Showing 18001 words to 21000 words out of 111837 words
Chapter 7 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
dole mu tashi tsaye.
"To ai duk laifin ku ne innah, inji Magaji da kun fara yun'kurin yadda xa mu yi mu koma birni da rayuwa, amma kamar Wad'anda aka yi wa d'aurin baki ku ka yi Watsi da abin, Ku ka ma daina xancen fada d'aya"
"Idan d'aurin bakin aka yi abin mamaki ne? Matar nan fa matsafiya ce na dad'e da sanin haka, a haka ne dai xaka ganta kamar mumina, tana rero xance wai ita ta Allah. Ai mun gamu tunda tayi mana haka, mu xuba mu gani.
Hirar da suka yi ta yi kenan har suka isa 'Dan batta.
Suna huci suka fito daga motar, ko sallama basu yi wa Wad'anda suka kawo su ba suka fito.
Cikin gida suka shige ran su yana ta musu xafi saboda abinda suka je nema basu samu ba, kuma bu'katar su bata biya ba. Habi suka tarar tana ta faman surfe, yadda taga yanayin su ta tabbatar da cewa, ha'kar su bata cimma ruwa ba, ga shi kuma ta ga Magaji ri'ke da hannun shi yana d'ingishi, sakin tabaryar ta yi ta 'karaso gurin da suke.
"Ya na ganku haka da wuri, kuma babu alamar Walwala a tattare da Ku?"
"Ta Yaya xaki ganmu da Walwala an mallake min jika ya xama na wata daban, kalli hannun Magaji ki ga aika-aikar da wani shegen yaro yayi masa"
"Xare ido Habi ta fara yi, Idan na yarda da abinda aka yi Wa jikana Allah ya tsine min, yaron nan ya ta6o bala'i da hannunsa, bai san mu ba labarin mu yake ji, shii yasa ya yi karmbanin ta6o mu, ai kuwa ya ta6o masifa.
"Mu shiga d'aki inji innah abin xai fi dad'in tattaunawa, kada wannan munafukin ya shigo ya ji dad'in kai musu labari.
'Daki suka shige gaba d'ayan su, tattauna abinda ya faru suka fara yi, suka cigaba da la'antar Ammin Nauwar.
innah ce ta fito da dubu ashirin d'in da aka basu ta mikawa Habi.
"Wad'annan kudad'en kuma na menene? Habi ta tambaya"
"Su ne wanda aka bamu aka kuma koremu, aka ci mana mutunci.
"Gud'a Habi ta saki, ahayye Nanaye !! Innah da Wad'annan kudad'en xamu ya'ke su, gobe mu tashi da wuri mu shirya, mu tafi gurin Bokan da Audu ya fad'a mana Kwanakin baya, mu je mu xube masa naira yayi mana aiki, ko ya Ku ka ce?
"Haba Habi wannan ai rashin hankali ne, inda muke cikin matsin nan, mu je mu xube wa Boka Wad'annan kudaden gaba d'aya, gaskiya baxai yiwu ba, ki ri'ka yin abu da lissafi mana.
"Tunda baxai yiwu ba a barshi, kowa ya tafi neman 'yancinsa ni xan tafi neman nawa yancin da na jikokina, ke kuma ki xauna a nan, tunda kashe kud'i a nemi magani rashin hankali ne da rashin lissafi".
"A'a uwar Audu ba haka nake nufi ba, yanxu dai ki fad'a mana yadda kike ganin xa a yi."
Maganar da na fad'a da farko ita xa a yi Idan kin amince.
Na amince mana Allah ya kaimu goben.
*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*ALMAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*yau shafin gaba d'aya naku ne masoya Almajirah, nauwar tana godiya da kaunar da kuke nuna mata*
*mariya Balarabe Adam*
*Xahra'u Ado Husain*
*xainab Abbah*
*Nusaibah Abdullahi galadima*
*Ummu Ammar*
*Bilkisu mai Gado*
*Amina saminu (maman Yousuf)*
*Maman Yusra*
*Fatima Ali*
*ina tare da Ku masoyana*
2⃣2⃣
Da sassafe suka yi shiri sai wajen Boka, tsaunuka da daji suka ri'ka ketawa, wani rami suka gangara wanda shi ne, xai kai su har gurin da Bokan yake, wani 'katon mutum suka hango a saman bishiya jikin shi sanye yake da fatar damisa, gashin kanshi kuwa a duddun'kule yake ya sakko masa har 'kasan wuya, wata tsawa ya daka musu sai da suka firgita gaba d'ayansu, me ke tafe da Ku!!! Ya tambaye su??
