Showing 72001 words to 75000 words out of 111837 words
Chapter 25 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
da xai min kenan kika sa na tunkare shi, Kin san haka yake amma baki fada min na shirya sosai ba, gaskiya baki kyauta min ba"
Rarrashinta habi ta shiga yi, "Wlh nima bansan haka yake ba xulai, da a tunanin mu xai yi saurin karbar ki tunda mun ga dan takarda ne, kuma Kin san duk yan takarda suna neman mata shi yasa, amma kada ki karaya tawan gobe dole xa a sake shiri a tunkare shi"
Daki suka shige suka cigaba da shirya makircin yadda xa a tunkare shi gobe.
Gari na wayewa Abban nauwar ya fito falo inda ya samu su innah karime na jiyyar magaji, fuskar shi a daure ya gaishe su, cikin kulawa da nuna soyayya suka amsa masa, kafin yace komai innah karime ta fara masa bayani.
"dama wata Shawara nayi da gwaggonka habi, nasan kuma Kai yaro ne mai biyayya baxa ka watsa mana kasa a ido ba"
Babu alamar wasa a fuskarsa ya amsa mata da
"ina Jin ki"
Mayar da ajiyar xuciya ta yi sannan ta cigaba da magana..
"dama gani nayi bai kamata a natsayinka na cikakken namiji wanda Allah ya yiwa baiwar arxiki da lafiya ka rika xama ba aure ba, tunda wannan gantalalliyar matar taka ta tafi yawon iskancinta ita da wannan shegiyar yar taka baka yi aure ba, kamar wanda aka magance "
Hannu yasa ya dakatar da ita..
"kinga innah Idan xaki yi magana kada ki kuskura Ki Kara aibata min iyalina Idan xaki yi maganar ki kai tsaye Kiyi, Idan baxa Ki yi ba kuma Ina da abin yi xan tashi na tafi "
Hakuri ta shiga bashi tare da rarrashinsa.
"Haba mudi abin ai ba na fushi bane gaskiya ce dai ta kama dole mu fada, amma a yi hakuri Allah ya huci xuciyar ka, dama yarinya mai hankali yar gayu na samo maka don naga xata dace da rayuwarka kuma kanwa ce a wajen gwaggonka da baban gwaggonka da yarinyar uwarsu daya ubansu daya"
Kafin yace mata wani abu har ta kwalawa xulai kira, cikin yanga ta fito tana duban shi tana fari da ido..
Cikin mamaki ya dubeta tare da nuna ta da hannu.
"wannan Shi ne xabin da kika yi min innah, wannan tsohuwar banxar ita ce ta biyo ni falo tana kokarin rungume ni, me xan yi da karuwa Mara kamun kai, duk a tunanina aljana na gani, saboda mace mai kamala da mutunci baxa ta yi abinda kika yi min jiya ba, don haka tun wuri ki tattara kayan ki Ki bar gidan nan, Idan na sake dawowa na ganki sai na lahira ya fiki Jin dadi "
Bai jira amsar su ba ya fice daga gidan.
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*ina matuqar nuna godiya da Farin ciki gare Ki UMMU RAHMA marubuciyar KOMAI NISAN DARE, na gode da kulawar Ki gare ni*
*Wannan shafin Gaba daya sadaukarwa ne gare Ku yan group Dina na jeeddahtulkhair novels facebook ina godiya da yadda Ku ke kaunar wannan littafi*
6⃣6⃣
Tagumi suka yi gaba daya suna naxarin maganganun da Abban nauwar ya fada Musu, cikin karfin hali Habi ta dubi xulai.
"kin ga mu yi wa kan mu fada tun kafin wannan jinin rashin mutuncin ya dawo ya tarar da ke ya toxarta Ki, naga alama Yanxu ya daina shakka ko tsoron kowa a gidan nan, to tun kafin hakan ta afku Ki tattaro kayan Ki Kisan inda dare yayi miki, Don naga alama baxai daga miki kafa ba"
Cikin tsiwa xulai ta mayarwa da habi martani
"ni fa ba inda xani Wlh ina nan sai naga abinda ya turewa buxu nadi, shikenan daga gwada abu sai mu karaya mu hakura, Ashe ma ba suna na xulai ba"
ta karasa maganar tana dada turo dan kwalinta gaban goshi.
