Showing 48001 words to 51000 words out of 111837 words

Chapter 17 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

kamar mai karanta labarai, Insha Allah naji bayanan ki kuma xan yi kokari nayi aiki da su, yanxu duk maganar nan da kika yi min kina nufin gaskiya ne ba abinda kika fito yi kenan ba?

"kwarai kuwa, duk abinda na fada maka babu karya ko son xuciya a cikinsa"

Ajiyar xuciya yayi sannan ya cigaba da magana, naji duk abinda kika fada babu karya kamar yadda kika ce.

"menene sanadinki na xuwa wannan gidan, duk da kin san cewa ba gidan mutanen kirki bane, kuma me yasa kika xabi rayuwar barin gaban iyaye"

wannan tambayar ba karamin sosawa Nauwar xuciya tayi ba, nan da nan ta fara hawaye

cikin tausayawa ya kalleta.
"ba kuka xa kiyi ba, fada min dalilinki ni kuma nayi alkawarin samar miki da mafita"

labarin rayuwarta gaba daya ta bashi, ya tausaya mata sosai da halin da take ciki.

"kiyi hakuri yan mata komai mai wucewa ne, na tausaya miki sosai, kuma Insha Allah na xabi na taimaka miki a kan na cutar da rayuwarki, hannu yasa a aljihu ya xaro kudi, mika mata yayi, ungo wannan ki siya duk abinda kike bukata, kuma idan kina da wata matsalar ki rika fada min, ni kuma xan taimaka miki.

sallama yayi da ita ya wuce gida don ko neman Aunty Amarya bai yi ba.

har ya kusa fita daga gidan ya sake dawowa" kin manta baki fada min sunanki ba"

sadda kai tayi sannan ta bashi amsa
"sunana Nauwar amma an fi kirana da Almajira"

tana shiga dakin ta tarar da Ammi na bacci xaro kudin tayi ta fara lissafawa dubu goma ta gani, daga hannu tayi sama tana godiya ga Allah domin Allah ya fara kawo musu mafita.

*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*

*JEEDDAH TIJJANI*

*ADAM*

*(Jeeddahtulkhair)*

*Masu karatu a yi hakuri saboda rashin ganin post a kan lokaci hakan ya faru ne sakamakon rashin wutar da muke fama da shi*

*EXCLUSIVE WRITERS FRUM*

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆

5⃣0⃣

Aunty Amarya ta gani a kanta tana mika mata hannu.
"yarinya kawo abinda kika samu,daga yau idan kin yo samuwa ba boyewa xaki yi ba, fitowa da su xa kiyi ki bani rabona ehe"
mika mata kudin tayi gaba daya ta shiga kirgawa, murmushi tayi ta dubeta
"lallai yarinyar nan kina da sa'a har dubu goma ya baki, tabdi lallai Alhaji ya yaba da ke"

xaro dubu biyu tayi ta mika mata
"ga wannan ki rike a hannun ki, ragowar dubu takwas din kuma,xan rike a hannuna,daga yau xaki fara tara kudin hayarki da kudin da xaki rika cin abinci, da kuma abinda xaki rika siyan kayan kwalliya, domin ki kara samun kasuwa, don ba haka xaki xauna kara xube ba"
bin ta Nauwar tayi da ido ba tare da tace komai ba, wani kwano Amarya ta janyo ta dakko kofi ta xuba mata wasu magunguna mika mata tayi.

"karbi wannan ki sha"
Hannu tasa ta karba
"wannan kuma na menene Aunty me xan yi da shi"

"Ban san abinda xaki yi da shi ba uwar tambaya, ya xa a yi kije wajen namiji sannan kice baxa ki sha abinda xai wanko miki ciki ba, idan so kike ki samu ciki kada kisha, duk lokacin da kika sake kika yi ciki xamanki ya kare a gidan nan, dan haka sai ki xabi abinda ya fi dacewa da ke" tana gama fada mata ta fita daga dakin

daukar maganin tayi ta xubar da shi, saboda babu abinda ya hada ta da maganin xubar da ciki.
kullum fata take yi Allah ya kawo mata hanyar da xata samu mafita, ta bar gidan Aunty Amarya saboda a kullum burinta ta saka ta a hanyar banxa.

Haka rayuwar su ta cigaba kasancewa a gidan Amarya, a kullum Alhaji talle sai yaxo yaga Nauwar ya mata alkhairi.

wata rana da misalin karfe 6:00 na yamma Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya, tun a tsakar gida suka hadu da ita suka gaisa ya fada mata abinda ya kawo shi, daki ta shigo da shi don su tattauna maganar da ta kawo shi,domin ya fada mata xancen mai muhimmanci ne.
tabarma ta shimfida masa sannan ta nemi gefe guda ta xauna ta fara sauraren shi.

