Showing 78001 words to 81000 words out of 111837 words
Chapter 27 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
bude idanu tare da ambaton Allah, mamaki ne ya cika xuciyarta ji take tamkar a mafarki, laluben gedenta ta shiga yi tana sake murje idanunta don ta tabbatar da gaskiyar abinda idanunta suke gane mata, sake bude idanu tayi sosai tabbas ba mafarki take yi ba su ne dai a wannan halin, Salati ta fara yi tana kuka tana ambaton Allah wani abinda ya Kara daure mata Kai shi ne, kofar kangon a kulle take Sannan basu ji wata alama na cewa an dauke su ba.mayar da kallonta tayi ga Ammi ganinta tayi tana ta faman bacci bata ma san abinda ake yi ba, tausayin Amminta ne ya kamata ta cigaba da share hawaye, tabbas lalurar hauka ba karamar tawaya bace ga dan Adam.
A hankali tasa hannu ta janye ta daga bakin bolar da take, dankwalinta ta shimfida ta Kwantar da ita, a hankali ta janye jikinta daga nata, kofar kangon ta nufa, budeta tayi Sannan ta leka kanta waje mutane ta gani suna ta xirga-xirga babu wanda ya lura da su a wajen, komawa tayi ta xauna ta fara Shawara da xuciyar ta yadda xata nemawa kansu mafita, kokari tayi ta fita sai dai rashin samun suturar da xata rufe jikinta ya hanata fita, kasancewar basu taho da komai ba sai kayan jikinsu, bata son ta dauki dankwalin da Ammi ta kwanta a kai gudun kada ta tashe ta.
Dudduba kangon ta shiga yi inda ta hango wani kwali a can nesa duk ya baci da kaxanta, tashi tayi ta dakko shi ta karkade Shi tsaf, shimfidar da ammi tayi a kansa sannan ta dauki dankwalinta ta daura.
Hawaye ta shiga sharewa tana neman taimakon Allah, tunanin Malam Haruna ne ya fado mata a ranta, tasan duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba, suna can suna tunanin halin da suke ciki, sosai ta rika ambaton Allah tana neman taimako a gare shi tasan bai manta da su ba, sake bude kofar tayi ta fita.
Rasa inda xata dosa tayi don haka ta tsaya tana karewa wajen da suke kallo, unguwa ce ta masu rufin asiri kuma da dukkan alamu mutanen unguwar basu damu da jin halin da wani yake ciki ba, don duk wanda yaxo kallonta Kawai yake ya wuce ba tare da yace mata komai ba.
Ganin tsayuwar da take yi baxai amfaneta da komai ba yasa ta fara bara tana neman sadakar kaya da abinci, haka tayi barar ta gaji don ko yar kallo bata ishi mutanen unguwar ba haka ta gaji da kewaye ta koma kangon, tana bude kofar taci karo da Ammi xaune a tsakiyar bola tana cin busashshen kashi, da gudu ta karasa ta kwace ta karkade mata hannu, fuskarta tayi ta mayar da ita inda ba bola.
Kuka nauwar ta shiga yi mai cike da tausayi,duk wani mai imani idan yaga halin da take ciki sai ya tausaya mata.
Rungume Amminta tayi tana hawaye, tana waigawa gefenta taci Karo da wani abin mamaki kwarya ta gani cike da nono an ajiye a gefenta, addua ta shiga yi gami da karanta ayatul kursiyyu nan da nan ta nemi kwaryar ta rasa.
Tsoro ne ya mamaye xuciyarta tabbas idan suka cigaba da xama a wannan kangon wata rana xasu wayi gari aljanu sun sace su gaba daya.
