Showing 63001 words to 66000 words out of 111837 words

Chapter 22 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

daga gidan nan,dan ni tsoron su ma nake ji baxan iya karasawa inda suke ba, kada naje su shake ni"


fatima ce ta taya Hajiya fadan da take yi.
"ni wlh idan har xasu xauna a gidan nan na daina kwana, sai sun tafi xan dawo, haka kawai muka sani ko mayu ne"


wani kallo doctor Abdallah ya watsa mata, nan da nan ta kama hanya ta bar falon, saboda tasan halinsa baya son raini.


rarrashin Hajiya ya shiga yi ta taimaka ta bari a bawa su Nauwar wajen kwana da kyar ta yarda, inda tace a basu wani daki da yake kusa da na mai gadi, kuma da sharadin sai an caje su an kwace kayan su, saboda kada su xo mata da abin cutarwa.


Cikin tsawa tayi wa su Nauwar magana
"bayin Allah sai a tasar min daga kan kujera kada a taho min da annobar kwarkwata"


jikin su a sanyaye suka mike, kofar fita daga falon suka nufa, xasu fita
ran doctor a bace ya dubi Hajiya


"Gaskiya abinda kika yi bai kamata ba, saboda Allah ya girmama dan Adam, mu ma ba wayon mu ko dabarar mu ce tasa Allah ya axurta mu ba"


ficewa yayi ya bi su Nauwar.


kuka Nauwar take yi sosai, saboda maganganun Hajiya ba karamin taba mata xuciya suka yi ba, hanyar fita daga gidan suka kama, dan ta kudurce a ranta ko xasu mutu saboda rashin gurin kwana baxa su xauna a gidan nan ba.


da sauri doctor Abdallah yasha gabanta,
"ina kuma xaki je"
cikin kuka ta bashi amsa
"xan fita daga gidan nan ne, dan xuciyata baxa ta iya jure wulkanci ba"


cikin tausayawa ya dubeta
"kiyi hakuri ni kaina da na san abinda xa a yi muku kenan da baxan kawo ku ba, ki sa a ranki wannan duk yana cikin jarrabawar da Allah yayi muku, kiyi hakuri ki daina xubar da hawayen ki, Allah yana sane da ke"


rarrashinta ya shiga yi, har sai da yaga ta dawo cikin nutsuwarta sannan ya nuna mata dakin da xasu shiga.


Fafur Nauwar taki shiga dakin tace sai ta tafi, da kyar ya shawo kanta ta shiga suka xauna.














*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*Dole na gode muku na kuma yaba da yadda kuke matukar kaunata, har ku ke kirana a waya dan jin lafiyata BINTA MUSA SALIS & UMMU SULAIMAN (Hasanatullah) ina matukar Allah ya bar xumunci*


*ku ma ban mance da ku ba yan uwa masoya kuma members na Al-majirah fans, ina matukar jin dadin comments din ku, kuma ina godia sosai*
Aisha Aliyu
ummu Hanash
juwaira lukman Amin
ummu sulaiman
ummy idris
Dr fateemah sabitu
feenah el sadeeq
Saadatu Ibrahim
zainab Abba sani (zainabi)
nanah firdausi
Princess Bilkisu Muhammad Zangi
marfu'a (amfu)
Abida
sumy
jamila bature
sumayya Ango Abdullahi
Haleema Ibrahim
sakinat Jibrin
Zahra'u Ado
Bilkisu muhammad
😊Meenert
maman ahmad
Maman twins
Badariyya Mu'az
Harfsart
Maman sahal
Ummu Khalifa
Maman jidda
Aysha s/fada(baby Hassan)
Maman Sudees
Surry Pinky πŸ’ž
Leemerh
Mamcy






