Showing 90001 words to 93000 words out of 111837 words

Chapter 31 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

nasan xai yi farin ciki idan yaga yadda jikinta yayi, idan na dawo gida sai na wuce wajen bada cigiyar"


"To shikenan dan albarka"


mayafi suka dauka, sai gidan mai magani, ba karamin mamaki yayi da gani Ammi ba, wajen xama ya basu, fuskarsa cike da fara'a ya dube su.


"Alhamdulillah, Allah maji rokon bawa, sannu baiwar Allah kin sha fama"


murmushi Ammi tayi ta dube shi.


"komai yayi sauki malam yanxu babu abinda nake ji mun gode sosai Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi"


hira sosai suka rika yi da Ammi akan rashin lafiyar da tayi, bayan sun gama ne suka yi sallama, kudade masu yawa yaya sadeeq ya bashi, cike da farin ciki mai maganin ya karba, adduar fatan alkhairi ya rika yi musu sannan suka tashi suka bar gidan.




kai tsaye gida yaya sadeeq ya mayar da su mamah sannan ya wuce wajen bada cigiya.


bai dade da tafiya ba ya dawo, tarar da su yayi a tsakar gida suna cin abinci da sallama ya karasa wajen da suke, cikin kulawa mama take masa magana
"sannu da xuwa
saddequ har ka dawo amma kayi sauri sosai"


takalmansa ya shiga cirewa.
" naje na kai mama sun ce Insha Allah xasu bada sanarwar har xuwa lokacin da xa a dace, na bada number wayar da xa a same mu"


Albarka ta shiga saka masa sannan ya shiga kitchen ya dakko abinci.


**********************


A bangaren Abban Nauwar kuwa, sun yi nema har sun gaji don haka suka yanke shawarar komawa gida kawai su cigaba da addu'a don sun san Allah maji rokon bawansa ne.


sallama yayi da Hamdan da Abbansa shi kuma ya wuce gida.


Yana nufo kofar gidansa yaga kofar gidan a bude alamun akwai mutane a ciki, da sauri ya doshi kofar shiga gidan, ihu yaji ana yi ana neman taimako, da hanxari ya shiga gidan don ganewa idonsa abinda ke faruwa.
















*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Ina yiwa al'umar musulmin duniya Barka da sallah da fatan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen*




8⃣3⃣








cikin fushi ya shiga gidan tarar da kofar yayi a kulle, buga kofar ya shiga yi ba kakkautawa amma ba a xo an bude masa ba sai ihu da yake tashi.
ganin ba a da niyyar bude masa ne yasa ya fita ya bar gidan, kiran me gyara yayi inda ya balle masa murfin kofar ya shiga.


cikin falon ya sa kanshi, ihu dai yake ji amma kuma bai ga komai a ciki ba, dakin Ammin Nauwar ya shiga, da sauri ya ja da baya yana ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, innah karime ya tarar maciji ya nade mata jiki, ihu kawai take tana neman taimako, jawo kofar dakin yayi ya kulleta, da sauri ya dauki mukullin moto ya fita, kiran masu cire maciji yayi, suna isowa suka shiga dakin da take.


kallo daya mai cire macijin yayi wa macijin da ya nadeta ya ja da baya, dafa kafadar Abban Nauwar yayi.


"Alhaji wannan ba irin macijin da muke cirewa bane, wannan da gani na iska ne, abinda xa a yi kawai turaren magani xan mata, idan ya saketa shikenan idan kuma bai saketa ba sai a yi hakuri, sbd aikin ya fi karfina"


wani gumi ne kawai yake yankowa Abban Nauwar, mamaki yake daga ina ma macijin ya shigo har ya makale mata a jiki bata sani ba.


"shikenan ba komai a gwada yin turaren idan an dace shikenan"


burgima innah karime take yi, tun tana ihu har muryarta ta dashe, turare ya saka a dakin ya kulle sannan suka dawo falo suka xauna.


tagumi Abban Nauwar yayi sbd abubuwan da suke faruwa a gidan sa suna matukar bashi mamaki, a xuciyarsa yake magana.


