ido ta dube shi, tayi mamakin jin ambatar sunanta da yayi kai tsaye ba tare da ya sakaya ba, saboda rabon da ya fadi sunanta kai tsaye har ta manta, wannan dalilin yasa ta bashi hankalinta sosai don tasan maganar da xai mata mai muhimmanci ce.
Kallonta yake ya kasa magana idanunsa sun kada sun yi jawur, karfin hali tayi ta fara yi masa magana..
"dearna ka kira sunana kuma kayi shiru, dan Allah ka fada min abinda yake damunka"
Sunkuyar da kanshi yayi bai iya cewa komai ba, sake maimaita masa tambayar tayi.
Cikin yanayin bakin ciki muryarshi na shakewa yake mata magana
"Ina cikin tashin hankali ana so a raba tsakanina da ke, a bawa mutumin da bai san muhimmancin ki gare ni ba, kwanana ya kare a duk lokacin da aka raba ni da ke, na tabbatar da cewa baxan samu mace kamarki ba, baxan taba son wata mace irin son da nayi miki ba, kisa a ranki daga yanxu xaki iya Jin labarin mutuwa ta a kowane lokaci, xuciyata baxa ta iya jure ganin ki Kina soyayya da wani ba ni ba"
Tashi yayi ya fita ya bar dakin kai tsaye dakinsa ya wuce, da sauri nauwar ta biyo shi tana masa magiya.
"ka tsaya ka saurare ni dearna wlh nima ba a son raina hakan xai faru ba har yanxu da soyayyarka a xuciyata kuma babu namijin da xan yiwa irin son da nake maka"
Juyowa yayi yana share hawaye yana Dubanta.
"na gode da soyayyarki gare ni, nima xan ji dadi idan kika yiwa Abba biyayya a bisa xabin da yayi miki, na miki uxuri nauwar nasan Kina sona kuma baki yaudare ni ba, kuma har yanxu ban fidda ran Ki xamo mata a gare ni ba, don haka ki share hawayenki, ki daina yi min asarar su ki adana min su har sai ranar da aka kawo ki gidana a matsayin matata nake son naga kin fitar min da su saboda farin ciki, amma akwai alfarma daya da xan nema a wajen Ki nasan kuma baxa Ki qi yi min ba"
Dago kai tayi "xan maka ko menene dearna "
Cike da tausayawa ya dubeta.
"Dan Allah ki nisanta da ni kinga Yanxu a matsayin matar wani kike, bai kamata na rika magana da ke a koda yaushe ba, yana da kyau mu fara koyawa kanmu rashin junanmu tunda mafarkin mu baxai cika ba" ya karasa maganar yana kuka, kulle kofar dakin ya yi ya fada gado yana kuka mai tsanani, a bakin kofar ta tsaya tana kuka tana shure-shuren kafa.
"me yasa xaka yi min haka Abba ka tausaya min ka bani xabin da xuciyata ke so, wlh baxan iya yiwa wani da namiji biyayya ba bayan Hamdan ka duba halin da xan fada Abbah ka taimake ni"
A gigice saimah ta fito daga daki ta tarar da nauwar a wannan halin dakin su Ammi taje ta sanar da su halin da take ciki, a sume suka tarar da ita cikin gaggawa suka dauketa sai Asibiti ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba, saboda taji abubuwan da nauwar ke fada tun tana bayi tana wanka sannan ta lura da walwalarta gaba daya ta canja, cikin damuwa take tambayar Ammi..
"Ammi wai me aka yiwa nauwar kuma me ake so a bata wanda bata so"
Murmushi Ammi tayi "ba komai saimah Kawai shirmen Ku ne na yara"
Xuciyar saimah bata amince da maganar Ammi ba don haka ta takura mata da tambaya amma taki gaya mata abinda ke faruwa, kyaleta tayi tare da yanke shawarar neman Hamdan taji abinda ke damun aminiyarta don shi ma ta lura da shi baya cikin walwala Kwana biyu.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
9⃣7⃣
A asibitin suka