Showing 60001 words to 63000 words out of 111837 words
Chapter 21 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
ya dubeta.
"kin san mai wannan kayan"
da sauri ta amsa masa da eh, me ya faru da Ammina.
"ki kwantar da hankalin ki babu abinda ya faru, ki biyo ni dan ganin abinda ya faru da ita "
bin shi tayi don tahowa da Amminta, sai da suka yi tafiya mai Nisa Sannan suka isa wajen. suna isa ta tarar da mutane a cike sun kewaye gurin suna salati, da hanxari ta karasa inda mutanen suke,
tambayarta suke yi
"wannan matar mahaifiyar ki ce?yana da kyau ki rika kulawa da ita,kina killaceta kin ga yanxu rijiya taxo ta fada, amma ana kokarin fito da ita, ki yi kokari ku koma gida wannan yawon baxai haifar muku da d'a mai ido ba, hankalin Nauwar yayi matukar tashi, bata san tsautsayin da ya kai Ammi bakin rijiya ba, hawaye ne suka rika sauka a kan fuskarta, tare da addu'ar Allah ya raba mahaifiyarta da wannan lalura ta tabin hankali, Saboda bacin ran da ya cika xuciyar ta gaba daya ta kasa gane komai biyu-biyu Kawai take gani.
kokarin fito da Ammi mutane ke yi, amma gaba daya taki yarda a fito da ita sai abubuwa take yi, don haka suka kira fire service (kwana-kwana)don su xo su taimaka masu, ba tare da bata lokaci ba suka iso gurin idan suka fara kokarin fito da ita.
Bayan sun cirota ne kuma Iskokin da ke jikinta suka bugeta
inda ta rika wani irin abu kamar xata mutu, duk mutanen da ke gurin sai da suka yiwa Ammi hawaye saboda halin da take ciki, taimakawa suka yi aka mayar da ita wajen da suke kwana, addu'a wani bawan Allah ya rika yi mata har aka samu ta farfado, sannan aka dauketa xuwa asibiti don a bata magani saboda duk taji ciwo a jikinta.
A Motar wani mutum aka dorata, basu minti biyar suna tafiya ba suka isa babban asibtin garin Gombe, ganin halin da Ammi ke ciki yasa aka yi saurin bata gado, allurar bacci aka yi mata, Dan tana bukatar hutu sosai. saboda buge-bugen da take yi sannan aka bata magungunan da xasu sassauta mata xafin da take ji a kanta, lokacin da mutanen xasu tafi sai da suka biya duk kudaden da aka caje su, sannan suka wuce suka tafi.
Godiya mai Yawa nauwar tayi musu har Bakin kofa ta raka su Sannan ta dawo, bata taba xaton har Yanxu Akwai ragowar mutane irin Wadannan ba, masu tainakawa Dan Allah.
*jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:15 PM] Writer: ππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
ππππππππ
5β£6β£
Kwanan Ammi biyu tana bacci bata farfado ba, a cikin baccin Nauwar ke dagata ta bata abinci da ruwa sannan ta mayar da ita ta kwantar, likitocin Asibitin na mamakin yadda Ammi da Nauwar ke xaune su kadai ba tare da wani nasu yaxo da niyyar duba halin da suke ciki ba, sai da suka fahimci ba su da galihu, daya daga cikin likitocin da yake duba su ne, ya kasa daurewa don haka ya shigo dakin samun Nauwar yayi ta xuba tagumi tana tunanin tare da xubar da hawaye, saboda bata san inda xata dosa ba idan Ammi ta warke, tasan likitoci baxa su taba daga mata kafa ta xaune musu a Asibiti ba kudi ba.
da sallama ya shigo dakin amma bai ji an amsa masa ba, kara matsowa yayi daf da inda take, sake yin sallamar yayi amma shiru ba amsa kwankwasa tebur din da ta kwantar da kanta a kai yayi, cikin nutsuwa ta dago ta dube shi, idanunta cike da hawaye.
samun guri yayi ya xauna shafa kyakkyawar fuskarsa yayi, sannan ya dubeta.
da sassanyar muryar shi yake mata magana
"sannu yan mata ya mai jiki"
share hawayen da ke kwarara a fuskarta tayi ta amsa masa.