5⃣8⃣




shigar su dakin ke da wuya, doctor ya shigo hannun shi rike da leda, kayan sawa ya kawo mata, da kuma kayan abinci, da sabulun wanka hade da kayan shafe-shafe, daga tsaye ya mika mata sannan ya fice saboda yana tsoron kada Hajiya ta gan shi tayi masa tijara, bude kayan ta shiga yi tana fito da su, farin ciki ne ya kamata, saboda rabon da taga irin wannan abin arxikin har ta manta,a jiye kayan tayi a gefe sannan ta dauki sabulu.
jawo kofar dakin tayi ta fito, dan tana jin tsoron ta barta a bude Ammi ta fito a ganta a waje su ci mata mutunci. mai gadi ta samu yana alwala a gefen dakin shi, tambayar shi tayi inda bandaki yake sannan ta roke shi ya bata aron bokitin wanka, nuni yayi mata da hannunshi sannan ya fada mata akwai bokiti a bandakin, cikin nutsuwa ta karasa tana daf da shiga ciki ne, taji tafiyar mutum a bayanta, waiwaya tayi don ganin wanda ya biyo ta a baya, ummy ta gani daya daga cikin kannen doctor tana watsa mata wata muguwar harara, tsayawa tayi ta karewa Nauwar kallon sama da kasa sannan ta fara mata magana.


"me xaki shiga kiyi a toilet din mu? daga xuwan ki har xaki fara cika mana shadda"


kan Nauwar na sunkuye saboda takaicin da ya cika xuciyarta ta maida mata da amsa, wanka xan yi.


xaro da manyan idanunta tayi gami da rike baki, kin xo xaki yi wanka ki goge kaushi, wato ki makalewa dan uwana ko, to wlh baki isa ba yaya babba ya fi karfin ki, kuma baki isa ki shiga wajen nan ba duk masifar ki. kwace bokitin ruwan tayi gami da jifa da shi gefe guda, ta bar Nauwar tsaye a nan tana tunani.


karasa wa wajen mai gadi tayi tana masa masifa
"daga yau sai yau, kada ka sake barin wadannan mahaukatan su shigar mana toilet sai sun shafa mana cutar hauka ko kuma sun kawo mana annobar ciwon sanyi, duk da bandakin ka ne, ban amince ka bar su suna shiga ba"


cikin ladabi da kaskantar da kai ya bata amsa.
"Insha Allah xan kiyaye Hajiya."


A dai-dai lokacin su feenah da zainab suka yi sallama, suna ganin Nauwar a tsaye suka ci burki suka tsaya, cikin mamaki ta dubi ummy.


"wannan kwashen kuma daga ina?"
ya mutsa fuska tayi sannan ta basu amsa
"yaya babba xaku tambaya don shi ne ya jajibo mana bala'i har cikin gida"
cikin masifa feenah ke magana tare da watsawa Nauwar wata shu'umar harara
"wai shi yayan nan me yasa yake mana haka ne, sai ya rika taro mana mutane a gida har da gayyar mahaukata, gidan nan fa ba gadon shi ne shi kadai ba, mu ma muna da gado, wlh yau sai wannan yarinya ta fita daga gidan nan dan baxai yiwu mu xauna da mahaukaciya ba" ta karasa maganar tana nuna Nauwar.


Ummy ce ta sake dubanta tana murmushin mugunta.
" to ai ke baki san wani abu ba, ba ita kadai ce mahaukaciyar ba har da mamanta suna cikin dan akurkin nan a nan aka sauke su"
bude dakin suka yi, lekawa suka sai da suka karewa Ammi kallo sannan suka kulle shi.


tabdi lallai mun yi sake a gidan nan da har ake mana kwashe-kwashe, kuma wai har shopping yayi mata, saboda tsabar taya bera barna.
shiga suka yi dakin suka kwashe duk kayan da doctor ya siyowa Nauwar.


wucewa suka yi suka shiga wajen Hajiya, samun ta suka yi tana shirin fita unguwa, yadda ta gansu sun taho gaba daya sai da suka fadar mata da gaba, duk a xaton ta wani abin ne ya afku, jifa zainab tayi da kayan da suka kwaso daga wajen Nauwar
bin su tayj da kallo mai cike da mamaki, kafin tace komai har suna sun fara kora mata jawabi.


