Showing 96001 words to 99000 words out of 111837 words
Chapter 33 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
nayi farin cikin yanayin da na tarar da iyalaina Allah yayi maka sakamako da aljanna"
Murmushi Abba yayi
"Ba komai ai d'a na kowa ne, kuma duk wanda ya taimaki wani Allah xai taimake shi, Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba"
Gaba daya suka amsa da ameen, Abban Hamdan shi ma addu'ar fatan alkhairi ya yiwa Abban saimah, bisa ga wannan alkhairi da yayi musu.
kiran wayar baffa aka yi suka hada shi da Abban saimah shi ma yayi masa addu'a da godiya, hira suka xauna suna yi sosai basu tashi tafiya ba sai wajen karfe hudu na yamma, kira Abban saimah ya kwalawa nauwar cike da ladabi ta karaso dakin.
tsugunnawa tayi tare da sunkuyar da kanta kasa.
Abbanta ne yayi magana
"nauwar kice da Amminki ta shirya xamu tafi yanxu"
Idanun nauwar ne suka cika da hawaye sbd jin abinda Abbanta ya fada.
"Yau xamu tafi Abba? "
Amsa mata yayi da eh
Hawaye ne ya ke sauka a kan fuskarta
"Abba dan Allah ka kyale mu xuwa wani satin mu taho, ban yi sallama da kawayena na makaranta ba"
Murmushi yayi ya dubeta
"to shikenan sarkin kuka na bari ki gama sallama da kowa sai naxo na dauke ki "
Abban saimah ne yayi saurin tarar numfashinsa.
"Aa ka bari Alhaji xan kawota ma da kaina ita da Aminiyar tata"
ran Hamdan bai so hakan ba sai dai ba halin yayi magana dole yayi shiru tunda manya sun sa baki.
Cike da farin ciki nauwar ta tashi ta fita, fadawa Ammi sakon Abbanta tayi, ran ammi bai so ba ta tashi ta bisu, har bakin mota mutan gidan su saimah suka raka su, sannan suka wuce suka tafi.
Kai tsaye Dan Batta suka wuce, suna isa suka shiga dakin Baffa yana ganin su ya Mike ya tarbe su cikin sakin fuska..
"Alhamdulillah Allah mun gode maka sannu da xuwa yata Barka da arxiki"
Wajen zama suka samu gaishe shi suka yi cike da girmamawa, cikin sakin fuska ya amsa musu, Abban nauwar ne ya bashi labarin yadda aka samu su Ammi, ba karamin farin ciki yayi da haka ba.
"mun gode Allah da wannan abin alkhairi da ya same mu, mun shiga kunci a baya gashi yanxu Allah ya kawo mana sauki, shi yasa dogaro ga Allah yake da riba gashi nan mun ga sakayyar da Allah yayi tun a duniya, 'yata Allah yayi miki albarka bisa ga hakurin da kika yi, Allah ya baki Ladan jarrabawar da kika shiga, dan Allah ina son kada ki rika tuna abubuwan da suka faru a baya ki dauka hakan kaddara ce kuma jarrabawa ce aka Yi miki gashi nan yanxu kin cinye, duk wadanda suka cutar da ke sun xama abin tausayi, innah Mahaifiyata ta makance duk jikinta babu abinda yake matsowa komai sai dai a yi mata, ita kuma dayar abokiyar xaman babar Mahmoud ta haukace yanxu haka ta baxama daji tun shekaran jiya ake nemanta ba a ganta ba, shi ma dayan mai taya su aikin sharrin yanxu haka baya gane komai ya bugu a kansa ga jikinsa ya karye, kafarsa daya ta rube an yanke ta. Duk wadannan abubuwan da suka faru, Allah ne ya miki sakayya tun a duniya kafin kuma a je lahira Allah ya tantance mai gaskiya, ki kwantar da hankalinki ki yiwa mijinki biyayya ku dawo rayuwa kamar yadda kuke yi a da cikin farin ciki da kwanciyar hankali "
Sun ji dadin wadannan kalaman na Baffa godiya mai yawa suka yi masa sannan suka tashi suka tafi saboda basa son yin dare a hanya, har xasu bar dakin baffa ya kira sunan su.