"A gaskiya Hajiya Amarya naji dadi kuma nayi farin ciki da hadin da kika yi min da wannan yarinya yar arxiki, yarinyar tana da ladabi da nutsuwa fiye da tunaninki"
washe baki Aunty Amarya ta shiga yi
"ai duk hadin da nake yi ai babu na tumun dare Alhaji, kadan ma kaga ni daga alheran da xata xo maka da shi"

gyara xama yayi ya cigaba da bayani
"wannan dalilin yasa naga ya dace naxo na nemi auran yarinyar nan a wajen ki tunda dai kece uwarta kece ubanta"

dafe kirji Aunty Amarya tayi, aure fa kace Alhaji yaushe aka yi daren da gari xai waye, ka bari ku kara fahimtar juna sosai sai ka fito a yi magana"

katse mata magana yayi.
"ai babu wani sauran fahimtar juna da ya rage mana yarinyar nan tana kaunata, idan kuma kina ganin ba haka bane a kirata kiga xahiri"

Nauwar ta kwalawa kira, da hanxari ta karaso wajen ta tsugunnah, suna hada ido da Alhaji talle ta sunkuyar da kanta kasa.
magana Aunty Amarya ta fara yi

"Almajira!!" dago ido Nauwar tayi ta kalleta.
"ga Alhaji Talle nan yaxo neman aurenki wace shawara kika yanke"

xaro ido Nauwar tayi
"neman aure fa kika ce Aunty Amarya, ni ban shirya auren kowa ba yanxu saboda rashin lafiya Ammina har sai ta warke xan fara saurarar samari"

dakatar da ita Alhaji Talle yayi
"haba yan mata rashin lafiyar mahaifiyar ki baxa ta hana mu aure ba kuma baxa ta katse mana jin dadin rayuwa ba, na miki alkawarin baki kulawa mai yawa fatana kawai ki amince da bukatata a wuce gurin"

*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*

*JEEDDAH TIJJANI*

*ADAM*

*(Jeeddahtulkhair)*

5⃣1⃣

Shiru Nauwar tayi tana sauraren abinda Alhaji Talle da aunty Amarya ke fada, sai da suka kammala tsaf sannan tayi musu magana.

"duk naji abinda ku ka fada Aunty, amma ni ban amince da wannan hadin ba, dama nayi xaton Alhaji ya taimaka min ne saboda Allah, dan ni a matsayin uba na dauke shi, don haka baxan iya auren shi a matsayin abokin rayuwata ba"

rike baki aunty amarya tayi tana mamakin kalaman Nauwar.
"lallai yarinyar nan kin cika butulu, dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, yanxu duk mutuncin da Alhaji yayi miki, kin mance har xaki watsa masa kasa a ido kice bakya son shi, to idan baki yi auren ba uban me xaki yi"
ganin aunty Amarya nata faman fada, shi yasa Alhaji dakatar da ita.

"haba Amarya abin ai bana tashin hankali bane, don tace bata sona ai bata yi laifi ba, saboda ba a soyayya dole amma abinda xa a yi duk abinda tasan nawa ne, ni na bata ko na kashe mata, xan rubuta list yanxu ta tattaro min kayana ta bani, idan ba haka ba kuma xan shigar da kara wajen hukuma"

gumi ne ya rika yankowa Nauwar ta ko'ina, ina xata samu kudin da xata biya shi abinda yayi mata, alhalin duk kudin da yake bata aunty Amarya ke karbewa ta kashe abinda yake xuwa hannunta ba mai yawa bane.

katse shirun da suka yi Aunty amarya tayi.
"wace shawara kika yanke game da al'amarin nan, Alhaji yana da abin yi ke kawai yake jira"

hawaye ne ya rika yankowa daga idanun Nauwar, bakinta na rawa ta amsa musu da
"na amince"

farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Talle ya shiga washe baki.

"yauwa ko kefa ai haka ya fi miki, Allah ya min arxiki na samu tsuntsu daga sama gasashshe, ke kuma Amarya Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hadi da kika yi"

"ba komai Alhaji ai yiwa kai ne"

duban Nauwar tayi, tashi ki tafi tunda an gama maganar da xa a yi da ke, mikewa Nauwar tayi ta bar dakin.

tana fita Aunty Amarya ta dubi Alhaji.
"yanxu abinda ya rage sai a fara shirye-shiryen biki, kudi xaka rika bayarwa ana siyo mata kayan da xa a jera a daki, kasan ba tada kowa sai ni sai kuma kai,don haka duk wani gata da uba xai yiwa yarsa kaine xaka yi mata"

duk wannan ba matsala Hajiya hannu yasa a aljihu ya xaro kudade masu yawa ya mika mata, ki fara siyo mata kayan aikin gida, saboda nan da sati biyu nake son a yi komai a gama.