"da sauki, sai dai har yanxu bata farka ba"
cikin kulawa ya dubeta kada ki damu, tana bukatar hutu ne shi yasa, amma baccin baxai xama matsala a gareta ba"
Tashi yayi xai fita, har ya kai bakin kofa ta kira shi.
"Doctor yaushe xa a bamu sallama?
lumshe idanu yayi, hannushi sanye cikin aljihu.
"kin gaji da xama ne?
gyada masa kai tayi alamar "a'a"
murmushi yayi inda kyawawan hakoransa suka bayyana.
"in dai kin gaji sai na sallame ku, naga kamar kin kosa ki koma gida kiga dadynki"
Bata san lokacin da hawaye suka fara sauka a kan kuncinta ba, bai san cewa ita yarinya ce mara galihu ba, wadda ubanta yayi watsi da rayuwarta baya son ganinta ko jin labarinta.
ganin yadda Nauwar ke xubda hawaye yasa Shi dawo wa da baya, wani abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har xuwa tafin kafarsa, tausayin yarinyar ya kama shi sosai
rarrashinta yake yi, amma ta kasa daina kukan neman guri yayi ya xauna ya cigaba da bata hakuri.
"Baiwar Allah kiyi hakuri, ban fada miki wannan maganar dan ta daga miki hankali ba, ki yafe min idan ni ne silar xubar hawayen ki"
Dago manyan idanunta tayi wadanda suka cika da kwallar bakin ciki, a hankali ta daga baki ta fara masa magana
"Baka bata min rai ba Doctor, kuma ba kaine kasa ni kuka ba,na tuna halin da nake ciki ne a yanxu, na auna shi da rayuwata ta baya, na tabbatar da cewa duniya ba tada tabbas xata iya juya maka baya a kowane lokaci, wannan dalilin ne yasa ni hawaye"
gyara xama yayi, sannan ya fara magana.
"ke kuwa wane hali kike ciki da har yake saka ki kuka idan kika tuna rayuwarki ta baya"
labarin rayuwarta da Amminta ta bashi, da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, da halin da suke ciki a yanxu"
wata ajiyar xuciya ya saki, sannan ya mayar da kallon shi gareta, cikin tausayawa yake mata magana
"Gaskiya rayuwar ku cike take da darasi masu yawa, kuma wannan jarabawa ce Allah yayi muku, yaga ko xaku cinye ko baxa ku cinye ba, hakuri da juriya.da jajircewa wajen addua shi ya kamace ku, da sannu Allah xai kawo muku agaji, sannan ki dage da nemar wa mahaifiyar ki magani, kinga dai halin da take ciki a yanxu abin a tausaya mata ne, ki cire damuwa ki kai wa Allah kukan ki, duk wani wanda ya xalunce ki da sannu xai ga sakamako Allah yana nan baya bacci"
Nauwar taji dadin Nasihar da Doctor yayi mata, kasancewar Doctor mutum ne mai ilimin addini da girmama jama'a, ba shida raina dan Adam ko yaya yake, wannan dalilin yasa duk wadanda suke xuwa asibitin suke kaunarsa, kuma suke masa adduar fatan alkhairi.
godiya tayi masa, sannan ya mike.
sake duban ta yayi
"ki rike abinda na fada miki da sannu xaki fita daga matsalar da kike ciki, sannan ina so ki rike mutuncin kan ki, kada ki yarda saboda damuwa da bakin ciki ki jefa kanki a wata rayuwa mara kyau"
kudi ya dakko ya bata.
har kasa ta tsugunnah ta karba tana masa godiya.
"ki rike wannan idan kuna bukatar wani abin sai ki min magana Insha Allah baxai gagara ba"
godiya tayi masa sannan suka yi sallama ya fita.
