Showing 6001 words to 9000 words out of 111837 words

Chapter 3 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

tayi da ameen, haka suka xauna suka rika hira har xuwa yamma sannan 'yan uwanta suka xo tafiya da su AL-MAJIRA. d'aki a ka basu a soran gidan, an gyara musu shi, an sa musu labule da ledar tsakar daki, shigar da su dakin aka yi, suna xama aka kawo musu abinci da kaya, nan da nan su AL-MAJIRA suka canja kaya suka ci abinci sannan tayi sallah.


"saimah ce ta shigo tare da momynta da Abbanta, sallama suka yi, fuskarta a sake ta amsa musu, gurin xama suka samu suka xauna, cikin ladabi ta gaishe su.


"Abba ne ya fara magana, muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar da kulawarku ta dawo hannunmu. muna fatan xaki kwantar da hankalinki ki d'auke mu tamkar iyayenki, duk abinda kike so ki tambaye mu, indai muna da hali xa mu yi miki, sannan nasa a sauke al-kur'ani a yi wa mahaifiyarki addua a kan Allah ya bata lafiya. risinawa tayi tana masa godiya.


"ba komai ki daina godiya ai d'a na kowa ne, bawa sai mai shi. mu dai fatanmu ku samu farin ciki ta sanadiyyarmu. tashi suka yi xasu fita tayi musu sallama sai da safe, har sun kai bakin kofa suka dawo "Au!!! mun manta bamu tambayi sunanki ba.




"sunana NAUWAR tayi maganar kanta a sunkuye" Masha Allah sunanki mai dadi da asali, daga yau mun daina kiranki da AL-MAJIRA tun dai mun ji sunanki, sallama suka yi da ita suka koma cikin gida, ita kuma ta koma ta xauna, mintuna kadan bacci ya dauketa.


A haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, ta xama tamkar yar gida, har makarantar islamiyya aka sanyata. ga shi yanxu Ammi na samun kulawa sosai saboda kullum suna tare da ita, a yanxu dai ba su da matsalar abinci da wajen kwana, ga shi sun samu kayan sa wa da yawa, Alhamdulillah Ala na'amihi.




*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRAH*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJJANI*

*ADAM* *(jeeddahtul-khaeer)*


*β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*Duk inda nake, a duk inda a kasance kuna raina, bana manta karamcinku da kaunarku gareni, Bilkisu Mmn Irfan (mai gado)$ Mamah Aleeyou kd ana tare*πŸ’―πŸ€




*wannan shafin gaba d'aya naki ne ZAINAB ABUBAKAR( YAR FILLO) ina yinki 😍😘*


1⃣2⃣




*H*aka Al-ajira ta cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali, sai dai fargabar ta d'aya ciwon Amminta, ko yaushe zata dawo kamar da? Kullum ta tuna yadda rayuwarsu take a baya, sai ta zubar da hawayen takaici, duk da karancin shekarunta, amma yarinya ce mai kaifin hankali da tunani
*ASALIN LABARIN*
Nauwar Mahmoud shine asalin sunan Almajirah, suna zaune ne a garin Kano a unguwar Nassarawa G.R.A(Dawaki Road).
Mahaifinta Mahmoud Abdullahi d'an asalin garin Danbatta ne dake garin Kano, wanda ya kasance shi d'aya tilo a wajen mahaifiyarsa, inda abokiyar zamanta Habi take da yaya hudu (4)Isa,Nasiru,Abdurrahman, sai kuma y'ar autarsu Dije. Kasancewar Mahmoud d'a d'aya tilo a wajen mahaifiyar sa
wannan yasa mahaifiyar Mahmoud take fuskantar matsalar gori da habaice-habaice a wajen uwar mijinta karime, da abokiyar zamanta. kasancewar tunda aka yi aurenta da malam Abdullahi bata haihu ba, sai da ta d'auki shekaru masu yawa,wannan yasa Inna karime tasa malamAbdullahi ya auri 'yar Aminiyarta Habi. tunda Habi tazo cikin gidan, Mahaifiyar Mahmoud ta kuma shiga cikin wani mawuyacin hali, har sai da ta kai ta kawo bata da kwana,mahaifiyar malam Abdullahi ta hana shi xuwa shimfidarta, saboda ba zai yiwu yaje ya kare karfinsa a kan juya ba, ita kuwa Aisha baiwar Allah bata nuna bacin ranta ba sai dai addu,a da take yawan yi kasancewarta mace mai tawakkali, tasan dukkan tsanani yana tare da sauki.


