Showing 51001 words to 54000 words out of 111837 words
Chapter 18 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
musa tambaya nake"
Dakatawa yayi da abinda yake yi ya tsaya don saurarenta
"Allah yasa na sani Hajiya"
Gyara tsayuwa tayi ta cigaba da magana
"Akwai baki da nayi a gidana a cikinsu Akwai wata mai tabin hankali, to mai tabin hankalin aka ce xa a kawo ta wajenka tasha magani tun yamma, har Yanxu ba labarin su"
"Subhanallah!! Wlh basu xo ba Hajiya amma ki tambayi mutane ko sun ga inda suka yi"
Godiya tayi masa sannan ta fice Daga wajen xuciyar ta cike da mamakin inda su nauwar suka yi.
A hanya taci Karo da daya daga cikin mutanen da suke xuwa wajenta har ta wuce bata ganshi ba yaja mayafinta ta dawo da baya.
"Haba hajajjaju wuce mu ma xa a yi baxa a kula mu ba"
"Wlh ban ganka ba Dan ladi raina a bace yake wai yarinyar nan da take gidana tun yamma ta fita har Yanxu bata dawo ba, ga aikin bikinta ina so ta taya ni"
Kwashe wa yayi da dariya
"wlh Hajiya yarinyar nan ta fece, yarinyar da na gamu da ita a tasha xata hau mota, ai sai dai ki rungumi sorry Kawai "
Salati Amarya ta fara yi"lallai yarinyar nan ta cika yar akuya sakayyar da xata yi min kenan ai kuwa duk inda take sai na Nemo ta"
Wucewa tayi a fusace ta shiga gida.
Tana shiga ta dauki waya ta kira Alhaji talle ta sanar da shi halin da ake ciki
Ashar ya danna mata
"Wlh bansan wannan zancen ba Amarya Sam ba haka Muka yi da ke nake, me yasa Kinsan xata gudu kika sa na yarda da ita na gama kashe mata kudade a banxa, Wlh bansan asara ba, ban kuma san hanyar gidansu ba, tun wuri ki nemota kafin lokaci ya qure miki"
Har kasa Amarya ta tsugunnah kamar yana kallonta, rokonsa ta rika yi saboda tasan tijararsa da cin mutuncinsa, bai Ki ya toxartata a kan wannan abin ba.
Kashe wayar yayi ya kyaleta a tsugunne tana magiya, sake kiran wayar Shi tayi Amma gaba daya yaki dauka sai hakura tayi ta kyale Shi, ta shiga daki tana tsinewa nauwar
"amma wannan yarinya ta cuce ni ta gama da ni, ta saka ni a tsaka mai wuya, Ina naga abinda xan biya wannan tijararren kudinsa"
ganin mutum tayi a kanta yana ta xare-xaren ido, a sanyaye ta dago
"Sannu da zuwa alhaji, ga guri bismillah xauna"
Hararta yayi
"ba wani Sannu da xuwa alhaji kuma babu wani guri da xaki bani na xauna Don ba xama ne ya kawo ni ba, Ina nauwar take??? A Yanxu ita nake bukata ba Kudi ba, Wlh sai kin fito min da ita ko ranki ya baci Yanxun nan, ni zaki ci wa amana, ni xaki yaudara ki karbe min kudade kice xaki aura min yarinya, Yanzu kuma Ki bata kudin mota ta gudu ta bar garin, wato an ci moriyar ganga ko, to Wlh baxa ta sabu ba, ko ki fito min da Matata ko jikinki ya gaya miki Sannan na mika Ki wajen yan sanda"
Tunda lokacin da Amarya ta fara Jin kalaman Alhaji ta tabbatar da cewa ba xai mutunta mata ba ta fara kuka tana rokon shi ya rufa mata asiri.
"ka taimake ni Alhaji Kasan baxan danfare ka ba, ban shirya abin nan a matsayin yaudara ba nima yarinyar nan yaudarata tayi ta barni a tsaka mai wuya, dan Allah kayi hakuri ka rangwanta min"
Cikin fushi ya mata magana
"ba wani rangwami da xan miki Domin Kowa yasan karuwa makaryaciya ce, sau nawa xaki fadi magana ki kuma abin ba haka bane, Ai ke ba abar yadda bace Amarya"
Bude baki tayi xatai magana kafin tace komai ya hauta da duka ta ko'ina yana xaginta, ihu ta rika yi kafin kace kwabo tuni Jama'a suka cika gidan suna tambayar su abinda ya faru.
