Showing 39001 words to 42000 words out of 111837 words

Chapter 14 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

tabbatar maka da ba guba yasha ya mutu ba,me yasa xaka rika irin wannan a matsayinka na babban mutum. sannan mun ji labarin cewa tunda yaron nan ya rasu, ba a sake gani ko jin labarin mahaifiyarsa ba amma baka neme ta ba, ka sani iyalinka amana ne a gareka, kuma sai an tambayeka a kan amanar da aka baka, shin ka kula da ita ko kuma kayi watsi da ita, ya kamata kasan abinda kake yi, kuma mu yanxu mun yanke shawara ko ka yarda ko baka yarda ba, xamu tafi gaba dayanmu tare da likitoci a karbo yarinyar nan sbd kowa yasan babu hannunta a ciki.


shiru yayi ya kasa magana, sai dai hawaye da yake sharewa kawai, da dukkan alamu yana jin xafin abinda yake yiwa iyalin nasa.


Dakata!!! malamai munafukai.


gaba daya daga idanunsu sama suka yi suna ganin ikon Allah, innah karime ce tasha dammara tana xare idanu tana nuna su da dan yatsa.
ina labe ina jin duk abinda ku ke kullawa, to babu munafukin da ya haifarwa mudi yarsa a cikin ku, don haka shi yake da ikon yanke duk hukuncin da yaga dama a kanta,me yasa lokacin da ta aikata abin baku xo kun hanata ba, sai yanxu xaku xo da wasu kafafunku kamar an kafawa katako kusa, kuce xa ku yi magana, to wlh baku isa ba, babu wanda ya isa ya hana a daure yarinyar nan ko a dauki hukuncin da ya dace a kanta, munafukan banxa munafukan wofi."


kallonta kawai suka yi babu wanda ya tanka mata, kasancewar duk ta haife su, don haka baxa su iya musu da ita ba, amma kuma maganarta bata sa sun fasa abinda suka yi niyya ba.


Tashi suka yi gaba daya suka fita daga gidan, kai tsaye police station suka wuce.


wajen D.P.O suka shiga suka fada masa duk abinda ya faru, sannan likitoci suka mika masa takardar da take tabbatar da cewa ba guba yasha ba, a daidai lokacin Abban Nauwar din ya shigo inda yace ya janye karar, don haka aka fito da Nauwar




"kallo daya xaka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin mawuyacin hali, duk tayi baki ta rame, tana ganin Abbanta ta rushe da kuka mai ban tausayi, ko kallonta bai yi ba, hakuri mutanen wajen suka shiga bata.


kiyi hakuri Nauwar kowane bawa da irin yadda Allah yake jarrabarsa ki kaddara cewa irin taki jarrabawar kenan, idan kika yi hakuri da sannu xaki cinye"


wadannan nasihohin su suka sanyaya mata ranta ta daina kuka.


mota suka shiga suka taho gida, su kuma mutanen suka wuce guraren harkokinsu.


yau ma tana nufo kofar gidan taji haniniyar doki irin wacce taji kwanaki, amma ta yau tafi ta kullum don yau din a kusa take jinta, tana sauka daga motar ta fara laluben inda sautin yake fitowa, mutum ta hango daure a cikin gidan da ake saka Gen, bude idonta tayi sosai don ganin wanda aka saka a ciki, da gudu ta karasa wajen tana isa ta iske Amminta ce, kuka mai tsanani ta saki ta fada kan kejin sumammiya.