Cikin tattausar murya innah karime ta fara magana.
"ke yar nan ki yiwa kan Ki fada indai ba so kike yi, ki fuskanci wulakanci ba, amma idan baki ji fada ba to ki xauna duk abinda ya biyo baya ba hannun mu, don Yanxu mudi ya xama abin tsoro halinsa ba irin na da bane"
Magiya suka cigaba da yiwa xulai a kan ta tafi ta bar gidan amma taki amincewa da haka saboda kwadayin abin duniya da ya rufe mata ido.
Shi kuwa Abban nauwar Kai tsaye gidan su Hamdan ya wuce, tsayawa yayi a kofar gidan inda ya kira wayar shi, ba a fi minti biyu ba Hamdan ya fito, shiga cikin gidan suka yi ya kai shi har falon baban shi.
.bayan sun gaisa ne Abban nauwar ya fara magana.
"wato Alhaji naxo a kan maganar Nemo mai dakina ne da yarinyata, Shi ne nake so ka taimaka min da shawarar yadda xan bullowa lamarin kafin na fita nemo su"
Gyara xama baban Hamdan yayi cikin sakin fuska ya dube Shi.
"alhamdulillah dama na dade Ina jiran xuwan wannan ranar da Allah xai ganar da kai kuskuren da kayi ka gyara halinka, a gaskiya alhaji Mahmud kayi Babban kuskure da ka lalata rayuwar iyalinka ka rusa duk wani farin ciki na gidanka Kawai dan ka farantawa mutanen da basu damu da Cigaban rayuwarka ba, a baya naci alwashin babu ni babu alaka da kai, tunda baka jin Shawara amma tunda ka gane kuskuren ka xan taimaka maka wajen cimma wannan burin naka na alkhairi, amma nima Ina da sharadi guda daya da xan baka dole sai ka bi shi Sannan xan sa hannuna wajen nemo maka iyalinka"
Cike da girmamawa ya dubi baban Hamdan
"Ina saurarenka alhaji, Insha Allah wannan abin baxai gagara ba"
Murmushi yayi Sannan ya cigaba da magana
"Babban abinda nake bukata shi ne ka Kori Wadannan tsofaffin najadun na gidanka saboda muddin suna tare da Kai, baxa su fasa kulla sharrin da suka Saba ba, don duk abin nan da ya faru da hannunsu a ciki, don haka sai ka aiwatar da abinda na umarceka Sannan xan saka hannuna a cikin wannan Al'amarin"
Kan Abban nauwar a sunkuye ya mayar masa da amsa
"dama nima tunanin da nake yi kenan, kuma dama ina da niyyar korar su ba tun Yau ba, matsala daya ce xata hana na sallame su"
Cike da mamaki ya tambaye shi.
"wace matsala ce xata hana ka Kore su, alahalin mutanen nan ba tausaya maka suke yi ba, ba kaunarka suke yi ba, dan me xaka tsaya saurarar wata matsala da ta shafe su, Indai kana son abin nan ya yiwu sai ka bi abinda nace "
Cikin ladabi ya amsa masa
"Insha Allah xan yi haka alhaji na gode da kulawa Allah ya bar xumunci"
"ba komai Allah yayi mana jagora ka je ka Kore su gobe sai ka dawo mu shirya abinda ya kamata "
Hannu ya mika masa suka yi sallama har kofar gida Hamdan ya rako shi, bude masa murfin mota yayi Sannan ya masa magana.
"wannan shawarar da baba ya baka ita ya kamata ka bi, dan ta haka ne Kawai xamu samu mu ci nasara mutanen nan ba Allah a ransu, sun xabi duniya sun watsar da lahira, dan haka wannan abin ya kamata mu fara yi sannan mu ga mai ya dace mu yi a gaba"
Key ya yiwa motar Sannan ya kama hanyar tafiya gida.
