Showing 66001 words to 69000 words out of 111837 words

Chapter 23 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

duk yadda suke tsoron doctor hakan bai hana su fadar duk abinda suka yi niyya ba, shiru yayi ya kyale su saboda a yau dai ba shi da bakin magana tunda aka taba mai gayya mai aiki.


daga Hajiya yayi ya komar da ita gefe guda, saboda dakuwar da tayi bata iya cewa komai duk jikinta ciwo yake yi.


komawa kan Nauwar yayi inda ya fara bata agajin gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, hawaye ta shiga xubarwa shi kuwa doctor sai hakuri yake bata yana lallashinta.


Cikin kuka take masa magana.
"doctor na gode da taimakon da kayi min, amma wlh baxan sake kwana a gidan nan ba, da kabari da wannan gidan duk daya ne a wajena, tunda naxo bayin Allahn nan basu bar ni na huta ba, na tabbata idan na cigaba a xama wata rana sai sun kashe ni da duka"


ummy ce taxo ta tsaya a kansu tana masifa.
"ai ni baxan so ki bar gidan nan ba, sai mun gama axabtar da ke mun ramawa mahaifiyar mu abinda Mahaukaciyar uwarki tayi mata, wannan kadan ki ka gani daga cikin axabar da muka fara gana miki"


feenah da sauran kannen doctor ne suka shiga dakin su Nauwar suka fara watso musu yan tsummokaran su, xuciyar doctor kamar ta fashe saboda bakin ciki, yasan ko yayi musu magana baxa su fasa ba, sai da suka gama watso kayan gaba daya, sannan suka kulle dakin.


cike da rashin kunya suke magana.
"mu ga wanda xai xo ya sake bude dakin nan ya saka wasu yan iska a ciki"


Hajiya na gama hutawa daga axabar dukan da tasha a hannun Ammi, mikewa tayi ta fara xaxxagawa doctor bala'i.


"baka isa na sake kwana gida daya da mahaukaciya ba, yanxu nake so ka tattara ka fitar min da su, idan kuma baxa ka iya ba, xan yi aikina da kaina"


hakuri ya shiga bata, tare da nuna mata illar wulakanta bil Adama amma saboda idanun Hajiya sun rufe sai tayi watsi da maganar sa.


su feenah tasa suka kinkimi Nauwar suka jefata waje tare da kayanta, ita kuma Ammi tasa doctor ya kamata ya fitar da ita, suka mayar da kofa suka kulle.


godiya Nauwar ta yi wa Allah da ya raba ta da gidan bala'i.


cikin tausayawa doctor ya dube ta
"kiyi hakuri bisa taimakon da na baki wanda ya xamo mana matsala ni da ke, ki kaddara komai ya same ki daga Allah ne, ba a son raina xaki bar gidan ba, amma saboda an fi karfina an rinjaye ni, haka xan kyale ki ba dan ina so ba, kada ki manta da ni a rayuwar ki, duk inda nake xan kasance mai yi miki addu'a Allah ya hada ki da mutane na gari wadanda xasu kula da ke"
compliment card din shi ya xaro ya mika mata.
"karbi wannna ki rike dan Allah kada kiyi wasa da shi, duk lokacin da kika samu nutsuwa kika koma gida, ki kira daya daga cikin numbers dina, Insha Allah xaki same ni, wannan tafiyar baxa ta yanke alakar da ke tsakanin mu ba, fatana ki kula da kan ki, ki kare mutuncin ki a duk inda kika kasance"ya karasa maganar yana share hawaye.


saboda kukan da Nauwar ke yi ta kasa cewa da doctor komai, saboda a dan xaman da tayi da doctor ya matukar shiga ranta.


Bayan doctor aka daka, gaba daya suka mai da hankalin su ga wanda yayi dukan, Hajiya ce taja wuyan shi cikin xafin rai take masa magana.


