Showing 15001 words to 18000 words out of 111837 words

Chapter 6 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

mu shirya mu je gurin wani Boka a bayan gari?
"Ai kuwa abinda xa a yi kenan inji innah, Allah ya nuna mana goben sai mu fita da wuri don mu samu, mu gabatar da abinda muke so a kan lokaci.
Amsa mata ya yi da amin, sannan ya tattara kan 'ya'yansa suka wuce gida.
Yana shiga gidansa ko sallama bai yi ba, ya fara sababi yana fad'awa matarsa murja abinda ya faru, da yadda suke son yi wa Mahmud da iyalan sa, ita ma ta ji haushi sosai a kan abinda yaron ya yi musu, sannan ta 'kara 'karfafa masa gwiwar su sake komawa wajen wani Bokan, saboda ita kanta tana son ta samu canji ita da 'ya'yanta.






**************************


Nauwar ce xaune a falo ita da Amminta suna karatun al-kur'ani mai tsarki, bayan sun idar suka yi addua suka shafa, sannan suka fara hirar duniya.
"Ammina ina son ki fad'awa Abbana ya canja min school, saboda sam bana jin dad'in yadda Abbanmu yake kashe kud'i masu yawa a kan karatun mu, murmushi Ammi tayi.
"Banda abin ki don an kashewa ilimi kud'i da yawa ai ba wani abu bane daughterna, ke dai ki taya Abbanki da addu'a, Allah ya 'kara masa yalwar arxi'ki, Amin tace, sannan suka cigaba da hirar duniya tana bata labarin 'kawayenta na makaranta suna ta nishad'i abin su.




Sallamar wani matashin saurayi ne ya katse musu hirar da suke yi, matashin baxai wuce 25years ba, Irin samarin nan ne da ake kira FIRST CLASS. He is handsome, well dressed nd classic. Kana ganin shi xaka tabbatar da cewa jinin Rehab ne, don kamarsu d'aya da su Nauwar, kamar an tsaga kara, abu d'aya ne ya banbanta su da shi, He's chocolate in complexion, while su kuma farare ne 'kal. Ammi na ganin shi ta mi'ke tana mishi barka da xuwa, da gudu fu'ad ya 'karasa gare shi ya rungume shi yana oyoyo ya Hamdan, Where is the sweets you promised me? To cika ni mana sarkin rigima, ai na taho maka da shi, hannu ya saka a aljihu ya ciro masa sweets d'in ya bashi. Thank you ya Hamdan!! ya koma ya xauna kan cinyar shi yana ta farin ciki da ganin shi, ita kuwa Nauwar ko d'an kallo bai isheta ba, ta cigaba da kallon TV abinta.