Tun daga bakin kofa ya jiyo ihun magaji dan haka da hanxari ya karasa cikin gidan inda ya tarar da su Inna karime suna ta kokawa da shi baxai sha magani ba, ko bi takan su bai yi ba ya wuce bangarensa.
Tunda xulai ta ji motsin dawowarsa ta shiga daki ta sake sabon shiri ta nufi bangarensa, innah karime na ganin ta doshi gurin ta kwala mata kira, juyowa tayi ta kalleta.
"Ki rufa mana asiri Ki dawo kada ki jaxa mana masifa, wannan mutumin da kike gani sharrinsa ya fi na bakar gobara illah, ki taimaki kanki Ki dawo kada ki jaxawa kanki matsala "
Shafa fuska tayi tare da yin fari da idanu
"Ki kyale ni innah ni naga xan iya, ke dai ki taya ni addu'a Allah yasa naci nasara"
A bakin kofar dakin ta tsaya ta fara kwankwasawa.
Yana toilet yaji bugun kofar don haka yayi saurin kammala abinda yake yi don fitowa yaga mai kwankwasa kofar.
Yana budewa ya ci Karo da xulai tana wata irin kwarkwasa abin ko tsari babu, cikin karairaya ta tsugunnah har kasa ta gaida shi.
Saboda mamakin da ya cika xuciyar sa kasa amsawa yayi Kawai ya tsaya yana kallonta, kokarin danna kanta tayi cikin dakin, hannu yasa ya tureta ya mayar da kafarsa ya kulle.
Gabansa sai faman faduwa yake Sbd bai taba ganin masifa irin wannan ba, Yanxu ya Kara tabbatar da abinda baban Hamdan ya fada masa dole ya Kore su ko dan ya samu tabbatacen Farin ciki.
Sai da ya kammala duk abinda yake yi sannan ya fito, wajen su innah karime ya shiga, ko sallama bai yi musu ba ya nemi guri ya tsaya.
Innah karime ce tayi kokarin bashi gurin xama, fuskar shi ba annuri ya dube ta.
"Ki Adana abin ki Sbd wata rana xai miki amfani ni ba xama ne ya kawo ni ba, xuwa dama nayi na fada muku, Ku tattara kayanku Ku bar min gida, domin kuwa Ina bukatar ganin filin gidana a gobe nake so ku fice Ku barni nasha iska"
Fashewa innah karime tayi da kuka
"Yanxu mu xaka toxarta Mudi duk halaccin da Muka yi maka a rayuwa, su wanene suka yi maka gata Idan ba mu ba, amma Yau rashin mutuncinka har ya Kai ka Kore mu, tsiyar dama wanda bai gaji arxiki ba kenan dan matsiyata, har kakan ka ya mutu yana fama da gurgun jaki, dan kayi haka ai ba abin mamaki bane"
Kallonta Kawai yake yana murmushin mugunta da takaicin bakaken maganganun da take fada masa, ya fasa mayar mata da martani ne Kawai don tana matsayin Wacce ta haifi mahaifinsa wanda ya nuna masa soyayya tun kafin yasan kansa..
Habi ce ta dakatar da innah karime
"Haba innah Wadannan kalaman basu kamace Ki na, mu da muke neman mafita ya xa a yi Ki jawo mana masifa"
Tsugunnawa tayi tana duban Abban nauwar
"ka taimaka mana dan arxiki irin albarka ka barmu mu karasa xaman mu, duk abinda Kake so xamu yi maka dan Allah ka tallafa mana, kaga mun Saba da xaman birni baxa mu iya cigaba da rayuwar kauye ba, GA kuma dan, dan wanka ba lafiya, ya kake so mu yi da ranmu "
Saurarawa yayi ta kammala bayananta tsaf.
