Showing 42001 words to 45000 words out of 111837 words

Chapter 15 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

da nake ciki ba, Allah ne Kawai xai iya fitar dani ka kyale ni, bana son na Kara tuna abinda na fara mantawa da shi"


Lallabata ya shiga yi a kan ta fada masa matsalarta Amma taki, sai gajiya yayi ya kyaleta. Dubanta yayi sake yi, yana murmushi tunda baxa Ki fada min ba bari na kyale ki, amma yanxu ina Zaki naga kin xauna a nan?


"babu inda xan tafi a nan wajen xamu Kwana "


Cikin mamaki yake mata magana.


"a nan wajen fa kika ce gaskiya baxan bari ku Kwana a nan ba, Sbd gaba daya babu security, kizo xan taimaka muku na baku gurin Kwana Amma fa idan kin amince"


Shiru tayi ta tafi dogon tunani,ya za a yi daga haduwa da mutum bata San halinsa ba yace xai taimaka mata, xuciyar ta bata amince da binsa ba


"Ki yarda da ni baxan taba Cutar da ke ba, Wlh da xuciya daya nake son taimaka muku don naga halin da kuke ciki "


Jin ya yi mata rantsuwa da Allah yasa ta amince xata bishi ya basu wajen Kwana.


Don haka ta Mike ya taimaka mata,ta tashi Ammi kasancewar ta fara bacci.


Gida ne mai daki biyu ciki da falo sai kuma falle daya sai toilet da kitchen da tsakar gida, gidan ya tsaru sai dai karami ne ba shi da girma.Amma Akwai kayan more rayuwa a cikinsa.


Nuni yayi musu da su shiga cikin dakin don haka,suka shiga dakin ita da Ammi, gurin xama suka samu cikin mintinan da basu wuce biyu ba ya xo musu da abinci mai rai da lafiya, Dan ruwa, duk abinda suke bukata shi yake kawo musu,da alama dai gauro ne ba shi da aure, bayan sun gama cin abincin ne ya shigo ya same su, kallonta yayi fuskar sa a sake yana murmushi.


"da fatan dai kin koshi kuma gajiya ta bar jikin ku"


Kallon shi tayi ta gyada masa Kai alamar "eh"


naga alama dai malamar nan bata son magana, Gashi ni kuma sarkin surutu ne da son tambaya kamar dalibi mai koyon aikin jarida


Kallonshi tayi tayi yar dariya


"tunda kun ci abinci kun huta bari na wuce dakina lokacin bacci yayi, Amma kafin na tafi Ina son Jin Sunan malamar"


Kanta a sunkuye ta amsa masa "Sunana nauwar wannan kuma mahaifiyata ce Allah ya jarrabeta da matsalar tabin hankali ne"


Cikin tausayawa da kulawa ya yi mata magana


"Subhanallah Allah ya bata lafiya, Insha Allah ina da taimakon da xan bata xata samu sauki da yardar Allah"


Cikin farin ciki ta amsa masa da Allah ya bada iko. Tunda taji ya ambaci xai taimakawa Amminta ta samu lafiya, xuciyar ta tayi dadi taji kamar an gafarta mata xunubanta, sallama yayi mata ya wuce dakin sa, yana fita tayi shirin kwanciya ta Kwantar da Ammi suka fara bacci cikin Farin ciki.


Cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita, a cikin baccin taji kamar tafiya a cikin dakin Don haka ta yi saurin bude ido a tunanin ta Ammi ce xata fita.


saurayin nan ta gani daga shi sai singlet da boxers ya nufo inda take, cike da mamaki ta dube Shi lafiya Malam, Kai da ka taimaka mana kuma me ya shigo da kai da tsohon daren nan.


Dubanta yayi yana wani shu'umin murmushi
" a tunaninki xan taimaka miki haka Kawai ne ba tare da kin taimaka min ba ai rayuwar Yanxu ban gishiri in baka Manda ne sai kin bani xan baki"


Kara matsowa yayi daf da ita tana ja da baya tana rokon shi ya tausaya mata ya dubi halin da take ciki ya kyaleta.