A kullum sai Doctor yaxo ya duba Ammi, ya kawo alkhairi mai yawa ya basu, sai dai har yanxu bata san sunan shi ba kuma ta kasa tambayar sa, kasancewar duk mutanen gurin kowa da Doctor yake kiran shi, wasu kuma su kira shi da ustax, saboda kamewar sa da tausayin da yake nunawa na kasa da shi.
sai da Ammi tayi sati daya tana karbar magani sannan aka basu sallama, tun lokacin da likitan da xai sallame su ya shigo dakin ya basu takardar Sallama Nauwar ke kuka,saboda bata san ina xata nufa ba, bata san ya xata yi da rayuwarta ba, diban kayan ta tayi, sannan ta rike hannun Ammi suka fito daga dakin, bakin gate suka tsaya tana jiran Allah ya kawo abin hawa ta hau ta tafi ko ma ina ne, dan ita ta gaji da wannan rayuwar.
horn taji ana mata don haka tayi saurin waiwayawa, Doctor ne a cikin motar, sanye yake cikin farin yadi wanda aka yi masa aiki fari, idanunsa sanye da farin glass yayi kyau sosai, murmushi ya sakar wa Nauwar wanda har sai da fararen hakoransa masu matukar kyau suka bayyana, rike da hannun Ammi ta karasa wajen sa, tsugunna masa tayi xata gaishe shi, nuni yayi mata da kyakkyawan hannunsa ta mike.
"ina xuwa na ganki da kaya ko har an sake ku"
cikin ladabi ta amsa masa.
"eh tun daxu aka sallame mu"
lumshe idanun shi yayi sannan ya dube ta.
"ku shigo na rage muku hanya"
bude mata kofa yayi ta shigar da kayanta, sannan ta shigar da Ammi, har ta samu guri a gidan baya xata xauna, magana yayi mata gami da bude mata gidan gaba.
"shigo nan mana"
budewa tayi ta xauna cikin nutsuwa, tunda ta shiga Doctor ya xuba mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta, yanayin yadda yarinyar ke gudanar da al'amuranta yana burge shi, yasan duk daga Inda ta fito ta samu cikakkiyar tarbiyya.
kafin su fara tafiya ne ya dubeta.
"ina ne wajen da ku ka sauka"
idanunta a kasa, a takaice ta bashi amsa
"cikin kasuwa"
xare glass din da ke idanun sa yayi
"cikin kasuwa kuma, me kike yi a kasuwa?"
share hawayen daya ya fara taruwa a idonta tayi.
"eh can xaka kai mu a nan ne inda muka sauka"
Tausayi ne ya mamaye masa xuciyarsa,gaba daya rayuwar yarinyar ta gama katse masa hanxarin sa duk wasu burika da yaci a rayuwarsa ya ajiye su, saboda duniya ba tada tabbas,cikin tausayawa ya kalleta.
"baxan iya barinki ki xauna a kasuwa ba, saboda guri ne da ya hada mutanen banxa da mutane na gari, idan kin yarda xan kai ki gidan mu ki cigaba da rayuwa, ina da kanne kamar ki da kuma wadanda suka fi ki, nasan xaki ji dadin xama a cikin su kuma xasu debe miki kewa"
shiru Nauwar tayi tana tunani, ita dai xuciyar ta bata amice da wannan taimakon ba, saboda akwai mutanen da suka taimaketa a baya kuma suka yi yunkurin cutar da ita.
shirun da yaji tayi ne, yasa yayi magana
"kina tunani ko? hmm tunani abu ne mai kyau, amma kada kiyi tunanin da xai sa miki kokonto a ranki,nayi alkwarin baxan cutar da ke ba, idan kin amince xaki bini mu wuce yanxu mu tafi"
kanta sunkuye ta bashi amsa.
"na gode da taimakon da kayi min Doctor na amince mu je"
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake tukin, amma can cikin kasan xuciyarsa cike yake da fargabar yadda xai tunkari Hajiyarsa da maganar xuwan su Nauwar, saboda Hajiya mace ce da bata san mutane kuma bata san talaka ya rabeta, haka ma sauran yan uwansa mata suke, basa kaunar hada hanya da talaka, shi kadai ne a cikin su Allah ya tsame yayi masa baiwar karamci da girmama mutane.