Bakin su na rawa suka amsa da "wajen mai gani har hanji muka xo"
Nuni yayi musu da su wuce su 'karasa wajen da Bokan yake, suna shiga suka iske shi a tsaye, hannun shi ri'ke yake da wata xabgegiyar takobi, fuskar shi kuwa kamar an shafe ta da ba'kin tukunya, kallo d'aya xaka yi masa ka tabbatar da cewa babu hasken imani a tattare da shi, a tsorace suka 'karasa inda yake, tsugunnawa suka yi da niyyar gaishe shi, dakatar da su yayi da hannu alamar baya bu'katar gaisuwar su, nuni yayi musu su samu guri su xauna.
Xama suka yi sannan ya nemi su fad'a masa abinda yake tafe da su.
Innah ce ta fara magana ran Boka shi dad'e yaro ne da mu, Allah ya axurta shi amma matarsa ta shiga tsakaninmu da shi ta hana shi ya Mora mana komai, yanxu abinda muke bu'kata a d'ora mu a xuciyar sa, ya xamto baya jin maganar kowa sai tamu, sannan muna son a sanya masa tsanar matarsa da ta ya'yansa, sannan a hana shi jin 'kan mahaifinsa, ya xamto baya son su baya 'kaunar ganinsu ko kad'an, bu'kata ta biyu kuma a d'ora wa matar sa warin ja6a.
Gyaran murya yayi, sannan ya bushe da wata irin dariya mai ban tsoro, wannan ita ce kawai bu'katar Ku, ya tambaye su yana mai xare musu jajayen idanunsa, amsa masa suka yi da eh!!.
'kasa ya dan'ko ya xuba a wata fatar damisa ya had'a musu da wata laya, layar yayi umarni da a jefata a cikin kogi, 'kasar kuma su ri'ka jikata suna wanka da ita, xai ji duk duniya babu Wad'anda yake 'kauna Idan ba su ba.
Godiya mai yawa suka yi masa, sannan suka xari dubu goma a cikin kud'in da aka basu suka mi'ka masa.
Suna isa gida suka kira Magaji ya xo ya kai layar da Boka ya ba su kogi, ba tare da 6ata lokaci ba, ya d'auki keke ya tafi, yana kaiwa bakin kogin yayi sa'a babu kowa a wajen don haka ya faki ido ya jefa layar cikin ruwa.
Da farin ciki ya dawo gida ya sanar wa su innah nasarar da ya samu na jefa laya, murna suka ri'ka yi kamar Wad'anda aka yi wa albishir da gidan aljannah, ruwa Habi ta shiga dafawa tana kiran jikokinta da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai suna wanka da ruwan.
Yau jama'a Abban Nauwar ya dawo daga bitar da ya je garin Abuja, ledodi ne ri'ke a hannunshi ya shigo gidan, da gudu yaranshi suka xo suka rungume shi.
"Oyoyo Abbanmu mun yi missing d'inka" murmushi yake ta musu.
"Nima ai nayi kewarku 'yan yarana"
Karbar kayan shi suka yi suka raka shi har d'akinsa, Ammin Nauwar ya tarar tana sallar la'asar, don haka ya tsaya jiranta har ta idar da sallar.
Jin kan shi yayi yana juya masa, jiri ya ji ya debe shi, har yana 'ko'karin fad'uwa don haka ya nemi kujera ya Kwanta a kanta.
Nan da nan idanun shi suka kad'a suka yi jawur, jin shi yake kamar ba a duniya yake rayuwa ba. Sai ya tsinci Kansa baya son jin muryar ko wane bil Adama a kusa da shi, don haka ya rarrafa ya shiga band'aki ya kulle Kansa.
Tana idar da sallar ta tambayi Nauwar inda Abbanta yake, sanar mata tayi da ya je toilet xai watsa ruwa, don haka tafi kitchen ita da Nauwar suka had'o masa kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, a tunanin su suna dawowa xasu tarar da shi ya fito amma sai suka ga sa6anin haka, xauna wa suka yi suka cigaba da jiransa amma bai fito ba har sama da awanni biyu.
