Showing 30001 words to 33000 words out of 111837 words
Chapter 11 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
tayi wanda sai da hankalin 'yan gidan su gaba d'aya ya dawo kanta.
mamanta ce ta shigo d'akin hankalinta a tashe take tambayar d'iyar tata.
"lafiya, me ya sameki na jiyo ihun ki har waje"?
wani kukan ta 'kara rushewa da shi.
"Mama Hamdan ya tsaneni baya sona, baya 'kaunata, ya ce baxai aure ni ba,saboda ba ni da tarbiyya, dan Allah mama ki taimake ni,ki nemi Hamdan ki bashi ha'kuri ya so ni, wlh baxan iya rayuwa idan ba tare da shi ba".
tausayin d'iyarta ne ya kamata,tabbas ita kanta tasan da cewa,tarbiyya ta yi wa 'yar tata 'karanci, kuma ita ce silar duk lalacewar da yarinyar tayi, a ganinta a bar yarinya ta shana, ta yi duk abinda take so shi ne gata, ga shi tun kafin tafiya tayi nisa, sun fara ganin illar hakan, Hamdan yaro ne kamili, idan har aka tursasa masa auren Ajmal an xalunce shi.
"kiyi ha'kuri ki cigaba da addu'a,nima xan taya ki da ita, insha Allahu, Allah xai karkato miki da tunaninsa ya dawo yana sonki"
"Mama Hamdan baxai ta6a sona ba,ko nayi addu'ar haka nan xa ta wuce, akwai wani malami da Haseenah ta ta6a xuwa wajen sa, a kan maganar saurayinta, tunda ya yi mata aiki ta samu kansa".
"Kul Ajmal!! kada na sake jin,kin yi xancen xuwa wajen wani malami, duk abinda Allah bai baka ba, babu wani d'an adam da xai baka shi, kuma duk wanda yake xuwa gurin malami,da sunan neman taimako kamar bai yarda da Allah bane, don haka ban son na sake jin kin yi xancen wani malami a gidan nan"
"To mama, baxa ki sake ji ba insha Allahu,ina so xan je gidan su Haseenah na kai mata kayan da ta bayar a d'inka mata"
"Ba inda xaki je, kina son ki fita ne ku had'e ki je inda na hanaki xuwa ko?"
"wlh mama na miki al'kawari babu gidan malamin da xan je"
"to shikenan na yarda ki gaida min da Hajiyar su"
tana fita daga gida ta samu adai-daita, sai gidan su Haseenah da ke unguwar gyad'i-gyad'i, tun a hanya ta sanar mata da xuwanta, don haka ta xauna ta jirata.
A falo ta tarar da Hajiyar su,don haka cikin ladabi ta gaida ta.
"ya mamanki Ajmal"?
"tana lafiya"
ta amsa mata kanta a sunkuye.
Hajiyar su Haseenah tana ganin hankalin Ajmal, ganinta take yi kamar yarinya ce mai tarbiyya da nutsuwa, shi yasa ma ta bar 'yarta da ita, bata san munafukar 6oye bace.
kai tsaye d'akin Haseenah ta shiga,tarar da ita tayi d'aure da towel tana shirin shiga wanka,tana ganinta tayi tsalle ta rungumeta, kwance towel d'in tayi, suka shiga shafe-shafen juna kamar yadda suka saba.
sai da suka dawo nutsuwar su Ajmal take sanar da ita yadda suka yi da Hamdan.
tsaki ta ja, gami da galla mata harara
"ke dai kina da matsala wlh, na gargad'eki ki fita a hanyar wannan banxan guy d'in, amma duk kin bi kin d'ora damuwarki a kansa,to ni yanxu da kika xo kina gaya min, me kike son nayi miki?"
"Baxa ki gane ba Haseenah, baxa ki gane girman soyayyar da nake yi wa Hamdan ba,ki taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ki,ki raka ni gurin da aka yi miki taimako,a kan Mujaheed d'inki, idan baki min haka ba na tabbatar da bakya 'kaunata"
"Ni ai ba nida matsala indai wannan ne,bara na watsa ruwa na xo na raka ki, amma ina fatan kin ri'ko kud'ad'e da yawa, don malam idi baya aiki a kud'i kad'an"
"kud'i ba matsalata bane, kema kin san haka, ke dai yi maxa ki shirya mu fice"
cikin mintunan da basu wuce biyar ba Haseenah ta gama shiri suka fito, suka yi wa Hajiya sallama sai gidan malam idi da ke jan Guza.