*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*

*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




*wannan shafin gaba daya naki ne LAILA SANI MUH'D (maman teemah) Thnx 4 d love and support*




4⃣2⃣


Mai gadi ne yaji faduwarta ya taho da sauri, tarar da ita yayi ta suma don haka yayi hanxarin lekawa cikin gida ya kira su innah karime ya fada musu abinda ya faru, amma gaba daya suka balbale shi da masifa, suka yi masa korar kare


ruwa ya samo ya yayayfa mata, cikin ikon Allah aka samu ta farfado, a hankali ta fara bude idanunta tana salati, hakuri ya shiga bata yana rarrashinta


"kiyi hakuri Allah yana sane da halin da kuke ciki, addu'a ita ta kamace ki ba kuka ba"


jinta take gaba daya bata cikin hankalinka, a hankali ta karfafa jikinta ta mike, xaunawa tayi don jiri ne ke dibarta, nasiha mai gadi ya cigaba da yi mata,har xuciyarta ta warware daga raunin da ta samu kanta a ciki. yanxu jinta take xata iya karawa da duk wanda ya takaleta da fada, ko ya taba mata mutuncin Amminta, don haka ta mike ta dubi gurin da Ammi take a daure.
sunan mai gadin ta kira


"malam Ali ina aka jiye mukullin wajen nan, kuma me yasa ka bari aka saka mahaifiyata a ciki"


cikin ladabi ya amsa mata


"wlh ban sani ba ranki ya dade, su Hajiya ne suka sakata a ciki kuma mukullin yana hannun su"


A fusace ta wace gurinsu innah karime ta same su tare da su magaji ana ta hira




nuna su tayi da hannunta


"abinda ku ke mana ya ishe ku haka, hakuri ba hauka bane, idan tura ta kai bango dan Adam baya jurewa, wane dan iskan ne ya saka min uwa a cikin keji?"


dafe kirji innah karime tayi tana mamakin kalaman da ke fita daga bakin Nauwar, gaba daya ta kasa magana sbd bata taba xaton jin hakan daga gareta ba.


magaji ne ya mike
"wane ne dan iskan a nan, babu wajen da ya dace mahaukaciyar uwarki ta xauna, idan ba xaman turu ba don baxa mu kyaleta a nan, ta bata mana guri da warin kashi ba"


bata san lokacin da ta daga hannu xata kwada masa mari ba, rike hannunta yayi.


"ko wannan mahaukaciyar uwar taki bata isa tace xata mareni ba, ballantana kuma ke, kuma wlh kin yi na farko kuskure ne idan kika sake yin na biyu ganganci ne, sai kinga yadda xan yi dake a cikin gidan nan, banxa shashasha wacce ubanta bai damu da ita ba"


kuka ne ya kwace mata ta fita a fusace ta samu wani katon katako, ta saukewa magaji a kansa, nan da nan ya kamata da kokawa suka rika yi, maigadi ne ya jiyo hayaniya ya shigo ya raba, amma su innah karime cewa suka yi baxa su raba ba, sai ya kasheta su ga abinda xai faru.


idanunta a rufe ta fita, gidansu Hamdan ta nufa, kai tsaye dakinsu ta shige ta tarar da momy xaune akan kujera tana isa wajenta ta fada kanta tana kuka, tambayarta ta rika yi.


"lafiya Nauwar na ganki a haka me ya faru da ke kike kuka, kiyi hakuri ki fada min matsalar ki"


ta kasa fada mata komai sai hawaye gami da ajiyar xuciya da take yi


"ki fada min Nauwar dan Allah hankalina ya tashi sosai"


cikin kuka take fada mata halin da Amminta take ciki da abinda su innah karime suka yi mata, mayafinta ta dauka suka tafi gidan tare, suna isa ta tarar da Ammi a wannan hali, hawaye ne suka rika xubo mata.


"Rehab yanxu kece kika xama haka, kece a wannan halin, gaskiya mahmud yaci amana, bai rike amanar da ya karbo a wajen mahaifanki ba, ya raboki da danginki ya kawo ki wajen da baki da kowa,kuma baki san kowa ba, gaskiya duniya abin tsoro ce"


kiran mai gadi tayi tasa ya balle wajen, tunda su innah karime sun hana mukullin, ana budewa tayo kansu da gudu xata dake su,da kyar maigadi yayi ta maxa ya riketa aka shigar da ita daki, gaba dayansu kuka suke babu mai iya rarrashin wani, sbd tausayin Ammi da suke ji.