Cigaba da dukanta alhaji talle yayi da kyar mutane suka kwaceta.
Cikin xafin rai yake musu bayani
"wai a ce ni matar nan xata damfara mun yi da ita xata aura min yarinya sai da na gama kashe kudina gaba daya Dan rainin hankali tace min wai yarinyar ta gudu Wlh baxan yarda ba sai na dauki mataki "
Rike baki mutanen suka yi suna mamakin wannan cakwakiyar da Amarya ta hadawa kanta, hakuri suka shiga bashi
"gaskiya Dan rashin kyautawa Amarya bata kyauta maka ba amma hakuri ya kamata kayi, Tunda Kaima kayi kuskure a matsayin ka na Babban mutum Kazo gidan mata masu xaman kansu kace xaka aure su wannan ai kuskure ne, hausawa sun ce kwarya ta gari tana ragaya, Yanxu ka daga mata kafa ta biyaka kudinka a hankali dama bariki ta gaji haka, garin banxa ne ya tafi a faraufarau din Wofi don haka sai ka rungumi na Annabawa"
Duk mutanen da ke wajen babu wanda ya gayi bayan a Kai Amarya wajen yan sanda Kowa hakuri yake bawa Alhaji talle Sannan suka saka shi a gaba ya fita ya bar gidan"
*****************
Yau da sassafe baffan Mahmoud ya shirya xuwa wajen sau, saboda ya dade bai xo wajen Mahmoud ba, shi ma kuma gaba daya ya dauke kafarsa Daga Dan batta, baya xuwa baya yi masa aiken komai.
kasuwa ya shiga Don siyowa yan jikokinsa mangwaro da gyada, bayan ya siya ya nufi Tasha don Hawa motar Kano.
Cikin kankanin lokaci suka shigo Kano inda ya samu adaidaita sahu ya kawo shi gidan Mahmoud.
A Bakin kofa ya iske mai gadi yana ganinshi ya tsugunnah har kasa ya gaishe Shi ya karbi kayan da ke hannunsa ya yi masa rakiya har cikin gida.
Sallama suka rika yi a Bakin kofar falon babu wanda ya amsa musu duk da cewa suna Jin hayaniyar jama'a, sai da aka dauki mintuna Sannan innah karime ta fito, tana ganin baffan ta hade rai kamar Wacce aka aikowa da naka'ikan mutuwa, har kasa ya tsugunnah xai gaisheta, dakatar da shi tayi.
"bana bukatar gaisuwarka tauraruwa mai wutsiya ganinka ba alkhairi ne ba, wane munafuncin ne kuma ya kawo ka, Tunda Muka zo garin nan saboda kana ji da kininbibi baka biyo mu ba sai Yanxu, to me kaxo yi? "
Kansa a sunkuye ya bata amsa
"dama naxo naga wannan yaron ne da yayansa saboda na Kwana biyu ban gansu ba, Sannan kuma ina so Habi ta koma dakinta saboda Yanxu ina dan fama da rashin lafiya bana samun mai kulawa da ni"
Wata shu'umar harara ta watsa masa
"to naji abinda ka fada, kana ta xuba kamar wani Dan Kanya, ina san ka sani Habi baxa ta koma cikin wahala ba, muna nan muna Jin dadin rayuwar mu, Allah ya kashe ya bamu, don haka ba inda xata je muna nan a tare"
Shigewa tayi daki ta barshi tsugunne, bayan lokaci kadan sai gata da tabarma da abinci watsa masa tabarmar tayi, shi kuma abincin ta ajiye masa shi.
"ga tabarma nan ka xauna kafin Dan naka ya dawo, don baxa ka shigar mana daki ba ko da wata jarabar kaxo mana, wannan abincin kuma kaci dama nasan shi ya kawo ka sbd an dade ba a hadu da shinkafa ba"
Shigewa daki tayi ta rufo kofa ta bar Baffa xaune yana hawayen Bakin ciki, da baisan innah karime ce mahifiyarsa ba, da cewa xai yi ba ita ta haife shi ba saboda yadda take nuna masa kiyayya kirikiri.