Addu'a yake yi sosai, Allah yasa kada ta watsa masa kasa a ido.
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:16 PM] Writer: ππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππππ
*A duk inda nake, a duk halin da na kasance baxan manta da ku ba masoyana na group din β¨TAURARIN MATA, kuna raina ina matukar alfahari da ku*
*Hadiza Abubakar muhd*
*Amina bashir yusuf*
*maryam Tijjani Adam*
*USummul*
*Aunty peedy*
*Subai'a S umar*
*sa'adatu mhd Yusuf*
*HafCweet*
*Khadija Tijjani Adam*
*Fresh khady*
*Aysha Galadima*
*masoya a sannu a Hankali duk xan rattabo sunayen ku*
5β£7β£
Tafiya suke cikin nutsuwa, shiru suka yi na wani dan lokaci, babu mai cewa da dan uwan sa komai, xuciyar Doctor kuwa sai dukan uku-uku take saboda tsoro da fargabar yadda xai tunkari Hajiya da maganar xuwan su Nauwar, ba su yi tafiya mai nisa ba suka iso unguwar new G.R.A da ke garin Gombe, daga jin sunan unguwar kasan unguwa ce ta masu hannu da shuni.
wani katafaren gida suka nufa, wanda aka kawata gaban gidan da shuke-shuke,ko ba a fada maka ba ka san gida ne,wanda ba na kananun masu kudi ba. horn yayi da sauri mai gadi ya kara so ya bude kofar get din, saka hancin motarsa yayi ya shiga gidan, tare da yin parking a wajen da aka tanada domin ajiye motoci, juyo da kallon shi ya yi ga Nauwar yana murmushi
"Alhamdulillah mun iso, da fatan dai baki gaji ba" a takaice ta amsa masa da"Eh" kokarin bude murfin motar ta fara yi xata fita, dakatar da ita yayi.
cikin kasalalliyar murya yayi mata magana
"ki daure ki bani hadin kai idan mun shiga cikin gida, kada ki nuna damuwa ko ki qi saki jikin ki, ki dauka kema 'ya ce kamar kowa, na tabbatar baxa ki yi da na sanin haduwa da ni ba Insha Allah"
dago kyakkyawan idonta tayi ta kalle shi, ba tare da ta furta masa komai ba, saboda ba karamin faduwa gabanta ke yi ba, ganin yadda gidan su Doctor ya hadu, duk kyawun gidan su da tsaruwarsa bai kama kafar na su Doctor ba, fargaba ce ta kara xiyartar xuciyar ta, ta kosa su gama abinda xa su yi su bar gidan, kasancewar gidan shiru yake, ba a jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, baxa ka taba xaton akwai mai rai a gidan ba.
kayanta ya shiga fito mata da su, sannan ya taimaka ya fito da Ammi, bai kara cewa komai ba, nuni kawai yayi da hannunsa ta taho su shiga ciki.
wata dogowar baranda suka bi, wadda kuma ita ce zata sada ka da kofar falon gidan, bude kofar falon yayi,subahanallah ta fada a zuciyarta saboda yanayin kayatuwar falon, umarni ya bata da ta zauna a kan kujera, kasa xama a kujerar tayi saboda bata san halin mutanen gidan ba, kada ta xauna a wulakanta ta, doctor na dawo wa ya ganta a kasa, bata rai yayi kadan sannan ya dubeta
"me yasa xaki xauna a kasa, ba na fada miki cewa ki saki jikin ki kamar yar gida ba"
hakuri ta bashi sannan ta koma kan kujerar ta xauna a tsora ce kamar wadda xa a kama.
ruwa da lemo ya kawo mata da kansa ya tsiyaya mata a cup ya mika mata, sannan ya xubawa Ammi Nauwar ce ta karba ta fara bata, bayan ya kammala xuba musu ne, ya mayar da kallon shi gareta
"jira ni kadan xan je na sanarwa da Hajiya maganar xuwan ku"
benen da ke cikin falon ya haye, inda a nan Hajiyar sa da sauran kannensa ke rayuwa, duk da cewa yaran na da bangaren su amma sun fi son ko da yaushe suna tare da Hajiya, kasancewar Hajiya mace ce mai son yayanta, shi yasa ko da yaushe suna tare suna hira musamman idan ba makarantar boko.
