Showing 57001 words to 60000 words out of 111837 words
Chapter 20 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
masa rahma. tambayar mai gadi ya shiga yi
"to ina matar gidan da ragowar yaran gidan?"
kamar mai gadi baxai bashi wannan amsar ba, amma saboda ya yi masa alkawarin fadar gaskiya, sai ya danne xuciyarsa ya fara yi masa bayani
"uwar yaran ta haukace, shi ne mai gidan nan ya kore su"
mikewa Baffa yayi yana salati, nan da nan kansa ya rika juyawa, ya fadi kasa sumamme.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne a gareki UMMU SULAIM MUHAMMAD LAWAN(hasanatullah) Nauwar na godia da yadda kike son wannan labari nata Allah ya bar xumunci*
5⃣4⃣
A gigice mai gadi ya shiga sashin su innah karime, samun su yayi suna shiryen-shiryen fita unguwa.
"Hajiya ku fito baba ya fadi dan Allah ku taimaka masa"
A fusace Habi ta dube shi ta bashi amsa
"faduwarsa bata shafe mu ba, ka karasa ciki ka fadawa dansa"
da gudu ya karasa bangaren Abban Nauwar, tarar da shi yayi yana bacci, dan haka ya tashe shi suka rankayo suka taho wajen Baffa
hankalinsa a tashe yake masa magana
"Baffa me ya sameka ka fadi, dan Allah ka tashi" da sauri mai gadi ya kawo ruwa aka yayyafa masa, ya fara bude ido sannan ya saka shi a mota suka yi asibiti"
suna isa aka fara duba Baffa inda aka tabbatar masa da cewa damuwa ce tayi masa yawa, kuma idan ya cigaba da kasancewa a cikin damuwa, yana da baraxanar kamuwa da hawan jini.
suna kammala duba shi suka dawo gida, a daki ya saka shi yana tambayar shi
"dan Allah ka daina saka damuwa a ranka Baffa ka dai ji abinda likita ya fada mana"
duban shi yayi yana hawaye
"dole nayi kuka mahmud, saboda babban bala'i ne ya sameka a rayuwa wanda idan ban yi da gaske ba, xai yi sanadiyyar shigarka wuta, ka dakko amanar yarinya gari i gari, tun daga sudan amma ka wulakanta ta, ka koreta da ita da yar jikata guda daya da na mallaka, wacce ita ce tayi ragowa a yayanka, mahmud dole na cigaba da kasancewa a cikin bakin ciki, jikana ya rasu amma saboda baka ganin darajata duk baka fada min ba"
shiru yayi yana sauraren Baffa,maganarsa na shiga kunnesa, duk abinda Baffa yake fada masa yasan ya aikata kuma bai kyauta ba, amma baxai iya daukan mataki a kan haka ba.
katse masa tunani Baffa yayi
"mahmud idan kana son ganin farin cikina da walwalata ka nemo yarinyar nan tare da yarta idan ba haka ba ban yafe maka ba"
a raxane ya dubi Baffa
"baka yafe min ba fa kace Baffana"
"eh ban yafe maka ba, har sai ka cika umarnin da nayi maka"
kuka mahmud ya rika yi yana rokon Baffa gafara, amma yaki yafe masa.
A ranar Baffa yace baxai sake kwana a gidan ba,duk da magiyar da mahmud yayi masa yaki hakura, sai daukan shi yayi a mota ya kai shi har Dan batta, suna tafe a mota Baffa na kuka, saboda tausayin halin da dansa ke ciki.
Bayan ya kai shi ya xaro kudi masu yawa ya bashi, amma sam Baffa yaki karba, kayan abincin da ya siyo masa ma cewa yayi ya juya dasu, saboda babu abinda xai yi da su, tunda ba shi da mai girka masa.