haka rayuwarsu ta cigaba da gudana, kwanaki na shudewa su zama sati daga nan su zama watanni. Aisha ta d'auki tsayin watanni bakwai ba tare da mijinta ya kalli ko da 'kofar d'akinta ba ballantana ta sami damar Le'kawa turakarsa, ana cikin wannan yanayin ne Habi ta sami juna biyu, murna kuwa a gidan ba a magana,Inna karime kuwa cewa tayi daga wannan ranar, Habi ta daina wanke-wanke,shara da girki, sai dai Aisha ta ringa yinsu, ba yadda malam Abdullahi ya iya, dole haka yasa ido Aisha taci gaba da wadannan ayyuka.






Wata rana Inna karime sun tafi unguwa, ita da Habi malam da ya dai-daici sun tafi, ya dawo gida jikinsa a sanyaye hawaye yake zubarwa, yana rarrashin Aisha yana bata hakurin zalincin da ake yi mata, share masa hawayen ta fara yi, tana fad'in malam ka kwantar da hankalin ka, ni ban ri'keka da komai ba, nasan ba laifin ka bane, kuma ko Inna da Habi ban rikesu ba na yafe musu duk abinda suka min, rungumeta yayi yana shafa kanta, albarka ya saka mata daga nan suka farantawa juna rai.




Haka rayuwarsu taci gaba da kasancewa, sai bayan da Habi ta haifi d'anta na biyu sannan Aisha ta haifi danta Mahmoud,haka rayuwarsu taci gaba da innarsa yau za'ki gobe mad'aci, ana cikin wannan halin ne, innar Mahmoud ta kamu da zazzafan zazzabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta Mahmoud yana da shekaru takwas a duniya, tun daga wannan lokacin Mahmoud ya koma rayuwar kad'aici da maraici, shi d'aya yake kwana a d'akin innarsa, abinci ma sai Habi taga dama take bashi. wata rana yakan kai kwana biyu ba tare da yasa komai a bakinsa ba, Sai dai Idan malam ya faki idonsu Inna karime da dare ya bashi abinda Allah ya hore masa.






A wannan lokacin baffansa yace masa Mahmoud ina son na kai ka birni kayi karatun allo a can, saboda takura ka da a keyi a cikin gidan nan yayi yawa, gara Kaje can kayi karatunka, abinda Allah ya hore min zan ringa kawo maka. sannan ina yi maka wasiyya da kaji tsoron Allah a duk inda Kake, ka zama mutum mai amana, ka sani duk tsanani yana tare da sauki, kasa a ranka komai mai shigewa ne kaji d'ana


shashshekar kuka baffansa ya fara yi,wanda yasa jikin Mahmoud ya 'kara sanyi Wanda dama tunda mahaifinsa ya fara jawabi yake zubar da hawaye,d'agowa yayi yana sharewa mahaifin nasa hawayen, Baffana kayi hakuri insha Allah zaka yi alfahari dani,na kasancewa ta danka, ka sani a duk inda nake ba zanyi watsi da tarbiyyar da kayi mini ba, rungume shi baffansa ya kara yi, yana yi masa addu,oi na fatan alkhairi,sannan suka nufi gida.




*WASHE GARI*




*M*isalin karfe 10:00 na safe suka iso cikin garin Kano ta Dabo, inda Mahmoud ya ji kansa na juya masa,kasancewar bai saba ganin cinkoso da yawan ababan hawa ba irin wannan take Mahmoud ya .................