Gajiya Ammin Nauwar tayi ta fara 'Kwan'kwasa 'kofar band'akin, tsawa ta ji ya daka mata.
"Bana son sake ganin wani a d'akin nan, kafin na fito kusan inda dare yayi muku, Idan ba haka ba gaba d'ayanku sai ranku ya 6aci.
Mamaki ne ya kama su gaba d'aya, Nauwar ce tayi karfin halin yin magana.
"Me ya faru Abbanmu waye ya 6ata maka rai??
"Ban sani ba, Ku fita nace Ku bar min d'aki wlh Idan na fito na sameku sai na sa6a muku.
Hawaye ne suke sauka a fuskar Nauwar ita kuwa Amminta gaba d'aya ma ta kasa aikata komai saboda abin ya gama d'aure mata kai, tunda take da Mahmud bata ta6a ganin fushinsa ba, amma yau gaba d'aya ya burkice musu ko 'yar tasa ma da ya fi so baya son ganinta.
Rarrashin Nauwar take yi sannan ta lalla6ata suka fita daga d'akin.
*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
Maijiddatijjaniadam@gmail.com
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*DUK A INDA NAKE KO NA KASANCE KUNA RAINA MASOYANA INA SONKU INA GODIYA DA 'KAUNARKU GARENI, ALLAH YA BAR XUMUNCI*
Ameenah Nasir
Zainab Muhammad
Hafsee Maman Humaira
Asma'u Abubakar Lolo
Meena luv
Haleemah MK
Hindatu A'kilu Sabo
Aysha Muhammad
Hauwa Tijjani
*Muna mugun tare*🤝
*WANNAN SHAFIN GABA 'DAYA NAKI NE 'YAR UWA RABIN JIKINA*
*SALEEMAH SAMMANI BABA, INA YINKI INA 'KAUNARKI'YAR UWATA, ANA TARE*💯🤝
2⃣3⃣
Falo suka dawo gaba d'ayan su suka xauna, sun yi jugum-jugum dasu, saboda jimamin canjin da suka samu daga Abbansu, wayar da ke gefen su ce tayi 'kara, gaba d'aya suka mayar da kallon su gareta, wadda ita ce ta katse musu shirun da suka yi, Hamdan ne ya kira bayan sun gaisa ya sanar musu da xuwan maminsa, farin ciki ne ya bayyana a fuskar Ammin Nauwar, tayi murna da xiyarar da xata kawo mata, saboda sun jima basu had'u ba, kasancewar Baban Hamdan mutum ne mai kulle, addu'a tayi musu Allah ya kawo su lafiya, sannan ta ajiye wayar.
Kitchen ta shiga ita da Nauwar suka had'a musu delicious, sannan suka Jere musu a kan dining.
Sashin Abbanta Nauwar ta shiga, samun shi tayi xaune kan kujera ya had'a kai da gwiwa, sallamar da tayi ne yasa ya d'ago kanshi yana ganin ita ce ya mai da kanshi 'kasa, d'aga mata hannu ya yi ya dakatar da ita.
"Kada ki fara 'karaso min nan, fad'i duk abinda kuke bu'kata na sallame ki, warin ki ya cika wajen nan gaba d'aya, ki fad'i ko menene ki 6ace min da gani.
Hawaye ne suka fara sauka a fuskar ta, ba abinda nake bu'kata a gurinka Abbana sama da dawowar farin cikin ka da Walwalarka tare da mu, ka daina kula mu ka daina son ganinmu, me muka yi maka Abbanmu??mu nemi gafara ka yafe mana, kai kad'ai ne rayuwar mu wanda muke kallo a kowane lokaci mu yi farin ciki, mu da Ammin mu, me yasa ka canja mana lokaci daya Abbana???
Kuka mai tsanani ne ya kufce mata
Ya tausayawa 'yar tasa, musamman da yaji Wad'annan maganganun daga gareta, gaskiya Nauwar yarinya ce mai hankali yanxu har ta fahimci halin da nake ciki na 'kunci da rashin son ganin su.
Ganin mahaifin nata ya shiga tunani ya kuma kasa bata amsa, sai ta 'kara rushewa da kuka, 'karasawa kusa da shi ta yi, ta ri'ke 'kafar shi tana cigaba da ro'kon shi ya yafe musu.
