Showing 33001 words to 36000 words out of 111837 words

Chapter 12 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

da annashuwa,a kullum Hamdan 'kara xurfi yake yi, a kogin 'kaunar Nauwar, saboda kulawa ta musamman take bashi, ga shi kuma Hamdan ya samu kar6uwa sosai a wajen Abban Nauwar.




Yau da sassafe su Innah karime suka tashi, don cigaba da tattaunawa a kan maganar komawa wajen gobe da nisa, a d'akin Habi suka taru gaba d'ayan su, magana suke yi 'kasa-'kasa,saboda kada Baffan mahmoud ya ji abinda suke fad'a.


Isah da magaji ne suka shigo d'akin, da girmamawa suka gaida su Innah karime,cikin kulawa suka amsa musu,Innah ce ta fara yin magana.




"yauwa Alhamdulillah tun d'axu dama muke jiran xuwan ku,saboda xaman nan haka ya ishe mu,naga alama yaron nan baxai neme mu ba, idan ba mu muka neme shi ba, yanxu na tattara 'yan kud'ad'en da ke hannuna, yau muna yanke shawarar xamu rankaya gaba d'aya mu je gurin gobe da nisa, mu fad'a masa matsalolin mu, ko da taimakon da xai bamu"


magaji ne ya gyara xama ya dubi Innah.


"Ni Innah babbar matsalata a yanxu, bai wuce auren yarinyar nan ba,saboda ta gama yi min,so nake muna mallaketa a yi bikin, bana
son a ja lokaci mai tsawo"


"kasha kuruminka d'an magaji, indai muka je ai magana ta 'kare an yi an gama".


koko da kosai ta mi'ka musu,suka fara sha bayan sun kammala ne,suka rankaya sai gidan gobe da nisa.


yau a 'kulle suka tarar da 'kofar shiga gurinsa, hakan ne ya tabbatar musu da cewa ya shiga aiki,sai yayi wasu mintuna sannan xai fito. don haka suka samu guri suka xauna don su jira shi.




ina son na sanar da ku dama"inji Innah
"kowa ya 'kudurce bu'katar sa a ranshi. saboda bama son mu je mu ri'ka inda-inda, nafi son ana tambaya mu bada amsa"


"ni ai bukatar mu iri d'aya ce Innah" inji isah


"A'a d'an nan akwai bambanci, ni burina na xauna har abada a gidansa,kai kuma nasan ba wannan ne a ranka ba"


"nima kusan hakan ne Innah, amma ni nafi son, na mallake shi mu koma can ni da iyalina, na yar da fatanya na huta da wahala"


Bushewa suka ji an yi da dariya, gaba d'aya hankalin su ya koma inda suka ji dariyar.


mutum suka gani tsaye a kan su,gemunsa har jan 'kasa yake, sanye yake da kayan fata, kansa kuwa cike yake da gashi, ko na wata macen albarka.


mi'kewa suka yi gaba d'ayan su suna dubansa, sake bushewa ya yi da dariya.


"Me ke tafe da ku!!!"


isah ne ya fara yi masa bayanin abinda yake tafe da su, umartar su yayi da su samu gurin xama, don xai fi gamsuwa da bayanan su.


bayan sun kammala gaya masa abinda yake tafe da su ne, ya basu wasu layu da tukwane, ya kuma umarce su da binne su, sannan ya basu turarukan da xasu ri'ka turarawa idan sun je birni, ya kuma yi Al'kawarin babu wani bil adama, da ya isa ya warware abinda ya basu sai dai idan shi ne, yaga damar warware aikinsa, godiya mai yawa suka yi masa sannan suka d'auki kud'ad'e masu yawa suka bashi, suka kuma yi Al'kawarin 'kara masa wani abin, idan sun samu yadda suke so.


basu baro dajin da boka yake ba,sai da suka binne dukkanin abinda gobe da nisa ya basu, sannan suka dawo gida, cikin farin ciki.


da baffan mahmoud suka had'u a kan hanya, don haka yayi musu magana, tare da tambayar inda suka je, amma babu wanda ya nuna ya san shi a cikin su, ballanta har ya samu arxi'kin samun amsa. share shi suka yi suka wuce cikin gida


shirye-shirye suka shiga yi, saboda sun gasgata abinda boka ya fad'a musu na samun biyan bu'katar su da gaggawa, yanke shawarar tafiya birni suka yi a washe garin da suka je wajen boka.