Maigadi ne ya ganshi yana kuka don haka ya nufo wajen da sauri ya fara bashi hakuri.
" kayi hakuri baba, Wlh da xan fada maka irin abubuwan da suke faruwa a gidan nan da kayi mamaki, ka share hawayenka komai ka barwa Allah xai yi maka magani"
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: Share hawayen yayi ya dubi mai gadi
"na gode Malam Ali Insha Allah baxan Kara tayar da hankalina a kan haka ba."
Bude masa kwanon abincin yayi
"kaci abincin nan baba kada ya huce"
Kallonsa yayi ya girgixa masa kai, "bana sha'awar komai Malam Ali Bakin ciki ya gama cika min cikina"
Tausayin baffan Mahmoud ne ya kama mai gadi
"kayi gefe da komai baba Insha Allah komai mai wucewa ne"
Hawaye Baffa ya cigaba da sharewa saboda kukan ne Kawai xai saukaka masa damuwar da yake ciki. Duban Malam Ali yayi
"wai ni ina matar gidan nan da yaranta ne Malam Ali tunda naxo banji motsinsu ba, ko sun tafi unguwa ne"
Shiru Malam Ali yayi ya rasa amsar da xai bawa Baffa,saboda Idan ya fada masa basa nan ba karamin tashin hankali xai shiga ba, Don haka ya ki bashi amsa ya kawo masa wata hirar. Duk da wannan dabara da Malam Ali ya yiwa Baffa sai da ya sake maimaita masa irin wannan tambayar, dabara ce ta fadowa Malam Ali yace masa sun tafi Makaranta, haka suka xauna har wajen sallar La'asar suna hira suna jiran dawowar Abban Nauwar.
Bugun kofa suka ji dan haka Malam Ali ya tashi Don bude kofar, Habi ce tare da magaji sun dawo daga unguwa, tana ganin Baffa tayi turus taja da baya
"me xan gani, nafarki nake ko idona biyu"
Magaji ne ya karbi zancen idonki biyu Don haka sake bude su Idan Kina ganin mafarki kike yi"
Wucewa magaji yayi ya shige daki ko kallon Baffa bai yi ba, ballantana ya samu arxikin Gaisuwa.
"Lallai annoba ta xiyarce mu har gida, me kuma kaxo yi nan gidan Malam, me yasa Kai ba kada hakuri duk kokarin da yaron nan yake yi a kanka sai ka biyo shi har gida maula salon ka zubar mana da mutunci ya gaji da mutuncinmu, gaskiya Malam baka kyauta mana ba wlh"
Sakin baki Malam Ali yayi yana ganin ikon Allah tunda yake bai taba ganin irin wannan rashin da'ar ba sai yau.
Hawaye ne ya cigaba da sauka a fuskar Baffa, saboda Bakin cikin da ya mamaye xuciyar sa da na sanin xuwansa gidan yake, ga Shi bai samu ganin Wadanda Yaxo dominsu ba, tashi yayi ya saka takalminsa xai fita ya bar gidan, da sauri maigadi ya tare shi yana bashi hakuri, Amma Sam yaki hakura ya fita.
Tararshi yayi yasha gabansa.
"kayi hakuri Baba baxan bari ka fita ranka a a bace haka ba, Yanzu xamani ne na lalura idan wani abin ya sameka fa, kayi hakuri ka jirayi xuwan mai gidan tunda dominshi dama kaxo kaga ba dadi idan baka hadu da shi ba"
.saboda kukan da Baffa ke yi ya kasa magana ma gaba daya, baki ya cigaba da bashi amma yaki komawa cikin gidan, suna tsaye a wannan halin suka ji karar mota, saurin waiwayawa mai gadi yayi da sauri ya tafi bakin motar ya tsugunnah..
"Sannu da xuwa ranka ya dade, Ga Baffa nan Yaxo tun daxu yake jiran xuwanka"
Da hanxari Abban nauwar ya fito daga motar ya fito, wajen Baffa ya nufa, Tsugunnawa har kasa yayi
"Sannu da xuwa baffana"
Kukan da Baffa ke yi shi ya hana shi amsa sallamar, shirun da yaji ne yasa ya dago kai don ganin halin da yake ciki.