"wlh Hajiya baxa mu yarda ba sai an fitar mana da mahaukatan nan daga gida,haka kawai a kawo mana mutane bamu san asalinsu ba, bamu san yadda suke ba kawai su xaune mana a gida sam baxa bamu yarda ba, ai mu ma muna da hakki a gidan, gashi nan har shopping sai da yaje yayi mata mu bai bamu ba.


lallai wannan yaron ya rika, gaba daya yanxu ya canja ya xama mai kunnen kashi, haka kawai muna xaune kalau ya jawo mana jaraba, tuntuni nace a fitar da mutanen nan amma ya kafe saboda baya jin magana,wai shi uban tausayi, nifa yarinyar nan kallon karuwa nake mata,kada taxo har gida ta lalata min yaro, dama da ya bi ta tawa da baxa ma kuxo ku tarar da su a gidan ba, saboda ni yarinyar gaba daya bata kwanta min ba"
suna cikin wannan maganar doctor Abdallah ya yi sallama, suna ganin shi suka koma gefe gaba daya suka bi bango saboda kwarjinin sa.


cikin bacin rai yake musu magana.
Gaskiya Hajiya abinda ku ke yi ke da yaran nan gaba daya bai dace ba, yara basa so a ci arxikin su, Hajiya ki tuna fa yaran nan mata ne baki san irin mijin da xasu aura ba, kuma baki san yadda Allah xai yi dasu ba nan gaba, amma ki xauna kisa su gaba kina koya musu saka da mugun xare,Gaskiya hakan bai kamata ba, ku kuma wlh indai ku ka cigaba da musgunawa yarinyar nan ni da ku ne"


Hawa kan Abdallah tayi da masifa dan haka ya fice ya kyaleta.


yana fita suka cigaba da tattaunawar da suke yi, feenah ce ta cigaba da magana


"wlh Hajiya dole mu takurawa matar nan har sai ta gaji ta kwashe kayanta, ki kyale shi kada ki sake yi masa magana, da kanta xata sulale ta gudu ba tare da ma ya sani ba.


kwashewa suka yj da dariya
"ai kuwa kin kawo haske feenah haka xa a yi musu duk wankin gidan nan su xasu rika yi, washing machine ya huta, su xasu rika aiki kamar jakuna, hatta inner wears su xasu rika wankewa


sun ji dadin wannan shawarar da Hajiya ta bayar, sbd sun yi tanadin kala-kalar axabar da xasu ganawa Nauwar da mahaifiyarta.






*Yawan comments yawan typing ehe*












*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*NA*


*JEDDAH TIJJANI*


*ADAM*


*(Jeeddahtulkhair)*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†




5⃣9⃣






Tunda suka bar Nauwar a tsaye bayan sun gama yi mata wannan cin mutuncin bata ko motsa daga inda take ba,saboda takaici da bakin cikin da ya mamaye xuciyarta, da kyar ta ja kafa ta koma daki, kifa kanta tayi a kasa,ta rusa kuka mai ban tausayi, turo kofar dakin aka yi tare da sallama, doctor ne ya shigo fuskar shi ba walwala, yana jin xafin wulakancin da ake yi wa Nauwar, tsugunnawa yayi yana fuskantar ta, sai faman kuka take yi bata ma san ya shigo ba.
kamshin turaren sa ne ya daki hancinta saurin dago da kanta tayi, ido hudu suka yi da shi, wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata. cikin karfin hali ta mayar masa da martani


samun guri yayi ya xauna yana fuskantar ta, cikin sassanyar murya tare da kulawa ya fara mata magana.


"kiyi hakuri da irin matsalolin da xaki fuskanta a gidan nan, kada ki rika saka damuwar hakan a ranki, domin kuwa halin yaran gidan nan ne raina dan Adam, tunda har kin fahimci haka bana so naga kin kara bata ranki a kan Abubuwan da xasu rika yi miki, kiyi hakuri ki daure wata rana xaki ci ribar hakurin da kika yi"


cikin kuka ta dago jajayen idanunta tana masa magana
"na gode da kulawar ka gare ni, amma xuciyata baxa ta iya jure cin fuskar da ake min a gidan nan ba, dan Allah ka bani dama na tafi inda xan fi samun sauki, ni wlh har na fi jin dadin rayuwar kasuwar da nake yi a kan dai rayuwar gidan nan, ga shi dai kana girmama ni, amma yan uwanka da mahaifiyarka sun hana ni jin dadi, bana so na xama silar hadaka da mahaifiyar ka, na yanke shawarar yau xan fita na bar gidan nan tun kafin wata matsalar ta afku"