"mutanen nan sai dai idan wani mugun abin suka kunno ya koma musu kansu, kadan ma suka gani daga aikin asiri"


bayan minti biyar da saka turaren ya tashi ya shiga dakin, tarar da macijin yayi ya sulale ya gudu, gaba daya innah karime ta galabaita ta fita daga cikin hankalinta, a hankali ya dagota, kiran Abban Nauwar yayi da hanxari ya karaso ciki.


"Alhaji abin nan ya illata baiwar Allahn nan saboda duk wata ga6a ta jikinta ya karyata, sannan kuma yayi mata tsattuwa a ido, gaskiya sai tsananin rabo xata samu ta mike, kuma ko ta mike ta rasa idonta biyu"


cikin jimami Abban Nauwar ya dubi mai magani.
"yanxu babu wani taimako da xa a bata kenan"


kallon shi yayi sannan ya mayar masa da amsa.
"taimako daya xamu yi mata shi ne mu bata maganin da xata yi aman dafin da ya xuba mata a cikinta, amma idonta gaskiya ya tafi baxai dawo ba sai dai hakuri"


magana suka jiyo ana yi a falo don haka suka kasa kunne don jin abinda ake fada, Habi ce ta shigo tana shewa.


"innah kina ina ki fito yau nayi ido hudu da gobe da nisa, ya fada min mahaukaciya baxa ta kara samun lafiya ba har abada, kuma shi ma mudi gobe ko jibi xai yi ajalinsa tunda yanxu wulakanta mu yake yi, gara ya hallaka shi kowa ya huta dukiyarsa kuma mun yi alkawarin xamu raba gida biyu mu bashi kaso daya"


duk wannan maganar da take yi a tunaninta babu kowa a gidan saboda bata nan Abban Nauwar ya dawo, shirun da taji ba a amsa mata bane yasa ta shigo cikin dakin, tarar da su tayi tare da mai magani sun yi tsaye suna mamakin maganganun da suka ji daga gareta.


tana ganin Abban Nauwar ta xube kasa tana borin kunya, shi kuwa kallonta kawai yake ya kasa magana saboda mamaki.


mai maganin ne ya buga mata tsawa.
"matsa ki bamu guri munafukar banxa munafukar wofi, kina tsammanin duk maganganun da kika fada bamu ji abinda kika ce bane, to yau karyar asiri ta kare wanda kike yi dominsa yaji komai, yanxu ma da shirin da kika taho da shi ki bani abinda kika karbo kafin na tona miki asiri"


rawar baki Habi ta fara yi.
"wlh ban karbo komai ba Allah ya gafarta malam, babu komai a xuciyata sai alheri"


sake daka mata tsawa yayi.
"xaki bani ko sai na mayar miki da duk asiran da kika yiwa wannan bawan Allahn da iyalansa kan ki"


rufe ido yayi, sannan ya mika mata hannu.
"miko min maganin da ya baki kafin na bude idona"


rawar jiki ta fara yi nan da nan, ta fara kwance gefen xaninta sai ga magunguna nan suna fadowa, a hankali ya sunkuya ya kwashe magungunan.


fuskarsa a daure ya dubeta.


"akwai binne-binnen da ku ka yi,ina so ki hako min shi yanxu ki bani"


sake duban Abban Nauwar yayi.


"wannan matar shaidaniya ce ita da wannan ta kwancen da maciji ya makalewa a jiki, kuma wannan macijin su suka kawo shi gidan nan don ya cutar da kai, sai kaikayi ya koma kan mashekiya, don haka baxan bata maganina ba saboda muguwa ce, gobe kuma xan dawo duk wani mugun aiki da suka yi a gidan nan sai na warware shi, ke kuma" ya nuna Habi da hannu.


