Showing 99001 words to 102000 words out of 111837 words

Chapter 34 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

wuri ba har sai da suka yi magariba a waje"


kasancewar Abba baya son su saimah su yi dare a unguwa shi yasa ma duk inda xasu je yake sawa a kaisu a kuma dakko su.


cikin ladabi ya sadeeq ya mayarwa da Abba amsa.


"Na biya Office ne Abba kuma ba a tashi da wuri ba shi yasa na makara wajen dakko su"


cikin kulawa Abba ya dube shi.
"to shikenan sannunku da xuwa"


cikin ladabi suka amsa masa da yauwa.


magana Abba ya cigaba da yi saddequ!!!! cikin ladabi ya sadeeq ya juyo ya dube shi tare da amsa wa da na'am Abba.




"ina son ganinka bayan sallar isha xamu tattauna wata muhimmiyar magana"


kansa a sunkuye ya amsa da
"to Abba"


tashi suka yi suka shiga cikin gida.


dakin mama suka shiga inda suka tarar da ita da bakuwa don haka suka koma dakin su don gabatar da sallar magariba, bayan sun idar ne wayar Nauwar ta fara ringing don haka tayi saurin daukan wayar, number Ammi ta gani cikin hanxari ta kara wayar a kunneta.


cikin nutsuwa tayi mata sallama.
"Ammina barka da dare"


cikin tattausayar murya ta mayar mata da amsa lafiya lau daughter ya kowa da kowa"


amsa mata tayi da lafiya lau.


bayan sun kammala gaisawa ne take tambayarta.


"ya kamata fa ki dawo gida daughter akwai muhimman abubuwan da ake so a tattauna da ke, abin baxai tafi daidai ba har sai kina nan"


rausayar da kai Nauwar tayi tare da cewa.
"to Ammina xan taho jibi, amma me xa a tattauna haka Ammi"
"Aa ki bari dai ki dao xaki ji komai"
sallama suka yi sannan ta ajiye wayar.


saimah ce ta juyo ta kalleta.


"ya naji kina cewa xaki tafi jibi Nauwar?"


"eh Ammi ce tace nayi sauri na dawo akwai muhimman abubuwan da xa a yi, ni ake jira na dawo"


Ajiyar xuciya saimah tayi tana duban Nauwar.


"nima kuwa wlh baxan tsaya ba tare xamu tafi, tunda dai ba a koma makaranta ba"


murmushi Nauwar tayi.
"nima nafi son mu tafi tare dan bana so na tafi na bar ki a nan jin gidan xan yi duk yayi min xafi"


Hirar su suka cigaba da yi suna tattauna yadda xasu shirya tafiyar su jibi.


da sallama yaya sadeeq ya shiga dakin Abba, a xaune ya tarar da shi yana karatun kur'ani, tsayawa yayi har ya kammala yayi addu'a suka shafa tare, a ladabce ya dubi Abba


"Gani Abba"


cike da kulawa ya dubi dan nasa


"Saddeequ ina so ka tattaro min hankalinka ka bani shi nan"


gyara xama yayi.


"to Abba ina saurarenka"


gyaran murya Abba yayi sannan ya fara magana.


"wato na fuskanci akwai alaka mai karfi tsakaninka da wannan yarinyar Nauwar"


gaban ya sadeeq ne ya fadi, saboda bai san me Abba xai ce dashi game da nauwar ba, cikin hanxari ya amsa masa da eh


"wannan dalilin yasa naga ya dace indai har da gaske kake kana son yarinyar nan kayi mana magana mai kyau, mu kuma mu samu mahaifinta mu nemar maka aurenta"


wani dadi ne ya tsirgawa sadeeq tun daga baban yatsansa har xuwa kwakwalwarsa, nan da nan farin ciki ya bayyana a fuskarksa cike da fara'a ya bawa Abba amsa da.


"ina sonta Abba"


ba karamin dadi Abba yaji da wannan amsa da ya bashi ba, cikin farin ciki ya dube shi.


"Alhamdulillah naji dadin jin wannan maganar daga wajenka, don haka baxa mu yi kasa a gwiwa ba xamu nema maka aurenta, fatan mu dai kada ka bamu kunya ka rike yarinyar nan da kyau da amana"


kansa a kasa ya amsa masa.


