Showing 111001 words to 111837 words out of 111837 words
Chapter 38 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
mai muhimmanci da shi Allah yayi miki albarka" bayan fitar Abba daga dakin angwaye suka shigo sanye suke da fararen Shadodi komai nasu iri daya Hamdan da doctor Abdallah suka saka, fuskar nauwar a rufe tana ta faman kuka karasowa inda take Hamdan yayi da sauri taja jiki ta matsa murmushi yayi yana mata magana
"yau kuma dodo na zama nauwar kike jin tsoro na"
Shiru tayi ba tare da ta bashi amsa ba ya rika tsokanarta, sai da suka gama magana sannan mai hoto ya shigo ya fara daukansu, bayan sun kammala suka fita doctor ya kama hanyar tafiya fataskum shi kuma Hamdan yayi gida.
A unguwar nassarawa G. R. A Abban Hamdan ya gina masa katafaren gida wanda kuma ba su da nisa da gidan su Hamdan, shi kuma doctor Abdullah a fataskum xai xauna a wani hadadden gida da ya samu gado a wajen mahaifansa, da misalin karfe daya na rana yan daukan Amarya suka zo, wadanda su ne xasu tafi da saimah gidan doctor, ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba kuka gaba daya yaki zuwar mata, amma dai kana ganinta kasan tana cikin damuwa a daki Saimah take iyaye nayi mata fada a dai-dai lokacin nauwar ta shigo ta tarar da saimah na ta faman sharar kwalla da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta kuka take yi mai cike da ban tausayi da kyar aka cire saimah daga jikin nauwar aka sata a mota sai gidan doctor.
.tunda aka tafi da saimah nauwar ke kuka rarrashin duniyar nan an yi mata ta kasa yin shiru har zuwa karfe shida na yamma wanda a wannan lokacin xa a kaita dakin mijinta, da kyar aka lallabata ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito aka Fara yi mata nasihohi a kan xama da miji, nan ma dai ta shiga tashin hankalin rabuwa da Amminta haka aka tarkatata aka kaita gidan Hamdan.
Rayuwa mai dadi suke yi a gidan mazajen su cike da xaman lafiya da kwanciyar hankali duk wanda yaga irin zaman da suke yi sai abin ya burge shi, watan Su nauwar biyu da aure Allah ya azurta su da samun ciki ba karamin lele nauwar ke sha a wajen Hamdan da mamansa ba kowa fata yake Allah ya sauketa lafiya.
Sai da saimah ta cika wata uku a gidan doctor sannan taxo ganin gida, sai da tayi sati biyu sannan ta tafi nan ma dai sai da suka sha kuka suka rabu.
A ranar da suka cika wata tara dai-dai nauwar ta haifo santalelen jaririnta kamar su daya da Hamdan komai da komai, sunan Abban nauwar aka sanyawa yaron inda suke kiran shi da Adeel, ba karamin gata kakannin Adeel ke gwada masa ba, don bai fiya xama a hannun nauwar ba kusan kullum yana tsakanin gidan mama da Ammi.
Yau da sassafe Ammi taji ana kwankwasa mata kofar falo da hanzari ta tashi don budewa tare da cewa "wanene " shiru aka Yi ba a yi magana ba, cikin karfin hali ta saka key ta bude kofar, mace ta gani tsirara haihuwar uwarta fuskarta baka kirin cikin rawar baki take mata magana"Habi Kece lafiya na ganki a wannan yanayin "
Hawaye matar take xubarwa "ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah mutuwa xan yi na wulakanta naga rayuwa yanxu haka ni nasan irin axabar da nake dandanawa ki yafe min " tana gama fada ta fadi kasa tana wani irin abu a dai-dai lokacin yayan Habi suka yi sallama
"yanxu Sai da kika taho baba Inna lillahi wa Inna ilaihi rahi'un"
Jujjuyata suka rika yi suka ga bata motsi cikin kuka suke wa Ammi magana.
"daga gidan magani ta gudo Hajiya da yake yanzu ana yi mata dan kokari tun jiya take cewa sai taxo ta roke ki gafara dan Allah ki yafe mata Hajiya " suka karasa maganar suna kuka.
Ita ma Ammi kukan take.
"na yafe mata Allah ya yafe mana gaba daya"
Daukanta suka yi suka tafi Dan Batta don yi mata suttura.
Sai da Abban nauwar ya dawo take Fada masa abinda ya faru,mamaki yayi da tace ta yafewa Habi
"yanxu sai ki yafe Mata duk irin cutarwar da tayi miki.
Murmushi Ammi tayi
"Menene don na yafe mata Allah yana tare da masu hakuri"
Haka suka cigaba da rayuwa mai dadi cikin farin ciki da annashuwa.
Lallai duk mai zalunci xai ga yadda Allah xai yi da shi tun a duniya domin Allah da kansa yace ya haramtawa kansa zalunci kuma ya sanya shi abin haramtawa a tsakanin mu, don duk Wanda ya cuci wani Allah bazai saurara masa ba bazai masa rahma ba, sai dai idan bawan Nasa ne ya yafe, don haka nake kira ga yan uwa mu nisanci zalunci da shirka ga Allah, duk abinda Allah bai bawa mutum ba babu wani malam ko boka da zai bashi don haka mu kiyaye. abinda na rubuta dai-dai Allah ka bamu ladan wanda nayi Kuskure Allah ya yafe mana, Allah yasa mutane su yi amfani da fadakarwar da ke cikin wannan littafi.
*Alhamdulillah*
Taku
*jeeddahtulkhair😘*
Sai kun sake ji na a sabon littafina.