A yi Hakuri da wannan yau ina busy a yi min afuwaπŸ‘πŸ»


*jeeddahtulkhir😘*
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


*EXCLUSIVE WRITES FORUM*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†


*wannan shafin gaba d'ayanshi sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin Almajirah, ina kaunarku kamar yadda kuke 'kaunata, Allah ya barmu tare, ana tare*πŸ’―πŸ€




*ina mika gaisuwar ban girma gareki big admin ummiey xee Abakson, ina godiya da kaunarki garen, da dukkan 'yan uwa na exclusive writer's Allah ya 'kara hada kanmu*πŸ‘πŸ»






1⃣3⃣


Fashewa mahmoud yayi da kuka, "Baffana mu koma gida, bana son xama a irin wannan garin, an ce mutum d'an iska yake komawa, yana yin maganar yana share hawaye da majina. dariya Baffa yayi, lallai mahmoud da abin dariya kake, wanene ya fad'a maka wannan ruwayar? haka mutanen 'kauyenmu suke fada Baffa. to ba haka bane mahmoudu na duk wanda kaga ya lalace shi yasa kansa, ni dai fatana ka kiyaye Allah, kaji tsoransa a duk inda ka kasance, kuma kada ka tara bautar Allah da waninsa, kuma banda abinka ma ai wannan birni ne na albarka, burina a yanxu bai wuce kayi karatu ba ka share min hawayena, kasancewarku d'a na gari shi xai sa nayi alfahari da kai.


'karasowa bakin hanya suka yi, ya siya masa robar Abinci da kwaki da sugar, basu yi wata tafiya mai nisa ba suka isa makarantar malam Audu da ke unguwar 'kofar wambai, inda a nan ne mahmoud xai yi karatu. da sallama suka shiga xauren da malam Audu yake karatu tare da almajiransa, yana ganin Baffan mahmoud ya mi'ke ya tarbeshi da farin ciki, hannu ya mi'ka masa dan yin musafaha, shi ma mi'ka masa yayi suka gaisa, cikin ladabi mahmoud ya tsugunnah har 'kasa ya gaishe shi, amsawa yayi fuskarsa a sake, da kuma farin cikin ganin d'an nasa, kasancewar malam Audu aminin Baffan mahmoud ne tare suka tashi tun suna kanana. bayan doguwar gaisuwar da suka yi, malam Audu yasa aka kawo musu Abinci da ruwa, bayan sun nutsu ne mahaifin mahmoud ya fara magana.


"malam dama wata bu'kata naxo maka da ita, ina son mahmoud ya xauna a wajenka, ya xama d'aya daga cikin almajiranka, dan gaskiya ina son ya samu haddar al-'kur'ani, ya kuma xama masani a bangaren littafan addinin musulunci, ina fatan xaka kar6i wannan bukatar tawa. shiru malam Audu yayi na d'an lokaci, "ba matsala malam Abdullahi ai mahmouda d'ana ne, ko ba ranka ni mai iya kulawa da shi ne, insha Allahu xan ri'ke maka amana, baxan wulakanta Alkawarin da nayi maka ba. godiya mai yawa malam Abdullahi yayi masa, sannan ya 'kara gargadin mahmoud a kan ya xama jakada na gari ga iyayensa. lokacin da malam Abdullahi xai tafi hankalin mahmoud ya tashi kwarai da gaske, kuka mai tsanani ya fara yi, nan da nan mahaifinshi ya fara lalla6ashi akan yayi hakuri, xamanshi a nan shi ne jin dadinsa da walwalarsa. sallama suka yi da malam Audu tare da yi masa godiya mai yawa, ya fito dan hawa motar garin 'Dan batta.