"Insha Allahu xaku yi alfahari da auren nan Abba, fatana dai ku cigaba da yi min addua"


"Addua Kullum a cikinta muke, fatan mu dai Allah ya tabbatar da alkhairan da ke ciki ya kade dukkan sharri, gobe idan Allah ya kaimu xan kira babanta na shaida masa, daga baya kuma sai mu je mu yi magana ido da ido"


xuciyar ya sadeeq fes ya tashi ya bar dakin.


da tunanin maganar da Abba ya fada masa ya kwana, ya kosa gari ya waye yaji amsar da ta fito daga gidan su Nauwar duk da cewa dai yasan baxa su hana shi aurenta ba.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆


9⃣3⃣




Nauwar da saimah ne suka fito da sauri daga dakin su dakin mama suka nufa inda suka mika mata wayar da ke hannun su tare da cewa Ammi ce xa tayi magana da ke, karbar wayar tayi ta kara a kunneta tare da yin sallama cike da annashuwa suke magana, a nan Ammi ta shaida mata cewa Jibi Nauwar xata taho gida, mama bata so tafiyar Nauwar ba amma dole ta hakura sbd yanxu ita ce 'ya daya tilo da tayi ragowa a wajen iyayenta, a ranar mama ta bawa Nauwar kudi inda saimah ta rakata kasuwa suka yi siyayyar tafiya.


Ya sadeeq ne xaune a Office gaba daya yau ya kasa sukuni jira kawai yake yaji sakamakon da xai fito daga bakin Abba, gashi har karfe hudu na yamma Abba bai kira shi ba, tashi yayi ya nufi gida don yau yana jin baxai iya aikata komai ba indai bai samu muradin xuciyarsa ba, A hankali cike da nutsuwa yake tuki, addu'a kawai yake yi, Allah yasa yaji alkhairi daga bakin Abba, yana isowa kofar gida ya fito daga motar, sai da ya tsaya yayi tunani na wasu yan mintuna sannan ya karasa cikin gidan, tarar da su saimah yayi suna ta fito da kayan da suka siyo a kasuwa, a hankali ya nemi gefe ya xauna kusa da mamah, jujjuya kayan ya shiga yi yana yaba kyan su, A hankali ya mayar da kallonsa ga mamah, tare da tambayarta ina Abba yake, cikin nutsuwa ta bashi amsa da yana cikin daki.


wani farin ciki da dadi ne suka sauka a cikin xuciyarsa, cikin nutsuwa ya mike yana taku a hankali har ya isa bakin kofar dakin, tsayawa yayi ya gyara tsaf, sannan ya taka a hankali ya shiga dakin tare da sallama, a kashingide ya iske Abba yana laxumi, dagowa yayi tare da amsa sallamar.


wajen xama yaya sadeeq ya samu, kansa a kasa yake magana.
sannu da hutawa Abba


ranshi a sake ya amsa masa da yawa Saddeequ ya aikin, ashe har ka dawo


dagowa yayi tare da sakin takaitaccen murmushi.


eh nima yanxu na shigo Abba.


murmushi Abba yayi tare da duban ya Saddeeq.


"nasan dai tatsuniyar gixo bata wuce ta koki, a kan maganar nan kaxo min nan, wato kaji shiru har ka kosa kaji abinda muka yi da su ko"


dago kai yayi tare da sosa keya.


"aa Abba dama naxo ne na gaisheka ne naga tunda na shigo ban ji motsinka ba, amma dai har da wannan maganar ma, ya ku ka yi da su Abba"


duban shi Abba yayi yana murmushi.
Allah ya shirya mana ku yaran xamani, yanxu yaro da kansa yake xuwa jin labarin auren sa mu kuwa a da sai dai a yi mana komai, har amaryar ma wani lokacin bai fi sau daya xaku hadu ku gaisa ba,daga nan sai aure kawai.


numfashi Abba yaja sannan ya cigaba da magana.
"na kira mahaifinta mun yi magana da shi ta fahimta, ya fada min cewa........."


saurin dagowa ya Saddeeq yayi don jin abinda xai fito daga bakin Abba.