A kan buxu suka tarar da shi ya tankwashe 'kafa, yana jan wani zabgegen carbi, tunda malam ya ga Ajmal yake ta tand'ar baki Allah ya kawo masa nama har gida, gaida shi suka yi sannan suka fara xano masa bu'katunsu, da yadda suke son su yi da Hamdan.
"Ba matsala kun kawo kukan ku inda xa a share muku, amma kafin nace komai, malama Haseenah d'an bamu guri xan d'an yi wa 'kawarki interview"
fita tayi ta bar musu d'akin,ta koma kan wani dutse ta xauna.
kallon Ajmal yake yi, wanda kallon nasa cike yake da ayoyin tambaya.
"d'an matso nan ki fad'a min abinda ke tafe da ke, ko da yake dai ke gimbiya ce, ni ya kamata na 'karaso"
matsawa yayi ya manne da jikinta, yana wasu 'yan surutai.
*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
maijiddatijjaniadam@gmail.com
*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Wannan shafin gaba d'aya Sadaukarwa ne gare ki AYSHA UMAR TAHIR TOFA (UMMEE) ina mi'ka gaisuwa ta musamman gareki*
3⃣4⃣
'Dan janye jikinta tayi daga inda yake, 'kara matsawa yayi daf da ita, yana mata wani kallo mai cike da yaudara.
"Ba magani kika xo nema ba?"
ta gyad'a masa kai alamar eh.
"To me yasa xaki ri'ka matsar da jikanki daga gareni?kinga ki kwantar da hankalin ki, ni ba abinda xan miki, aiki kika xo a yi miki, kuma cikin ikon Allah xaki samu biyan bu'kata. Yanxu dai mi'ko min hannunki akwai abinda xan rubuta miki".
Hannu ta mi'ka masa, yana murmushi ya ri'ke mata hannun.
"ko kefa 'yar gari, kina wayayyiya ki mayar da kanki bagidajiya"
tawaddah da al'kalami ya d'akko ya shiga xana mata wasu rubuce-rubuce marasa kan gado, bayan ya kammala ya umarce ta da ta shanye, bata musa masa ba ta shiga lashe abinda ya rubuta mata.
bayan ya kammala, ya 'kara matso da jikinsa, ya manne da ita kamar xai shige cikinta, shafa kanta ya shiga yi, yana karanta wasu abubuwa, ganin yana shafa wuyanta ne yasa ta dube shi.
"Malam har yanxu ba a gama addu'ar bane, naga lokaci yana tafiya"
dubanta yayi yana wata 'yar dariya mai cike da alamomin tambaya.
"Aikinki fa babban aiki ne, lamarin mallaka sai an kai xuciya nesa, dole kiyi ha'kuri nima nayi ha'kuri, wlh banda kece baxan xauna, har na 6atawa kaina lokaci ba, na ri'ka tofa miki abubuwa, amma idan kinga bakya bu'kata xaki iya tashi ki tafi,ga hanya nan, aikina babu lallai ba dole"
jin wad'annan kalaman nasa ne yasa, ta kwantar da hankalinta, saboda idanunta sun rufe a son Hamdan,ta manta da nasihohin da mamanta tayi mata akan bin bokaye.
shiru tayi ya cigaba da shafa ko'ina na jikinta da niyyar yi mata magani.
wani garin magani ya sake d'akkowa ya xuba a 'kwarya,ya gauraya da wani ruwa wanda duk 'kurullarka baxa ka iya gane, ruwan menene ba, ya umartarta yayi da ta cire kayanta xai yi mata wankan magani.
kuka ta shiga yi tare da magiyar ya bata maganin tayi wankan da kanta, kallonta yayi yana xare mata ido.