cikin tashin hankali ya dubeta
"dan Allah ki daina tunanin barin gidan nan, indai kin ga kin fita to na nemo gidan ku da yan uwan ki ne, amma wannan dalilin baxai sa na bari ki tafi ba
saboda wahala bata kisa, kuma komai na Allah yana da ka'ida"


kuka ta cigaba da yi saboda shi ne kadai abinda xai sanyaya mata xuciya a yanxu, duba dakin ya shiga yi, cikin mamaki ya dubeta
"in kayan da na siyo miki"
share hawaye tayi sannan ta bashi amsa
"an xo an kwashe"


"an kwashe kuma? wanene yayi wannan aikin"


tsugunnawa tayi har kasa ta fara yi masa bayani
"kannenka ne suka kwasa amma dan Allah kada kaje kace xaka yi musu wani abin saboda haka, kayi hakuri ka kyale su, kada hakan ya jawo min matsala a wajen su, ni na yafe musu duk abinda suka yi min"


tausayin yarinyar ne ya kama shi, cikin kulawa ya dubeta


"ba komai na rabu da su,amma yanxu xan fita xan sake siyo miki duk kayan da kike bukata, kada ki sake bari su dibar miki"


godiya tayi masa sannan ya fice, bayan mintuna kadan ya dawo mata da kaya masu yawa, umarni yayi mata da ta boye su gudun kada kannensa su sake kwashewa.


kwanan su Nauwar uku a gidan su doctor kullum da irin bakin cikin da take fuskanta, tunda taxo gidan bata samu ta watsa ruwa a jikinta ko da sau daya ba,saboda sun hana ta shiga bandaki dan kada tayi kwalliya ta kwace musu doctor din su.


yau da sassafe doctor ya fita saboda yana da aiyuka da yawa a Office, ganin baya nan ne yasa Hajiya ta taho tare da tawagar yayanta, kwankwasa kofar dakin su Nauwar tayi, a raxane ta taso ta bude musu.


tsugunnawa tayi har kasa ta gaida Hajiya, wata harara ta watsa mata sannan ta fara magana.


"lallai yarinya kin samu sakewa wato har lokacin bacci kike samu, to gidan nan ba na bacci bane.fitowa xaki kiyi aiki tukuru kamar sabuwar jaka, dan baxa ki xauna haka kawai kina cin arxikin mu ba, mu kuma ba ma morar ki"


watsa mata kayan wanki tayi a fuska sannan ta jefeta da sabulu




"dauki maxa ki xo ki fara aiki, kina gamawa shara na jiran ki, kuma ki shirya jibi xaki bar gidan nan, ko kina so,ko bakya so"


ficewa tayi ta barta a tsugunnah tana naxarin irin wannan wahala da kaskancin ta tsinci kanta a ciki.


watsi tayi da kayan wankin tana masifa


"ba a isa nayi wannan aikin ba, dan nima 'ya ce kamar kowa kuma ina da galihu kaddara ce ta sauka a kaina, dan haka ba katuwar da xan xauna ina yi wa wanki, sai dai idan xa a kore ni a kore ni,
dama abinda nafi bukata kenan, tunda rayuwar da nayi a baya bata kashe ni ba, wannan ma ba abinda xata yi min dan na koma kasuwa da kwana"


mayar da kofar dakin tayi ta kulle.


ta baranda zainab ta hango dakin Nauwar a kulle da gudu ta shiga daki ta fara kwalawa Hajiya kira.


"fito ki ga abinda wannan mahaukaciyar tayi"


cike da mamaki Hajiya da sauran yaran gidan suka leka suka ga dakin Nauwar a kulle, komawa daki suka yi, kowanne su ya dauki abin duka, cikin masifa Hajiya ke magana.