Abba ya lura da yanayin yadda ya saddeq ya kosa yaji yadda suka yi.


"ya naga har ka tsorata saddeequ tun kafin na fada maka abinda yace dani"


A hankali ya dago manyan idanunsa, tare da yin dan murmushi.
"ba tsorata nayi ba Abba"


"yauwa yaron kirki a harkar aure babu tsoro, kowa rabonsa xai aura babu wanda xai auri matar wani kaji ko"


amsa masa yayi da to sannan ya cigaba da magana.
"ya shaida min cewa yarinyar nan suna soyayya da wani dan uwanta wanda dashi suka xo gidan nan, nasan ma ka ganshi"


wani kishi da bakin ciki ne suka tokare makogoron ya sadeeq da kyar ya iya amsawa Abba da eh.


"to wannan yaron shi ne yake sonta tun tana yarinya kuma ita ma ya tabbatar min da cewa tana son shi, dan sun shaku sosai sai dai kawai ba a yi maganar auren su ba, yace idan kana ganin xaka iya shigowa cikin manemanta sai ka shigo yana maraba da kai, ya tabbatar min da cewa babu alfarmar da xamu nema a wajensa ba tare da yayi mana ba,idan kana ganin xaka iya neman aurenta to kofa a bude take"


wata Ajiyar xuciya ya sadeeq ya saki, idanunsa sun yi ja, ya dago ya dubi Abba.


"to shikenan Abba Allah ya xaba mafi alkhairi amma ina ganin kafin lokacin ya kamata nayi istikhara na nemi xabin Allah ina ganin xai fi sauki"


ba karamin dadi Abba yaji ba shi yasa yake son sadeeq sbd hangen nesan sa, cikin farin ciki ya bashi amsa.


"hakan yana da kyau sadeeq Allah yayi jagoranci"


amsawa yayi da aameen.


jikinsa a sanyaye ya fita ya bar dakin, ba karamin tafasa xuciyarsa take yi ba, ya tsani hada taraiya da wani a kan abinda yake so, gashi har wani ya shiga xuciyar yarinyar da ya gama tsara rayuwarsa da ita, tunanin ta inda xai fara bullowa lamarin ya shiga yi, dakinsa ya bude yana shiga ya fada kan gado tare da runtse idanunsa ko xai ji saukin hayakin da ke taso masa daga kasan xuciyarsa, xikirin Allah ya fara yi, sbd shi ne kadai abinda xai saukaka masa damuwrsa domin yanxu ji yake gaba daya duniya tayi masa xafi babu wani abu da xai faranta ransa idan ba xikirin ba.










*Jeeddahtulkhair😘🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆






9⃣4⃣




Kansa ne yake rika juyawa a hankali ya tashi xaune ya dafe kan nasa tare da rungumar pillown da ke hannunsa, innalillahi ya shiga ambata, bai san inda xai tsoma rayuwarsa ba idan har aka ce ya rasa Nauwar, lokaci guda ta shiga xuciyarsa ta samu gurin xaman da fitarta sai an sha wuya, ba karamin axaba rayuwarsa xata fada ba idan aka ce wani ya kwace masa abar kaunarsa, a hankali ya ja jiki ya shiga bayi ya daura alwala ya fara jero nafila rokon Allah yake yi sosai har da xubar da hawaye yana neman agaji, ya bashi nasara a bisa abinda yasa gaba sannan ya xaba masa abinda ya fi xama alkhairi a gare shi, yana gamawa ya shafa ya nemi guri ya cigaba da xurfafa tunanin guguwar da take shirin tunkaro shi.
Har bayan sallar magarib yana daki ya kasa yin katabus idanunsa sun yi jawur,da ganinsa yana cikin tsananin damuwa, kamar daga sama yaji mama na kwala masa kira, da hanxari yaja jiki ya shiga cikin gida a bakin kitchen ya sameta, da flask din abinci a gabanta, tunda ya nufo wajenta ta bishi da wani kallo mai cike da ayoyin tambaya jikinta ya bata dan nata yana cikin matsananciyar damuwa, duk wani walwalarsa da nishadinsa sun ragu, ganin kallon da take masa ne yasa ya karfafa jikinsa tare da sakin rai yana fara'a ya karasa wajenta, tsugunnawa yayi yana fuskantarta.
"gani mama"
cike da damuwa da halin da yake ciki ta bashi amsa.
"me yasa yau ka shige cikin daki ban ganka a cikin yan uwanka ba, bana xaton yau a jama'i kayi sallah, sannan ga abincinka har yana shirin salamcewa amma babu labarin xuwanka duk da cewa nasan baka wasa da cikin ka, fada min abinda yake damunka"?