"bin ta xaka yi ne uban tausayi, shige mu tafi kafin na tsine maka ka bi duniya, ke kuma ki tashi ki bar nan dan idan na dawo na tarar da ke sai ranki ya baci"


doctor na kuka ta ixa keyar shi har cikin gida ta mayar da kofa ta kulle.


Tashi Nauwar tayi suka bar kofar gidan, suka kama hanyar tafiya kasuwa.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*


*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆




*masoya bansan da wane kalmomi xan gode muku ba saboda kaunar da ku ke nunawa wannan littafi, ina godia da kulawar ku gare ni, idan da hali xan kira sunan ku daya bayan daya a next post da xan yi*


6⃣1⃣




Har cikin daki ta shigar da doctor, xaunar da shi tayi gami da dukan kansa.
"ko xaka yi kuka hawayenka ya kare baxan bari ka bi wannan tsintacciyar magen ba, ni fa lamarinka ma mamaki yake bani Abdallah, daga ganin yarinya baka san abinda ya rabo ta daga gida ba kawai dan ta shirya maka karya da gaskiya, kai kuma ka hau ka xauna saboda rashin lissafi, wa ya sani ma ko su suka yi wa wata asiri abin ya koma kan su, amma duk ka bi ka damu xuciyar ka har da kukan rabuwa da ita, ko dai ba haka ta bar min kai ba???"


dago jajayen idanunsa yayi ya kalleta ya cigaba da share kwalla, saboda bakin cikin da ya mamaye xuciyar sa gaba daya ya kasa magana, tunanin Nauwar kawai yake yi da halin da xasu tsunduma bayan rabuwar su, ji yake kamar ya bi ta ya dawo da ita, tsoron tsinuwar Hajiya ne kawai ya hana shi tafiya.


kifa kanshi yayi a kasa ya rika kuka tamkar yaron goye, a ranar gaba daya bai rintsa ba, saboda bakin ciki.


Yau kusan kwanan su Nauwar biyar da tafiya, gaba daya Hajiya ta rasa kan Abdallah baya kwana a gida baya cin abinci sannan ya daina yi wa kowa magana, sai dai idan yana da abinda xai dauka ya shigo ya biya bukatar sa yana gamawa kuma xai fice,baxai sake dawo wa ba sai wata bukatar ta kawo shi, hankalin Hajiya ya tashi sosai saboda wannan sabuwar dabi'ar da doctor ya bijiro mata da shi. hankalinta a tashe tasa driver ya dauketa ya kai ta Asibitin da doctor yake aiki, tambaya tayi a nuna mata Office din da yake.


da sallama ta shiga wajen, samun shi tayi ya dora kan shi bisa tebur hawaye na gangarowa daga fuskarsa, cikin tsananin nuna damuwa ta nemi guri ta xauna, cikin kulawa ta dube shi.


"Abdallah wai me ke damunka ne kwana biyu, ko duk a cikin damuwar rabuwa da yarinyar da baka san asalinta bane? ya kamata kasan inda kanka yake, a kan wata shashar yarinya xaka jefa rayuwarka a garari, har ka daina walwala ka bar gida ka daina kula kowa, wato kana nuna cewa yarinyar ta fi mu daraja a idonka ko, to wlh tun wuri ka farka daga bacci mai nauyin da ya dauke ka, kafin na ci maka mutunci, dan baxan yarda da wannan shashancin a gidana ba"


Hannu yasa ya share hawayen da ya cika idonsa, cikin sassanyar murya yake mata magana.