ko sallama basu yi wa baffa,ba kawai sai filin gida ya gani, Habi da xuri'arta gaba d'aya sun tattara sun koma.




su Nauwar na kitchen tana taya Amminta aikin girki, sai kawai ji suka yi ana shigo da kaya, tana le'kowa don ganin su waye, ta yi ido hud'u da innah karime, wata harara ta dalla mata, wannan yasa Nauwar komawa ta sanar da mahaifiyarta.


"Ammi annoba ta dawo mana"


"annoba kuma? ban fahimce ki ba daughter"


"su Innah karime ne 'kwansu da kwarkwatar su suka dawo"


jin wannan maganar ta Nauwar yasa Ammi ta fad'i a sume,saboda bata san da bala'in da suka sake xuwar mata ba, fitowa tayi tana ihu tana neman taimako, amma babu wanda ya kalleta a cikin su.






*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




maijiddatijjaniadam@gmail.com




*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆




*wannan shafin gaba daya naka ne halak malak, 'kanina na kaina, ina ji da kai d'an auta NASIR TIJJANI ADAM, Allah yayi maka albarka ya baka ilimi mai amfani, ina yinka irin mugun sosai d'in nan*😍








3⃣7⃣






Waje ta fita tana ihu, tana neman taimakon jama'a, cikin ikon Allah tayi sa'a mai gadin su na nan, don haka ya taimaka mata suka d'auketa sai asibiti,taimakon gaggawa aka shiga bata, amma shiru ko d'an yatsanta bata iya motsawa, ganin halin da take ciki ne yasa aka yi wa Abbansu waya, cikin xafin nama ya baro office ya xo asibitin.




kuka ya tarar Nauwar nayi, tana ganin shi ta fad'a jikinsa tana kuka"Abba ka taimake ni kada Ammina ta mutu ta barni" kuka take yi mai cike da ban tausayi




"kiyi hakuri Amminki xata samu lafiya nan bada dad'ewa ba, ki yi mata addu'a sosai kin ji 'yar albarka"


waya ya d'auka ya sake kiran likita don cigaba da aune- aune ko xa a gano matsalar da take damunta,'karin ruwa aka shiga yi mata, amma duk da haka idanunta na bud'e ko 'kiftawa basa yi, sannan ga numfashinta yana kai wa da komowa.




Nauwar da fu'ad kuwa babu abinda suke yi banda faman kuka, sun riga sun san idan Ammi ta mutu sun kad'e daga su har ganyen su.




Bayan sallar magrib Hamdan ya iso asibitin shi da mahaifiyarsa, sun tausayawa Ammi sosai saboda halin da take ciki, ga shi ba tada wani babban d'a,da xai xauna ya kula da ita, sai wad'annan yaran da ba wani shekaru ne da su masu yawa ba, mahaifiyar Hamdan ce ta yanke shawarar xama don jinyar Ammi har xuwa ta samu lafiya, amma Abban Nauwar ya'ki fafur, saboda a ganin shi xata shiga ha'k'kin iyalanta, haka tayi ha'kuri ta koma gida,tare da Al'kawarin xata ri'ka xuwa kullum tana kulawa da ita, godiya yayi mata sannan suka wuce gida.




suna ficewa Nauwar ta fara hawaye, tambayarta yayi dalilin da yasa take kuka, da 'kyar maganar take fita,saboda tashin hankalin da ya cika xuciyarta.


"Abba da ka sani ka 'kyale mami ta xauna tare da mu,kaga akwai abubuwan da mu baxa mu iya ba idan baka nan"


"ku kwantar da hankalinku, komai xai xo da sau'ki, dama naje gida kwaso kaya na tarar da su gwaggo Habi sun xo,to xan lalla6a d'aya daga cikin su,taxo ta xauna tare da ku"


"zare ido Nauwar tayi, innah Habi fa kace Abbah!!!!"