Idanun mahmud cike da hawaye ya dubi Baffansa
"Dan Allah ka yafe min Baffa,me yasa xaka ki karbar abinda ya fito daga hannuna gaba daya"
fuskar Baffa ba annuri ya dubi mahmud
"tunda ka xama mara adalci baka kulawa da iyalinka ka xabi wasu ka barni ka wulakanta amanar da ka dakko, babu ruwana da kai, kaje ka kama mutanen da kake ganin sun fini daraja a wajenka"
tashin hankali ne ya bayyana a fuskar mahmud
"wlh ban kama kowa ba baffa, nasan kaine kayi min gata, ka soni a lokacin da kowa ke guduna, ta yaya xan ki ganin darajarka, kayi hakuri kayi min afuwa"
tausayin dansa ne ya kama shi, yasan duk abinda yake yi ba a hankalinsa yake ba, amma ya kuduri niyyar yi masa addu'a Allah ya dawo da shi hanya madaidaiciya.
"shikenan na ji bayanan ka mahmud ka tashi ka tafi kada dare yayi maka a hanya, Allah ya ganar da kai gaskiya, ya fito da kai daga duhun da kake ciki"
amsawa yayi da ameen ya mike ya tafi.
xuciyarsa cike da bakin cikin Abubuwan da yake aikatawa, mamakin kansa yake,ta yaya ma aka yi hakan ke faruwa? haka ya isa gida da wadannan tunane-tunanen ya kuma kudiri niyyar korar Habi daga gidansa, dole ta koma Dan batta ta kula da tsohonsa.
Yana isa gidan ya shiga sashin su innah karime da niyyar fadawa Habi ta shirya gobe xai mayar da ita dakinta, amma abin mamaki sai bakinsa ya kulle ya kasa furta mata komai, sai gaisawa suka yi ya fito ya tafi dakinsa xuciyarsa cike da bakin ciki.
Bayan komawar Baffa dan batta da sati biyu, ciwonsa ya kara dawowa saboda kullum ya tuna su Nauwar da mahaifiyarta sai yayi kukan bakin ciki, wannan dalilin ne yasa ciwon nasa yake dawowa danye.
A ranar da ciwon sa yayi xafi Audu ya kira mahmud ya sanar da shi, a gigice ya nufi hanyar xuwa dan batta, inda suka dakko Baffa suka dawo da shi asibitin kano, taimakon gaggawa aka rika bashi, cikin ikon Allah ya samu sauki, bayan ya warware ne ya tambayi mahmud.
"wai ina malam Abdullahi ne? tunda na fara rashin lafiyar nan banga yaxo ya gaishe ni ba, anya ya sani kuwa?"
A kunya ce mahmud ya amsawa Baffa saboda rabonsa da yaje wajen malam Abdullahi har ya manta, ko waya malam din yayi masa baya dauka, gashi kuma shi ne yayi silar xuwansa birni,shi ne silar duk wani arxiki da yake takama da shi.
"A'a ban fada masa ba Baffa naga abubuwan ne sun yi yawa bana san na takura masa"
cikin fushi Baffa yake wa mahmud magana
"bana san shashanci aminin nawa xaka ki fadawa abinda ya dameni, maxa dauki waya ka kira shi ka fada masa kafin na bata maka rai"
daukan wayar yayi ya kira malam Abdullahi.
"mamaki ne ya kama malam, yau kuma mudi ne aka tuna da ni aka kira ni Allah da iko yake"
daukan wayar yayi ya kara a kunnesa, sallama yayi sannan ya kira sunan mahmud
"wata sabon gani yau kuma xumuncin ne ya motsa an tuna da ni"
kunya ce ta kama mahmud saboda ya dade bai kira shi sun gaisa ba.
"dama Baffa ne ba shi da lafiya, shi ne yace bai ganka kaxo dubiya ba"
"subhanallah ai ban sani ba wlh, ka fada masa gani nan xuwa yanxu insha Allah"
suna gama wayar ya dauki takalmi sai wajen Baffa, da sallama malam Abdullahi ya shigo wajen.
Baffa na hada ido da shi ya fashe da kuka mai ban tausayi, karasowa malam Abdullahi yayi yana rarrashin Baffa.
"kayi hakuri malam cuta ai ba mutuwa bace, in Allah ya yarda xaka samu sauki"
bayan sun dawo hayyacin su ne suka gaisa, ya tambayi Baffa abinda ke damunsa.
hawaye Baffa ya share
"wlh ba komai ke damuna ba malam sai bakin cikin mahmud"
malam Abdullahi ne ya dubi mahmud
"kai yaro, yanxu bakin cikinka ne yake son hallaka mahifinka, anya kana san cikawa da imani kuwa?
sunkuyar da kai mahmud yayi saboda ba shida amsar da xai bawa malam.