Tashi ya yi daga gurin da yake, ya dawo kusa da ita ya ja kunnenta, 'kara ta 'kwalla, Wayyo Ammina!! Fuskar shi a d'aure yake magana.
" baki ga mutane bane?? kina ganina ki d'auke kan ki don ba ki da kunya ko?
"Ka sakar min kunnena Ya Hamdan Allah ban ganka ba am sorry, oya get up ki bani juice a fridge, turo baki tayi, Allah ya Hamdan ban son tashi Idan ina kallon film d'in nan, dukan bakinta yayi, Wayyo bakina fa ka daka Yaya. xan fasa bakin da yake min rashin kunya ne. tashi tayi ba a son ranta ba ta d'akko mishi juice d'in ta kawo ta Ajiye.
"Sai na ro'ke ki xaki xuba min ko?? I will deal with the hell in you,Idan kina min 'kiwa fa.
"Harar shi ta fara yi da dara-daran idanunta, ta Mi'kewa tsaye tayi tana murgud'a masa baki, mai dukana sai dai ruwa yaro, a guje suka xuba ta fada jikin Amminta tana numfarfashi.
"Me ke faruwa ta tambayeta? Ammi ki yiwa ya Hamdan magana ya........ A dai-dai lokacin ya shigo d'akin.
"Khala Rehab yarinyar nan ta rainani da yawa, Kwana biyun nan rashin kunya take min kamar wani sa'an wasan ta.
"To ba Kaine kake sa ni aiki ba, kaje kayi da kanka mana.
Duka ya sake kawo mata, ta 'kara shigewa bayan Amminta ta 6oye.
Ita dai Ammi dariya take musu, sannan ta yi mata fad'a a kan ta ri'ka girmama shi tunda dai yayanta ne ya girmeta nesa ba kusa ba.
kuka Nauwar ta fara yi, "Ammi Sam bakya ganin abinda yake min, Allah ya tsaneni ya takura min,ta 'kara rushewa da wani kukan.
Khalas share hawayen ki yi hakuri nace.
Falo suka 'kara d'unguma suka koma aka cigaba da hira.
Horn d'in motar Abbansu suka ji, a guje Nauwar da fu'ad suka fita, kowannen su 'ko'kari yake yi ya bud'e motar Abbanshi, yana fitowa suka rungume shi suna murna "oyoyo Abban mu suka fad'a a tare"
"Yauwa dama ina ta jira ka dawo Abbana ya Hamdan ya sa ni kuka d'axu"
"Ni kuma sweets ya bani Abbana"
murmushi Abbansu ya yi, to duka na ji Ku sarakan surutu, mu shiga ciki sai a yi maganar a xaune xai fi ko.
Dukan su da sallama suka shiga falon, d'ur'kuswa Hamdan ya yi ya gaida shi, Nauwar na ma'kale da Abbanta tana ta harar Hamdan, Idan ta harareshi sai ya gyad'a kai alamar xai kamata.
Bayan sun gaisa ya yi sallama da su ya wuce gida.
Abbansu ya d'an huta ya ji matsalolin yaranshi ne ya wuce part d'inshi, sannan ya sanar da Ammin su Nauwar yana son ganinta ,xasu tattauna magana mai muhimmanci da ita, umartar yaranta ta yi, da su yi alwala su yi shirin Kwanciya bacci, sannan tasa suka yi addua ta nufi sashin Mahmud.
Cikin nutsuwa take takawa har ta isa gare shi, ruwan da ke a Ajiye a gabanshi ta tsiyaya mishi a cup, sannan ta xuba masa abinci ya ci, bayan ya gama ne ya fara mata magana.
"Ina son ki taya ni da addu'a akwai abubuwan da suke tunkarar mu ko nace xasu tunkaromu, kuma abubuwan suna da had'ari a cikin rayuwar mu da ta 'ya'yanmu, kada na ja ki da nisa, jiya Baffa ya kirani a waya yake sanar da ni, irin makircin da su innah karime ke son yi mana mu da yayanmu, ba su da buri a yanxu banda su mallakeni da abinda na mallaka, sannan su rabani da ke, abinda nake so kada ki tada hankalin ki, kice xaki sa damuwa a ranki, duk yadda suka so cutar da mu sai Allah ya nufa abin xai same mu, kuma duk wanda ya dogara da Allah to Allah xai isar masa, nasan ke mace ce mai addu'a da dogaro ga Allah, ina son ki 'kara jajircewa sosai a kan wannan dabiar taki, kuma ki 'kara gargad'in yaran nan da kada su saki jiki da su innah, Kin ga yanxu Nauwar na da shekara sha hud'u a duniya, ta fara mallakar hankalin kanta xata iya fahimtar wad'ansu abubuwan.


"Haka ne insha Allah xa mu dage da addua, Allah kuma ya karemu da karewar sa.
Amsa mata yayi da Ameen sannan ta fara shirin Kwanciya bacci.






*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEDDAH TIJJANI*
*ADAM*


*(jeeddahtulkhair)*


*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆




*Wannan shafin gaba dayan shi sadaukarwa ne gareka ABDULLAHI MUHAMMAD LAIMAJI, ina godiya a gareka Allah ya bar xumunci*






*Ina mi'ka gaisuwar ban girma gareki ZAHRA'U ADO HUSSAIN SORON 'DINKI (MAMAN ISLAM) ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci, ya raya Islam a kan tafarkin addinin Islama da sunnar Annabi (S.A.W)*


*Ina neman afuwar ku masu karatu saboda rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar da nayi, da fatan xaku min afuwa*