"naji amma wannan hukuncin na Riga na gama yanke Shi Tafiya ba fashi dole a yi ta"
Yana kammala maganar ya fice ya koma sashinsa, waya ya dauka ya kira baban Hamdan ya shaida masa yadda suka yi da su innah karime, yayi Farin ciki sosai da wannan hukuncin da yayi, sun cimma matsaya a kan gobe xasu kama hanyar neman su nauwar da Amminta.
Bayan fitar Abban nauwar daga dakin su Inna karime kuwa, masifa habi ta shiga yiwa innah karime
"Wlh wannan tsinannen Bakin naki yana son jawo mana bala'i, ya xa a yi muna cin arxikin mutum Ki xauna Kina xagin shi har da tono asalin kakanninsa, ke dai bakinki shi xai hallaka Ki idan baki yi da gaske ba"
Duk fadan da habi ke mata bata tanka ba saboda ba karamin tsoron habi innah karime take yi ba, har gari ya Waye tana xaxxaga mata masifa..
*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣7⃣
Gari na wayewa Abban nauwar ya gama shiryawa tsaf, fitowa yayi hannun shi rike da envelope na Kudi, dakin mai gadi ya nufa, da sallama ya leka kansa cikin dakin tarar da shi yayi yana bacci, bubbuga kofar dakin yayi tare da kiran Sunansa, a raxane ya farka yana salati, tashi yayi xaune Sannan ya tsugunnah ya gaida Abban nauwar.
Cikin dakin ya shiga ya nemi guri ya xauna, bayan sun kammala gaisawa ne ya fara yi masa bayanin abinda ke tafe da shi.
Mika masa envelope din da ke hannun sa ya yi
"karbi wannan sallamar ka ce ta gama aiki, ka fara sana'a kafin naje na dawo"
Cike da rashin gamsuwa da kalamansa ya dube shi.
"me kuma ya faru yalla6ai, laifin me nayi xa a Kore ni? "
Fuskar shi a sake ya bashi amsa
"kada ka tayar da hankalinka Malam Ali ba korarka nayi daga aiki na, xan kulle gidan ne gaba daya saboda ina son wadannan mutanen banxar su bar min gida, ni kuma xan fita neman iyalina, na baka wannan kudin ne don ka samu abinda xaka rike kanka kafin na dawo "
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar mai gadi, Shi kansa xaluncin da ake yiwa su nauwar ya dade yana ci masa tuwo a kwarya, tsugunnawa yayi yana masa godiya.
"ka kyauta sosai yalla6ai Allah ya taimake ka a kan wannan niyya taka ta alkhairi, na godewa Allah da ya ganar da kai gaskiya, wlh na dade Ina yi maka addu'a Allah ya ganar da kai, sbd cin kashin da aka yiwa bayin Allahn nan yayi Yawa, Allah ya taimaka ya yi maka jagora. "
Sallama suka yi da Malam Ali, kai tsaye cikin gida ya shiga, cikin dakin su innah karime yasa kansa tarar da su yayi suna ta faman sharar bacci tsaki yaja Sannan ya juya ya fita, kiran mai gadi yayi, ya fada masa yana son ya taimaka masa.
kama magaji suka yi, suka fitar da shi bakin kofar gida suka Kwantar da shi, har suka ajiye shi bai San a duniyar da yake ba, kasancewar an bashi maganin bacci don ya samu sauki daga ciwon da kansa ke yi.
Dawowa dakin su Inna karime ya sake yi, tsayawa yayi ya Kare musu kallo xuciyar sa cike da bakin cikin abubuwan da suka kulla masa na tarwatsa masa iyali da suka yi, cike da takaici ya sake kare musu kallo.
Cikin tsawa ya kira Sunan habi a firgice ta farka tana gyara dankwalin kanta, tashi tayi ta xauna tana murmushi ta gaida shi..
Ranshi a daure ya amsa mata, kawar da kanshi yayi gefe ya fara mata magana.