Tun a mota malam Abdullahi yake ta share kwallar rashin d'ansa mai biyayya a gareshi, ya rasa me yake masa dadi a rayuwar duniya, amma ba yanda ya iya, dole ya kaishi karatun saboda ya samu sassaucin tsanar da Habi da Inna karime ke yi masa, ransa babu walwala ya shiga gida, yana sallama ya iske inna karime a tsakar gida tana jiran ya dawo ta sauke masa kwandon bala'i, fad'a ta fara yi masa, ina kaje tun safe nake ta jiranka, kaxo ka bani kud'in mota xamu je hayi ni da jikokina, amma har dare baka dawo ba, yi min bayanin ina kaje ka shanyani haka? tsugunnawa yayi har 'kasa yana bata hakuri, sai a lokacin yake sanar da ita cewa ya kai mahmoud makaranta ne a birni dan yayi karatu, nan fa tayi tsalle ta dire, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, dole a dawo dashi gida ya cigaba da rainon 'ya'yan Habi da yi musu wanki. hakuri ya shiga bata a kan ta dubi Allah ta duba maraicin da yaron yake ciki da irin matsalolin da yake fuskanta a cikin gidan ta kyaleshi yayi karatun shi a can, kasa fahimtarshi tayi ta cigaba da fadanta, ta kuma qudiri aniyar cewa, indai bai bi maganar da ta fad'a masa ba, sai ta tsine masa ya bi duniya. Hawayen takaici yake sharewa yana neman gafararta, d'akin habi ya shiga ko xai samu xuciyarsa ta sarara daga rad'adin da take masa, nan ma dai bala'in ya kara tararwa don har ya dame wanda inna karime tayi masa, a ranar dai kwanan ba'kin ciki yayi,dan ko rintsawa bai yi ba saboda takaici.


gari na wayewa ya fito ya shiga d'akin inna karime don ya gaisheta, habi ya gani da y'ay'anta suna magana, ana ganinshi aka yi shiru, da dukkan alamu dai xancen mahmoud ake yi, har 'kasa ya tsugunnah ya gaisheta, cikin fara'a da walwala ta amsa masa, yayi mamakin ganin hakan daga gareta, tunda ya san fushi take yi da shi.


"magana ta fara yi, Audu ka kai mahmoud birni ko? hmm ai nasan xa a rina wai an saci xanin mahaukaciya, tunda ka auro 'yar iska (uwar mahmoud)jinin 'yan iska, nasan dole sai ta haifi kamarta, dole malam idi ya samu magaji, dan haka a da, ina takaicin kai mudi birni, amma yanxu xuciyata fes-fes take, a barshi ya xauna a can ya xama tantirin d'an iska kaga ba nida asara, tunda ga nawa jikokin nan ina ganinsu ina jin dadi. maganganun innah sun yi wa malam Abdullahi ciwo amma ba shi da yadda xai yi ya rama, sai dai ha'kuri kawai, kansa a sunkuye yake magana "inna makarantar Muhammadiyya fa na kai mahmoud ba wani waje ne mara kyau ba" rufe min baki nan shashan banxa da wofi, yara nawa aka kai makarantar Muhammadiyyar suka lalace? ni dai ina nan ina addua Allah ya cika min burina na lalacewar d'an nan, she'kewa suka yi da dariya ita da habi har da tafawa kamar wasu 'kawayen juna. jikinshi a sanyaye ya fita ya bar d'akin, xuciyarsa kuwa kamar ta fad'o 'kasa don takaici.




*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*AL-MAJIRA*
πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*Wannan shafin gaba d'ayanshi saudaukarwa ne a gareki, RUKAYYA HASSAN OTHMAN marubuciyar IBTEESAM Allahu ya 'kara basira da d'aukaka, jeeddah ta gaisheki kyauta*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Gaisuwa ta musamman gareku manyan yayyena, ina godiya da kulawarku gareni Muhammad Ghali &Aunty Zahra, Allah ya 'kara muku soyayya da kaunar juna, Auntyna kuma Allah ya saukeki lapiyaπŸ™ˆ*






1⃣4⃣


*H*aka mahmoud ya cigaba da rayuwa a gidan malam Audu, inda matarsa Rahmatu ke bashi kulawa kamar d'an da ta haifa a cikinta, saboda mahmoud yaro ne mai nutsuwa da biyayya, duk wani aikace-aikace na gida yana taimaka mata dashi, hakan yasa ya 'kara shiga ran dukkan wani mai rayuwa a cikin gidan, ga shi kuma yana dagewa wajen karatu, wannan dalilin, yasa malam Audu ya fara tunanin saka shi a makarantar boko, saboda yana ganin yaron xai yi 'kwaxo da kaifin basira. wata rana bayan sallar isha'i malam Audu ya shigo gida, ya samu Rahmatu tana tu'ka tuwon dare, xaunawa yayi a gefenta bayan ya mata sannu da aiki, sannan ya fara magana.