2⃣0⃣






*W*ayewar garin litinin, tafiya ta kama Abban Nauwar xuwa garin Abuja, domin gudanar da wata bita da gwamnatin tarayya ta shirya musu a can, da wuri Ammin Nauwar ta tashi ta had'a mishi break fast bayan ya kammala, ya bata umarnin kiran Hamdan a kan ya kai su fu'ad makaranta, saboda baya so driver ya riqa yawo da yaran shi, qarfe 7:00am ya wuce garin Abuja. A dai-dai lokacin kuma ta kira Hamdan ta yii sa'a kuwa yana gida, bai yi sammakon fita wajen aiki ba, roqonshi ta yi ya kai yaran makarantam bai musa mata ba ya d'auki mota ya nufi hanyar gidan su Nauwar.




Da misalin 'karfe 8:00 ya 'karaso gidan, da sallama ya shigo falon da suke, samun yaran yayi har sun yi shiri, shi kawai suke jira,gaisawa ya yi da Ammin su Nauwar, sannan ta tambaye shi lafiyar mutan gidan su. da gudu fuad ya 'karaso ya rungume shi, "Alhamdulillah yayana nafi son dama ka kaini school" ni kuwa nafi son Abbana ya kaini inji Nauwar, kamar ma na fasa xuwa makarantar Ammi tana maganar tana kallon idon Hamdan" duk maganar da take yi Hamdan d'in na jin ta amma ko tanka mata bai yi ba, ya cigaba da wasa da fuad, jakunkunansu suka d'auka suka wuce mota.




Gidan baya Nauwar ta bud'e ta shige ta kame abinta, shi kuwa fu'ad duk inda Hamdan yasa 'kafa yana biye da shi, gaban motar ya shige , har Hamdan ya xauna a motar ya fito, fuskar shi a d'aure yake magana "ni direbanki ne da xaki xauna a baya, littafinta take dubawa ko kallon shi bata yi ba, magana nake miki fa!! ya fad'i haka yana mai daka mata tsawa. a haraxane ta d'ago kai ta kalleshi yadda taga fuskarshi ta canja ba wasa, shi yasa idanunta suka cika da 'kwalla "yi hakuri yaya ban ji abinda ka fad'a min ba"
"Ai yanxu kin ji ko? Gyada kai tayi alamar eh.
"To oya dawo nan ki xauna.
tashi tayi ta koma ta xauna, suna tafe yana mata masifa, a tsorace take a motar don haka ta 'kosa su isa makaranta ta huta da jarabar sa, ana xuwa bata bari motar ta gama tsayawa ba ta fito, ji kake kiiiiiiiiiiiiii! Motar ta goge mata kafarta, jini ne ya ri'ka xuba daga 'kafar tata, tashin hankali ne ya bayyana a fuskar Hamdan,
Sunan Allah ya shiga kira, "subhanallah!! saurin me kike yi haka xaki je ki ji wa kanki ciwo, me yasa bakya son yin abu a nutse?? Shiru tayi ta kasa cewa komai sai fito da idanu take yi tana kuka.
lalla6ata ya shiga yi kamar xai yi kuka, share hawayen naki ki daina kuka kin ji dear , Kin ga ciwon ba shi da yawa. nan da nan ya sungumeta sai asibiti aka yi treatment d'in ciwon, sannan ya dawo da ita gida, ranar fuad shi ma bai shiga makarantar ba saboda firgitar da ya yi.
Kai tsaye daga asibiti gida suka dawo, Ammi na ganinsu, hankalinta ya tashi a xatonta wani al'amarin ne ya faru, Hamdan ne ya fara sanar da ita yadda aka yi, ita ma dai lalla6a Nauwar d'in tayi, ta kuma yi adduar Allah ya kare faruwar hakan a gaba.