A yi hakuri ba Yawa
*jeeddahtulkhair π*
[9/9, 9:17 PM] Writer: πππππππ
*AL-MAJIRA*
πππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
πππππππ
7β£1β£
Haka suka kasance a wannan hali a kullum akwai kalar abubuwan ban tsoro da xata ci karo da shi, ga ciwon Ammi ya dada dawowa sabo saboda rashin kulawar da take samu, sannan ga kwana a kusa da bola, a lokuta da dama har ji take ana kiran sunan ammi ana cewa ta taso su tafi sai ta tsananta addu,a sannan take daina jin muryar da take kiranta, ba karamar wuya take sha ba a halin yanxu ita kanta aljanun na mata baraxana da rayuwarta, dagewa tayi da fadawa Allah matsalarta Sannan taji saukin abubuwan.
Yau ma kamar kullum dankwali ta yafa ta fita yin bara, kallo daya xaka yi mata ka gane tana cikin matsala kuma tana matukar bukatar taimako, duk kayan jikinta sun yage, takalmin kafarta ya tsinke sai kullewa tayi da Leda, ga dauda ko ta ina saboda ta dade bata ga ruwan wanka ba, duk tayi baki ta fita daga hayyacinta, kafin ta fita sai da ta daurewa ammi kafa da tsumma don gudun kada ta haura katanga ta gudu, kulle kofar kangon tayi sannan ta fita, yau dai a sa'a ta fita domin kuwa ta samo alkhairi masu yawa, mutane da dama sun tausayawa halin da suka ganta a ciki, wannan dalilin yasa suka rika bata sadaka, sai dai ta samu abincin da xai riketa kwana uku ba tare da ta fita bara ba.
Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa har tsawon sati bakwai yau da dadi gobe ba dadi, wata rana su samu abincin kaiwa bakin salati, wata rana kuwa sai su yi kwana biyu basu samu abinda zasu ci ba, haka suka xauna cikin wannan hali har xuwa lokacin da Allah yasa saimah ta kai su gidan su inda ta roki mahaifanta alfarma ya ba su daki.
Lallai baxa ta manta da karamcin da iyayen saimah suka yi mata ba, su suka fitar da su daga halin kunci da takaicin da suka kasance a ciki na shekara da shekaru.
Tana kammala tunanin da take yi ne, taji anyi sallama cikin dakin da suke, saimah ce da Abbanta da mamansu tare da yayyenta guda biyu suka shigo dakin, sallama suka yi, cikin nutsuwa nauwar ta amsa musu sallamar samun guri suka yi suka zauna.
Cikin nutsuwa ta tsugunnah har kasa ta gaida su, tare da sakin fuska suka amsa mata da lafiya lau.
Duban Ammi suka yi suka yi mata sannu, kwance take tana ta faman sharar bacci cikin kulawa Abban saima ke mata magana.
"Tunda kun samu watanni a gidan nan kun huta kun dawo cikin nutsuwar ku, ya kamata musan tarihin rayuwarki da abubuwan da suka faru da ku domin mu san irin taimakon da ya kamata mu baku."
Share hawaye nauwar tayi ta fara basu labarin abubuwan da ya faru da su da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, kuka sosai suka rika yi saboda labarin su cike yake da abubuwan takaici da bakin ciki.
Cikin karfin hali Abban saima yake magana.
"lallai yarinya kina cikin yanayin da ya kamata duk mai imani ya tausaya muku, kuma insha Allah muna da taimako na musamman da xamu baki, abinda xamu fara yi yanxu shi ne mu nemo nahaifinki mu sanar da shi halin da ake ciki yanxu"
Mayar da kallon shi yayi gareta.
"kina da number wayarsa ne mu kira mu sanar da shi inda zai same mu?
Share hawayen da ya cika idonta tayi.
"ba nida ita Abba, ammi ce kawai ta haddace "
Cike da tausaya ya dubeta.
"bana so naga kina kuka, kiyi hakuri mu bi komai a sannu insha Allah xamu same shi ba tare da mun sha wahala ba"
Godiya ta yiwa Abba.
"ba komai nauwar insha Allah kinxo inda xa a tausaya miki daga nan kuma Xaki hadu da abbanki"
Murmushin farin ciki ta rika yi sbd dadi har da rufe fuska tana dariya, tunda suka bar gida bata taba jin dadi irin na yau ba, saboda an mata albishir din haduwa da mahaifanta.