"Amma dai ba tsohon gidanka xata koma ba ko Mahmoud "
Tsugunnawa yayi sannan ya amsa masa.
"nan xata koma baffa"
Girgiza kai Baffa yayi.
"Ba zai yiwu ta koma wannan gidan ba saboda har yanxu baxa a rasa mugwayen shaidanu a ciki ba, ka gyara mata daya gidan naka ta koma "
Amsawa Baffa yayi da to
Sannan ya bashi kudi masu yawa.
Albarka ya shiga saka masa.
"Allah ya kula da bayanka kamar yadda kake kula dani Mahmoud na gode dan Allah ku karasa wajen innah ku gaisheta.
Wajen innah karime suka shiga tarar da ita suka yi tana ta numfarfashi kamar xata wuce lahira, gaisheta suka yi da kyar take iya magana.
Bayani Abban nauwar ya fara yi mata.
"innah ga maman nauwar fa taxo ta gaishe ki ta samu lafiya yanxu babu abinda yake damunta"
Wani hawaye ne ya rika zubawa daga idon innah karime. Cikin kuka take magana
"Allah sarki Baiwar Allah ki yafe min cutar da nayi miki, baki min komai ba na dora miki Karan tsana wlh kuskure ne ki yafe ni dan Allah "
Shiru Ammi tayi bata cewa innah komai ba haka ta rika surutai tana sambatun ta yafe mata, amma bata samu amsa daga wajen Ammi ba.
Tashi suka yi suka fita suka barta a wannan halin.
*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
9⃣0⃣
Gidan su Hamdan suka wuce cikin farin ciki mama ta tarbe su, abinci kala-kala ta kawo musu sannan suka fara hirar yaushe gamo, cikin tausayawa ta dubi Ammi.
"ikon Allah ban taba xaton xaki dawo daidai ba Rehab kin shiga cikin mawuyacin hali sanadiyyar wadannan axxaluman, Allah ya dube mu da idon rahma ya baki lafiya, dole mu gode masa"
murmushi Ammi tayi.
"Nima nayi mamaki da aka rika bani labarin yadda na xama a da amma gashi yanxu komai ya xama tarihi, Allah ya kara kiyaye mu daga sharrin masu sharri"
amsa mata tayi da "Ameen"
sallamar Hamdan ce ta katse musu hirar da suke yi, da sakin fuska ya nufo wajen su,wajen xama ya samu yana fuskantar Ammi yana magana.
"Yauwa Alhamdulillah dama so nake ku dawo a yi wata magana"
gaba daya suka mayar da hankalin su gare shi
"wace magana kuma xa a yi"
gyara xama ya yi yana dan murmushi.
"maganar aurena da Nauwar mana ko xuba min ido xa ku yi nayi ta xama a gauro"
Harar shi mama tayi.
"lallai xan baka sarautar rashin kunya Hamdan, yanxu a ce ko kunyar idona baka ji ba kake wannan maganar, lallai dan xamani"
murmushi Ammi tayi.
"ni fa Hamdan dan gidana ne kin san ba jin kunyata yake yi ba, ya saba irin wannan rashin kunyar a gabana"
dariya kawai Hamdan yake yana sosa kewa.
"to yanxu mama dan nace ina son aure ai ban yi rashin kunya ba, kiga fa abokaina da yawa sun yi wasun su har da yaya"
dukan bayansa mama tayi.
"ni tashi ka bamu guri mara ta ido, xamu yi magana anjima"
mikewa yayi sai da ya kai bakin kofa ya kalli mama yana dariya.
"mama yau fa xa a yi maganar nan dan na kosa naji Abinda aka yanke"
yana gama fada ya fice.
cikin mamaki mama ta dubi Ammi
"lallai halin yaran xamani sai dai a kalle su kawai, yanxu yaro har xai iya furta yana son aure dan rashin kunya, Allah dai ya shirya mana yaran mu"
Hira suka cigaba da yi sannan suka tattauna maganar auren Hamdan da Nauwar da lokacin da ya kamata a yi, sannan kuma suka yanke shawarar samun maxajen su don su yi musu maganar.