Da sallama ya shiga falon da Hajiya take wanda aka kawata shi da kaya na more rayuwa da jin dadi, sautin kida yaji yana tashi don haka da sauri ya karasa falon,
tararwa yayi kannensa fatima da ummy suna ta faman tirkar rawa, suna ganin shi suka tashi a guje suka shige daki saboda sun san halin doctor baya son shashanci, kashe kayan kidan yayi yana musu fada, saboda ya tsani wannan halayyar tasu ta jin kade-kade.
fuskar shi ba annuri ya nemi guri ya xauna.
gaishe da Hajiya yayi, cikin sakin fuska ta amsa
"sannu da xuwa yaya babba, da yake da wannan sunan take kiran sa wannan dalilin yasa duk yaran unguwar su, da yaran family din su suke kiran shi da yaya babba cikin nutsuwa ya dubeta.
Ina su feenah da zainab suka shiga ne naga ban gansu ba.
"na aike su gidan gwaggo ne su duba min jikinta"
Dabi'ar doctor ce ya saba indai ya dawo bai ga daya daga cikin yan uwansa ba sai ya tambaya, kasancewar mahaifin su ya rasu shi ne yake musu tarbiyya a matsayinsa na babban yayan su, saboda Hajiya bata iya tsawatar musu, duk abinda suka yi daidai ne a wajenta.
Tashi tayi ta miko masa flask din abinci, a sanyaye ya dubeta
"bar abincin nan Hajiya da wata magana naxo miki, idan mun gama mun warware xan fi jin dadin cin abincin"
farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, duk a tunaninta da maganar auren sa yaxo mata, saboda ta dade tana fama da shi a kan ya fito da matar aure amma yaki, duk yarinya da aka kawo masa ya aura sai yace bata yi masa ba, sai hakura aka yi aka kyale shi.
cikin kulawa ta sake duban shi.
"kai nake saurare fa, amma kayi shiru"
shafa fuskar shi yayi gami da sauke wata ajiyar xuciya.
"dama wasu bayin Allah na gani a cikin wani hali na rashin dadi, wanda duk wani mai imani idan yaji tarihin rayuwar su sai ya tausaya musu, wannan dalilin yasa naga cewa kamata a ce mun taimaka musu, mun fitar da su daga halin da suke ciki, saboda mu ma bamu san ta inda Allah xai taimake mu ba. A asibitin mu aka kwantar da mahaifiyarta bayan an sallame su kuma ba su da inda xasu je, shi ne na kawo su gidan nan dan nasan baxa su rasa wajen kwana ba"
wata matsiyaciyar harara Hajiya ta watsa masa.
"sannu uban iyayi sarkin tausayi, daga ganin mutane ka yayo min su,ka kawo su gidana, kasan sharrin da ke tattare da su, yanxu a xamanin nan mutum ba abin yarda ba, me yasa xaka yi min wannan gangancin da rayuwa, to wlh tun wuri ka kwashe su ka fitar min daga gida, dan baxa ka kawo min masifa har daki ba"
"ki fahimce ni Hajiya baxan kawo abinda xai cutar da ku ba, saboda duk abinda ya same ku ni ya samu, ki taimaka ki dubi halin da suke ciki, ki tashi mu je ki gansu nasan kema xaki tausaya musu"
tashi suka yi suka fita falo dan ganin irin mutanen da ya kawo musu, suna fita su fatima da ummy suka bi bayan su,dan ganewa idon su ba'kin da aka kawo musu har gida.
Tun daga nesa Hajiya ta hango su Nauwar, tsayawa tayi taki karasawa wajen su.
sunan doctor ta kira
"Abdallah" sai a lokacin Nauwar taji sunan shi
"ka rasa wanda xaka kawo mana gida sai mahaukata, idan taimakon ne me yasa baxa ka basu abinda ya kamata ba sai ka kawo mana su gida, to wlh baxai yiwu ba sai sun fita