Ba su fi minti goma da dawo wa daga asibiti ba, suka jiyo hayaniya a bakin gate ana xage-xage, ana dukan 'kofar gidan , jin haka yasa Ammin Nauwar ta umarci Hamdan ya le'ka ya ga abinda yake faruwa, wata mata ya hango ta yi d'amara da mayafinta, tana fad'i in fad'a da mai gadi, a tare da ita akwai wani matashin saurayi wanda ba xai wuce shekara ashirin da biyar ba, nuna inda Hamdan yake tsaye take yi tana xage-xage, duk da baya jin abinda take cewa amma sai da yaji shakkar 'karasawa gareta saboda bai san da me ta xo ba, jikinshi a sanyaye ya isa inda take, a tunanin shi xai ga yarinya matashiya ce take wannan xagin da wannan tijarar, amma sai ya ga tsohuwa 'yar kimanin shekara 70, kallon mamaki yake mata ya kasa cewa da ita komai, ita kuwa sai ashariya take d'ungumawa tana nuna shi.
"Ka kaini inda shegiyar matar da ta mallake min jikana take,don nayi maganinta, ta mallake gida, ta rabamu da abinda d'ana ya haifa mana, ga shi nan har ta kawo wannan d'an mai kama da buxaye, daga jin yanayin kalamanta ya tabbatar da cewa innah karime c Wacce khalarsa ta d'ad'e tana bashi labarin mugun halinta, don haka ya juya ya koma cikin gida, tausayin khalarsa ne ya kama shi, ya ma rasa ta yaya xai fuskance ta da maganar. Da sallama ya 'karasa d'akin ya iske Ammi tayi tagumi tana jiran labarin da xai xo mata da shi.
yanayin yadda fuskar Hamdan ta canja shi ya tabbatar mata da cewa yana cikin damuwa, yana shigowa ta mi'ke, ta fara tambayar shi abinda ke faruwa, sunkuyar da kanshi yayi ya fara sanar mata cewa tayi ba'kar bakuwa ne daga 'Dan batta.




Jiri taji yana 'ko'karin d'ibarta don haka ta nemi guri ta xauna ta fara tunanin ko da me innah karime ta xo mata, tasan dai ita tararuwa ce mai wutsiya ganinta ba alkhairi ba ne, banko 'kofar da aka yi ne,ya dawo da ita daga tunanin da take yi, inna karime ta gani tsaye a kanta, hannunta rike da 'kugunta tana jijjiga kanta da jikinta sai watsa mata wani mugun kallo take yi, mai cike da alamomin tambaya, tsugunnawa Ammi tayi gwiwoyinta har kasa ta gaisheta, dakatar da ita tayi.
bana bu'katar gaisuwar ki irin tsiya,kin xo kin mallake min jika, kuma kin hana mu more shi da komai, banxa ta fadi wato har da gayyato yan uwa a xo a ci arxiki. Hawayen da take 'boyewa ne ya fara zuba a kan kuncinta, ha'kuri ta shiga bawa inna karime.
"Mahmud d'anku ne duniya da lahira ban isa na raba Ku da shi ba, wlh na tabbatar da cewa Mahmud yana 'kaunarku, kuma kuna ranshi a kowane lokaci.
"Kya fad'i haka mana munafukar banxa irin mugun abu, kun bi dare kun bi rana,kun bi bokaye, kun rabamu da d'an mu, mun tattaro mun dawo mu sa ido, mu ga tsiyar da kike shukawa jinin matsiyata"
Kuka Ammin Nauwar ke yi kamar ranta xai fito ta bakinta, ganin hakan bai sa innah karime tayi shiru ta daina fad'ar abinda taga dama ba. Ganin haka yasa Hamdan yace da ita *Khalaty khalliha wa sha,aniha*kai yaro kar ka Xage ni gadon rashin mutunci, da mugun hali sai in tsine maka albarka Idan ka sake cewa wani abu.
A dai- dai lokacin da inna ke magana ne Magaji d'an gurin Audu ya shigo, dama tare da shi ta taho.
"inna xagin ki wannan d'an marasa mutuncin ya yi. hannu biyu ya warware da niyyar marin Hamdan, ri'ke hannun Hamdan yayi, tare da murd'e shi, har sai da yayi 'kara mai 'karfi sannan yace masa *kalli balak* shiga hankalin ka, wallahi tallahi sai na rama ni xaka yiwa targad'e ko? 'ko'karin kuma cakumar Hamdan da kokawa yayi, kafin ya 'karaso inda yake tuni Hamdan yayi kukan kura ya had'a Kansa da bango, sai da ya xane shi sosai, sannan ya Kyale shi, inna karime kuwa sai ihu take yi xa a kashe mata jika, Ammi da ta ga abin yafi 'karfinta, sai ta d'auki wayarta ta kira Abban Nauwar, ta fad'a masa abinda yake faruwa ransa ne ya 6aci sosai.
" kar ki barsu su kwanar min a gidana ki d'auki 20,000 ki basu xan kira driver da mai gadi su fitar min da su, cikin Mintunan da basu fi uku ba sai ga driver da mai gadi sun shigo, sun cakumi Magaji innah karime tana ina xaku kai min shi?? ko kallonta basu yi ba, kawai hannu suka d'aga mata alamar ta biyo su, binsu tayi har bakin mota. a motar suka saka shi, ita ma ta shiga motar suka tafi, ganin haka yasa Ammi sakin gwauruwar ajiyar Xuciya, kud'in ta mi'kawa inna karime, fusgewa tayi tare da bawa Ammi mummunan kallo xaki gani da ni kike maganar.






