Showing 24001 words to 27000 words out of 111837 words
Chapter 9 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
d'in ta koma d'aki.
fad'awa jikin Amminta tayi tana kuka.
"lafiya na ganki haka Nauwar,me yake damunki wa ya ta6a ki,kike kuka da sassafe haka?
"Ammina na so na fad'a miki abinda ke faruwa tun jiya, amma Fu'ad ya dakatar da ni, Magaji ne yace yana so na, yanxu kuma ina kitchen ya shigo yana ta6a kayan da nake aikin da su, wlh Ammi ku raba ni da shi, idan ba haka ba sai na 6ata masa a kan maganar nan"
"ki kwantar da hankalin ki daughterna ai ba a aure dole, kuma ai Magaji ba tsaranki bane, da har xaki tayar da hankalin ki a kansa, tashi ki koma ki cigaba da aikin ki, Allah ya fi shi, ni dai bana son na ganki kina damuwa"
tashi tayi ta koma kitchen d'in ta cigaba da aikinta, duk maganar da yayi mata baya samun amsa, haka ya gaji ya kyaleta ya koma gurin innah karime.
A d'aki ya samu innah karime, tana karanta wasu sihirce-sihirce da Boka gobe da nisa ya bata, kyaleta yayi har ta kammala, sannan ta juyo ta kalle shi, kirari ta fara yi masa.
"Magaji, Magaji, Magajin gida da gari, angon Nauwar idan mai duka ya so"
"murmushi ya ri'ka yi, ya ji dad'in kirarin da ta yi masa, ai har yaso d'in ma innata,don akwai alamun nasara, amma ina ganin sai mun mi'ke sosai, don ganin an shawo kanta, an cusa mata soyyata, kuma ina so ki yi wa Alhajin magana da kan ki, saboda yasan da maganar tun da wuri.
"Duk wannan mai sau'ki ne, Alhaji mudi namu ne sai abinda muka ce shi xa a yi, yarinyar ma xata xama tamu nan ba da dad'ewa ba, wuyarta dai mu je gurin Algafarta malam shikenan an yi an gama.
"Yanxu yaushe kike ganin xamu je? don wlh na 'kosa na mallaketa, yarinya shekara goma sha biyar ba mashinshini ai abar tausayi ce"
"ina ganin mu je gobe, saboda ba a bori da sanyin jiki, To Allah ya kaimu innata"
********************
Da misalin 'karfe 4:30 Hamdan ya shirya tsaf don xuwa gidan su Nauwar yi musu lesson, key d'in motar shi ya d'auka ya fito, yana 'ko'karin kulle 'kofar d'akin shi ne, ya ci karo da maminsa.
"Alhamdulillah dama gurinka xan xo yanxu, tun safe nake jiran fitowarka, me kake yi haka ne a d'aki tun safe ko break fa baka xo kayi ba"
sosa 'keyar shi yayi, "am wlh mami ina ciki ina wani aiki ne, kinga gobe Monday idan ban samu na kammala ba abin xai yi min yawa"
"to ai bai kamata a ce aiki ya hana mutum cin abinci ba, irin haka ne wata cutar take shiga jiki, saboda an bar ciki da yunwa, ni dai bana son haka"
"haka baxa ta sake faruwa ba insha Allah mamina"
"na gode Allah yayi maka albarka" amsa mata yayi da ameen.
Gyaran murya tayi sannan ta mayar da kallon ta gare shi, "Hamdan ina da muhimmiyar magana da kai, nayi wani naxari ne na fahimci cewa kai gaba d'aya aure baya gabanka
kafi son ka cigaba da xama a gauro, ni kuma hakan ya fara damuna, ina son na ganka da iyali tunda dai ka kammala karatunka, ga shi har Allah ya baka abin yi, na yanke shawarar kaje gidan Hajiya maryam ka nemi auren Ajmal, don yarinya ce mai tarbiyya kuma duk inda ake neman cikakkiyar mace ta kai"
"Rawar baki Hamdan ya fara yi, wlh mami ni tsarin yarinyar sam bai yi min ba, ta fiye rawar kai, ni kuma a tsarina bana son mace haka, kuma ni gaskiya bana sonta gaba d'aya, sam ban yarda da tarbiyyarta ba, in dai aure kike son nayi, ki bari xan nemo mace da kaina, wacce xa kiyi alfahari da ita".