Hawaye yaga na sauka a kan kuncin Baffa
Tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa "lafiya naga kana kuka baffana, me yake damunka ko jikin naka ne"
"ka Kwantar da hankalinka Mahmoud lafiyata kalau kukan Farin cikin ganinka nake yi shi yasa".
Murmushin karfin hali yayi ya sake Duban baffanshi
"nasan ba haka bane baffana Kawai ka Boye min ne saboda kada na shiga damuwa amma a xahirin gaskiya Akwai abinda yake danunka"
"na fada maka babu komai Mahmoud"
Kiran Malam Ali yayi ya fara tanbayarsa abinda ya faru da baffanshi, bayani yayi masa dalla-dallah, a fusace ta wuce xai shiga gidan.
Kiran sunanshi Baffa yayi
"kada kace xaka yi tashin hankali akan wannan abin, kamar yadda na barwa Allah Kaima kayi hakuri ka barwa Allah, innah mahaifiyata ce baxan iya bari ka yi mata abinda bai kamata ba, kayi hakuri ka kyale su Duk abinda mutum yayi Dan kansa"
Dawowa yayi ya Rike hannunsa suka shiga cikin gida
Ko sallama bai yi ba, yasa kafa ya doki kofar falon, yana shiga falon su innah karime suka Mike suna masa Sannu da xuwa
"Barka da zuwa Alajin Allah Ashe har ka iso bai basu amsa ba ya wuce sashinsa"
Mamaki ne ya kama baffan Mahmoud wai Mahmoud din da aka tsana ne har ake kiransa da Alajin Allah Lallai duniya ba gaskiya"
Suna shiga dakin ya kunnawa Baffa AC ya shiga kitchen da kansa dan hada masa abinci bayan ya kammala ya kaishi bandaki ya umarce Shi da yin wanka.
Yana fitowa ya bashi kaya na alfarma ya saka Sannan suka fara cin abincin suna yi suna hirar Yaushe gamo. A cikin hirar ne ya jefo masa tambaya
"wai ni ina matar gidan nan da yayanta ne tunda naxo fa banji motsinsu ba, na tanbayi mai gadi yace suna unguwa gashi har kusan karfe takwas basu dawo ba, kuma ban ji kayi cigiyarsu ba, anya lafiya kuwa Mahmoud"
Wannan tambayar ba karamin tayar masa da tabon da ke ransa tayi ba
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
*NANAH JUWAIRIYYA, SHAMSIYYA ZAYYANU RIMI, SAKEENAT JIBRIL, naji dadin comments dinku Ina godiya da yadda kuke kaunar wannan littafi na AL-MAJIRA Allah ya bar xumunci, yasin ina yinku irin mugun sosai din nan*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
5⃣2⃣
Har bayan isha'i Amarya na dakon dawowar nauwar Amma shiru ba Labari, gajiya tayi da jiranta, dan haka ta dauki aikinta ta fara yi, tana aikin tana masifa, jira Kawai take nauwar ta dawo ta sauke mata kwandon bala'i, bayan ta kammala ta dauki mayafi ta fita dan xuwa chemist din da tace mata xata je.
Da sallama ta shiga shagon inda ta tarar da mai chemist din yana shirye shiryen kullewa, gaisawa suka yi Sannan ta fara yi masa bayani
"Malam musa ya gida ya aiki"
cikin sakin fuska ya amsa mata
"alhamdulillah Hajiya Amarya "
"Dan Allah Malam musa tambaya nake"
Dakatawa yayi da abinda yake yi ya tsaya don saurarenta
"Allah yasa na sani Hajiya"
Gyara tsayuwa tayi ta cigaba da magana
"Akwai wasu baki da nayi kwanakin baya, a gidana a cikinsu Akwai wata mai tabin hankali, to mai tabin hankalin aka ce xa a kawo wajenka tasha magani tun yamma, har Yanxu ba labarin su"
"Subhanallah!! Wlh basu xo ba Hajiya amma ki tambayi mutane ko sun ga inda suka yi kinsan lamari idan aka ce da mai tabin hankali dole sai hakuri "
Godiya tayi masa sannan ta fice Daga wajen xuciyar ta cike da mamakin inda su nauwar suka yi.
A hanya taci Karo da daya daga cikin mutanen da suke xuwa wajenta, har ta wuce bata ganshi ba yaja mayafinta ta dawo da baya.