"Kada ki 6ata min lokaci fa, ba ni na kira ki ba ke kika kawo kanki,don haka idan kina bu'kata ki tsaya, idan kuma bakya so ki wuce ki tafi, me xan gani a jikinki wanda ban saba gani ba, da har xaki bi ki tayar da hankalinki, kina 'yar 'karamar yarinya da ke me xan yi da ke, ki kalleni da kyau kinsan dai na haifeki,ni ba d'an iska bane, maganin da kike bu'kata shi xan baki"
cire kayanta ta shiga yi, tana cirewa tana hawaye, ganin boobs d'inta sun bayyana yasa malam ya kara rikicewa, ya matso gabanta ya kwara mata 'kwaryar maganin,sannan ya shiga aika mata da sa'konni, wadanda xasu taimaka masa wajen cimma burinsa, ta haka ya samu nasara a kanta, ya santa a matsayin d'iya mace.
bata tashi farkawa ba sai bayan sallar isha'i, ganin halin da take ciki ne yasa ta rushe da kuka,tana duba gefenta,taga babu kowa a d'akin sai ita kad'ai,tuni malam idi ya tattara kayansa ya gudu ya barta cikin yanayi mara dad'i.
wayarta ce take ringing da 'kyar ta ja jiki ta d'akkota, mamanta taga ta kirata sama da sau 20,hawaye ne yake xuba a Fuskarta ba ka'k'kautawa,saboda bata san me xata ce mata ba,ba kuma tasan da wane ido xata dubi mahaifiyarta ba, saboda sai da ta nuna mata illar bin bokaye,amma tayi buris da maganarta,ta bi son xuciyar ta,kuka ta 'kara rushewa da shi,a yanxu babu komai a xuciyarta sai nadama, wacce baxa tayi mata amfani ba, ganin kukan da take yi baxai kai mata ba, sai tayi 'karfin halin tashi, ta saka kayanta, ta kuma d'auki wayarta. mamaki ne ya kamata, domin kuwa ta nemi jakarta ko sama ko 'kasa bata ganta ba,wani kukan ta 'kara rushewa da shi,saboda ko kud'in komawa gida ba tada shi.
"yanxu ina xan sa kaina, ya xan yi da rayuwata na cuci kaina, na cuci mahaifiyata,abinda nake nema kuma baxan same shi ba na tabbatar, Hamdan baxai ta6a auren macen da ta 6ata rayuwarta ba, ga shi na barwa kaina mummunan record d'in da baxai ta6a gogewa ba a rayuwata. "
tayi kuka kamar ranta xai fito ta bakinta,da taga ba sarki sai Allah, sai ta fito daga d'akin,tana tafe tana jan 'kafa,saboda ta jigata da yawa a hannun malam.
ringing ta ji wayarta na yi, 'karfin hali tayi ta d'auka, kara wayar tayi a kunneta ta kasa cewa komai sai kuka.
"Ajmal ina kika shiga ana ta nemanki tunda kika bar gida har yanxu baki dawo ba, kuma har gidan su Haseenah naje nemanki, amma tace kun rabu tun d'axu,ki fad'a min inda kika tafi ko na 6ata miki ranki?"
kasa bada amsa tayi sai kuka,saboda bata san me xata ce wa mamanta ta yarda da ita ba.
"magana fa nake miki kin min shiru, sai faman kuka kike, kina ina yanzu?"
"Ina jan guxa mama"
"kina jan me???"
"wane rashin mutuncin ne ya kai ki jan guxa,baki sanar dani ba, ki duba kiga yanzu 8:30, babanki har ya dawo,sai faman fad'a yake yi,me ya kai ki garin jan guza,wa kika ajiye a can, da xaki je d'auka"
tunani amsar da xata bata take yi,saboda ta rasa 'karyar da xata 'kir'kira ta gaya mata.
"kin yi shiru ke nake sauraro"
"mama adaidaitan masu satar mutane na hau, shi ne suka kaini can yanzu haka ma sun min fyade"
ta 'karasa maganar tana kuka
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un,na shiga uku yanzu me xan ce da babanki, sai da ya hanani barin ki fita kowane lokaci amma na kyale ki,ya xan yi da rayuwata, wad'annan mutane sun cuceni
gaba d'ayan su kuka suke yi,mai cike da ban tausayi da nadama a cikinsa.
'karfin hali ta yi,ta tashi taje ta samu baban Ajmal a d'aki ta sanar da shi abinda ya faru da 'yar su, tashin hankali ne ya bayyana a Fuskarsa, sannan ya kar6i wayar ya fara yi mata magana.
"yanxu abinda ya faru da ke kenan Ajmal, subhanallah,xaki iya gane gurin da mutanen da suka kama ki suke,don wlh baxan bar abin nan ba sai na d'auki mataki, ki kwatanta min wajen, ga ni nan xuwa na d'auke ki"
cikin mintunan da basu wuce 30 ba suka iso gurin, xuciyarsa a harxu'ke yake magana.