"gobe ki shirya duk abinda kika yi na sharri sai na mayar miki da shi kanki, xaki bada labarin illar xalunci da kanki"


faduwa Habi tayi tana rokon shi ya taimake ta ya rufa mata asiri amma ko kallonta bai yi ba ya fice a fusace ya bar gidan.




shi kuwa Abban Nauwar bakin ciki ma ya hana shi magana, kawai wani hayakin bakin ciki ne yake taso masa a xuciyarsa, jiran gobe kawai yake yi ta ga ruwan rashin mutuncin da ya tanadar mata.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆








8⃣4⃣


Gwiwoyi biyu Habi
tasa a kasa tana rokon shi gafara.
"Dan Allah kada ka bari mutumin nan ya maido min da abinda ba nida hakki a kansa, wlh ba nida wani hannu cikin 6atan yayanka, ban san abinda ya faru ba ka taimaka ka tallafi rayuwata, kasan babu yadda xa a yi a hada baki da ni a cuci iyalanka ko dan alkhairin da kayi mana"


Hawayen takaici Abba Nauwar ya shiga xubarwa ficewa yayi ya barta a dakin tana ta sambatu, sashinsa ya nufa yana shiga dakin ya fada kan gado ya cigaba da share kwallar bakin ciki.


waya ya dauka ya kira baffa, cikin kuka yake masa bayani abinda ya faru.


"Baffa ashe duk halin da na shiga da sa hannun Gwaggo Habi da innah karime"
salati Baffa ya shiga yi.
"Ai dama kaine baka gane ba Mahmud ni na dade da fuskantar hakan, fatana dai kayi hakuri kada ka saka damuwar hakan a ranka kuma ka cigaba da addua komai na Allah yana da iyaka, ya labarin jikat kuwa"


gyaran murya yayi sannan ya fara yi masa bayani.


"wallahi Baffa nayi neman duniya babu labarin su, mun kai cigiya duk inda ya kamata amma har yanxu bamu ji wata magana mai karfi ba, dan Allah ka taya ni da addu'a ina cikin kunci da damuwa ko bacci bana iya yi, xaka yi mamaki idan kaga yadda na rame na fita daga hayyacina"


Hakuri Baffa ya rika bashi yana rarrashinsa har sai da xuciyarsa tayi sanyi, daga karshe Abban Nauwar yake shaida masa abinda ya faru da innah karime, cikin tashin hankali Baffa yake tambayarsa.


"yaushe ita kuma wannan ibtila'in ya afka mata"


"jiya ne Baffa nima bana nan sai dawo wa nayi na tarar da ita a wannan halin"


ba karamin damuwa Baffa yayi da halin da innah karime ke ciki ba.
"Dan Allah kada ka duba abubuwan da suka yi maka, ka danne xuciyarka ka kula da ita ko dan tsufanta, na roke ka kayi haka dan Allah Mahmud"


"Insha Allah xan yi yadda kace Baffa"
sallama suka yi sannan ya kashe wayar, a ranar kwana yayi cikin bakin ciki da jimamin sharrikan da su innah karime suka kulla masa.


washe gari da misalin karfe goma na safe mai magani ya iso gidan, bai tsaya an shigo da shi ba ya karaso har cikin falo, kiran sunan Abban Nauwar ya shiga yi cikin xafin nama ya karaso inda yake, bayan sun gaisa ne yake tambayarsa ina Habi take.


"ni tun safe ban ji motsinta ba don ko sallah bana jin ta fito tayi"


bakin kofar dakin ya nufa, buga kofar ya shiga yi amma shiru ba a bude ba, mai maganin ne ya taso da kansa ya fara bugawa yana yi mata masifa, a hankali ta jawo jiki ta karaso bakin kofar.


"Baxan bude kofar nan ba har sai kayi min alkawarin baxa ka tona min asiri ba"


dabara yayi mata har taxo ta bude.
Bayan ta fito ne yace ta karaso falo su yi magana, bata yi gaddama ba ta fito.