"Haba hajajjaju wuce mu ma xa a yi baxa a kula mu ba"
"Wlh ban ganka ba Dan ladi raina a bace yake wai yarinyar nan da take gidana tun yamma ta fita har Yanxu bata dawo ba, ga aikin bikinta ina so ta taya ni"
Kwashe wa yayi da dariya
"wlh Hajiya yarinyar nan ta fece, yarinyar da na gamu da ita a tasha xata hau mota, ai sai dai ki rungumi sorry Kawai "
Salati Amarya ta fara yi"lallai yarinyar nan ta cika yar akuya sakayyar da xata yi min kenan, ai kuwa duk inda take sai na Nemo ta"
Wucewa tayi a fusace ta shiga gida.
Tana shiga ta dauki waya ta kira Alhaji talle ta sanar da shi halin da ake ciki
Ashar ya danna mata
"Wlh bansan wannan zancen ba Amarya Sam ba haka Muka yi da ke nake, me yasa Kin san xata gudu kika sa na yarda da ita, na gama kashe mata kudade a banxa, Wlh bansan asara ba, ban kuma san hanyar gidansu ba, tun wuri ki nemota kafin lokaci ya qure miki"
Har kasa Amarya ta tsugunnah kamar yana kallonta, rokonsa ta rika yi saboda tasan tijararsa da cin mutuncinsa, bai qi ya toxartata a kan wannan abin ba.
Kashe wayar yayi ya kyaleta a tsugunne tana magiya, sake kiran wayar tayi Amma gaba daya yaki dauka,sai hakura tayi ta kyale Shi, ta shiga daki tana tsinewa nauwar
"amma wannan yarinya ta cuce ni ta gama da ni, ta saka ni a tsaka mai wuya, Ina naga abinda xan biya wannan tijararren kudinsa"
ganin mutum tayi a kanta yana ta xare-xaren ido, a sanyaye ta dago kai
"Sannu da zuwa alhaji, ga guri bismillah xauna"
Hararta yayi
"ba wani Sannu da xuwa alhaji kuma babu wani guri da xaki bani na xauna Don ba xama ne ya kawo ni ba, Ina nauwar take??? A Yanxu ita nake bukata ba Kudi ba, Wlh sai kin fito min da ita ko ranki ya baci Yanxun nan, ni zaki ci wa amana, ni xaki yaudara ki karbe min kudade kice xaki aura min yarinya, Yanzu kuma Ki bata kudin mota ta gudu ta bar garin, wato an ci moriyar ganga ko, to Wlh baxa ta sabu ba, ko ki fito min da Matata ko jikinki ya gaya miki Sannan na mika Ki wajen yan sanda"
Tun lokacin da Amarya ta fara Jin kalaman Alhaji ta tabbatar da cewa ba xai mutunta mata ba, kuka ta fara yi tana rokon shi ya rufa mata asiri.
"ka taimake ni Alhaji Kasan baxan danfare ka ba, ban shirya abin nan a matsayin yaudara ba, nima yarinyar nan yaudarata tayi ta barni a tsaka mai wuya, dan Allah kayi hakuri ka rangwanta min"
Cikin fushi ya mata magana
"ba wani rangwami da xan miki Domin Kowa yasan karuwa makaryaciya ce, sau nawa xaki fadi magana kuma abin ba haka bane, Ai ke ba abar yarda bace Amarya"
Bude baki tayi xatai magana kafin tace komai,ya hauta da duka ta ko'ina yana xaginta, ihu ta rika yi kafin kace kwabo tuni Jama'a suka cika gidan suna tambayar su abinda ya faru.
Cigaba da dukanta alhaji talle yayi da kyar mutane suka kwaceta.
Cikin xafin rai yake musu bayani
"wai a ce ni matar nan xata damfara mun yi da ita xata aura min yarinya, sai da na gama kashe kudina gaba daya Dan rainin hankali tace min wai yarinyar ta gudu
Wlh baxan yarda ba sai na dauki mataki "
Rike baki mutanen suka yi suna mamakin wannan cakwakiyar da Amarya ta hadawa kanta, hakuri suka shiga bashi
"gaskiya Dan rashin kyautawa Amarya bata kyauta maka ba
amma hakuri ya kamata kayi, Tunda Kaima kayi kuskure