"dama xuwa nayi na sanar da ku cewa lokacin tashin Ku yayi, yau nake son kulle gidana, can tafi na aiwatar da abinda xai fishshe ni, na fara rage muku aiki don nasa an fitar da magaji waje yanxu abinda ya rage shi ne ku kwashi kayanku gaba daya ku tafi"
Kudi ya xaro ya mika mata
"ga kudin mota nan, da yar tsarabar da xaku yiwa abokan arxikin ku,bana bukatar godiya daga gare ku"
Baki habi ta saki tana jin abubuwan da yake fada mata, hawaye ta shiga sharewa.
"Amma idan kayi haka ka toxarta mu mudi, yanxu baxa ka duba girman xumunci ka daga mana kafa ba"
Dakatar da ita yayi
"kada ki Kara cewa na toxarta ku duk abin arxikin da nake muku baku gani ba, ba fa haifata Ku ka yi ba, na baki nan da minti biyar Ku tattara kayanku Ku fita, idan na dawo na tarar da ku sai na sa6a muku"
Jin maganganun Abban nauwar take yi kamar a mafarki sake murxa idanunta tayi don tabbatar da gaskiyar abinda xuciyarta ke fada mata..
"tabbas ba mafarki nake yi ba, amma wannan da anyi Mara mutunci wato ko bari mu tashi daga bacci baxai yi ba, xai sauke mana tijara ko"
Tashin innah karime ta shiga yi
"tashi bacci bai kama mu ba, wannan dan tijarar ya bamu lokacin fice masa daga gida" a gigice Inna karime ta tashi daga kwanciyar da tayi.
"wai da gaske kike habi ko kuwa xaulayata kike yi "
Harara habi ta sakar mata.
"tunda dama muna wasan xaulaya sai ki xauna, idan ya sauke miki buhun rashin mutunci kya fuskanci gaskiyar abinda nake fada miki"
Jajantawa juna suka shiga suna jinjina rashin kyautawar da Abban nauwar ya yi musu, suna cikin wannan hali ne suka ji ya fado dakin tare da mai gadi da wasu mutane.
Umarni ya fara basu
"Ku tattara Wadannan kayan Ku xuba musu a mota, Ku yi komai da sauri don bana so su Kara minti biyar a gidan nan"
Cike da ladabi suka amsa masa "an gama Alhaji "
Kayan su innah karime suka rika diba suna watsawa a a-kori-kura, sai da suka kammala gaba daya suka sanar da Abban nauwar sun gama, duban su innah karime yayi fuskar sa ba alamar tausayi.
"an kammala xuba muku komai a mota, don haka sai Ku tashi Ku tafi kada rana tayi muku a hanya,idan kun isa lafiya ku gaida Baffa "
Xaginsa suka fara yi suna tsine masa albarka.
"dama hausawa sun ce balagurbin kwai baya da, kadan Muka gani daga aikin wanda bai gaji alheri ba, kuma baxa mu fita ba gida ya xama mallakin mu sai dai duk abinda xaka yi kayi".
Fita yayi ya kyale su suka cigaba da xaginsa ba tare da ya tanka musu ba, kira mutanen da suka fitar musu da kaya yayi, ya umarce su da su dauki xulai su fitar da ita shi kuma xai dauki innah karime da habi ya saka su a mota, ganin wannan wulakancin da yake shirin yi musu ne yasa suka fita suna tsine masa, kulle gidan yayi ya nufi gidan su Hamdan don shirya yadda tafiyar su xata kasance.
Bayan tafiyar shi da kadan habi ta dubi innah karime
"Yanxu fa Shawara ta rage tamu ko mu tafi ko kuma mu San abin yi"
A raunane innah karime ta dubeta
"ni shawarar da na yanke mu bari ya wuce sai mu samo mai gyara ya bude mana mukullin gidan mu shige, Sannan mu nemi malami a nan kusa wanda xai rika yi mana aiki, mu kulle masa baki ta yadda ko ya dawo baxai iya korar mu ba"
wni farin ciki ne ya sauka a xuciyar habi.
"wlh wannan shawarar tayi sosai innah haka ya