Toilet suka shigar da ita suka canja mata kaya masu kyau, kasancewar tafi sati guda rabonta da taga ruwan wanka, bayan sun dawo da ita daki suka dafa mata abinci mamin hamdan ce take bata,amma da sun bata sai ta furxo da shi ta rika wani ihu kamar na kukan jaki, a haka ta cigaba da bata har ta koshi.


mamin Hamdan bata bar gidan ba har sai bayan sallar isha'i


Bayan tafiyarta ne Abban Nauwar ya dawo, tana jin karar motarsa ta fito da saurin don ta tarbe shi, amma yana ganinta ya nuna kamar bai ganta ba ya shige bangarensa.


bai fi minti biyu da shigowa ba, innah karime ta shiga ta same shi ta xayyana masa abinda ya faru ta hada masa da abinda ya faru da wanda bai faru ba shi kuma ya hau kai ya xauna.


A fusace ya fito, yana kiran sunan Nauwar


"Nauwar!! Nauwar!! kina ina ne??


jikinta na rawa ta fito don tasan ba alkhairi ne yasa shi kiran sunanta ba.


har kasa ta tsugunna, idanunta na kasa tayi masa magana.
"gani Abbah"


nunata yayi da hannu
"kada ki kuskura ki kara kirana da Abbanki ni ba ubanki bane, ni ban haifi wacce xata kashe dan uwanta ba, ban haifi wacce xata ce xata kashe dan uwana ba, daga yau sai yau idan kika kara ikrarin xaki kashe magaji wlh sai na daure ki, sai kin kare rayuwar ki a gidan yari, kuma yanxu yanxu ina son ki tattara kayanki ki fita daga gidan nan, bana son kara ganinku daga ke har mahaukaciyar uwarki"




gaba daya ta nemi hawaye a idonta ta rasa, wani daci ne yake taso mata tun daga kasan xuciyar ta, xata bude baki tayi masa magana ya dakatar da ita.












*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne ga members na Al-majira fans 1 $ 2 Ina godiya da yadda kuke nuna kulawar ku da kaunar ku ga wannan littafi na gode Allah ya bar xumunci*






4⃣3⃣




Haka ta tashi jikinta a sanyaye ta wuce daki, a hanyar shigarta dakin taci Karo da Habi, bushe mata da dariya tayi Sannan ta dube ta
" ba dai ke Mara kunya ba, Kadan kika gani kuma barin gida ya xama dole, sai dai idan rashin xuciya ne xai xaunar da ku"


Hawaye masu Xafi ne suka rika kwarara a kan fuskarta, Kai tsaye ta shige daki ta fada kan gado ta fara kuka mai cike da ban tausayi, ta rasa wanda xata ra6a taji dadi ballantana har ta samu damar tattauna matsalarta dashi taji sanyi a ranta.


Bugun kofar da ake yi ne yasa ta dawo hayyacin ta a hankali ta tashi don bude kofar dakin,Abbansu ta gani tsaye babu alamar annuri a fuskarsa, suna hada Ido gabanta ya fadi, tasan ba alkhairi ne ya kawo shi ba.


Cikin tsawa yake mata magana.


"me kike yi har Yanxu baki tattara kayan ki kin bar min gida ba, bana son Ki Kara minti biyu ba tare da kin bar gidan nan ba, Ina nan tsaye Ki hada kayanki Kisan inda dare yayi miki,da ke damu nahaukaciyar mahaifiyarki, bana bukatar na sake bude ido naga giftawar ku a gidana.