"baxan taba samun kwanciyar hankali ba matukar ban san inda rayuwar yarinyar nan ta shiga ba, shikenan nan kawai dan kun ga mutum a haka sai ku munana masa xato, ku ka sani ko xaluntar su aka yi, ba su suka xalunta ba, kun yi kuskuren wulakancin da ku ka yi musu, kuma na tabbatar Allah baxai kyale ku ba, dan kaga bawa a cikin wani hali ba shi yake nuna kana da damar da xaka cutar da shi ba, saboda baka san baiwar da Allah yayi masa ba, ni a yanxu baxan iya dawo wa gidan nan ba, alhalin ina ganin dakin da bayin Allahn nan suke ciki, saboda xai rika tayar min da ciwon abinda aka yi musu ne na rashin kyautawa, kawai ku yi hakuri ku kyale ni, dan nasan nima na kusa shiga wani hali, tunda ku ka toxarta su a gaban idona" ya karasa maganar wasu sababbin hawaye suna xuba a fuskarsa.


hankalin Hajiya ya tashi sosai da jin maganar doctor dan tasan indai ya furta magana haka take, baya canjawa.


cikin rarrashi take masa magana.


"Haba yaya babba ya xaka yanke wannan danyen hukuncin, bai kamata a matsayinka na babba ka rika haka ba, shikenan kai baxa ka koyi hakuri ba duk abinda ya faru ba, sai kace sai ka dau mataki, idan kace ka fita daga gidan nan wa ka bar mana ya kula da mu, kuma yarinyar nan nasan yanxu sun kai inda suka kai, a ina xamu nemo ta, ni da ina da halin da xan ganta, da na dawo da ita ko dan cikar farin cikin ka, kayi hakuri ka dawo gida ka kuma dawo da walwalarka kamar da"


doctor yaji dadin maganar Hajiya yasan da xai kara ganin su Nauwar ya dawo da su baxa a sake yi musu irin wulakancin da aka yi musu a baya ba.
cikin girmamawa ya fara yi mata magana.


"ba komai Hajiya ta wuce, amma ki ja kunnen yaran nan da kyau, daga yanxu kada su sake ganin mutum su wulakanta shi, indai suna haka wata rana xasu neme ni su rasa baxa a sake ganina ba"


"Ai baxa a yi haka ba yaya babba, yanxu dai yaushe xaka dawo"


sosa keya yayi ya dubeta
"sai gobe Hajiya"
xaro idanu tayi.
"Haba yaya bai kamata ka xauna a nan ba har sai gobe kayi hakuri ka dawo yau"


"To shikenan xan dawo anjima"


farin ciki ne ya bayyana a fuskarta.
"yauwa ko kai fa, Allah yayi maka albarka"


amsa mata yayi da "Ameen"
tashi tayi ta nufi gida, tana xuwa ta fadawa su feenah yadda suka yi da doctor, sannan tayi musu fada sosai, abinci mai rai da lafiya tasa suka dafa masa saboda farin cikin dawowar sa.


A bangaren su Nauwar kuma, tunda suka bar gidan su doctor suke tafiya ba dare ba rana, ba karamin galabaita suka yi ba, saboda tsananin yunwar da suke ji, ga gajiya duk inda suka tsaya ba a barinsu su xauna saboda tsoron su da ake ji, gaba daya sun fita daga kalar su ta mutane saboda dauda, ga bakin cikin da ya cika xuciyar Nauwar tun tana kuka har ta hakura ta jure saboda babu maganin da kukan xai mata.


duk tsawon lokacin nan da suke tafiya basa samun abinda xasu kai bakin su, saboda babu kudi a hannun su,sai dai nauwar tayi bara idan mutane sun ga Allah su bata, wasu kuma xaginta xasu yi su koreta.


suna cikin tafiyar ne suka iso cikin gari, inda suka iske wata makarantar Almajirai, samun guri suka yi suka tsaya gudun kada su xauna a tashe su, tun lokacin da malamin Almajiran nan wanda Ake kira da malam Haruna yaga Ammi ya tsura mata ido ya kasa dauke kallonsa daga gareta, amma bai ce dasu komai ba, har xuwa lokacin da aka tashi daga makarantar aka sallami Almajiran don su je su nemo abinci.


Har aka tada sallar magariba su nauwar na wajen, sai da malam ya gama addu'a tsaf sannan yaxo ya same su, sallama yayi musu.


cikin damuwa Nauwar ta amsa masa sallamar, cikin kulawa yake tambayar su.