Hawaye ne ya ri'ka sauka a kuncin sa, tallafo fuskarta yayi da hannunsa, yana kallonta yana'kara xubar da hawaye, ji yake gaba d'aya ya tsani kan sa, ya tsani rayuwar duniyar ma gaba d'aya.
Magana ya fara yi mata bakin shi yana rawa
"Wlh ina sonku 'yata, ban San me yasa na Wayi gari a cikin tsanarku ba, xuciyata tafasa take yi idan na d'ago ido na kalleku, xamana ni kad'ai ba tare da xama tare da Ku ba, shi ne Kwanciyar Hankalina, Ku gafarta min Ku cigaba da hakuri da ni a duk yadda ku ka sameni, ni dan Adam ne, Ku ri:ka yi min uxuri, kuma Ku tayani addu'a Allah yaye min abinda yake damuna.
"Mun yafe maka Abban mu, kuma baka yi mana komai ba, ka kula da mu ka so mu, kuma insha Allah xamu cigaba da addu'ar Allah ya yaye maka matsalolin ka.
Kuka suka ri'ka yi gaba d'ayan su babu mai iya rarrashin wani a cikinsu.
Tausayin mahaifinta ne ya kamata,nan da nan ta ji xaxxabi ya rufeta don haka ta tashi ta koma wajen mahaifiyarta.
Tana shiga ta sameta xaune kan sallaya tana addu'o'i,ganin yadda yanayin 'yar tata ya canja, ga fuskarta tayi jawur alamun tasha kuka ta koshi, shi yasa ta mi'ke ta tare ta hnkalinta a tashe take tambayarta abinda ya faru da ita.
"Hawaye ta shiga sharewa ta xayyane mata yadda suka yi da mahaifinta, ita ma dai ha'kuri ta bata ta kuma rarrasheta a kan su cigaba da addua komai mai wucewa ne.
Tsayawur mota suka ji, don haka suka fito gaba dayan su waje saboda sun San ba'kinsu ne suka samu iso wa, 'karasawa suka yi garesu rungume juna suka yi suna farin ciki, d'unguma suka yi gaba d'aya suka shiga ciki. Kayan abinci aka halarto musu da shi suna ci suna hirar yaushe gamo.
Ita kuwa Nauwar na gefe tun daga gaisuwa bata sake cewa da kowa komai ba, kallo d'aya xaka yi mata kasan tana cikin damuwa, magana Amminta tayi mata.
"Kira Abbanki kice masa mamin su Hamdan taxo xa su gaisa.
Kamar Wacce Kwai ya fashewa a ciki haka ta tashi ta tafi kiran shi, tarar da 'kofar dakin shi tayi a rufe don haka ta dawo ta sanar da Amminta.
Tashi Ammin tayi da kanta ta je ta samu 'kofar tashi a kulle, kamar yadda ta fad'a mata, Kwan Kwas 'kofar ta ri'ka yi, amma ya yi banxa da ita, ta fi Minti 30 tana bugu bai bud'e ba, sai da ya gaji da bugun da take yi ya taso a fusace ya fara masifa.
"Me kike so ne a tare da ni,da kike bibiyata haka?, kin turo 'yarki d'axu duk bai isa ba sai kin xo da kan ki. yanxu kuma me kike son nayi miki, wlh idan har ku ka takura min xan yi yaji na bar muku gidan gaba d'aya, kun dameni, ke warin ja6a 'yarki ma abinda take yi kenan. kada Ku 'kara xuwa inda nake ko da wasa, Idan kuma ku ka sake yi, xan nuna muku 6acin raina, kin ji na fad'a miki.
Mayar da 'kofar d'akin ya yi ya kulle ya barta da ciwon xuciya.
Hawaye ne cike da idanunta,don haka ta kasa fadawa ba'kin dalilin rashin xuwan sa su gaisa, ganin yadda ta canja lokaci d'aya daga farin ciki xuwa akasinsa ne, yasa suka tambayeta abinda yake damunta, amma sai ta'ki fad'a musu tace ba komai, don haka suka 'kyaleta suka bud'e wani babin hirar.
*jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆 🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
Maijiddatijjania dam@gmail.com
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*sadaukarwa gare Ku 'yan uwa na amana ina godiya da gudunmawar ku gareni*
*MAIJIDDA BELLO*
*UMMU EL-NAJEEB GYARA KANKI*
*FEENAH YAHYA (feenah berry)*
*RAHMATULLAH MAMAN UMMY*
*JUMANA AHMAD*
*JAWAHEER SALEEM*
*ASLAMIYYA ISLAM*
*MAMAN IKRAM*
*INA YIN KU KUMA MUNA TARE HAR ABADA*
*gaisuwa ta musamman gare ki Takwarata kuma aminiyata*
*MAIJIDDA SALEH*
2⃣4⃣
Haka suka cigaba da kasancewa a cikin gidan yau da dad'i gobe ba dad'i, ba wani kyautatawa tsakanin su da shi, sai tsangwama da cin xarafi ne kullum ke biyo baya, yanxu ta kai ta kawo ko hidimar makaranta ya daina yi wa yaran sa, komai sai dai Ammin su tayi musu, gaba d'aya ya burkice ya xama wani irin mutum Mara dad'in kai.
Safiyar ranar asabar ya sanarwa da Ammin Nauwar xai je 'Dan batta, addu'a tayi masa sannan ta bashi kud'i da shadda ta bayar a kai wa Baffa, ita ma Nauwar turare ta d'akko ta bashi ya bai wa kakanta, saboda ta sha'ku da Baffa suna son shi, a ko da yaushe ba su da burin da ya wuce su je su gaishe shi, amma basa samun goyan baya daga Abbansu.
Mota ya d'auka ya fice sai 'Dan batta, tarar da gidan yayi ba kowa, don haka ya xauna don ya jira su, bai dad'e da xuwa ba, ya ji sallamar Baffansa, don haka ya mi'ke da sauri ya isa inda yake, fuskarsa a sake ya gaishe shi.
"Ina Kwana Baffa
"Lafiya lau ya iyalin naka"
"Suna lafiya, gurin xama ya ba shi suka karasa gaisa wa.
ga wannan kayan da kud'i, tace na baka ga kuma turare Nauwar ce ta baka.
"Lallai amaryar tawa tana yi da ni, yaushe xaka kawo min su na gansu ne, na dad'e fa rabona da yaran nan.
"Xa su xo insha Allah Baffa makaranta ce take tsare su, shi yasa basa samun damar kawo maka xiyara a Kai a Kai amma suna nan xasu xo insha Allah.
To Allah ya kawo Ku lafiya, ai yana da kyau a mai da hankali wajen karatun yaran, Allah yayi jagora. Amsawa yayi da Ameen.
Godiya mai yawa Baffa yayi masa, sannan suka fara tattaunawa a kan dad'ewar da yake yi bai kawo masa xiyara ba.
"Wlh matsalar gurin aiki ne Baffa amma ai kana raina insha Allah xaka ri'ka ganina"
"To Allah ya taimaka, ameen yace sannan suka cigaba da hira, yana bashi labarin girman da su Nauwar suka yi, yana ta farin cikin yadda iyalan d'an nasa suke cikin Walwala da Kwanciyar hankali.
Inna karime suka hango, ta dawo daga unguwar da ta tafi, tun daga nesa ta gano Abban Nauwar, sai bud'e masa baki take yi, Baffa yayi mamakin ganin hakan daga gareta saboda yasan a da ko 'kaunar ganinshi ba ta yi, don haka ya saki baki yana ganin ikon Allah.
"Yau muna da manyan ba'ki a gidan namu kenan, barka da xuwa Alhaji Mudi, ya Kwana biyu, ka ya da mu gaba d'aya, d'an le'kowar da kake yi a gaisa duk ka daina.
Ita ma dai uxurin aiki ya bata, sannan ta tashi ta shiga d'aki ta kawo masa fura, kafin ta kawo masa sai da ta 'kara barbad'a garin maganin da suka je wajen wani Boka ya basu.
"Ga wannan Alhaji Mudi, ka sha hanya kuma nasan baka sa komai a bakin ka ba. ai kuwa dai innah, kamar kin San ina jin yunwa ji nake yi kamar an min sata a cikina.
Hannu biyu yasa ya kar6i furar, ya fara sha, Baffansa bai so ya sha furar