"Eh mana, Menene " ya fad'a yana kallonta


"A gabansu fa ta fad'i Abbah,amma babu wanda ya kallemu ballantana ma su taimaka mana, harkokin gaban su suka cigaba da yi, ni dai Abbah ka kyale su dan Allah, kasan mutanen nan ba 'kaunar mu suke yi ba".


"A'a baxa a yi haka ba, sun ce basa nan lokacin da abin ya faru, don haka xasu xo, kuma kada ku nuna musu komai, kin ji 'yar lele, kuma bana son ki ri'ka cewa basa 'kaunar ku, jininsu ne ku baxa su ta6a gudunku ba".




ita dai xuciyarta bata amince ba, haka ta yarda ba don ranta ya so ba.


Yana xuwa gidan ya tarar da su, suna ta sha'anin su, ana ta dafe-dafen abinci tamkar gidan biki, suna ganin shi suka yi tsilli-tsilli kamar marasa gaskiya, har 'kasa suka tsugunnah gaba d'ayan su, suka gaida shi, sannan suka yi masa ya mai jiki.




guri ya samu ya xauna, cikin damuwa yake musu magana




"Dan Allah ina son mutum d'aya daga cikin ku, ta taimaka ta xauna da yaran nan a asibiti,saboda akwai abubuwan da baxa su iya yi mata ba"
cikin kulawa Habi ta amsa masa.


"Ba komai Alhaji Mudi, ai ba sai ka ro'ke mu ba, dama muna da niyyar hakan, ai ba a hana maba da rago fata Alhaji, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad'a"


Amsa mata yayi da ameen.
"ki fara shiri idan na dawo daga siyo magani xan biyo mu tafi"


"to Alhaji ina jiranka"


yana ficewa suka kalli juna ita da innah suka bushe da dariya.


"lokaci fa yaxo innah, wanda xa mu yi amfani da damar mu, wajen 'kara kwantar da wannan shegiyar matar, kada mu kuskura mu barta ta tashi, kullum mu ri'ka yi mata turaren da Boka ya bamu, a rasa gane kan ciwonta, daga nan kin ga gida ya xama namu,ko ba haka ba?"


"kwarai kuwa Habi haka xa a yi kin xo da magana mai kyau"


wani buhu ta d'akko daga gefenta, wani turare ne 'kunshe cikin takarda
"Ungo ki tafi da turaren nan asibiti, ki ri'ka turara mata shi,ba dare ba rana idan mai gidan yayi magana,kice maganin mayu ne, ni kuma xan cigaba da turara d'ayan a gidan nan, xan fad'a masa cewa ciwonta yana da ala'ka da jinnu,dole sai an turare gidan sannan xasu fita,a haka har sai mun cire mata son xaman gidan nan,daga xuciyar ta da 'ya'yanta gaba d'aya"




kar6a tayi ta 'kulle shi a gefen xaninta, sannan ta shirya tsaf don tafiya asibitin.


Abban Nauwar bai dad'e da fita ba, ya dawo don haka suka rankaya xuwa asibiti.










*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


maijiddatijjaniadam@gmail.com


*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Wannan shafin gaba d'aya naku ne, ku yi yadda kuke so da shi, NADEEYAH BABA IBRAHIM & MARYAM LAWAL (MAAMA)*






3⃣8⃣




Abban Nauwar ne ya nuna mata d'akin da suke, shi kuma ya wuce gurin likita, da sallama ta shiga d'akin da su Nauwar suke, gurin zama ta samu, babu wanda ta kula sai faman kallon d'ai-d'ai take wa kowa na gurin, a dai-dai lokacin ne Abban Nauwar ya shigo, tare da likitoci don su cigaba da checking na lafiyar Ammi, tana ganin shi ta saki ranta ta hau subad'i, ita a dole sai ya fuskanci tana 'kaunar su.


cigaba da juya Ammi suka yi, ana mata allurai gami da bata magunguna, aka yi sa'a ta farfad'o ta fara dawo wa hayyacin ta.


kallon Abban Nauwar Habi tayi tana murmushin munafunci.


"Alhamdulillah Alhaji, Allah ya taimaka wannan baiwar Allah ta fara samun sau'ki, yanxu kamata ya yi kuma a had'a mata da maganin hausa, saboda da alamar ciwon nan yana da nasaba da aljanu"


cikin mamaki likitan ya dubeta.