Murmushin yaudara ya cigaba da yi mata.
"yadda kike budurwar nan son Kowa kin wanda ya rasa me yasa xaki cuci kanki, arxiki yana kiranki Kina gudunsa kin fi son ku cigaba da kasancewa a wahala ke da mahaifiyarki, Ki bani dama na shigo cikin rayuwar Ki na sanya Ki Farin cikin da xaki dauwama a cikinsa har Avada, idan kuma kince baki yarda ba, ni baxan miki dole ba sai ki bayani abincina da kika ci min ke da mamanki.






*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Ba nida Bakin da xan gode muku masoyana sai dai fatan Allah ya bar xumunci*


4⃣5⃣




Hannu tasa a jakar da take adana yan kudadenta ta ciro masa naira dubu biyu ta mika masa. kallonta yayi cikin fushi ya fara mata magana


"Sbd ba kida hankali Kudi nace Ki xaro ki bani ko abinda na ciyar da ke,ba Kudin ki nake bukata ba
abinda kika ci min xaki baya ni Yanxu"


Tsugunnawa tayi har kasa tana masa magiya
"ka taimake ni kayi hakuri a Ina zan samo maka abinda xan biyaka Yanxu"


Kara matsowa yayi daf da ita ya matseta jikin bango numfashinsa na sauka a kan fuskarta, kokarin matsawa tayi ta xille ta kasa, da sauri yasa hannu ya kamota ya manna fuskarsa da ta ta, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da yana cikin jaraba


"kan ki nafi bukata a Yanxu ba Kudi ko abinci ba, ina so ki biyani ne da abinda Allah ya axurtaki da shi. me yasa kike son yi min rowar abinda kike da shi, me yasa xaki yiwa kanki muguntar samun arxiki, idan kika rabu da gidan nan nasan babu wanda xaki samu ya karbe ki a wannan halin da kike ciki ke da mahaifiyarki, don haka na baki minti biyu kiyi Shawara da xuciyar ki duk abinda kika yanke Ina maraba da karbarsa ,Amma ki sani baxan miki dole ba"


Komawa kan kujera yayi yana mayar da numfashi ita kuwa Nauwar sai faman share hawaye take yi, tunda take bata taba ganin bala'i irin wannan ba, kana tunanin mutum xai taimake ka asheba kyakkyawar niyya ce ta kawo shi ba.


Tausayin kanta ne ya kamata, komai na duniya ya cakude mata, burinta Allah ya dauki ranta ta huta da jarrabawar da take ciki.


Sake kallonta yayi ya mata magana
"ke nake saurare Wace Shawara kika yanke idan har baki amince da kudirina ba ki tatttara kayanki Yanxu ki bar min gida, in yaso ko Menene ya same ku ba nida asara"


Fadar wannan maganar da yayi ba karamin faranta mata ranta yayi ba, da hanxari ta amsa masa.


"Ban amince ba"


Cikin mamaki ya dubeta
"amma ban taba tsammanin cewa ke wawiya bace sai Yanxu, a ce kina cikin wannan masifar ki qi amincewa da abin alheri, na miki alkwarin xame miki uwa da uba Sannan watsi da damarki kice bakya so, kada kiga cewa dare yayi ko xan daga miki kafa na fasa korarki
Wlh Yanxu xaki fita ki bar gidan nan, tunda ba gadonki a ciki banxa shashasha Mara rabo"


Bin sa tayi da ido bata ce masa komai ba,tashin Ammi tayi suka fito daga dakin har waje ya rako su yana xaginsu yana cewa Nauwar Mara rabo, sai da suka fita,Sannan ta kalle shi cikin tsiwa take masa magana.