"dole mu dauki mataki a kan yarinyar nan, wato har tayi sakewar da xan sakata aiki taki yi, yau sai naga mai raba ni da ita, wlh yau ko dukan nan xai xama ajalinta kowa sai ya xaneta a cikin ku"


bakin kofar dakin Nauwar suka nufa, bugun tashin hankali suka rika yi, a firgice ta tashi ta bude musu, jawo wuyanta Hajiya tayi ta rika duka kamar baxa ta barta da rai ba, sannan yayanta suka dora da dukanta basu kyaleta ba har sai da suka ga ta kai kasa, tana wani irin abu kamar na masu cutar farfadiya.








*yawan comments yawan typing, idan an yi comments da yawa na karasa ciko ragowar pages din*








*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*




πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*Yan uwa ina jin dadin comments din ku, kuma hakan na kara min karfin gwiwar yin typing da yawa ina godiya sosai*




6⃣0⃣




Duk da yanayin wahala da suka jefa Nauwar a ciki hakan bai sa sun sassauta da dukanta ba, har sai da suka ga ta daina motsi, ganin abinda suka yi mata ne yasa aljanun Ammi suka tashi, nan fa ta shakewa hajiya makoshi ta rika duka ta ko'ina duk yadda yayan nan suka yi su kwaceta suka kasa saboda gaba daya bata cikin hankalinta ,sai da ta gama xane ta tsaf ta sake ta, kan su zainab ta sake yo wa da gudu suka shige daki suka bar Hajiya kwance jina-jina.

suna shiga daki suka dauki waya, suka kira doctor, cikin kuka feenah ke masa magana


"daga cikin masifar da ka jawo mana, ka kawo mana su har gida, daya daga cikin su ta hau Hajiya da duka, da kyar ne ma idan bata hallaka ta ba"


hankalin doctor a tashe ya mata magana


"me kike fada min haka feenah, yaushe al'amarin ya faru"


Cikin tsiwa take masa magana.
"yanxu ne idan kaxo ka ganewa idanunka ni ba ni da lokacin tsayawa na baka amsa ta halin da mahaifiyata ke ciki nake yi"


xage-xage su feenah ke yi suna tsinewa doctor saboda ya kawo musu kwai tara tsinana har gida, kokarin fita suke yi wajen Hajiya amma saboda tsoron Ammi ta kasa ta tsare tana jiran fitowar su ta sauya musu halitta. shi yasa suka yi wa kansu fada suka xauna a daki, suna leken halin da ta jefa mahaifiyar su a ciki.


cikin gaggawa doctor ya dakko mota, yana tuki yana kiran innalillahi wa inna ilaihi raji'un saboda babban masifa ce ta tunkare shi, wacce kuma idan bai yi da gaske ba sai ta haifar masa da bakin ciki na har abada, a waje ya yi parking saboda baxai iya jira har sai an bude masa gate ya shiga da mota ba, shigar sa gida ke da wuya ya tarar da Hajiya kwance tana numfarfashi, ga Nauwar ita ma a kwance jini na kwarara a kan fuskarta, hawaye ne ya shiga fitowa daga idanun doctor ta ko'ina, yana karasawa wajen Hajiya Ammi ta matsa daga wajen, duk da kasancewar ta mahaukaciya tasan mai kyautata masu.


daga kan Hajiya yayi yana mata sannu, bude ido tayi kadan ta dube shi, da hanxari ta xabura xata gudu a tunaninta Ammi ce ta sake dawo wa xata dake ta, cikin nutsuwa tare da rarrashi yake mata magana.
"sannu Hajiya, kin ga irin abinda nake fada muku ko, ga irinta nan ai, kun kama karamar yarinya kuna kokarin hallakata ba a kan hakkinta ba, ko da ku ke ganin mahaifiyar ta a matsayin mahaukaciya ita ma tasan ciwon haihuwa, kuma tana jin xafi idan an taba yarta, nasan kuma duk laifin daga wajen ku yake, da baku taba su ba hakan baxai faru ba, yanxu da kun kasheta ai ni ku ka jawo wa masifa "


yana Cikin wannan maganar ne gaba daya yayan gidan suka fito suka fara xage-xage, suna cewa ya kawo musu abinda xai kashe su har gida,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login