hadiye damuwarsa yayi ya saki rai yana mata magana
"babu Abinda yake damuna mama kawai dai bana jin nishadi ne yau din nan"


hade rai tayi babu alamar wasa a tattare da ita.
"ka fada min gaskiya sadeeq bana son boye-boye ni mahaifiyarka ce duk wani abu naka na sani, nasan farin cikinka nasan akasin haka kaga kuwa babu abinda xai canja a tattare da kai ba tare da na gane ba, dan nasn halin dana sarai ba mutum ne mara son jama'a ba"


kasa mallakar xuciyarsa yayi, kafin kace me hawaye ya cika idanunsa tuni ya fara kwarara a saman fuskarsa. hankalin mama a tashe ta dago fuskarsa tana tambayarsa.
"lafiya Abubakar me ya faru da kai, ko dai korarka aka yi a wajen aiki"


saboda bakin cikin da ya cika xuciyarsa ya kasa magana, rarrashinsa mama take yi kamar yaron goye, sai da yayi kukansa ya koshi ya share hawayensa sannan ya fara yi mata bayanin dalilin kukan nasa, cike da tausayawa ta dube shi.
"kayi hakuri sadeeq idan Nauwar rabonka ce xaka samu, nayi mamakin yadda yarinyar nan ta shiga ranka haka lokaci guda, kai da baka sa abu a ranka,kuma damuwa bata hanaka walwala, dan Allah ka saki ranka muna nan muna yi maka addu'a Allah xai xaba maka mafi alkhairi, banda abinka ma yarinyar da ba aure aka daura mata ba kawai cewa aka yi fa da wanda yake sonta, kana da damar da xaka bayyana mata soyayya, idan rabonka ce sai kaga ka aureta har ka haifa min yan jikoki" ta karasa maganar tana murmushi.


shi ma ya sadeeq murmushin yayi saboda ba karamin faranta masa mama tayi ba da ta ambaci yayan da xai samu a jikin Nauwar, lallaba shi ta rika yi har sai da ya saki ransa ya ci abincin sosai ya manta da duk damuwar da ta dame shi.


yau ta kama litinin kuma ita ce ranar da Nauwar xata koma gida, tun safe ta kammala shirye-shiryen da xata yi, tana daki ta xuba tagumi tana kukan rabuwa da gidan su saimah, ita ma kukan saimah ke yi saboda ba karamar shakuwa suka yi da juna ba, kiran sunan su Abba yayi da hanxari suka taso suka fito tsakar gida, cikin kulawa yake musu magana.
"kukan me kuke yi Nauwar, ai ba a rabu ba ana tare kuma xa a rika xumunci ku share hawayenku"


hannu suka sa suka shiga share hawayen
"yauwa ko ku fa, to ku dakko jakar kayan ku yanxu xamu tafi kano,baba son yin dare a hanya"


wani sabon kukan suka cigaba da yi, ita ma mama hawaye ne suka cika idanunta amma taki bari su xubo, saboda bata son hankalin yaran ya sake tashi, jakar kayan suka dakko suna tafe suna kuka rungume mama Nauwar tayi da kyar aka cireta daga jikinta, suna kuka suka rabu, kiran ya sadeeq Abba yayi don shi ne xai ja motar da xasu yi tafiyar da ita.


fitowa yayi daga dakinsa sanye yake da shadda golden colour wadda aka yiwa aiki da xare kalar shaddar,hularsa ma kalar kayansa ne haka ma takalmin da ke sanye a kafarsa, ya kuma sanya agogo wanda ya kara fitar masa da wankan sa, ba karamin karbar jikinsa kayan suka yi ba, yayi matukar yin kyau sai dai kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa don a yan kwanakin nan har ya dan rame.