Baffa ne ya cigaba da yi masa bayani
"yanxu ace malam yaron nan ya kori yarsa da matarsa, dansa ya rasu duk ban sani ba"
cikin mamaki malam Abdullahi ya dubi mahmud.
"kanka kalau kuwa ka aikata wannan danyen aikin, gaskiya da wata a kasa"
tashi ka fita xamu tattauna da baffanka.
bayan ya fita malam Abdullahi ya dubi Baffa
"wannan abin fa ba na lafiya bane, ka daina saka bakin cikin yaron nan a ranka, ina ganin akwai lauje cikin nadi"
"Nima haka nake tunani malam"
"Tunda abin haka ne, addu'a ya kamata a yi, Yanxu xansa a yi saukar kur'ani, Allah ya warware duk wata matsala dake damun yaron nan, su kuma Allah ya bayyana su"
cikin farin ciki Baffa ya dube shi.
"Gaskiya hakan yayi kyau, Allah ya amsa mana adduar da xamu yi, shi kuma Allah ya shirye shi"
sallama suka yi da Baffa, yayi masa alkawarin taho wa da mahmud magungunan karya sihiri.
godiya mai yawa yayi masa sannan suka rabu
*Jeeddahtulkhairhb😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJAN*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gareki AYSHA KABIR (Mrs shehu Murtala) Allah ya qara muku xaman lafiya da yarlawar arxiki, thanks 4 d love and support*
*ina bawa Makaranta littafi hakuri saboda rashin ganin post jiya, hakan ya faru ne sakamakon rashin caji, a yi min afuwa kun san rayuwar kauye sai a slow*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
5⃣5⃣
Bayan Baffa yayi sallama da malam Abdullahi ne ya 'kwalawa mahmud kira,da sauri yaxo ya samu baffa, cikin ladabi da girmamawa ya dube shi.
"Gani baffa"
"Nemi guri ka xauna mudi maganar mu bata tsugunnawa bace, bude kunne xaka yi ka saurare ni da kyau"
tashi yayi ya samu gefan gadon da baffa yake ya xauna, xuba masa ido yayi yana jiran jin abinda xai fito daga bakin sa
"Mahmoud ina tunanin duk abinda kake aikatawa ba a hankalin ka kake ba, duk wanda ya dubeka yasan baka cikin nutsuwa kamar da, Sannan duk wani mai lissafi baxai aikata abinda kake yi ba, gaba daya ka canja salon rayuwarka, ko dai wani ne a gefe yake koya maka sa'ka da mugun xare? To Idan ta haka ne na yanke shawara ni da malam Abdullahi, xa a yi saukar kur'ani a yi sadaka Allah ya yaye maka abinda yake damunka, sannan xai rika kawo maka maganin karya sihiri xaka rika sha kullum, idan ma wani ne yayi maka wannan sharrin Allah xai mayar masa da abinsa kansa, saura kuma kace baxa ka sha ba nasan taurin kan ku na yayan xamani"
mahmud bai ji dadin abinda Baffa ya fada masa ba, saboda innah karime ta fada masa kada ya karbi maganin komai daga hannun kowa,saboda kada a Cutar da shi, anga Allah yayi masa arxiki sharewa kawai ya yi ya amsawa baffa da to, amma yayi alkawarin ko an bashi maganin baxai rika sha ba xubarwa xai yi.