"Abinda nafi bukata a yanxu kawai ki tashi salun alun, mu tafi ki nuna min guraren da ku ka binne asiri idan ba haka ba kuma ni xan nuna gurin da kaina kuma sai na toxarta ki a idon duniya"


jikin Habi na rawa ta tashi, da farko kitchen ta shigar da su inda ta nuna wani waje tace a nan ma sun binne asiri, ha'ko wajen ya fara yi inda aka fito da layu an sanya su a cikin tukunya, a take ya doka su da kasa ya fasa sannan ya kone layun.


sake tasa keyarta yayi ta rika kai shi gurare mabanbanta da suka binne asirai a cikin gidan, har dakin Abban Nauwar sai da suka je nan ma sun yi ajiye ajiye a cikin pillow.


Bayan sun gama xageye ko ina na gidan amma bata nuna da dakin Ammi ba, a cewarta tace babu komai a ciki.


cikin fushi mai maganin ya dubeta.
"kada ki rainawa kan ki hankali, na riga nasan komai game da abubuwan da ku ke yi,kawai ki tashi mu je ki nuna min inda kika binne mugun abin ku"


kuka sosai Habi take yi tana rokon shi ya kyaleta bata san wajen da suka ajiye ba, tilasta mata yayi sai da ta tashi ba a son ranta ba.


suna shiga ta nuna karkashin gado tace duk Abinda ya faru da Ammi a nan suka xo suka binne.


nunata yayi da hannu.
"xo ki hako da kanki ki kona tunda ku ka xo ku ka saka"


nan ma dai tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta, nan da nan gumi ya rika yanko mata ta ko'ina, rokon shi ta fara yi.


"ka taimaka ka kyale ni wlh Aljanu aka turo suka binne abin nan kuma wanda yayi aikin ya fada mana cewa duk wanda ya taba wannan asirin shi ma sai yayi hauka irin wanda matar Mudi tayi,ka rufa min asiri ka kyale ni"


Sake daka mata tsawa yayi yace ko tana so ko bata so sai ta hake abin da hannunta.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆




8⃣5⃣






Gigicewa Habi tayi hawaye ko ta ina zuba yake a kan fuskar ta, sake tsugunnawa tayi tana rokonsa amma ya toshe kunnuwan sa yaki saurararta, innah karime na kwance duk ta zama abin tausayi da kyar take iya bude baki tayi magana, cikin karfin hali ta fara yiwa mai magani magana.


"Dan Allah malam ka dubi girman Allah kayi mana alfarma kada ta taba abin nan, wlh ita kadai ta rage mai kula da ni, jikanta mai jin tausayina ya samu tabin hankali, ni kuma yanxu ba nida ido ita take min jagora ta bani abinci tayi min duk abinda ya kamata, dan Allah ka duba wannan Al'amari kayi mana rangwami "


Babu alamar tausayi a fuskarsa ya dubeta.
"me yasa lokacin da xaku aikata sharrin baku dubi girman Allah kun fasa ba, kunga kuwa tunda baku ji tsoron Allah kun ki aikata sabo ,nima bazan fasa mayar muku da sharrin ku kanku ba, don haka dole sai ta dakko abin nan da Kanta ta warware, tunda hannunku ne ya ajiye, kema Allah ne ya rufa miki asiri wannan bala'in ya afka miki amma wlh da kinga yadda xan mayar da ke a cikin gidan nan"


Jin wadannan maganganun da yake fada ne yasa innah karime taja baki tayi shiru, tun daga lokacin bata sake cewa komai ba.


Sake dakawa Habi tsawa yayi jikinta na rawa ta mike ta nufi karkashin gadon Ammi, taimaka mata suka yi suka tayata janye gadon sannan ta fara tono abinda suka binne.