Abba yaji dadin yadda yaga nauwar na farin ciki, magana ya cigaba da yi mata
"yanxu nasa a kira mai magani ya fara bata taimakon gaggawa saboda tana bukatar a kula da ita sosai idan ya kama ma sai an mayar da ita gidan maganin duk xamu amince sabd Lafiyar ta tafi mana komai a halin yanxu."
Mikewa suka yi gaba daya suka bar dakin, har bakin kofa nauwar ta raka su, tana dawowa ta fadi tayi sujjadar godiya ga Allah, tabbas duk wanda ya dogara ga Allah xai shiga cikin lamarinsa ya taimake shi.
Tun daga wannan lokacin rayuwar nauwar ta fara canjawa daga bakin ciki zuwa farin ciki, kullum addu'arta bata wuce Allah ya bawa amminta lafiya ba, ya kuma juyo da hankalin Abbanta kansu.
Saima ce ta shigo da gudu dakin nauwar, tana murna, kwala mata kira ta shiga yi
"sisina tashi naxo mana da albishir din arxiki"
kwance ta tarar da ita, a raxane nauwar ta mike tana harar saima.
"ni har kin bani tsoro kawata, wane abu kika kawo min haka"
"Sai kin tashi daga kwanciyar da kika yi xan nuna miki idan ba haka ba kuma na koma da kayana"
Da sauri ta tashi tana dubanta tana murmushi
Uniform ta mika mata.
"karbi gobe ki shirya akwai makaranta saura kuma kiki tashi don nasan mutuniyar tawa akwai nauyin bacci"
Tsalle nauwar tayi ta rungume saima tana godiya
"Alhamdulillah na gode sisina Allah ya biya Abba da aljanna babu abinda xamu iya biyansa dashi Sai dai addu,ar fatan alkhairi domin yayi mana komai "
Wani hawaye taji ya taho mata da sauri saima tasa hannu ta share mata hawayen.
"to uwar saurin kuka har idanun ki xai kawo ruwa ko, kinga bana so kike wannan kukan mun zama daya fa"
Share hawaye tayi suka cigaba da wasa da dariya kamar yadda suka Saba.
*jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:17 PM] Writer: πππππππ
*AL-MAJIRA*
πππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
πππππππ
*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ku kewaye na amana Masoya wannan littafi na Al-majira, Ina matukar jin dadi da yadda kuke nuna masa kulawa*
Maijidda Saleh
Aysha mai unguwa
Saratu ma'amun
Khadija umar musa
Hafsat Abdullahi nasidi
*ina matukar jin dadin comments din Ku ana mugun tareπ€*
7β£2β£
Hira suke yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, tattauna yadda tafiyar su makaranta gobe kasance suke yi, sallamar da aka yi ne ya katse musu hirar su, gaba daya suka mayar da hankali da inda aka yi sallamar, yayan saimah ne ya shigo tare da likita, a ladabce suka gaida su, fuskar su a sake suka amsa musu, har yayan saimah na tsokanar nauwar
"mai idanun kuka har kin daina kukan ko har yanxu akwai sauran rigimar? " kunya ce ta kamata taja Hannun saimah suka fita, bin ta yayi da kallo yana mai tausayawa halin da rayuwar su take ciki.
duba Ammi aka fara yi domin tabbatar da gaskiyar abinda ke damunta.
Cike da kulawa likitan ya dubi yayan saimah.
"gaskiya wannan matar sai an mata abubuwan da xata samu kamar Kwana uku tana bacci, saboda tana bukatar ta huta sosai, wannan Shi ne taimako na farko da xamu fara bata "
Cikin nutsuwa yayan saimah ya bashi amsa.