Fadawa kan shi tayi tana kuka
"Haba Abba me Muka yi maka ka tsane mu, idan ka Kore mu ina Kake son mu je, ya Ka ke son mu yi da rayuwar mu ina Kake son mu ra6a mu ji sanyi, bamu da Kowa sai Kai Abbana sai Allahn da ya hallicce mu, Idan kace ka juya mana baya a Yanxu wane hali Kake tunanin xamu fada, na rasa dan uwana, mahaifiyata ta rasa hankalinta,ya zan yi da rayuwata Abbana" ta karasa maganar tana kuka.


Saboda tsanin kukan da take yi wasu maganganun ma basa fita.sai da ya gama saurarenta tsaf, ya tureta gefe guda, ya fara mata magana da kakkausar murya.


"Ina ruwana da inda xaki, duk inda kika ga ya dace ki tafi mana ba damuwata bace, ai ita duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba, ku tafi ku girbe abinda ku ka shuka na sharri ke da uwarki"


Yana karasa maganar ya fara jefo musu kayan su fall, yana gamawa ya Kira magaji suka fitar da kayan waje Sannan yasa aka jefo Ammi da Nauwar kofar gidan, Sannan ya mayar da kofar gate din shi ya kulle.


Kukanta ne ya Kara tsananta
Anya kuwa ba mafarki take yi ba, wannan masifa da me tayi kama, ko a mafarki bata taba zaton xata samu kanta a cikin wannnan halin ba, murxa idanunta tayi don ta Kara tabbatar da abinda take ganin ba Gaskiya bane, Yanzu babanta mahaifi wanda yake kaunarsu wanda baya son ganin bakin cikinsu shi ne yayi mata haka, gaskiya asiri bala'i ne, baza ta taba yafewa wanda ya shiga tsakaninta da Abbanta mai kaunar ta ba, kwantawa tayi a kan kayan su tana ta faman kuka, tafi rabin awa tana abu daya, ganin baza ta samu mai taimakonta ba kasancewar dare ya yi, duk makotan su sun kulle gidajen su, wannan yasa ta dago ta fara tunanin nemawa kansu mafita, dagowar da xata yi ta nemi Ammi ta rasa, hankalinta ne ya Kara tashi ta bazama nemanta tana tafiya tana rusa kuka.


"Allah ka taimaki rayuwata kaga halin da nake ciki, Allah ka bayyana min mahaifiyata "


Tafiya tayi mai Nisa Sannan ta hangota kwance kan wata bola tana tsintar kaxanta tana ci, da hanxari ta karasa ta karbi abinda take ci, dabara tayi mata ta tashe ta daga wajen,suka Kara komawa kofar gidan su ko Allah xai sa Abbansu yaji tausayin su ya bude musu su shigo, abin mamaki tararwa tayi an kwashe kayan da suka Bari gaba daya babu abinda aka bar musu sai kayan jikin su.


Haka suka xauna a wajen har xuwa lokacin sallar asubah,yana fitowa ya tarar da su ya sake yi musu sabuwar tijara, maigadi ne ya jiyo hayaniyar sa ya fito don ganin abinda ke faruwa, tunda yasan yanxu gidan ba xaman lafiya ake yi ba.


Hakuri ya rika bashi
"Gaskiya Alhaji idan aka yi wa bayin Allahn nan haka ba a kyauta ba, kuma ba a yi musu adalci ba, yanxu idan ka Kore su ina xasu je?ka duba fa halin da Hajiya take ciki yanxu gaba daya bata hankalinta, Idan ka koresu Waye xai karbe su, Tunda kaine dolen su, bai kamata kayi musu haka ba, Idan ka kyale su kamar kayi toxarta rayuwar su ne"


Tsawa ya daka masa
"saurara Malam aikin gadi na dauke ka ko kuma bada Shawara? Bana son munafunci da sa ido, daga Yau ba ruwanka da abinda ya shafi harkar iyalina, ka tsaya iya matsayinka na Mai gadi".