"wlh duk wanda na kama da laifin yi miki wannan abin sai na sa an kashe shi, saboda an cutar min da dukiya mafi tsada da na mallaka a rayuwata, Allah ya isa"
shiga mota suka yi sai asibiti, aka dubata aka bata magunguna sannan suka wuce gida
*************
Tun lokacin da Hamdan ya samu sassaucin rabuwa da Ajmal,xuciyarsa tayi haske, dad'i da farin ciki ne,ke mamaye xuciyarsa a kowane lokaci, a yanzu babu yarinyar da ya ji yana 'kauna sama da Nauwar, amma yana jin nauyin furta mata soyayya saboda 'karancin shekarunta,da kuma yadda take ganin darajarsa,yana jin tsoron ya fad'a mata, saboda bai sani ba ko xata amshi soyayyarsa, ko xata juya masa baya ta sanadin haka.
08094136204
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
maijiddatijjaniadam@gmail.com
*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*wannan shafin gaba d'aya Sadaukarwa ne gareki uwata ta gari, maganin kukana, mai share min hawayena, HAJIYA RABI'A SABO ABDULLAHI (maman khalid)ina yinki irin sosai d'in nan mamana,ina sonki, ina 'kaunarki, kuma muna mugun tare*🤝😍
3⃣5⃣
Su Ajmal na komawa gida,ta shige d'aki,ta fara tunanin cutar da boka idi yayi mata,wayarta ta d'auka ta kira Haseenah, sai da ta yi mata kusan 5missed calls,sannan ta d'auka.
"kin cuceni Haseenah, kin cutar da 'kawancen da ke tsakanina da ke,yanzu dama kin san haka Wannan malamin yake, kika had'a ni dashi,da nasan haka halin shi yake me xai kaini gurin shi"
"Haba kawata,ni na cuceki ko ke kika cuci kanki?tun farko sai da na baki shawarar kada kije gurin kowa,da niyyar neman maganin mallaka, tunda muna biyan bu'katar junanmu nace ki kyale maganar maxa,saboda ke kanki kin san 'kungiya baxa ta barki yin aure ba."
dakatar da ita tayi tana mata tsawa.
"ni dai kin cuce ni kin gama da rayuwata, na tabbatar ba wannan malamin ne yayi miki aiki a kan Mujaheed ba, saboda ke bu'katarki ta biya,shikenan ni duk halin da xan shiga ba ki da asara ko?gashi nan kin xalunce ni,ban samo komai ba sai ba'kin ciki da bacin rai,Wannan shi ne 'karshen amincina da ke, ba ni ba ke,kowa yayi harkar gaban shi".
kashe wayar tayi tana huci, ashe duk maganar da take yi a kunnen mama, ji tayi an rufeta da duka.
"Daman sai da na kawo a raina duk abinda kika fad'a min 'karya ne,ashe wajen malamin da na hanaki xuwa kika je ko?kin ci amanata Ajmal kin cuce ni kin cuci kanki"
kuka mama take yi, mai cike da ban tausayi, jin hayaniyar da suke yi ne, yasa mahaifinta ya shigo dakin.
tarar da su yayi suna ta shar6ar hawaye.
"Lafiya me yake faruwa da ku?
"Alhaji ashe yarinyar nan yawon neman asiri ta tafi, a can aka yi mata wannan aika-aikar"
shi ma dukanta ya shiga yi, sai da jikinta ya gaya mata sosai sannan suka 'kyaleta.
Hankalin Haseenah a tashe yake,saboda jin abubuwan da Ajmal ta gaya mata,don haka ta shirya don xuwa su sasanta.
a falo ta tarar da maman Ajmal, har 'kasa ta tsugunnah don gaisawa da ita.
"Ina kwana mama?"
wata harara ta galla mata
"Bana bu'katar gaisuwar ki macuciya, ina nan ina tufka kina warware min kina xaluntata, na hana yarinyata yin abu, kin d'orata a kan hanya, har kiyi mata jagora xuwa inda na hanata,me kika xo yi gidana? maxa ki tashi ki fita kafin na ci miki mutunci"
jikinta a sanyaye ta fice daga gidan, saboda bata ta6a tunanin, mama tasan da abinda ya faru ba, wayarta ce tayi ringing tana dubawa ta ga Ajmal ce ta kira, kamar baxa ta d'auka ba, saboda bata san da abinda taxo mata ba, 'karfin halin d'aukan wayar tayi, a sanyaye tayi magana.