Tana tonawa tana hawaye, wani wari ne na tashin hankali ya rika fitowa daga ramin, a hankali ta rika hakowa har sai da taxo dai-dai wajen da aka binne asirin, wata tukunya ta dakko wadda aka nadeta da fata ga kuma layu da aka kewayeta da su, karba mai maganin yayi ya ajiyeta a gefe, cigaba da tonawa tayi sai kuma ga gafiya an saka laya a bakinta duk jikinta ita ma an xagaye shi da layu, sai da ta gama fito da kayan tsafin tsaf, sannan ta koma gefe ta tsaya.


Cikin fushi mai maganin ya dubi Habi.


Kin fito da kaya saura kuma warware su, ke kika kulla kuma Kece xaki kwance.


Nan ma dai tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta saboda tasan matukar ta warware wadannan kaya kashinta ya bushe.


Sake dubanta yayi yana xare mata idanu ki warware nace kafin naci mutuncin ki.


Cikin kuka ta dubi Abban nauwar
"yanzu mudi a gabanka xa a tozarta ni a ci min xarafi amma kayi shiru baka ce komai ba, amma wlh idan ka bari aka ci min mutunci baka cika dan halak ba, ka tuna a matsayin uwa nake a wajenka"


Ransa a bace ya mayar mata da martani.
"babu abinda zance sai dai Allah ya Kara, dama hausawa sun ce idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, gashi nan kin gina kina tunanin ni kadai da iyalaina ne xamu fada ciki, to gashi nan kema kin fada cikinsa, kuma wannan kadan kika gani daga cikin illar zalunci wata shari'ar ma sai a lahira dan wallahi baxan taba yafe abinda ku ka yi min ba"


Ya karasa maganar yana kuka..


Cikin kulawa mai magani ya dube shi.


"kada ka damu Alhaji sai fa ta warware abin nan, ko da hakan xai yi sanadiyyar mutuwarta dama irin su ba su da amfani a cikin al'ummah gara ta mutu kowa ya huta "


Kuka Habi ta rika yi saboda taji an ambaci mutuwa gaba daya ta gigice sai faman magiya take yi.


Umarni ya kara bata a kan tace fara warware asirin da hannunta, wani hayaki ne da duhu suka turnike dakin, ga kuma wari na tashin hankali, tana warware asirin yanayin halittar ta da kamanninta suna juyewa suna komawa irin na dabbobin daji, shi kansa mai maganin sai da abin ya bashi tsoro, sai da ta gama warwarewa gaba daya ya umarceta ta tashi..


A hankali taja jiki ta koma kusa da innah, wani bacci mai nauyi ne ya dauketa dan haka suka fito suka bar dakin..


har kofar gida Abban nauwar ya raka mai magani sannan yayi masa alkhairi mai yawa.


Godiya mai magani yayi masa sannan ya dube shi.


"Alhaji na gode da wannan karamcin naka ina mai tabbatar maka da cewa mutanen nan sai sun ga karshen su, ka jira xuwa lokacin da matar nan xata farka xaka ga abinda xai faru, fatana dai kada kayi sake da addu'a saboda gidan nan naka sun lalata shi da shaidanu yanzu haka shaidanu ne cike a cikinsa, don haka sai ka dage da karatun kur'ani."


Godiya Abban nauwar yayi masa sannan suka yi sallama ya tafi.








*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆






8⃣6⃣






Kai tsaye daki ya wuce ya fara tunanin halin da su habi suka jefa kansu, tashi yayi ya rika kewaye dakin yana jinjina irin mugun halin su, alwala ya dauro ya fara jero salloli yana addu'a Allah ya bayyana masa matarsa da yarsa.


A ranar bai runtsa ba addu'a ya rika yi sosai yana neman taimakon ubangiji, bai kwanta ba har sai da yayi sallar asubah sannan ya koma bacci.


Cikin mafarki ya jiyo ihu da hayaniya a firgice ya farka,salati ya fara yi, sannan ya dakata don jin daga ina hayaniyar take, sakkowa yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login