Tsugunnawa yayi har kasa


"Allah ya huci xuciyar ka Alhaji, na fada maka gaskiya ne Sbd xaman tare bai ce haka ba, Amma kayi hakuri baza a sake ba Insha Allahu"


Binsa yayi da harara, wucewa dakinsa yayi ya barshi yana ta balbala fada.


Korarsu yayi, sai da ya raka su har karshen layin unguwar Sannan ya dawo.




Haka suka wuce suna tafiya Nauwar na kuka tana tuna rayuwa
"tabbas duniya abar tsoro ce kuma ba tada tabbas tana iya juya maka baya a kowane lokaci.










*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


*wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne gareki QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci ina yinki irin mugun sosai din nan*


*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*




4⃣4⃣






Haka suka rika gararanba a cikin unguwa har kusan magariba,duk wanda ya Kalli halin da suke ciki sai ya tausaya musu, ya kuma yi Allah wadai da halin mahaifin Nauwar.


Tafiya suka cigaba da yi ba tare da sun tsaya ba, saboda tana gudun kada a samu masu tsaigumi su je su fadawa Abbanta, cewa har Yanxu basu bar cikin Unguwar ba, Don haka tayi gaggawar neman hanyar da xata tsira da mutuncinta da na mahaifiyarta, tana tafe tana kuka ita kuma Ammi na kokarin xillewa ta barta kasancewar yanxu bata gane komai ba kuma ta iya fahimtar komai.


Sai da suka yi nisa da Unguwar sosai sannan suka tsaya, bakin kofar wani gida ta samu domin sun gaji da tafiya tana son su huta kuma su Kwana a wajen, idan gari ya Waye kuma tayi tunanin inda ya dace su tafi, domin xaman su a haka ba mai yiwuwa bane. tunanin zuwa Dan batta tayi, sai kuma taga cewa idan taje Dan batta Akwai yiwuwar Abbansu Yaje ya Kore su,don haka ta yanke shawarar tafiya tasha duk motar garin da ta samu, Kawai xasu hau tunda Akwai yan canji a a jikinta.


A Yanxu babu abinda ya fi damunta Sama da lalurar Amminta,da rashin wanda xai taimaka mata wajen nema mata magani, tana tunanin hawaye na sauka a kan fuskarta.


Wata murya mai sanyi taji ta mata Magana, saurayi ne wanda baxai wuce shekara talatin ba xuwa talatin da biyu yayi mata magana, da dukkan alamu yana da nutsuwa da addini.


"Assalamu alaikum yan mata"
Dago fuskarta wadda ke cike da hawayen bakin tayi, hanxarin goge hawayen tayi ta dube Shi, cikin ladabi ta amsa masa sallamar
"wa alaikumussalam wa rahmatullah "


Dubanta yayi yana murmushi.


"kin burgeni yan mata kin iya amsa sallama, kuma ba kida wulakanci da girman kai, yadda kike mai kyan nan ya kamata a ce Kina da girman kai amma da yake Kin san darajar dan Adam sai kika amsa min cikin sakin fuska, Allah yayi miki albarka "
Amsa masa tayi da Ameen, ya cigaba da surutu.


Duk ya cikata da magana ta kosa, ya fadi abinda ke tafe da shi ya bata guri, ta cigaba da dogon tunanin da take yi, domin wannan surutun nasa babu abinda yake Kara mata sai takaici.
maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.


"Da dukkan alamu Kina cikin damuwa Don gashi Ina magana ma hankalin Ki na wani wajen, dan Allah ki saki ranki da ni Ki fada min abinda yake damunki ni kuma na kudiri niyyar taimaka miki da baki mafita a kan abinda ya dameki"


Shiru tayi ta kasa bashi amsa sai kalloshi da take yi hawaye na sauka a fuskarta.


"kiyi hakuri Ki share hawayen Ki fada min damuwarki dan Allah, ke nake saurare".


Cikin kuka take masa magana
"baza ka iya fitar da ni daga cikin matsala da kuncin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login