*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Sadaukarwa gare Ku 'yan uwa rabin jiki NADEEYA BABA IBRAHIM, AISHA BALA ILU & AISHA ISMA'IL ISAH, Allah ya bar xumunci da kaunarka juna*






2⃣1⃣




Tunda Ammi ta koma d'aki ta rasa abinda yake mata dad'i, duk tunanin duniya ya mamaye mata xuciya, tsoro da firgici ne fal xuciyarta, sai ta kasa fad'awa su Hamdan abinda innah karime ta fad'a mata. nan da nan xaxxabi ya rufeta, gumi ne yake ta yanko mata, saboda ta san sharri da makircin innah karime, tasan ko kad'an ba 'kaunarta suke yi ba ita da iyalanta.
Alwala ta d'auro ta fara jera salloli tana ro'kon Allah ya bata kariya ita da abinda ta Haifa. Bayan ta idar ne Hamdan ya lura da yanayin tashin hankalin da take ciki,tambayarta yayi
" Khalaty me yasa naga yanayin ki ya canja gaba daya? kada fa ki sa damuwar wannan mahaukaciyar matar a ranki, har hakan ya cutar da ke, ki sa a ranki baxa ta miki abinda Allah bai 'kaddara miki ba. ke da ki ke da Allah wace damuwa ce xata dame ki, shiru tayi har sai da Hamdan ya gama nasihohinshi gareta.


"Hankalina ya tashi da maganar da ta fad'a min lokacin da xata shiga mota ne Hamdan"
Me tace miki? Ya tambayeta
Xan gani tace min, kuma kasan sharrinta.
"Au don. Wannan maganar ma ai ba abar d'aga hankali ba ce, alheri xa ki gani insha Allah, ki manta da ita kawai".
Amsawa tayi da ameen suka shiga hirar duniya.




Tunda su innah karime suka hau mota suke ta tsine wa Ammin Nauwar a tunanin su, ita ce ta bada umarnin a fitar da su daga gidan.
"Innah wlh dole mu d'auki mataki a kan shegiyar matar nan, saboda na fuskanci ta gama shanye min 'kanin mahaifi ta gama mallake shi , ni fa innah so nake yi ma gaba daya rayuwata ta dawo gidan, don naga wata yarinya mau kyau ta min a gidan, kin ga Idan na dawo sai ki bani ita na aura, komai na ubanta ya dawo hannuna,kuma ita ma fa innah baxa mu barta haka ba, dole sai mun mallaketa.


"Dadina da kai kaifin hankali Magaji, ashe kaima ka fara fuskantar halin da ake ciki, wannan matar da kake gani ba karamar shu'uma bace, dole mu tashi tsaye a kan d'an nan Idan ba haka ba xa mu ga ana yi babu mu, ga shi har d'an uwanta ta kawo ya ci arxi'ki mu kuma ko oho, Wai a ce har ya samu damar yin dambe da kai, saboda yana da d'aurin gindi, to wlh baxa ta sa6u ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login