Showing 3001 words to 6000 words out of 111837 words

Chapter 2 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

gunji da buge-buge a haka suka kasance har Allah ya wayi garinsa.






da sanyin safiya ta fita don ta samo musu ruwan da xa su yi alwala, sannan ta samu wanda xata wanke mahaifiyarta da shi.






fita tayi waje sannan ta kulle kofar kangon, tafiya kadan tayi ta tarar da wani burtsatsai ta tsaya ta debi ruwan ta dawo masaukin da suke, ba tare da bata lokaci ba ta fara alwala, ta nemi Amminta tayi, yau ma kin yi alwalar tayi don haka ta kyaleta, ta tafi don yin sallah.






bayan ta idar da sallar tayi addu'o'i sannan ta matso wajen Amminta don ta tsaftace ta daga dattin da tayi, da kyar ta bari tayi mata wankan, ta canja mata kayan da aka kawo musu sadaka jiya.






sai da ta nutsu sannan ta fara tunanin yau kuma ina xata dosa don nemar musu abinci, ta fuskanci yau Amminta a yunwace take, don duk abinda ta gani kusa da ita kokari take ta kai bakinta, don haka yau ma ta yanke shawarar kulle kangon ta fita neman abin karin kumallon safe.






"tashi tayi don ta fita, cikin hanzari Amminta ta riqo kafarta alamar ba inda xata je, sai ta koma ta xauna ta fara rera mata wakar da take mata tun tana yar shekara 8, tana rera mata wakar tana dariya, a haka har ta saki jiki da ita ta sakar mata kafarta.






fakar idonta tayi ta fice da sauri, har ta kai bakin kofa tana cigaba da wani gunji alamun ta dawo take nufi, amma babu yadda xa tayi haka ta kulle kangon ta fita ta barta, haka ta cigaba da dukan kofar har tayi nisa tana jin sautin bugun da take yi.




"sauri ta rika yi a tafiyar saboda tana tsoron kada yunwa ta ishi Amminta ta fara cikin kaxanta, wani mutum ta iske yara a kewaye dashi yana musu sadakar waina, sauri ta rika yi ta karasa wajen, sai dai kash!!! tana karasawa wajen har ya gama sadakar sai hakuri ya bata.






juyawa tayi zuciyarta cike da 6acin rai da damuwa, sauri ta cigaba da yi, tana tafiyar tana hadawa da addua Allah ya dubeta ya bata abincin da xata samu ta ci.




tuwon dawa taci karo da shi a hanya da alama *AL-MAJIRAI* ne suka yar da shi, da fara'arta ta karasa wajen da yake ta dauka ta karkade kasar jikinshi ta samu leda ta nade tuwon da shi.






bakin wani famfo ta samu ta fara wanke tuwon sannan ta karasa wani kanti ta sayi sugar da leda, hanyar komawa gida ta nufa, tana tafe tana godiya ga Allah da ya bata abinci ba tare da ta sha wahala ba.






"tura kofar kangon tayi, yau ma da sallama ta shiga, Ammi na ganinta ta taso da farin ciki, tana mata murmushi, ita ma murmushin ta hau yi mata, rikota tayi ta xaunar da ita akan kwalin. *"Ammi yau tuwo xamu sha, kina so ko"*? ishara tayi mata da kanta alamar eh tana son sha.






saka tuwon tayi a leda ta fara dama shi da ruwa sannan ta zuba sugar, cikin nutsuwa take bata tana sha, a haka har sai da ta shanye gaba daya, ita kuma sai ta side ledar ta sha ruwa.




"A haka suka kasance har zuwa sallar azahar, bayan tayi sallah, ta yanke shawarar sake fita don ta nemo abincin rana da na dare, yanxu ma sai satar hanya tayi ta fita ba a son ran mahaifiyarta ba.






yau kai tsaye kasuwa ta nufa, don tana da yaqinin anan sai tafi samun taimako, rumfar kasuwar ta rika lekawa tana neman taimako, yau kam ta fita a sa'a don abinda ta samu ya kusa 500, don haka ta tsaya ta siya kwaki da sugar da sabulun wanka.