A bangaren Nauwar kuwa samun saimah tayi a daki tana kwalliya matsawa kusa da ita tayi, tana murmushin farin ciki.
"ni fa ba karamin dadi nake ji ba kawata da Abbana ya bar ni xan karasa hutu a nan,amma da an ce na bi su Ammi, ban san bakin ciki da irin kewarku da xan yi ba"
juyowa saimah tayi tare da dafa kafadarta.
"wlh nima haka kawata, dama dai Abba xai bar mana ke a nan da naji dadi, yanxu idan ma kin tafi dole mu yi kewar juna,komai fa tare muke yi, ya xamu ji idan wata ra muka wayi gari bamu ga junanmu ba"
idanun Nauwar har sun fara kawo ruwa.
"Har bana son ranar nan taxo wlh, saboda ban san irin yanayin da xan tsinci kaina a ciki ba"
cike da kulawa saimah ta dubeta.
"dan Allah mu bar wannan maganar saboda xata iya bata mana farin cikin mu"
rada saimah ta yiwa Nauwar a kunne, a xabure Nawwar ta dubeta.
"yaya fa kika ce saimah, shi yace ki fada min haka"
"Eh mana ya dade da bani wannan sakon amma yace kada na fada miki har sai an samu iyayenki saboda idan na fada miki a lokacin xaki iya shiga damuwa shi yasa na fada miki yanxu"
maganar nan bata yiwa Nauwar dadi ba saboda tana ganin girman yaya sadeeq saimah ce ta lira da yanayin da ta tsinci kanta.
" ya naga yanayin ki ya canja ko bakya son yayan nawa ne"
xare idanu Nauwar tayi.
"Haba ni na isa nace bana son yaya sadeeq ko dan karamcin da kuka yi mana, kawai dai ina jin kunyar yadda xan cigaba da kasancewa a gidan nan ne"
hararta saimah tayi.
"Haba Nauwar sai kace ba yar birni ba, mun xama daya fa da ku, ki dauka kece yar gidan nan shi yaxo bakunta ki saki jikinki nasan yaya baxai takura miki ba dan shi mutum ne mai saukin kai,kuma baxai so ya ganki a damuwa ba"
"shikenan kawata na gode da karfafa min gwiwa Allah ya bamu dacewa"
Hirar duniya suka fada suna yi suna shewa, a daidai lokacin yaya sadeeq ya shigo dakin, da sallama ya karaso wajen su, Nauwar na ganinshi ta kwantar da kanta a kan gado wai ita a lallai bacci take.
kiran sunanta yayi cikin salo mai kayatarwa, shiru tayi ba tare da ta amsa ba, sake kiranta yayi a hankali ta bude ido ta dago ta kalle shi mayar da kanta tayi saboda yanxu gaba daya nauyin shi take ji, murmushi yayi sannan ya sake yi mata magana.
"tunda kunyata ake ji bara na tashi na fita kada na hana ki sake wa"
mikewa yayi da niyyar barin dakin, yana maganar yana kallon saimah, cikin xaulaya saimah tayi masa magana.
"yaya ka kwantar da hankalinka ba kunyarka take ji ba, fuskar masoyinta principle take son a gani"
A xabure ta dago ta kaiwa saimah duka
"wlh karya take yaya kawai kaina ne yake ciwo"
shi dai yaya sadeeq dariya kawai yake, ficewa yayi ya barsu suna abin su.
Cikin tunani Nauwar ta kwana xuciyarta sai shawarwari take bata, ta karbi soyayyar sadeeq ko kada ta karba, wata xuciyar tace ta karba wata kuma ta tuno mata da maganar Hamdan da irin gudunmawar da ya basu a haka ta kwana tana wadannan tunanin.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Wannan shafin gaba daya naki ne halak kiyi yadda kike so da shi, SISTER FURERA MUHAMMAD (Maman Hauwa) ina yinki ina kaunar ki, Allah ya bar xumunci da kaunar juna*
9⃣1⃣
Yau tun safe nauwar bata fito ba a daki ta wuni saboda tana jin kunyar fitowa tsakar gida don kada ta hadu da yaya sadeeq ya rika sakar mata wannan asirtaccen murmushin nasa mai sanya mata kasala, don ko gaida mama da Abba bata fita tayi ba, shirun da mama taji ne babu motsin ta a waje shi yasa ta shigo dakin dan jin dalilin da yasa bata ganta ba.