"Alhamdulillah na godewa Allah da bai baka damar Cutar da mu ba, macuci maciyin amana, Indai a kan na xauna ka lalata min rayuwa ne gara na rasa rabon duniya gaba daya, don nasan Akwai tanadin da Allah yayi min a lahira"


Kallonta ya rika yi ya rasa bakin magana Sbd a tunaninsa bai xaci tana da baki haka ba, mayar da kofar gidan yayi ya kulle, ita kuma ta kama hanya suka cigaba da tafiya, gari yayi shiru ba a Jin komai sai haushin karnuka, kasancewar lokacin karfe biyu da rabi na dare.


Bakin wata Makaranta suka samu ta roki masu gadin a kan tana so su bata wajen kwana, ta fada musu su matafiya ne dare yayi musu a hanya, Washe gari su cigaba da tafiya, basu yi musu gardama ba suka basu aji suka kwanta.


Gari na wayewa suka taimaka musu da koko da Kosai bayan sun kammala karyawa suka yi musu sallama suka nufi tashar Na'ibawa don su hau mota.


Tunanin nauwar gaba daya ya dauke ta rasa motar garin da xasu hau, tana tsaye tana wannan tunanin taji an yi mata magana.


"yan mata ina xaki je Kaduna xaki ko maiduguri ga motocin mu nan Saura gurin mutum biyar su cika"


Da sauri ta bashi amsa da Maiduguri sbd ta tuna Abbanta a nan yayi bautar kasa inda ya hadu da wasu mutane suka yi xaman mutunci suka xamo tamkar yan uwa har ya taba kai su xiyara mai dugurin dan haka taji dadin samun motar garin.


Shiga suka yi suka xauna ita da Ammi, ba a Fi mintuna biyar ba aka karasa cika motar suka dauki hanyar garin mai duguri.


Da misalin karfe shida da rabi na yamma suka sauka a tashar garin inda Kowa na motar ya fita ya kama hanyar inda xai je, tun a hanya taga gaba daya garin ya canja mata, ba irin yadda ta san shi a baya ba, gefe guda ta samu ta tsaya tana tunanin Sunan mutumin da zasu je wajensa, cikin ikon Allah ta tuna Sunan


wani bawan Allah ta samu xaune. Sallama tayi masa ta tambaye shi ,nawa ne kudin motar da xai kaita unguwar Hausari, cikin kulawa ya fada mata farashin kudin Sannan ya taimaka mata ta samu adaidaita sahu.




Har bakin layin gidan Alhaji musa aka kaita sai dai ta kasa gane gidan kasancewar an canjawa Unguwar fasali saboda fadan da ake yi.


Tambaya tayi aka nuna mata gidan tana nufar kofar shiga ta tarar an rushe gidan ba Kowa sai fili, mamaki ne ya kamata saboda bata taba xaton xata tarar da wajen a haka ba.


Ganin ta tsaya cak ta kasa aikata komai ne wani bawan Allah ya sameta yayi mata sallama


Cikin girmamawa ta amsa masa, tambayarta yayi wanda take nema.
Cikin sakin fuska ta amsa masa


"gidan Alhaji musa Abbakura nake nema"


Cikin tausayawa ya dubeta
"Ai Allah yayi masa rasuwa sanadiyyar fadan da ake yi, duk an kashe iyalinsa dansa daya ne yayi ragowa shi ma kuma ba a San inda yake ba"


Sunkuyawa tayi ta rushe da kuka mai ban tausayi.


"Wayyo Allah Naga ta kaina, Yanzu Ina zan dosa ga yamma tayi Gashi ba nida kudin komawa Kano ga kudaden hannuna gaba daya sun Kare Allah ka dube ni da rahamarka da Jin kanka"


Cikin tausayawa mutumin yayi mata magana
"kiyi hakuri Allah xai dubeki ya baki mafita, da ina da wajen Kwana da na baku saboda na tausaya miki, to nima bako ne a gidan wasu na sauka, amma ki cigaba da tambayar mutane ko xa a samu mai taimaka muku, na barki lafiya Allah ya hadaki da naka gari dari biyar ya xaro a aljihu ya bata"


godiya tayi masa suka yi sallama ya tafi, rasa inda xasu dosa tayi kuma ta kasa rokon Kowa ya taimaka musu, saboda tana Jin tsoron kada abinda ya faru da ita a baya ya sake faruwa.