"musu xa kayi min a kan xa6in da nayi maka,ka fi ni sanin dai-dai ne ko ya aka soma? umarni nake baka fa ba shawararka na nema ba, don haka can nake son kaje ka nemi aure"
jikin shi ba karfi ya tashi, ya nufi bakin mota, a sanyaye ya yi wa motar shi key sai gidan su Nauwar, yau a compound ya tarar da su xaune a kan kujera suna ta nishad'i abin su, kujera ya ja ya xauna, gaishe da shi suka yi sannan suka d'akko littafansu suka fara karatu, suna karatun suna had'awa da wasa da dariya, magaji ne ya hango su daga can nesa, don haka kishi ya kama shi ya je ya fad'awa innah karime xuwan Hamdan, masifa da xage-xage ta ri'ka yi, a wane dalilin xa a kula mishi mata, shawara ta bashi a kan ya ciko bokiti da ruwa yaxo ya watsa masa.
ai kuwa haka aka yi magaji ya ciko bokiti ya shammace su, ya watsa shi jikin Hamdan, a firgice ya mi'ke..........
*Jeeddahtulkhair*π
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
Maijiddatijjaniadam@gmail.com
*β»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*wannan shafin sadaukarwa ne gareku'yan uwana ina yin ku yasin*
*SUMAIYYAH SANI KYAUTA*
*AISHA SAMMANI ALATU (maman sultan)*
*RAHINATU IBRAHIM (maman sadiq)*
*ina yin ku muna mugun tare*π€
ππππππππ
*jinjinar ban girma gareki AYSHA ALI GARKUWA, ina taya ki murnar kammala litttafinki na RUBUTACCEN AL'AMARI, muna godiya da yadda kika fadakar kika nishad'antar da mu, Allah ya 'kara miki basira, Allah yasa ki fi haka, ina yin ki, muna tare irin sosai d'in nan*
ππππππππ
2β£8β£
*A* firgice Hamdan ya mi'ke, cikin mamaki yake kallon Magaji, me ya faru,Wannan wane irin jahilci ne, me nayi maka xaka min haka?
Kallon raini Magaji yake wa sannan ya dube shi, cikin tsawa yake masa magana.
"Menene dalilin ka na kula min mata, ka dad'e da sanin an mallaka min ita, sauran 'kiris ta xama iyalina, raini ne yasa ka kulata, ko kuma wula'kanci? to wlh ka sani wannan shi ne na farko kuma na 'kashe, In dai ka cigaba da yi min haka, ka fara ganin haukana kenan"
Murmushi Hamdan yayi masa, "tabbas ko baka fad'a ba,aikinka ya tabbatar min da cewa kai cikakken mahaukaci ne, kuma ka nuna min cewa kai a cikin jahilan ma irin murakkaban nan ne, sannan kuma ina son tabbatar maka da cewa fadar Nauwar ta fi 'karfin 'kaxamin mutum irin ka, ni baxan tsaya nayi cacar baki da kai ba, saboda nasan 6atawa kaina lokaci xan yi, babu komai tsakanina da kai sai dai nasiha.
Mari Magaji ya kai masa, ai kuwa nan Hamdan ya xuciya shi ma ya kai masa mari, innah karime ce ta jiyo hayaniyar su don haka da gudu ta fito, tana ganin halin da Magaji ke ciki ta fad'i 'kasa tana burgima gami da salati xa a hallaka mata d'an jika. Ita kuwa Ammi na d'aki bata ma San abinda ake yi ba, sai masu gadin gidan ne suka xo suka raba su.
Gefe ya koma yana ta haki, ita kuwa innah sai xage-xage take yi, tana aibata Hamdan.