"Hajiya ke xaki nuna mana yadda xamu yi aikin mu, ba wani maganin gargajiya da xa a bata, ki barmu mu gwada ta mu sa'ar, idan aikin mu bai yi ba,sai ku je ku gwada na gargajiyar"


girgixa kai Abban Nauwar yayi.
"gaskiya ne ni kaina ban so shaye-shayen magungunan gargajiyar nan, gara a yi na asibitin xai fi sau'ki".


ganin bata samu goyan baya bane,yasa tayi shiru xuciyarta cike da takaicin, ta samu dama amma bata yi amfani da ita ba.


haka suka gama xaman asibitin bata samu damar turara mata komai ba,innah karime ce kawai ta samu damar yin nata turaren,ita ma kuma ba kullum ba, a haka suka kasance har suka dawo gida.


A kwana a tashi kullum Ammi na 'kara samun sau'ki, kuma ko da yaushe mamin Hamdan na xuwa tana d'ebe mata kewa, su innah karime kuwa, d'aki aka ba su a cikin falon gidan, don haka duk abinda suke shukawa bata sani ba, kuma babu abinda ya canja na xamantakewar ta tsakaninta da mai gidanta, yana kulawa da ita gwargwadon iko.


yau da kasala suka tashi, don ko abincin safe basu samu damar girkawa ba, Nauwar ce ta 'karfafa jikinta don shiga kitchen ta soya musu ko doya ce, innah karime da Habi ta gani,suna barbad'e-barbad'en magani, a cikin kayan abincin su, la6ewa tayi sai da suka kammala, taga duk guraren da suka xuba, sannan ta juya da sauri ta koma d'aki ta sanar da Amminta,bayan sun tafi ne, tasa aka fitar da kayan abincin gaba d'aya aka bai wa mai gadi sadakar su.




ganin duk tsafe-tsafen da suke yi baya tasiri ne yasa suka canja sabon salo,saboda a nasu d'an 'karamin tunanin suna ganin ita ma asirin take yi, shi yasa duk abinda suke yi baya kamata, sai suka 'kara yanke shawarar komawa wajen boka, domin a shagalar da ita ga barin yin addu'a, saboda ta haka ne xa su samu damar cinta da ya'ki.


wannan karon magaji suka aika don yaje ya kar6o musu maganin, cikin farin ciki ya kar6i aiken, a ranshi ya fad'a banxa ta fad'i xan je na shana son raina


kai tsaye gidan magajiya ya xarce, don ya dad'e yana son samun kud'i,don ya hole son ransa, amma hakan ya ci tura, saboda rashin kud'in da ya baibaye shi.


yana fi to ya shiga gidan, ya iske magajiya a xaune kan kujera, tana faman busa sigari,tana ganin shi ta mi'ke tana farin ciki, tasan duk lokacin da magaji xai xo da kud'i yake xuwa, d'aki ta shigar da shi ta bashi lemo da abinci, sai da ya ci ya 'koshi sannan ya fara mata magana.


"Uwar shagalallu 'yar duma-dumar yarinya nake so yau a nan xan huce gajiyata"


busa sigarin da ke hannunta ta cigaba da yi, sannan ta kalle shi tana juya idanunta.


"duk 'yan matana basa nan sun fita, amma idan xaka iya jira sai ka jirasu har su dawo, amma fa ka tabbatar kaxo da wadataccen kud'i"


"Haba uwar daba, kin san idan ba nida kud'i babu abinda xai kawo ni gidan nan, aljihuna a cike yake"


zama yayi har sai da 'yan matan suka dawo, ya gama duk abinda xai yi, da yamma li'kis ya koma gida, suna ganin shi suka ri'ka murmushin farin ciki a tunanin su, yaje ya isar musu da sa'kon da suke so.


xama yayi ran shi a 6ace, kamar wanda wani abu ya same shi, tambayar shi innah karime ta fara yi


"lafiya naga kaxo ranka ba walwala, me ya faru"


idanun shi ne suka firfito waje, alamar rashin gaskiya ya baiyana a fuskar sa.


"wlh innah tun da na fita nake ta yawo a garin nan, kudin da ku ka aikeni da shi, sun fadi gaba d'aya,kuma ban san ya aka yi ba".


dafe kirji tayi tana duban shi.