*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDA TIJJANI*


*ADAM*


*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Bansan da bakin da xan gode miki ba QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kyautatawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci*




4⃣6⃣




Duk wanda yaxo wucewa kallon su yake yi, saboda kowa tunani yake yan ta'adda ne suka yi basaja. wani babban mutum ne yayi ta maxa yaxo ya sami Nauwar. sallama yayi mata, ita kuwa saboda tsananin kukan da take yi,ta kasa magana sai a cikinta ta amsa sallamar, magana ya fara yi mata


"me ku ke yi a nan, kika xauna ke da wannan mahaukaciyar, me ya fito da ku daga gida da yammacin? kin san dai duk kwarya ta gari tana ragaya ko? ya kamata ki tashi ki tafi, don gaskiya bama barin wadanda bamu sani ba su xauna mana a unguwa, sai dai idan da ixnin mai unguwa xasu xauna"


kallon shi take yi kawai,ta kasa ce masa komai saboda bakin cikin da ya tokare mata makogoro. sake dubanta yayi


"magana nake fa kin kasa bani amsa sai faman kuka da kike yi, na fada miki sharadin xama a nan, ko ki tashi ko nasa yara su yi muku a tire, don irinku ba abin yarda bane"


kafin tayi magana tuni ya fara kiran yaran unguwar,kan kace me, tuni sun taru sun fara jifan su da dutse,suna yi musu waka, ganin xasu illata su ne, yasa taja hannun Ammi da kyar suka bar gurin,tana tafe tana kuka, sai da suka yi tafiya mai nisa sannan ta samu suka xauna, idanunta sun kad'a sun yi jawur, ga yunwa da kishiruwa ga gajiyar tafiya ga bacci da ya dameta, don rabon da ta samu ta rintsa tun lokacin da Abbanta ya koreta daga gida.


Ammi ce tayi wani gunji mai ban tsoro inda ta kama Nauwar da duka ta ko'ina, shake mata wuya tayi ta hadata da jikin bango, ta rika gwara kanta da bangon, kamar baxa ta barta da rai ba. tunda Ammi ta fara rashin lafiya bata taba shiga irin wannan halin ba sai yanxu, ihu Nauwar ta rika yi, tana neman taimako amma Ammi ta ki ta daina dukanta, kasancewar gurin babu jama'a sai su kadai sai gidaje a kulle, wasu mutane Allah ya kawo da kyar suka kwaceta a hannunta, da gudu tayi kansu da duka tana jifan su da duwatsu. Haukan Ammi yanxu ya koma na duka, sai da ya kasance duk wanda yaxo wucewa sai ta jefe shi ko ta watsa masa kasa. a ranar kwanan xaune suka yi, saboda da Nauwar ta kwanta xata rufe ta da duka, sai tsallakawa tayi ta kwanta a gefen wani kanti.


washe gari da Asuba ta farka, tarar da Ammi tayi kwance cikin kwata tana ta bacci abinta, da sauri ta karasa wajen tana kuka, duk jikinta ya baci da kwatar, wani bawan Allah ne ya taimaka mata suka fito da ita, inda ya kawo sabulu da ruwa ta wanke mata jikinta. duk wanda ya kalli Ammi yasan ta xama mahaukaciya tuburan saboda abinda bata yi da, shi take yi yanxu.


tambayarta ya yi.
"ke kuwa baiwar Allah daga ina kike haka, ga ki da mai lalura"
share guntun hawayen da ke idonta tayi, ta fara bashi labarin abinda ya faru da su, da kuma garin da suke. tausaya musu yayi kwarai da gaske, sannan ya bata shawarar xuwa gidan mai unguwa ta fada masa abinda ya faru da su.


cikin nutsuwa tayi masa magana
"ai ban san gidan mai unguwar ba"


dansa ya kira yayi mata rakiya, kasancewar shi xai wuce asibiti wajen mahaifiyar sa.


ba tare da bata lokaci ba, yaron yaxo don yi musu rakiya, suna tafe Ammi na turjewa, a haka har suka isa gidan.