"Dole ne Alhaji ya d'auki mataki ya hana wannan d'an banxan yaron xuwa gidan nan gaba d'aya, ai ba gidan ubanka bane, saboda na fuskanci kai ba d'an arxi'ki bane, tsiya ce take kawo ka, da neman bala'i, banda masifa an yi wa yarinya miji sai bibiyarta kake yi, kana janye ra'ayinta Wato ta bujire wa iyayenta ko? Kuma an yi na farko an yi na 'karshe,baxa mu sake Kwana a gidan nan ba, naga alama wannan yaron so yake ya kashe min kai, wancan karon haka ya karya ka, yanxu kuma sun had'u suna 'ko'karin kashe ka"
Cikin gida suka koma suka had'o kayan su, sannan suka dawo bakin gate suka xauna suna jiran dawowar Abban su Nauwar.
Bayan sun fita ne fu'ad da Nauwar suka shiga d'akin da aka bawa su innah karime, suna shiga suka ci karo da wasu layu, sannan ga kan miciji wanda shi ma layun aka cusa a ciki, a firgice suka fito daga d'akin don haka suka sanar wa Ammin su abinda suka gani.
Tashi tayi da kanta ta shiga d'akin tayi bismillah ta d'auki abin, sannan tasa aka 'kona mata, tasan ba komai bane face kayan asirin su innah.
Kuka suka ji yo daga waje don haka suka yi saurin lekawa, innah suka gani sunkuye gaban Abbansu tana karanta masa labaran karya da gaskiya.
"Wlh Alhaji yaron nan da yake xuwa wajen yaran nan, yana koya musu karatu ne, ya samu Nauwar ya rungumeta, shi ne Magaji yayi masa nasiha, Wai a kan wannan dalilin ya hau shi da duka kamar xai kashe shi, kaga wancan karon ma haka yayi masa ya karya shi, ni dai wlh Alhaji baxan sake Kwana a gidan nan ba, saboda tsoron yaron nake ji, naji yana cewa xai aiko a kashe mu, tana maganar tana sharar hawayen munafunci.
A fusace Abban Nauwar ya shiga cikin gida, tarar da Hamdan yayi suna tattauna abinda ya faru tsakanin sa da Magaji.
Ammi ce ke masa nasiha
"Me yasa xaka daka ta tashi, kasan ba hankali ne da shi ba, 'kauye har yanxu na damun shi"
"Wlh Khalaty muna xaune ya Watsa min ruwa, sannan ya mareni Kin ga duk ha'kurina dole nima na harxu'ka.
"Haka ne amma dan Allah a ri'ka ha'kuri ana kai xuciya nesa"
"I will insha Allah my khala"
Abban Nauwar ne ya shigo ko sallama babu, ranshi a 6ace ya wuce ya shiga 6angaren shi, ba tare da ya kula kowa ba, tunanin abinda ke faruwa ya fara yi shi kanshi, abubuwan sun fara d'aure masa kai, tambayar kanshi ya ri'ka yi, ko menene dalilin ma da ya kawo su innah karime gidansa, da har hakan ke faruwa, yasan 'yar shi kamila ce, sannan Hamdan ma mutum ne mai hankali, ya tabbatar da cewa baxa su aikata abinda aka fad'a masa ba. Alwala ya daura ya fara sallah,yana adduar Allah ya fitar da shi daga cikin duhun da yake ciki.
Su kuwa su innah karime suna waje suna ta farin ciki,a tunanin su ana can ana ci wa su Nauwar mutunci, shirun da suka ji ya yi yawa ne yasa suka le'ko, sai suka tarar da su tare da Hamdan, ana ta shan hira ana nishad'i,Hamdan na ganinsu ya sako wata hirar daban don kawai su ji haushi.
"Dear kullum 'kara kyau kike yi a cikin idanuna, addu'ata a kullum Allah ya mallaka min wannan kyakkyawar fuskar, na ri'ka kallonta har abada"
Kashe masa ido d'aya Nauwar tayi
"Ni dai xaulaya na kake yi yayana ai ka fi ni kyau Allah"
Suna hirar Fu'ad na taya su ana dariya, duk dan su 'konawa magiji rai.