Kwance ta tarar da nauwar kanta na kallon sama da sallama ta shigo dakin, tsayawa tayi ta karewa nauwar kallo sannan ta karaso inda take.
A hankali ta dago kai ta Kalli mama, tare da tashi xaune.
"sannu da gida mama"
Cikin sakin fuska mama ta amsa.
"yauwa nauwar, lafiyanki yau gaba daya ban ji motsinki ba, ko dai tunanin Amminki kike yi baki fada mana ba"
Murmushi nauwar tayi.
"A'a mama yau bana jin dadi ne kawai "
Cikin kulawa ta dubi nauwar.
"Ayya Allah ya baki lafia amma ai bai kamata kiyi shiru baki fada min ba, shikenan da ban shigo ba haka xaki xauna da ciwo a jikinki baki yi magana ba"
Kiran saimah mama tayi cikin xafin nama ta karaso dakin Tsugunnawa tayi.
"Gani mama"
"yanxu dan sakarci Kin san nauwar ba lafiya amma baki fada min ba, sai da na shigo yanxu naga yanayinta nasan ba tada lafiya da ban shigo ba sai dai ciwo yayi ta cin jikinta kenan Allah ya shirye Ku yaran nan"
Dariya saimah take yi
"Lallai mama Kina cikin gidan nan amma ana binne Ki, duk abinda yake faruwa baki sani ba, to nauwar lafiyarta kalau "
Cike da mamaki mama take duban saimah, ita kuwa nauwar kara danna kanta tayi cikin bargo saboda ruwan da saimah ta ballo mata "
Magana mama ta cigaba da yiwa saimah
"kin fara magana kuma kin yi shiru, ni fa wannan sakarcin ne bana so"
Duban nauwar saimah tayi tana dariya.
"na fada ko nayi shiru? "
Shiru nauwar tayi mata ba tare da ta bata amsa ba, sai hararta da take yi kawai.
Cikin kakkausar murya mama ta sake maimatawa saimah tambayar da tayi mata.
"xaki fada min ko sai na Saba miki"
Murmushi saimah tayi tana kallon mama.
"mama ya naga duk kin tashi hankalin Ki abin farin ciki ne fa xai faru ke dai kiyi addu'a kawai "
"to
naji ko na Farin cikin ne ki fada min yanxu ina saurarenki"
Rufe fuska saimah tayi.
"da ke da Ammi kun xama surukai mama"
Cikin mamaki mama ta jawo saimah ta xaunar da ita tana kallon fuskarta.
"da gaske kike ko kuma xancen Ku ne na yara"
"Wlh da gaske nake mama yaya Sadeeq yana son nauwar "
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta.
"kai amma naji dadin wannan al'amari ashe xumunci baxai yanke tsakanin mu da Ku ba nauwar, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ai kuwa xan samu sadeeq yanxu yasan da wannan abin alkhairin bai fada min mun yi magana da ammi ba har ta tafi"
Saimah ce ta bata amsa.
"to ai kunyar ki yake ji ne mama shi yasa bai fada miki ba, kuma baya son a fada miki saboda kada nauwar ta rika jin kunyar ki ta kasa sakewa a gidan nan"
Mikewa mama tayi tana magana..
"ni ai nauwar ba surukata bace yata ce duniya da lahira dan haka ni ba wani sarakuta da xa mu yi da ita"
Fita mama tayi ta bar dakin xuciyarta cike da Farin cikin faruwar wannan al'amari.
Mama na barin dakin nauwar ta dago tana harar saimah.
"kin bata min rai wlh me yasa xaki fadawa mama, ni kin jawowa kanki ma gobe xan yi tafiyata gida"
A firgice saimah ta dago fuskar nauwar tana bata hakuri.
"kiyi hakuri sisina menene amfanin boye abin da xa a yi, gara a fada mata ta sani, Kinsan na kosa na fara xuwa gidanki cin taliya"
Duka nauwar ta kai mata.