A soro suka tarar da mai unguwa inda suka yi masa sallama, cikin girmamawa ya amsa, ya kuma tambaye su abinda ya kawo su, bayani tayi masa ya tausaya mata sosai, sai dai xuciyar sa bata gama amincewa da su ba, saboda yan ta'adda sukan xo da wannan sigar su cuci mutane, daki ya basu wanda yake a tsoron gidan, ya kuma yi umarni a kawo musu abinci da ruwa.


**********************


A bangaren su innah karime kuwa farin ciki ne ya cika xuciyar su,saboda sun kori su Ammi da yayanta sun mallake komai, gida ya xama nasu, su da jikonkin su, Habi ce ta shigo rike da kwanan abinci a hannunta, guri ta samu ta xauna ta dubi innah karime.


"wai kuwa innah kina tunawa da tsinanniyar matar nan, da taso ta hana mu xaman lafiya a gidan nan"


"uhmmm habi kenan kema baki tuna da ita ba sai ni, da ta tsane ni taki jinina, ai na godewa Allah na godewa Boka da yayi mana wannan aikin,ya tarwatsa musu rayuwa, yanxu ma so nake a kara yin wanda xa a farraqa tsakanin yar da uwar, taki taimaka mata, kin ga abin xai mata yawa,ga hauka ga ya ta gujeta, daga nan kinga sai mutuwa kenan"


hada hannu suka yi suka tafa, suka bushe da dariya, sallamar da aka yi ne ya katse musu hirar da suke yi.


mamin Hamdan ce taxo, a tunaninta har yanxu su Nauwar na gidan, babu wanda ya kalleta ballantana tasa ran xai amsa mata sallamarta, duba dakinsu Nauwar tayi,taga ba kowa gaba daya kayan dakin su an fitar da shi,ya xama kamar kango.


mamaki ne ya kama ta, don haka kai tsaye ta fito daga dakin ta tsaya a wajen da su innah karime suke
tambayar su tayi.


"bayin Allah ban yi xuciya ba, dan Allah ina mai dakin nan take ko bata nan"


A yatsine Habi ta kalleta
"ga amsar nan ai kin bawa kan ki"


fitowa tayi ta rabu da su, mai gadi ta tarar yana ta faman shara, har kasa ya xube ya gaishe ta, tambayar shi tayi ina su Nauwar.


sunkuyar da kai ya yi yana share kwalla.
"Ai Alhaji ya kori su Hajiya yau kusan kwana biyar kenan"


cike da mamaki ta dube shi.


"ya kore su fa kace malam Ali"


"wlh da gaske nake Hajiya, nima da nayi masa magana sai da ya ci min mutunci"


salati mami ta rika yi, tana hawaye
"amma mahmud bai kyauta ba,bai yi adalci ba, amma ba komai akwai Allah"


fita daga gidan tayi kafin ta isa gida xaxxabi ya rufeta.


tana shiga falo ta tarar da jaka a ajiye, samun guri tayi ta kwanta, tana mamakin ganin jakar da kuma abinda ya faru da su Nauwar.


Hamdan ta gani a kanta yana mata murmushi.
kallon shi tayi ta harare shi.


"yanxu Hamdan kasan xaka dawo amma baka yi min waya na hada maka komai ba"


dubanta yayi cikin sakin fuska
"kada ki damu mami xan je gidan su matata Nauwar naci"


hawaye mami ta shiga sharewa tausayin Nauwar da Hamdan ne ya kamata, ta rasa ta inda xata fara fada masa abinda ya faru.












*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*


*(Jeeddahtulkhair)*


*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku, JUWAIRIYYA LUKMAN AMIN (maman shuraym) & HAUWA'U HAMZA SA'EED ZARIA ina godiya da kaunar ku gare ni*








4⃣7⃣




cikin kulawa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login