Satin Baffa guda a asibiti aka sallame shi, A ranar da aka sallame shi yayi waya da malam Abdullahi inda suka tattauna a akan xai rika kawo wa mahmud magani kullum yana sha, sannan kuma, xai sa a fara saukar kur'ani, A ranar Baffa yasa rigima dole a mayar da shi Dan batta saboda idan ya xauna a gidan Mahmoud yana ganin abinda su Habi ke yi hankalin sa ne xai rika tashi ,suna cin arxikin dansa amma suna wulakanta shi, duk rashin Lafiyar nan da yayi babu Wacce tayi tunanin xuwa ta gaishe shi, ko magaji basu tura ba, amma Abban nauwar ko bacin ransa bai nuna a kan haka ba, saboda baya ganin laifin su kuma baya son abinda xai bata musu rai, duk nacin da Abban nauwar ya yiwa baffa a kan ya xauna fafur yaki yarda, dan haka ya hakura ya dauke shi, sai garin Dan batta
Bayan tafiyar su Baffa bai fi da minti goma ba, su innah karime da habi suka fito falo suna gulmar Abban nauwar da Baffa, innah karime ce ta dubi habi tana yatsina fuska
"Nifa habi naso a ce uban mudi ya mutu mun huta, shegen yaro kamar bani na haife Shi ba baya kaunata baya San ganin farin cikina, nifa da a asibiti na haife Shi sai nace musanya mun shi aka yi,gaba daya Dan nan baya ta tawa, shi yasa nima ko Sannu ban masa ba da ya kwanta Cutar nan"
"hmm ai kece baki San wani abu ba innah, Malam fa bakin cikin xaman mu yake a gidan nan,shi yasa kika ga ko xuwa baya yi, kuma xama Yanxu Muka fara ba wani kauye da xan koma dan banga abinda na ajiye a can ba.
Suna cikin wannan hirar suka ga Hamdan tsaye a kansu, lumshe idanu yayi tare da sakin murmushin takaici, suna ganin shi suka Mike tsaye, kallon kallo Habi da innah karime ke yi,saboda basu taba tsammanin ganinshi ba, a xatonsu tafiyar da yayi baxai dawo ba. Cikin fushi gami da daka tsawa
innah dube Shi.
"Sannu da xuwa bakin biri, motar arfa mai saurin kashe hausawa, gayyar na iyya an iso, me kuma ya kawo ka gidan jikana, Ina xaton an maka tsakani da gidan nan tun kafin wannan shegiyar yarinyar da wannan mahaukaciyar uwar tata su bar gidan nan, yau kuma ubanka kaxo yi"
Hannunsa harde da kirjinsa yake kallonta yana murmushi, masifar innah karime dariya take bashi saboda gaba daya bata San Annabi ya faku ba.
"naxo ne na ja kunnen ki tsohuwar banxa Wacce tsufanta bai tsinana mata komai ba,Wacce bata tsoron Allah kuma bata tsoron abinda xata je ta tarar a kabari, duk abinda ku ka aikatawa su nauwar da khala Rehab bayan bana nan ya dawo kunnena, da kisan da kuka yi wa fu'ad, Ina nan xuwa xan dauki mataki a Kai baxan iya yafe wannan xaluncin da kuka yi ba, Sannan ina mai tabbatar muku da cewa Nauwar suna nan zasu dawo muhallinsu nan bada dadewa ba dariya ikon Allah, kuma Indai Ina da ragowar numfashi sai kun girbe abinda kuka shuka, mu xuba ni da ku"
Jikin Habi gaba daya yayi sanyi,saboda tasan halin Hamdan sosai indai ya yi alqawarin yin abu sai ya aikata, karfin hali tayi ta fara magana.
"me xaka yi mana dan banxa lalatacce, Wanda bai san mutuncin furfura ba, Kai a su wa, babu abinda xaka iya Wlh mun buga da Wadanda suka fika ma, basu ci riba ba ballantana kuma Kai karamin alhaki, kayi duk abinda kayi niyya, idan ka fasa baka kaunar uwarka da ubanka"
Wucewa yayi ya kyale su saboda ya isar da saqon ya dade yana son isarwa
Gida ya wuce a falo ya tarar da maminsa na shirin tayar da sallah, ganin shi tayi ran shi a bace don haka ta dakata, ta fara tambayar shi abinda ke faruwa, guri ya samu ya xauna ya fara fada mata abinda ya faru tsakanin sa da su innah karime, Sannan ya fada mata a lokacin xai tafi ya sanar da hukuma duk abinda suka aikata, sai kuma sun warware sharrin da suka kulla.