Abba ne yayi masa magana.
"mu shige mu tafi ko sadeeq"


A ladabce ya amsa da to Abba.
kama hanyar tafiya suka yi, su Nauwar sai faman kuka suke duk irin rarrashin da Abba yayi musu suka ki dainawa sai hakura yayi ya kyale su, sai da suka kusa shigowa kano sannan suka Hakura.


kama hanyar xuwa gidan su Hamdan suka yi tunda yanxu a nan Ammi take, kasancewar gidan da ake gina mata ba a kammala shi ba, a kofar gida suka hango Hamdan tsaye yana jiran isowar su Nauwar, hannu shi rungume yake a kirjinsa, kallon motar da ke nufo kofar gidan su yake yi, kamar a mafarki ya hango Nauwar tana masa murmushi, cikin doki da shaukin son ganinta ya karaso wajen, parking ya sadeeq yayi sannan ya matso daf da su, cikin ladabi yake gaida Abba, cikin sakin fuska ya amsa masa, hannu ya mikawa ya sadeeq shi ma fuskarsa a sake ya mika masa suka yi musabaka, juyo da kallonsa yayi wajen Nauwar wani kallo yake mata yana wani kashe mata ido, murmushi ya rika sakar mata,ita ma murmushin take masa cikin shagwaba take masa magana.


"Na tafi na dade nasan ko missing dina ma baka yi ba"


Cikin marairaicewa yake mata magana
"Haba queen ya xa a yi na manta da ke, indai xan manta da ke ai xan mant da kaina"


duk maganganun da suke yi a kunnen ya sadeeq, ji yake xuciyarsa kamar ta fito saboda kishi da bakin ciki, da sauri ya fito daga motar ya koma gefe ya tsaya saboda baxai iya jure kallon wannan bakin cikin ba, sai da suka gama maganar su tsaf sannan ya shigar da su cikin gida a sitting room aka sauke su, su kuma su Nauwar suka wuce cikin gida.


Ruwa da abinci aka kawo musu, an karrama su sosai,an yi musu karbar mutunci, ruwa Abba ya dauka ya sha sannna ya dubi sadeeq.
"ka dauki ruwan ka sha mana sadeeq mun sha hanya ai kana bukatar kasha ruwa"


muryar shi a dashe ya bawa Abba amsa.
"bana jin kishiruwa na koshi"


ji yake kamar ya fashe da kuka sbd abin takaicin da ya gani yanxu,da na sanin xuwansa yake yi da ya xauna a gida duk da bai ga wannan abin takaicin ba, baya jin yau xai iya runtsawa saboda tsananin kishin da ya cika zuciyar sa.


Sallamar Ammi da Abban nauwar ne ya dawo da shi hankalinsa, cike da ladabi ya gaishe su, hira suka fara yi da Abba tare da yi masa godiya abisa karamcin da yayi musu, da kulawa da su da yayi na tsawon wani lokaci ba tare da ya nuna gajiyawa ko kosawa a bisa haka ba.
fuskar Abba a sake yake basu amsa.
"ba komai ai mun xama daya da ku, Allah ya kara mana dankon xumunci"
gaba daya suka amsa da ameen komawa ciki Ammi tayi ta bar su da Abban nauwar don tattaunawa dangane da maganar auren sadeeq da Nauwar.
Abban nauwar ne ya fara bayani.


"naji dadin wannan maganar da ta fito daga wajen ku Alhaji "
Cikin sakin fuska Abba ya bashi amsa
"ban tari bunfashinka ba Alhaji ni ina ganin mu bar maganar auren nan"


gaban ya sadeeq ne ya fadi jin Abba yace a bar maganar aurensa.
da sauri Abban Nauwar ya dubi Abba.
"ya xaka ce a hakura Alhaji"?


"ba wani abu ne yasa nace a bar maganar ba, sai don yarinyar nan tana da wanda take so, shi ma kuma yake sonta, idan aka ce sadeeq ya shigo cikin masu neman aurenta ina ganin ba a yi mata dalci ba, saboda tuntuni da akwai wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login