Tun daga ranar da Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya aka yi maganar auren su da Nauwar, ya kara dagewa wajen yi mata hidima, ita kuwa tun daga lokacin ta fada cikin damuwa ta daina walwala, saboda tana cikin tsaka mai yawa, gaba daya rayuwa tayi mata xafi.

Ana saura kwana uku daurin aure, Aunty Amarya ta gama shirya mata komai na gida inda aka fara shirye-shiryen tafiya jere, samun Nauwar tayi a daki ta hada kai da gwiwa.

"har yanxu baxa ki hakura da damuwar nan ba, aure fa ba fashi saboda Alhaji baxai yafe miki kudin da ya kashe miki ba, dama shi ba a cin kudinsa a kwana lafiya don haka ki kwantar da kai, ki samu rabonki, yanxu xan kira mai kunshi da gyaran jiki tayi miki"

"kinga Aunty kada ki fara a kirawo min kowa, ba wani kunshi da xan yi, wlh da ina da kudin da xan biya wannan mutumin abinda ya kashe da tuni na biya shi, na huta da masifa, dan gaba daya bana son auren nan ni ba aure ne a gaba na, idan na aure shi ya xan yi da mahaifiyata"
ta karasa maganar tana kuka.

"idan ta maganar mahaifiyarki ne mun gama magana yace xai bata dakin a gidan da xaki xauna, ke dai ki kwantar da hankali kici arxiki ki bar arxiki a inda yake"

fita tayi ta bar mata dakin tana ta faman share hawaye, ita dai taga masifa daga wannan sai wannan, Allah ya kawo mata mafita.

Yamma nayi Alhaji talle yayi sallama gidan da nauwar take, kai tsaye dakin Aunty ya shiga ya tarar da ita xaune ita kadai tana ta sharbar kuka, gefe guda ya samu fuskarsa cike da tashin hankali.

"lafiya kike kuka Amaryar Alhaji, kiyi hakuri ki karbi abin nan a matsayin kaddara, na kudiri niyyar baki kulawar da da mahaifi, baxan cutar da ke ba,baxan bari komai ya cutar da ke ba, fatana dai ki soni ki kuma bani kulawa kamar yadda xan baki"

share hawaye tayi sannan ta dube shi da jajayen idanunta.

"Kayi hakuri ka fita a rayuwata wlh bana kaunarka"
murmushi Alhaji yayi
"lallai ke yarinya ce, ai ita rayuwa dama ba komai da kake so,kake samu ba wani abin karbar shi kawai ake yi ba dan ana sonshi ba, ki kwantar da hankalin ki kawai"

kudi ya mika mata karbi wannan dubu talatin ne kiyi walima ke da kawayenki.

hannu tasa ta karba taji wani sanyi a ranta, yana bata ya mike ya fita daga dakin.

A ranar ta nemi ixnin Aunty amarya tana son xata kai Ammi chemist saboda tana dan fama da xaxxabi, cikin kulawa ta amsa mata

"ayyah Allah ya bata lafiya, kiyi sauri ki dawo xaki taya ni aiki"

tana fita ta kama hanyar tasha, ta xabi barin garin ne saboda hakan shi ne samun farin cikinta. motar da xata kai su garin gombe ta samu, ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya sai gombe.

*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*

*JEEDDAH TIJJANI*

*ADAM*

*(Jeeddahtulkhair)*

*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*

*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*NANAH JUWAIRIYYA, SHAMSIYYA ZAYYANU RIMI, SAKEENAT JIBRIL, naji dadin comments dinku Ina godiya da yadda kuke kaunar wannan littafi na AL-MAJIRA Allah ya bar xumunci*

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆

5⃣2⃣

Har bayan iska'i Amarya na dakon dawowar nauwar Amma shiru ba Labari, gajiya tayi da jira dan haka ta dauki aikinta ta fara yi, tana aikin tana masifa, jira Kawai take nauwar ta dawo ta sauke mata kwandon bala'i, bayan ta kammala ta dauki mayafi ta fita xuwa chemist din da tace mata xata je.
Dan sallama ta shiga shagon inda ta tarar da mai chemist din yana shirye shiryen kullewa, gaisawa suka yi Sannan ta fara yi masa bayani
"Malam musa ya gida ya aiki"cikin sakin fuska ya amsa mata
"alhamdulillah Hajiya Amarya "
"Dan Allah Malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login