"Yauwa idan aka yi hakan ma daidai ne, muna so mu yi mata wannan ne kafin daga bisani mu fara mata na islamic "
"yayi kyau Allah ya taimaka, Allah yasa kuma a dace"
allurai ya ciro ya fara yi mata, cikin kankanin lokaci suka kammala yi mata, bude tagogin dakin suka yi, suka xuge mata labule, bayan sun fito ne suka samu nauwar da saimah sun hada kai suna hira, rankwashin kan saimah Yaya yayi.
yar Kara ta saki tare da dafe kanta, cike da shagwaba take magana, "Wayyo Yaya da Xafi fa"
"to iyayen gulma kun hada kai kuna sirrin na ku ko, dama fada muku xan yi, kada ku Kara shiga dakin nan ana bukatar ta samu hutu sosai, ke nauwar, dago kai tayi ta kalle shi, yau a dakin saimah xaki Kwana kin ji ko "
Bai saurarI abinda xasu ce ba ya wuce suka fita tare da likita saboda yasan shagwabar saimah bata ki ta fara kuka ba.
Haka suka xauna a soro har xuwa lokacin sallar magariba sannan suka shiga cikin gida don yin sallah.
Washe gari da sassafe saimah ta tashi nauwar don xuwa makaranta, bayan sun kammala shiryawa ne Abba ya basu Kudin Makaranta Sannan ya basu wata takarda yace su kai wa principal, dakin mama suka shiga don yi mata sallama addu'a tayi musu sannan ta kara musu wani kudin, cike da farin ciki suka wuce suka tafi.
Suna tafe a hanya suna hira, kusan duk wanda yaga saimah da nauwar sai ya tambayi a ina ta samota saboda kyawunta da yadda Allah ya tsara mata surar jikinta, wani lokacin ta bawa wasu amsa da cewa yar uwarsu ce, wasu kuma ta kyale su sai dai Kawai su bita da kallo, a haka har suka isa makaranta, Kai tsaye office din principal suka nufa,da sallama suka shiga wajen, cikin kulawa ya amsa musu, bayan sun gaida shi, takarda saimah ta mika masa, karba yayi ya bude ya fara karantawa.
Xare gilas din idon shi ya yi ya dubi saimah
"wannan ita ce nauwar Mahmud wadda Babanki yaxo ya yiwa registration "
Kanta a sunkuye ta amsa masa da eh
Kiran nauwar tayi ta xauna a kujera don yi mata interview ita kuma saimah yace ta wuce aji, Alkur'ani ya dakko ya fara budo mata surori mabanbanta duk inda ya karanta mata sai yaji ta biya ba tare da tayi ko batan wasali ba, da aka dawo bangaren ilimin boko ma haka, duk abinda aka tambayeta sai ta bashi amsa, cike da mamaki ya dubeta.
"haka dama kike da kokari, ni ai da aji daya xan kai ki a tunanina baki iya komai ba, a wane gari kika yi Karatu kafin Ki dawo nan"
Kanta a kasa ta bashi amsa da Kano
"Lallai Kina da jajircewa, to anan ma ina so Ki jajirce Ki fi ragowar kokari da komai"
Gyada masa kai tayi, kallonta Kawai yake yana tasbihi ga ubangiji saboda yadda yarinyar ta dauki hankalin sa, dadin dadawa gata da kokari da nutsuwa, litattafai ya mika mata, hannu biyu tasa ta karba sannan ya mike, tashi mu je na nuna miki ajin da xaki xauna ya fada yana mai dubanta.
A ladabce yayi gaba ta bishi a baya, a bakin kofar ajin ya tsaya ya kira malamin inda ya fara yi masa bayanI.
"wannan sabuwar daliba ce muka yi sunanta nauwar Mahmud tana da kokari sosai na mata interview shi yasa ma na kawota babban aji a kula da ita sosai kada a bari ta hadu da yara masu wasa "
"Insha Allah xan lura da ita "
shiga ajin tayi tare da malamin ashe ajin su saimah ne, tana ganin shigowar nauwar ta taso da gudu ta rungumeta tana murna.