*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRAH*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*


*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


*β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*Gaisuwa ce ta musamman nake mikowa gareki, yar uwa babbar yaya gareni Hajiya Ameena Basheer (Maman siyama) Allah ya raya, Sadeeq, siyama, saudah, safiyya & suhaila, ina godiya da kulawarki gareni, ana tareπŸ€πŸ’―*

*wannan shafin gaba dayanshi naki ne halak malak Dr. Aysha Abubakar ishaq, ina godiya da kulawarki gareni, Allah ya bar zumunci* 🀝






πŸ”Ÿ




*T*ana dawo wa kangon da suke kwana ta nufa, da sallama ta shiga ta iske Amminta na wasa da kasa tana ganin yartata sai ta saki dariya da alamar murna da farin cikin ganin d'iyarta ta, 'karasawa wajenta tayi ta rungumeta "Ammi kin san yau me muka samu kuwa?? kwaki na samo mana..... ai kina son shi ko Ammina? kallonta kawai take ba tare da tace mata komai ba, sai murmushi da take yi, tana wasa da 'yan yatsun d'iyartata, kallo take mata mai cike da soyayya da tausayi, sai dai babu bakin magana ballantana ta gode mata.






"cikin nutsuwa ta janye hannunta gareta, kallonta tayi tana mata murmushi. Ammina xan fara wanke mana kaya sai na jika mana kwakin kin ji, ita dai bin ta tayi da ido kawai.






"tana mi'kewa ta ri'ke mata hannu gam ta'ki sakinta, sai ta koma ta xauna. "Ammina ba kya son na tafi na barki ko?nima bana son nisa da ke, dole ce ta sa nake tafiya na barki. murmushi mahaifiyar take yi tana shafa kan yarinyar tata, tausayin *Amminta*ne ya kara kamata, ji take a ranta ina ma dai ta rika d'aukanta suna tafiya, sai dai ba tada halin yin hakan, cigaba da lalla6ata tayi a kan ta saketa, amma taki sakinta. sai ta mika hannunta ta wanke kwakin ta xuba sugar ta fara bata, sai da tasha ta 'koshi sannan ta daina bata, cigaba da lalla6ata tayi har sai da tayi bacci sannan ta tashi ta fita.





"kayan su ta dauka ta nufi wani famfo da almajirai ke d'iban ruwa don ta wanke musu , da isarta wajen tayi sa'a babu kowa, don haka ba tare da 6ata lokaci ba ta fara wanke tsummokaransu, tana yin wankin tana tunanin yanzu a haka zasu cigaba da rayuwa ba tare da kulawar dangi ba, ko kuma mahaifi. ya Allah kana sane da mu, a wajenka muke neman taimako.






"tsawar da ta ji an daka mata kamar daga sama har sai da tayi kamar xata kifa qasa ita ce, ta dawo da ita hayyacinta. "ke *AL-MAJIRA* 'yar mahaukaciya matsa ki bamu guri muna da abin yi a wajenmu,kin wani xo kin tara mana tsummokarai masu wari a waje, an fad'a miki nan famfon mahaukata ne? matsa dallah can, kada ki shafa mana qarxuwar hauka. d'agowa tayi ta kallesu idanu cike da hawaye tace Allah ya baku hakuri. shigewa tayi ta barsu a wajen suna ta mita har da xaginta, har tayi nesa dasu basu daina nunata suna aibata ta ba.




"mutane ta hango cike da bakin kofar kangonsu, tana ganin tarin jama'ar taji gabanta ya fadi, a tunaninta ko wani abu ne ya sami Amminta, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta shiga karantawa, 'kosawa tayi ta isa bakin wajen, saboda ta ganewa idonta abinda yake faruwa da su. tunda ta kusanto wajen take jin maganganu sama-sama da alama dai taron nasu ne, gani tayi wasu mutane sun bude 'kofar kangon suna jefo musu kayansu waje, a sanyaye take tafiya jan kafa kawai take yi, babu abinda yake sauka a fuskarta sai hawayen takaici. ganin yadda ake jan Amminta ne yasa ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka, wasu mutanen har da dukanta saboda gaddamar da ta yi musu.




masifa suke yi sosai"wallahi baku isa ba, baxa ku qara kwana a anan ba, yau-yau d'in nan sai kun bar layin nan, banda bala'i da masifa mutane ba a san asalinku ba, kawai kun xo kun tare a kangon mutane, to wallahi baxa ta sa6u ba sai kun tashi kun bar wajen nan"




kuka mai tsanani take yi "dan Allah ku taimaka mana, wlh ba mu da kowa sai Allah sai ku, idan ku ka koremu bamu san inda xa mu je ba.




"rufe mana baki munafukar banxa da wofi, duk matar arxiki tana gidan mijinta, kuma duk yarinyar arxiki tana gidan iyayenta, idan kuma mahaukaciya ce tana gida an killace ta, wulakantacciya ita ke bin kangwaye tana kwana, watakila ma a garin asirinku ne na mata, ku ka yi, ya koma kanta, kasa cewa komai tayi, saboda ko tayi maganar ma baxai saurareta ba.




muryar wani mutum taji "ku wai dan Allah ba ku da imani ne? banda kuna da karamin tunani wad'annan mutanen sun yi muku kama da mugwaye, ku riqa aiki da lissafi mana.