Hajiya Rahmatu ni fa ina wani tunani a kan yaron nan, tambayarsa tayi tare da ajiye aikin da take yim tunanin me kake yi haka malam? gyaran murya yayi, am dama ina so ne na kai yaron nan mahmoud makarantar boko, saboda naga yaron yana da haxaqa sosai, amma akwai wani hanxari ba gudu ba, kin san sha'anin mutanenmu na karkara kada na kai shi, mahaifinsa yaga kamar xan lalata masa d'ansa ne, tunda kinga duk sauran 'yan uwansa ba karatun suke yi ba.




Haka ne malam, amma ni a ganina hakan ba komai bane, kasan halin malam Abdullahi, mutum ne mai fahimta,na tabbar da cewa ba zai maka mummunar fassara ba, kuma ya riga yasan da cewa rayuwar nan baxa ta tafi dai-dai ba, har sai mutum ya had'a da ilimin addini da na zamani, amma abinda xa a yi yanxu, ka kira mahmoud ka tambayeshi idan yana so sai a kai shi, sannan kuma ka nemi malam d'in ka shawarceshi, abinda kuka yanke shikenan sai a xartar ko ba haka ba? eh gaskiya ne Rahmatu insha Allah xan yi yadda kika ce, to madallah malam Allah yayi mana jagora, amsawa ya yi da Ameen.




Mahmoud ne ya shigo da sallama, cikin ladabi ya 'karaso inda suke, har 'kasa ya tsugunnah ya gaishesu,fuskarsu a sake suka amsa masa, har ya mi'ke malam ya kira sunanshi, Mahmoud ina da wata magana mai muhimmanci da kai, sake sunkuyar da kanshi yayi cike da ladabi ya amsa da To malam. dama na yanke shawarar xan sanyaka makarantar ilimin xamani ne, tunda dai kaga yanxu kayi nisa a karatunka, shi yasa naga ya dace a ce kasan ilimin boko sbd ilimi abu ne mai muhimmanci, amma yanxu ya kake gani?




farin ciki ne ya bayyana a fuskar Mahmoud, domin ya dad'e yana sha'awar karatun boko, kasancewar abokansa da yawa suna yi, amma ina karime ta hana a saka su, saboda tace jikokinta baxa su xama bayin bature ba, amsawa yayi da ina so malam, nayi farin ciki Allah ya saka da alkhairi, amma kafin na fara ka tambayi Baffana ko xai barni. murmushi malam Audu yayi, ka kwantar da hankalinka Mahmoud Baffanka ba shi da matsala, xai yarda insha Allahu. godiya Mahmoud yayi, sannan matar malam ta bashi Abincinsa ya shiga d'aki don ya ci.




malam Audu bai samu wata matsala da malam Abdullahi ba, sai ma dai adduar fatan alkhairi da samun nasara da ya yi wa d'an nasa.


*BAYAN SHEKARA SHIDA*


Bayan shekara shida, Mahmoud ya samu nasarar kammala makarantar primary, inda malam Audu ya umarce shi da ya je ganin gida, kasancewar tunda aka kawo shi wajensa bai je ba, kuma wani bai xo daga gidansu ba, a ranar da malam ya fad'a masa maganar xuwa gida, kwana yayi bai yi bacci ba, saboda xuciyarsa cike take da kewar su isah, don haka da asubah ya shirya jaka sai d'oki yake xai je dan batta, da misalin karfe 9:00 na safe, malam ya kai shi tasha ya biya kud'in mota,ya umarci driver ya kai shi har 'kofar gidansu, duk da farin cikin da Mahmoud yake yi na ganin gida, amma sai da yayi 'kwallar rabuwa da malam, sbd riqon mahaifi yake masa, bai ta6a neman wani abu ya hanashi ba, sai dai idan bashi da halin bashi.




Ana sauke shi a mota, yaran unguwarsu suka taho da gudu suka rungume shi, suna farin cikin ganin abokinsu, wanda suka yi kewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login