"Ai da yake ke xama xa kiyi ba auren ko, Allah yasa sai an yi bakin ki xa a yi nawa"
Murmushi saimah tayi mata.
"ni da ko mijin babu gara ke kin samu, naki xa a fara yi duk abin ki yarinya "
Juyar da kai nauwar tayi tare da cewa ba amin ba.
Tashi saimah tayi.
"Nauwar Ki tashi kin manta xamu je gidan kawayen mu ki fara yi musu sallama ko kin manta ne? "
A hankali ba dago ta bata amsa.
"tunda kika bata min rai na fasa"
Rarrashinta ta shiga yi har sai da ta tashi suka tafi.
A daren mama ta fadawa Abba abinda taji daga bakin saimah, ba karamin farin ciki Abba yayi ba dama ya dade yana wannan tunanin.
Don haka suka yanke shawarar kiran sadeeq don Kara tabbatar da maganar daga bakinsa.
*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*A yi min afuwar rashin ji na kwana biyu hakan ya faru ne sakamakon abubuwa da suka yi min yawa*
9⃣2⃣
Bayan sallar magariba ya sadeeq ya tafi don dakko su Nauwar, a bakin titi ya tsaya, kiran wayar saimah yayi inda ya shaida mata cewa yana jiran su, cikin sauri suka hada kayan su suka fito inda suka samu rakiyar kawar su Halima, wacce kuma dama gidan su suka je.
tun daga nesa ya sadeeq ya hango Nauwar, cikin nutsuwa take taku daya bayan daya, wani kallo mai cike da soyayya yake mata tare da sakar mata kyakkyawan murmushi mai kayatarwa, har sai da taji kunyar kanta, har suka karaso wajen hankalinsa na kan Nauwar bai san ma sun iso ba, gaida shi Halima tayi amma bai san ana yi ba,sai da saimah ta dan taba kafadarsa.
"yaya ina hankalinka yake haka, mun karaso amma hankalinka na wani wajen ga Halima na ta gaisheka tun daxu"
a raxane ya dago yana murmushi.
lafiya lau ya amsa mata dashi, sannan ya cigaba da aikin kallon Nauwar.
sake taba shi saimah tayi.
"yaya wai yau ina hankalinka yake tafiya ne?"
murmushi yayi
"Ayya sorry my saimah, nayi nisa a tunanin tauraruwar matan da haskenta ke haske sararin samaniya shi yasa kika ga yau din nan sai a hankali".
turo baki saimah tayi.
"dama kana da wata tauraruwa ne bayan sisina"
murmushi yayi tare da dafa kafadar saimah.
"nima ai ita nake nufi sarkin fushi wato har ranki ya baci ko, to ina so kisa a ranki Nauwar ita ce mace daya tilo da na bawa gurbi a wannan xuciyar tawa, kuma har abada baxa ta taba fita ba"
tsalle saimah tayi tare da rungume ya sadeeq.
"na gode yayana na kaina Allah ya kaimu lokacin auren ku mu sha biki"
cike da sakin fuska ya amsa mata da Ameen
duk xancen da suke yi a kunnen Nauwar duk nauyi da kunyar ya sadeeq ta mamaye ta, a hankali ta bude murfin motar ta shiga gidan baya, juyowa yayi ya kalleta, cikin sassanyar murya yake mata magana.
"Tashi ki dawo nan kusa da ni Nauwar"
makale kafada tayi alamar.
"aa"
cikin rarrashi da lallabawa yace ta dawo ta xauna, kin tashi tayi sai da saimah tayi mata magana a karo na biyu sannan ta tashi ta shiga, kanta a sunkuye yake ta kasa hada ido da ya sadeeq shi kuwa sai janta da hira yake yana mata barkwanci, saimah ce kawai take taya shi, a haka har suka iso gida.
A kofar gida suka ci karo da Abba, kiran sunan su yayi gaba daya suka karasa wajensa suka xube don jin Abinda xai fada musu.
Fada ya fara yiwa yaya sadeeq.
"me yasa baka je ka dakko yaran da