"kai dallah gafara can shi. mugu yana da kama ne, kana ganin yadda matar nan ta takurawa yayanmu, ba halin a aikesu sai duka da jifa da dutse, to me yayi xafin haka, yara da unguwarsu ba a isa a
hanasu sakewa ba"




"dan Allah ku yi hakuri ku tausaya mana, ku duba halin da muke ciki, idan kuka koremu daga nan wlh ba mu san ina zamu dosa ba.




"ku tafi 'karshen duniya ma ina ruwanmu, ai duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba"




"da 'kyar aka sasanta suka barsu dan su cigaba da kwana, amma da sharad'in sai an d'aurewa Ammi 'kafa, a cewarsu wai tana takurawa yaransu, haka ta yarda aka daureta ba don ranta ya so ba, saboda tasan sharri aka yi wa mahaifiyarta, Ammi ita da ko fita bata yi, a ina taga yaransu har ta dakesu.




hawaye masu xafi ne suka cigaba da sauka a kan kuncinta, kayansu ta rika kwashewa tana shigar da su ciki. sannan ta rike hannun Amminta don ta shigar da ita ciki, suna tafe tana d'ingisawa kamar mai ciwon 'kafa saboda daurin da aka yi mata.




"xaunar da ita tayi ta rika duba gurin da mutanen suka daketa, tana bata hakuri gami da rarrashinta, ita dai bin ta take da ido ba abinda take iya ce mata.




sallama taji kamar daga sama, wannan matashiyar yarinyar ce ta sake dawowa dauke da kwanon abinci, yau dai babu alamar tsoro a tattare da ita, da karfinta take takawa, 'karasowa kusa da ALβž–MAJIRA ta yi, don a yanxu ta fuskanci ba ita ce mai lalurar haukan ba, don haka ta mi'ka mata hannu don yin musabaha, ita ma hannun ta mika mata suka gaisa. Ta mika mata kwanon abincin tayi mata godiya mai yawa sannan ta karbi kwanon da ta kawo musu abinci jiya.




har bakin kangon ta rakata, har ta juya don ta kulle 'kofa, sai taga ya dace tasan sunan yarinyar da dalilin da yasa take tausaya musu haka, duk da cewa bata san asalinsu ba.






"murmushi tayi sannan tace ni sunana *Saimah* gidanmu yana nan bayanku, mahaifina ne ya ganki kina bukatar taimako shi ne ya sanarwa momyna yace a rika baku abinci, sbd yaga halin da kuke ciki na talauci ga shi mahaifiyarki tana da lalura, mu a xatonmu ke din ma ba ki da lafiya sai yanxu muka gano lafiyarki kalau.




a jiyar xuciya tayi sannan tace wlh lafiyata kalau, halin da ya samu mahaifiyata ne yasa ake min kallon mahaukaciya, Amma sam ba nida lalaurar hauka.




"ko xaki iya fada min matsalarku ni kuma na sanar a gida, ko Allah xai sa a mu iya taimaka mu ku??hawaye ta cigaba da sharewa, na tabbatar baxa ki iya yi mana maganin matsalarmu ba, saboda abubuwa ne masu yawa suka faru da mu.






'kara tambayarta saimah tayi ko kin san lokacin da amminki ta kamu da wannan lalurar? eh "na kiyaye wasu abubuwa saboda a lokacin ban fi shekara tara ba tun daga wannan lokacin muka bar gidanmu dangin mu da garin mu muka dawo wata rayuwa tun daga sannan muke fuskantar qalubale, kala-kala idan muka je wani wajen ma cewa suke ni ba yar halak bace.......




tausayi ne ya bayyana a fuskar *Saimah* tabbas kina cikin wani yanayi wanda kuke bukatar a jawo ku ajiki,don kuji sanyi da nutsuwa a rayuwarku. xan je na tambayi Abbana a kan ya baku wani d'aki asoron gidanmu ku karasa rayuwarku anan kafin Allah yasa a ga danginku,sbd xamanku anan ba dadi.




"bata san lokacin da ta yi wani murmushin farin ciki ba. "dama har yanxu akwai irinku masu tausayawa bayin Allah,... Allah ya biyaku da aljannah"




"kada ki damu ki daina godiya ai komai kayi kanka ka yi wa.kuma alheri danqo ne ba ya faduwa kasa banxa.