Mamaki ne ya kama su. Ko menene dalilin da yasa Abban nauwar bai d'auki wani mataki ba, kishi ne ya kama Magaji, ya rasa ina xai sa Kansa, saboda jin abinda su Nauwar ke fad'a jikin su a sanyaye suka shige d'aki.
*jeeddahtulkhair*π
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
maijiddatijjaniadam@gmail.com
*β»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
ππππππππππ
*Dan Allah masu karatu ku yi ha'kuriππ»saboda rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon lalacewar da wayata tayi*
2β£9β£
*S*una shiga suka tarar da komai na d'akin an hargitsa musu shi, mamaki ne ya kama su, har suka rasa bakin magana, innah ce tayi 'karfin halin tambayar Magaji.
"Wane ne ya shigo mana d'aki yayi mana kaca-kaca haka?"
"nima dai mamaki nake innah, duba ki ga duk kayan amfanin mu an kwashe, idan fa babu abubuwan nan akwai matsala innah,kashin mu ya bushe, duk wani shirye-shiryen mu an rusa mana shi"
shiru innah karime tayi tana naxarin maganganun magaji.
"kin yi shiru innah, idan fa ba mu yi magana an fito mana da kayanmu ba, Allah mun lalace a cikin gidan nan"
"To naji, wuce mu je nayi tijara a bamu kayan mu"
fita falo suka yi, innah karime na ri'ke da 'kugu take magana cikin tsawa
"Uban waye ya shiga d'akina ya yi min bincike?"
shiru suka yi mata suka cigaba da hirar su.
"nace uban waye ya bincike min d'aki? tambayar ku fa nake yi.
Nauwar ce ta mi'ke, "Mu ne muka shiga, yau duk abinda ku ke ta'kama da shi na asiri ya xo 'karshe, mun 'kone shi a gidan nan, kuma insha Allahu, Allah baxai 'kara baku nasara a kan mu ba har abada.
kallon mamaki innah take mata, cikin 'karfin hali ta fara magana.
"Nasara tuni mun ci mun gama, tunda ko yanxu na nemi ku bar gidan nan sai kun bar shi, kun ga kuwa ko yanxu an ci ku da ya'ki,kuma wlh ku fito min da abubuwana, idan ba haka ba ranku gaba d'aya sai ya 6aci a gidan nan".
Dariya suka ri'ka yi mata suka mayar da ita tamkar wata sabuwar mahaukaciya, don haka ta kwashi jiki sai 6angaren Abban Nauwar, tarar da 'kofar shi tayi a kulle, don haka ta ri'ka bugawa kamar xata karya 'kofar d'akin, a firgice ya farka daga bacci ya 'karaso bakin kofar, kamar a mafarki ya ga innah karime, tambayar ta ya fara yi.
"lafiya innah yaushe ku ka xo garin nan ban sani ba" fuskarta cike da mamakin maganarsa ta kalle shi,
"yaushe muka xo ma kake tambayata."
"Eh mana wlh ban san kun xo ba, ya su baffa?
"Ba wannan ne abinda ya kawoni ba, na fi wata biyar a gidan nan, amma saboda cin fuska kace wai baka ma san ina nan ba, to ka fito ka raba ni da 'ya'yanka, sun gama raina ni a cikin gidan nan basa ganin darajata, saboda d'aurin gindin da suke samu daga wajen wannan shegiyar uwar tasu".
Dakatar da ita yayi da hannu
"Dakata innah duk abinda xaki fad'a ki fad'a, amma bana son naji kin sake xagin iyalina"
Sai na xaga d'in, saboda an shanye ka,ban isa na fad'i gaskiya ba, yaran nan sun cuce ni saboda kana jin tsoran su,baxa ka iya tsawatar musu ba, to wlh baxa ta sa6u ba idan kai baxa ka iya ba ni xan iya".
"to ina ruwan ki idan ma an shanye ni, naga dai matata ce baxa ta ta6a cutar da ni ba, ke har kin manta da irin cutarwa da ku ka yi mini, sai yanxu da Allah ya rufa min asiri xaki ce kina sona, ni sam ban yarda da wannan soyayyar taki ba".
ficewa yayi ya barta a tsaye tana ta balbalin fad'a, falo ya fito ranshi a 6ace yake tambayar Ammin Nauwar.