"alhamdulillah naji dadi da aka hada mu"
Gaba daya idanun yan ajin suka dawo kansu, tsawa malamin ya yiwa saimah, a firgice ta juya ta dube shi
"cikata Ki koma Ki xauna ko ranki ya baci"
Sakinta tayi ta koma wajen xamanta, ya saka nauwar a layin farko saboda baya son ya hada ta da saima, don idan ya hada su baxa ta bari tayi Karatu ba, ana karatu Malam na kallon nauwar kamar ya hadiyeta, har sai da ta gane ta fara jin kunya.
Tunda nauwar ta shigo ajin ta xo da farin jini, duk kusan yan ajin suna kaunarta kuma suna son kawance da ita saboda kokarin ta da nutsuwarta, a lokuta da dama malam shi yake hanata kawaye saboda cika umarnin amanar da ya karba a Hannun principal.
A kullum saimah da nauwar tare suke xuwa Makaranta su koma tare, rayuwar nauwar ta canja gaba daya, ta saki jiki da saimah komai tare suke yi tamkar tagwaye.
*jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:17 PM] Writer: πππππππ
*AL-MAJIRA*
πππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
πππππππ
*Yau shafin gaba daya sadaukar wa ne gare ki MISS RAFIN DADI, kiyi yadda kike so da shi na baki halak mallake, halinki da iya mu'amlar ki yasa dole na jinjina miki, wlh ke ta daban ce kin bambanta da mutane da dama, Allah ya Kara miki daukaka yasa kifi haka, ana mugun tareπ€*
πππππππ
7β£3β£
Nauwar ta samu kusan wata biyu tana zuwa makaranta, don yanxu tayi nisa sosai a haddarta har sun fita musabaka ta samu nasarar xuwa na daya, wannan dalilin ya kara mata farin jini a wajen malamai, kamar kullum yau ma da wuri suka kammala shirin tafiya makaranta, basu tsaya bata lokaci ba suka nufi makaranta suna xuwa suka shiga Aji, bayan sun xauna an fara Karatu ne aka aiko wani yaro kiran saimah.
Cikin ladabi yayi sallama tare da gaida malam, dago kai malam yayi ya kalle shi kasancewar lokaci ne da ake karatu, tambayar shi yayi dalilin xuwan sa, tsugunnawa ya sake yi, a hankali yayi masa magana.
"principal ne ya aiko ni yace yana son ganinta yanxu"
Shi ma cikin rada ya mayar masa da amsa.
"ka fada masa xamu karasa Karatu gata nan zuwa"
Bayan an kammala malam ya dubi saimah.
"Tashi kije principal na son ganin ki"
Kirjinta na dukan uku-uku ta amsa masa da to, duban nauwar tayi
"Allah yasa dai ba wani sharrin aka hada mana ba, tunda kika ga mutumin nan yana kirana ba lafiya"
Kwantar mata da hankali nauwar ta shiga yi
"kada ki damu insha Allah alkhairi ne, ke dai ki tafi kina addu,a don kinsan halin fadansa sarai, ba bakon ki bane"
Cike da tsoro take tafiya tana hadawa da addu'a, cikin nutsuwa tayi sallama office din principal samun shi tayi yana rubuce-rubuce, waje ta samu ta xauna a kasa, sai da ya kammala sannan ya dago ya dubeta.
"ya xaki xauna a kasa, tashi ki koma kan kujera"
Tashi tayi ta xauna, kana ganinta xaka san cewa a firgice take, don dosana jiki tayi ba wani xama tayi sosai a kujerar ba.
A ladabce ta gaida shi, fuskarsa a sake ya amsa mata, sake dubanta yayi yana murmushi
"wasu tambayoyi nake so nayi miki ina fatan dai xaki fada min gaskiya"
Kanta a kasa ta gyada kai alamar Eh, duk ta kosa ya kammala dogon jawabinsa ya fada mata abinda yasa ya