"hello!!!"
"Hello 'kawata, naji duk yadda ku ka yi da mama, dan Allah kiyi hakuri, 'kawancen mu Allah ne ya had'a,babu mai rabawa, idan na rabu da ke ai ban huce ba,kuma baxan ta6a samun nutsuwa ba, xan yi 'ko'kaarin sakko da mama, daga doran fushin da ta hau,sannan ki je ki yi mana tunanin yadda xamu samo kan Hamdan"
ajiyar xuciya tayi.
"Na gode 'kawata, xan yi miki tunani mai kyau, kuma kiyi 'ko'kari mu had'u gobe,a gidan uwar gida da akwai meeting"
sallama suka yita kashe wayar, ita kuma ta wuce gida.
*****************
Yau Hamdan cikin tunanin Nauwar ya wuni, ran shi cike yake da kewarta, saboda ya dad'e bai yi toxali da kyakkyawar fuskarta ba, falo ya fito don tattauna da mahaifiyarsa ko xai ji dad'i, 'yar damuwar da ke ransa ta tafi, yana fitowa ya tarar bata nan, don haka ya samu guri ya xauna, tagumi ya xuba yana ta tunane-tunanen, yadda xai tunkari Nauwar da maganar soyayya.
"Hamdan!!!!!!" ya ji an kira sunan shi, a firgice ya juya.
"Na'am mamina, sannu da fitowa"
"yauwa sannu, wai kwana biyu me yake damunka ne, naga a kullum ba kada wani aiki sai tunani"
sosa keya yayi
"wlh mami nima haka kawai naga ina tunani,na rasa me yake damuna"
"Hmm bana son gulma,ka fito sarari ka fad'a min abinda yake damunka yaro"
"Dama mami........shiru yayi yana kallon fuskarta.
"Dama me, fad'a min abinda yake ranka"
"Dama mami so nake kije gidan su Nauwar,ki nemar min aurenta,wlh ita kad'ai nake so mami ki taimake ni"
"dama wannan maganar xaka fad'a min, amma kake inda-inda gobe insha Allah xan je"
tashi yayi cikin farin ciki, Allah-Allah ya ri'ka yi,Allah ya kaimu gobe ya d'auki mami ya kaita gidan su Nauwar,ta nemar masa aure.
washe gari da misalin 'karfe 4:00,suka isa gidan su Nauwar, mami ce ta shiga cikin gidan,shi kuma Hamdan ya xauna a mota, a falo ta tarar da Ammi da fu'ad suna hira, ita kuma Nauwar na kwance ba lafiya, bayan sun gaisa aka kawo mata abinci da ruwa,Nauwar ta gani kwance.
"ita kuma wannan me yake damunta na ganta kwance?"
"wlh na rasa me yake damunta,nayi tambayar duniya ta'ki fad'a min, ba tada aiki kullum sai tunani"
"oh!!! ai yaran xamani halinsu sai su, kayi ta tambayar yaro abinda yake damunsa ya'ki fad'a maka"
Ammi ce take tambayarta.
"ya Hamdan kwana biyu yayi mana yaji"
murmushi mami tayi
"hmm ai d'an nan naki ya xama d'an rigima Ammi, jiya yasa ni a gaba yana kuka, wai sai naxo wajen ki,shi a dole Nauwar yake so"
Nauwar na jin haka ta mi'ke idanunta a rufe, saboda tsananin kunya da farin cikin da suka lullu6eta.
ji tayi taci karo da mutum a hanya, tana bud'e ido taga Hamdan, wata kunyar ce ta 'kara lullu6eta, jayo hannunta yayi, ya tsura mata ido yana murmushi.
"kin ji sa'kona ko?"
gyad'a kai tayi alamar eh
" to yanxu menene amsar sakon da na bayar a baki?"
juyar da kai tayi tana d'an murmushi mai cike da farin ciki
"ina sonka"
tana fad'a ta juya a guje ta bar wajen da yake.
murmushi ya bi ta da shi, yarinyar tana matu'kar burge shi, xai yi alfahari da ita a duk lokacin da ya mallaketa.
*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
maijiddatijjaniadam@gmail.com
*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
3⃣6⃣
Haka suka cigaba da gudanar da soyayyar su, cikin farin ciki