"sun fad'i!!! kana hauka ne kaje ka xubar mana da kud'ad'e haka"?


"kaddara ce innah, wlh bansan lokacin da suka fadi ba nima, kawai gani nayi babu kud'in a aljihuna"


"karya kake yi tsohon munafuki, ko dai kaje ka bawa 'yan mata kud'in, don nasan yanxu abinda kasa a gabanka kenan"


Habi ce ta le'ko da kai daga d'akin.


"A'a innah karime kada ki yi wa jikana sharri,wane mata yaje yana rabewa kud'i, bana son irin wannan maganar ehe"


ganin bala'in da Habi take mata ne, yasa ta yi shiru saboda tasan tsiyar Habi ta fi tata.










*Jeeddahtulkhair*?[9/9, 9:09 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


maijiddatijjaniadam@gmail.com


*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Wannan shafin gaba d'aya naku ne, ku yi yadda kuke so da shi, NADEEYAH BABA IBRAHIM & MARYAM LAWAL (MAAMA)*






3⃣8⃣




Abban Nauwar ne ya nuna mata d'akin da suke, shi kuma ya wuce gurin likita, da sallama ta shiga d'akin da su Nauwar suke, gurin zama ta samu, babu wanda ta kula sai faman kallon d'ai-d'ai take wa kowa na gurin, a dai-dai lokacin ne Abban Nauwar ya shigo, tare da likitoci don su cigaba da checking na lafiyar Ammi, tana ganin shi ta saki ranta ta hau subad'i, ita a dole sai ya fuskanci tana 'kaunar su.


cigaba da juya Ammi suka yi, ana mata allurai gami da bata magunguna, aka yi sa'a ta farfad'o ta fara dawo wa hayyacin ta.


kallon Abban Nauwar Habi tayi tana murmushin munafunci.


"Alhamdulillah Alhaji, Allah ya taimaka wannan baiwar Allah ta fara samun sau'ki, yanxu kamata ya yi kuma a had'a mata da maganin hausa, saboda da alamar ciwon nan yana da nasaba da aljanu"


cikin mamaki likitan ya dubeta.


"Hajiya ke xaki nuna mana yadda xamu yi aikin mu, ba wani maganin gargajiya da xa a bata, ki barmu mu gwada ta mu sa'ar, idan aikin mu bai yi ba,sai ku je ku gwada na gargajiyar"


girgixa kai Abban Nauwar yayi.
"gaskiya ne ni kaina ban so shaye-shayen magungunan gargajiyar nan, gara a yi na asibitin xai fi sau'ki".


ganin bata samu goyan baya bane,yasa tayi shiru xuciyarta cike da takaicin, ta samu dama amma bata yi amfani da ita ba.


haka suka gama xaman asibitin bata samu damar turara mata komai ba,innah karime ce kawai ta samu damar yin nata turaren,ita ma kuma ba kullum ba, a haka suka kasance har suka dawo gida.


A kwana a tashi kullum Ammi na 'kara samun sau'ki, kuma ko da yaushe mamin Hamdan na xuwa tana d'ebe mata kewa, su innah karime kuwa, d'aki aka ba su a cikin falon gidan, don haka duk abinda suke shukawa bata sani ba, kuma babu abinda ya canja na xamantakewar ta tsakaninta da mai gidanta, yana kulawa da ita gwargwadon iko.


yau da kasala suka tashi, don ko abincin safe basu samu damar girkawa ba, Nauwar ce ta 'karfafa jikinta don shiga kitchen ta soya musu ko doya ce, innah karime da Habi ta gani,suna barbad'e-barbad'en magani, a cikin kayan abincin su, la6ewa tayi sai da suka kammala, taga duk guraren da suka xuba, sannan ta juya da sauri ta koma d'aki ta sanar da Amminta,bayan sun tafi ne, tasa aka fitar da kayan abincin gaba d'aya aka bai wa mai gadi sadakar su.




ganin duk tsafe-tsafen da suke yi baya tasiri ne yasa suka canja sabon salo,saboda a nasu d'an 'karamin tunanin suna ganin ita ma asirin take yi, shi yasa duk abinda suke yi baya kamata, sai suka 'kara yanke shawarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login