"Ammi suka gani ta kwance daurin kafarta tana kokarin kama katanga xata haure ta gudu, don haka da hanxari suka 'karasa wajen tare da yin salati, "ina xaki je?suka fada tare. muxurai kawai take yi, bata ce musu komai ba,sai kawai gani suka yi har ta d'ane katangar , ga shi su kuma baxa su iya hawa ba, dan haka suka fita waje suna neman d'aukin jama'a, sai dai kafin su dawo sai filin wajen suka tarar.


kuka ALβž–MAJIRA ta fara yi. Ammi ki taimakeni ki dawo ba nida kowa sai ke, idan kika tafi kika barni waye xai karbeni a duniyar nan. kukan da take yi shi ya bawa kowa tausayi a wajen, don haka wasu samari suka yanke shawarar bin ta.


*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*AL-MAJIRAH*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*

*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
*β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*Alhamdulillah, Allahu mun gode maka bisa da ni'imar da kayi manaπŸ‘πŸ»A Yau Allahu madaukakin sarki ya nufemu da kammala karatun mu na degree, Allah ya bamu abinda muke nema na sakamako kyakkyawa*πŸ‘πŸ»






*congratulation MARIAM TIJJANI ADAM on your POP (NYSC) I Wishes all d best, in all your indeavors may mighty Allah, guide help and give you all d best*






1⃣1⃣



*C*ikin xafin nama Ammi ta sheqa da gudu, take samarin suka bita, amma ina tuni ta yi musu nisa sosai, don haka suka yanke shawarar su samu machine su bi ta, gudu take yi ba kak'kautawa, don haka suka nemi taimakon mutane akan su riqe ta, cikin taimakon Allah suka samu nasarar kamata. dawo da ita suka yi kangon sannan suka bawa Almajira shawara ta daina fita ko'ina gudun kada ta sake guduwa, godiya ta yi wa samarin sannan suka yi sallama da saimah ta wuce gida.


"zaunar da Amminta tayi tana xubar da kwallah, ita kuma Ammin sai xare idanu take yi tana naushinta da hannu".




"Ammi ina xaki je alhalin baki san kowa a garin nan ba, kina son na shiga garari ne Ammina? kece farin cikin rayuwata, ke kadai nake gani naji dadi, idan kika tafi kika barni ina xan sa kaina, muxuranta ta cigaba da yi, tana 'kara kai mata duka, sai dai tana kawo hannunta Allah yake bata sa'a sai ta kauce.


********************************


saimah ce a gaban mahaifinta ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta. kanta na kasa ta kasa fad'awa mahaifinta abinda take son isarwa gareshi, ganin shirun yayi yawa, yasa ya fara magana.


"yar lelen Abbanta da magana kenan tunda naga kin yi wannan gurfanan." Shiru tayi da d'an lokaci sannan tace, eh!! Abbah dama......dama cewa nayi da xamu taimakawa su AL-MAJIRA mu basu d'akin soro su xauna, saboda a can kangon da suke ba su da daki, ga shi damina ta kusa sauka"


shiru yayi na d'an lokaci " haka ne Autar Abbah, kin yi tunani mai kyau, saboda Allah yana taimakon bawansa, matukar bawan yana taimakon d'an uwansa. yanxu kije xan yi waya kasuwa a taho musu, da ledar tsakar daki da labule xuwa yamma sai mu je mu taho da su".


hawayen farin ciki ta fara yi "Abbah na gode Allah ya saka da alheri Allah ya 'kara arziki" Amsawa yayi da ameen yar Abbanta Allah yayi miki albarka.


"kai tsaye waje ta fito, ta nufi wajen su AL-MAJIRA, tararwa tayi ana kokawar mayar da Ammi cikin kangon saboda ta sake yunqurin fita, da kyar aka samu aka shigar da ita. shiga cikin kangon tayi fuskarta cike da annashuwa, take sanar da ita yadda suka yi da Abbanta, farin ciki ne ya lallu6e AL-MAJIRA har ta rasa bakin godiya sai kuka da take yi, har kasa ta tsagunnah tana yi wa saimah godiya, tashinta tsaye tayi ta dafa kafadarta, kada ki damu kawata da sannu xa kiyi rayuwa ta jin dadi ki koma kamar kowace diya mace.


"godiya ta 'kara yi mata, ban ta6a tunanin xan yi rayuwa mai dadi ba ko da a mafarki, saboda tunda muka bar gida, bamu sake had'uwa da wanda ya tausaya mana ba, koda da ruwan sha ne ballantana musa rai da wajen kwana, sai gashi Allah ya yanke mana wahala, tunda na hadu da ke na bar fargabar abinda xa mu kai bakinmu, shi yasa a kullum nake muku addu'a, yadda ku ka sakamu farin ciki, ku ma Allahu ya yaye muku bakin cikin duniya da lahira.


"amsawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login