A raxane ta dube shi
"kaga Hamdan bana San shiga irin wannan rigimar Idan baka iya kama barawo ba sai ya kamaka, gara ka taya su da addu'a Allah ya kawo musu mafita, Sannan ka tafi neman su kamar yadda kayi alkawari Amma ni bana goyon bayan wannan matakin da xaka dauka"
"shikenan Allah ya wuce mana gaba Mami, amma zan yi kokari xuwa gobe na wuce neman nasu, saboda lokaci yana ta kurewa "
Addu'a tayi masa Sannan ta tayar da sallar, tana idarwa ta fara yiwa dan ta adduar samun nasara a kan abinda yasa gaba na alkhairi.
Bayan fitar Hamdan daga gidan su nauwar, su innah karime suka cigaba da tattauna maganganun da Hamdan ya fada musu,xage-xage suka rika yi suna tsine masa albarka, innah karime har da cewa shi ma sai sun ga bayansa.
A dai-dai lokacin ne magaji ya shigo dakin wajen xama ya samu, tambayar su dangane da abinda yasa suke masifa.
"Wlh magaji Dan banxan yaron nan da ya kusa kashe ka, shi ne Yaxo yau ya Kare mana tanadi, Sannan yace wai mu ne Muka kashe Dan wajen Mudi, kuma Kaima yace sai yaga bayanka.
A fusace magaji ya shiga daki ya xaro Adda, sai gidan su Hamdan a kofar gida ya tsaya yana ta xage-xage, yana ci musu mutunci Hamdan na jin abinda magaji ke fada ya tashi xai fita, da sauri mami ta tare shi ta hana shi fita,saboda tasan Hamdan yana da xuciya xai iya yi masa ba daidai ba, sai da ya gama xage su tas,Sannan ya shige ya tafi, xuciyar Hamdan sai faman tafasa take yi saboda bakin ciki.
A haka ya Kwana ran shi a bace, washe gari da sassafe ya shirya ya kama hanyar tafiya neman su nauwar addu'a Mami tayi masa Sannan suka yi sallama ya tafi.
*GARIN GOMBE*
A tasha direba ya sauke su Nauwar, fitowa tayi daga tashar ta kama hanyar xuwa kasuwar garin dan ta siya kayan da suke bukata, bayan ta fito daga kasuwar ne ta rasa inda xata nufa, dan haka ta yanke shawarar samun guri a kasuwar ta xauna,saboda tana gudun kada matsalar da ta same su a baya, ta sake samun su, a wannan xaman da tayi bata fuskanci wani kalubale ba, don ko bara bata xuwa kullum tana tare da Amminta tana tarairayarta kasancewar yan kudaden da ta samu a hannun Alhaji Talle basu kare ba, kullum da safiya take fita don siyo musu abinda xasu kai bakinsu, idan da matsalar da take fuskanta bata wuce Farfadiyar da Ammi ke fama da ita ba.
Yau ma kamar kullum shiryawa tayi tsaf, don nemo musu abincin safe, Ammi na kan cinyarta ta kwantar da kai tana ta sharadi bacci, A hankali tayi dabara ta sauke kan Ammi daga cinyarta, ta tashi a hankali ta nufi wajen siyo musu abinci, sauri take yi sosai gudun kada ta farka tayi wani gurin.
wajen mai shayi ta tsaya inda ta siyo musu indomie da shayi, da sauri ta karaso wajen da suka sauka, amma abin mamaki sai ta tarar babu Ammi babu dalilinta sai filin wajen kawai, tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta ajiye abincin da ta siyo tayi, ta shiga neman Amminta amma shiru ba labarinta, fita tayi daga wajen ta baxama cikin unguwa tana tafe tana salati hade da kuka Allah ya bayyana mata mahaifiyarta, tambayar mutane ta shiga yi ko sun ga inda mahaifiyar tata tayi amma babu wanda ya kalleta ballanta tasa ran samun amsa, kusan duk wanda ta hadu da shi kallon mahaukaciya yake mata, sake komawa wajen da suke kwana tayi ko Allah xai sa taga ta dawo, wani mutum ta hango hannunsa rike da irin kayan da ke jikin Ammi yana tahowa inda take, saurin mikewa tayi ta tare shi tana hawaye, cikin tausayawa