"Me ya kawo wannan tsohuwar gidan nan, ku ne ku ka je,ku ka d'akkota ko?yana maganar yana kallon su.
gaba d'ayan su kasa fahimtar abinda yake nufi suka yi.
magana fa nake kun share ni"
"waye yace wannan tsohuwar taxo min gida, alhalin kun san halinta amma ku ka 'kyaleta ta xauna, ga shi nan taxo xata 6ata min rai"
Nauwar ce tayi 'karfin halin yin magana
"To ai kaine ka d'akkota da kan ka Abbah, kuma kayi alkawarin duk wanda ya 6ata mata rai a cikin mu sai ka kore shi daga gidan nan.
Hawaye ne ya fara sauka a kan fuskarsa.
"wlh ban san na fad'a ba, dan Allah ku yi ha'kuri ku yafe min, ban san na ci xarafin ku haka ba, insha Allah daga yau ta gama kwana a gidan nan"
'Bangaren shi ya koma ya tarar da ita tayi tsaye ko tunanin me take yi oho, a gabanta ya tsaya, fuskar shi ba walwala yake mata magana.
"duk naji abinda ya faru kuma insha Allah gobe xa a mayar da ku 'Dan batta"
yana gama gaya mata
ya shige d'akin shi ya barta nan tsaye.
kanta ne gaba d'aya ya 'kulle ta rasa abin cewa.
*Jeeddahtulkhair*π
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
maijiddatijjaniadam@gmail.com
*β»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
ππππππππππ
3β£0β£
*W*ashe gari da sassafe Abban Nauwar ya gama shiri ya fito falo don yin breakfast, Nauwar ce ta tashi ta fara xubawa Abbanta abinci, kallonta yayi yana murmushi I can't eat up the food because I'am not a big eater. kallon shi tayi tana dariya to ai Abbah naga jiya baka ci abinci ba shi yasa na xuba maka da yawa.
okay, Give me a little.
kadan ta xuba masa sannan ta xubawa kowa suna cin abincin suna nishadi.
bayan sun kammala yasa aka kira su innah karime, kallo d'aya xaka yi mata ka fahimci tana cikin ba'kin ciki da tashin hankali.
kallon su ya yi fuskar sa sam babu alamar wasa.
"kun had'o komai da komai naku dai ko, don yau xaku wuce inda ku ka fito"
xare idanuwa innah karime tayi "wai dama Alhaji da gaske kake mayar da mu xa ka yi, ni fa nayi tunanin raha ka ke yi"
"Da gaske nake yau xaku koma, let me change now, kafin na fito kai magaji kayi sauri ka fara saka kayan ku a mota, don yau ina da aiki amma na katse xan kai ku"
kamar xasu yi kuka haka suka shiga mota suka wuce 'Dan batta.
su kuwa su Nauwar farin ciki baya misaltuwa a gurin su saboda Allah ya raba su da masifa.
Suna isa 'Dan batta ya ajiye su, ko cikin gidan bai shiga ba ya juya kan motar shi ya dawo gida.
Habi ce ta gamu da su a bakin 'kofa, ita ma tana shirye-shiryen tafiya gidan suna, yanayin su kawai ta kalla tasan tafiyar ta su ba ta dad'i bace, ga shi innah karime na ta faman xubar da hawaye, gurin xama suka samu bayan sun ajiye kayan su, shiru suka yi kamar wad'anda aka xarewa laka.
'karfin halin tambayar su tayi, ta gama tsorata a tunaninta wani abin ne ya same su.
"Innah waye ya mutu naga kuna kuka?
"Ba mutuwa bace uwar Audu amma abinda ya same mu ma har ya fi mutuwar ciwo " ta 'karasa maganar tana kuka
"Dan Allah fada min Innah wlh hankalina ya tashi da jin wannan maganar ta ku, ina ganin ku nasan ba a hayyacin ku, ku ke ba me ya faru dan Allah"
Magaji ne ya kar6i maganar.
"Ai gwaggo yau cin mutunci kawu Mudi ya yi mana,