"lafiya na ga kun xauna a nan, tun muna makaranta na gan ku nayi xaton xaku tafi ne amma gashi naga har yanxu ba ku da niyyar tafiya"


kwalla ce ta cika idanun nauwar ta dube shi.


"ba mu da gurin kwana kuma muna cikin damuwa shi yasa muka xauna a nan"


tausayin su ne ya kama shi, kallon Ammi yayi ya girgixa kai sannan ya dubi Nauwar.
"wannan wace ce?"


"mahaifiyata ce" ta amsa masa kanta a sunkuye


ajiyar xuciya ya sauke, sannan ya cigaba da magana.
"akwai al'amura masu girma a tattare da wannan baiwar Allah, sannan tana tare da bakaken Aljanu kafirai, kafin na cigaba da yi miki bayani xan tambaye ki, wai kuwa yanxu tana sallah"?


gyada masa kai tayi sannan ta cigaba da magana
"bata sallah yanxu kuma da ba haka take yi ba"


cikin tausayawa ya sake dubanta.
"An yi mata asiri ne saboda a cimma wata manufa, kuma an hanata sallah ne saboda kada ma ta samu kusanci da Allah ya bata lafiya, riko hannuta ki tashi ku shiga gidana akwai taimakon da xan baku"


Tashi suka yi, suka shiga cikin gidan Malam Haruna.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆






6⃣2⃣






A soro Ammi ta da'kire ita a lallai baxa ta shiga cikin gidan ba, Addu'a malam Haruna ya shiga tofawa Ammi nan da nan, ta fara fita daga hayyacinta, wani hayaki ne ya rika fitowa daga bakinta tana fesawa malam, tana kawo masa duka, bai kakkauta da yi mata addu'a ba har sai da ta daina fitar da hayakin, ta koma yin wani ihu mai ban tsoro, duka ta shiga kawo wa malam, da kyar aka samu ciwon nata ya lafa, daukan Ammi suka yi suka karasa cikin gidan.


Da sallama suka shiga,tarar da matar malam Haruna suka yi tana ta faman tankade, tana ganin su ta mike tana musu barka da xuwa, daki ta shiga ta dakko musu tabarma ta baxa musu a tsakar gida, taimakawa tayi a ka sauke Ammi aka kwantar da ita, ruwa ta kawo musu, sannan ta koma ta cigaba da aikinta.
gaisheta Nauwar tayi sannan malam haruna ya fara mata bayani.
"baki ne na kawo miki, xasu xauna tare da mu xuwa wani lokaci, xa a yi wa wannan baiwar Allahn magani idan an dace shikenan, amma tabbas tana tare da bakaken shaidanu"


fuskarta a sake ta bashi amsa.
"shikenan malam Allah ya taya ni rike su Amana, ita kuma Allah ya bata lafiya"


amsa mata yayi da "Ameen"


Tashi yayi ya fita, Nauwar ce ta taso ta karbi aikin ta fara taya matar malam suna yi suna hira, kamar sun dade da haduwa.
bayan sun kammala suka dora girki, suna gama girkin ne aka xubawa Nauwar taci ta koshi.


gidan malam Haruna gida ne karami, dauke yake da dakuna guda biyu, ciki da rumfa sai kuma falle daya, a falle dayan aka sauki su Nauwar aka saka musu katifa. shekarar malam Haruna ashirin da aure tare da matarsa Hajara amma Allah bai bashi haihuwa ba.


A wannan ranar da su Nauwar suka sauka a gidan malam, gaba daya basu yi bacci ba, saboda tashin da aljanun Ammi suka rika yi cikin dare, kokarin fita ta rika yi xata bar gidan tana ihu tana komai sai da kyar aka samu kanta.


washe gari ma abinda ta rika yi kenan, wannan dalilin yasa malam ya kira Almajiransa aka saka Ammi a gaba ana mata karatu, ihu ta rika yi har sai da ta fita hayyacinta sosai, saboda an tabo mata manya manyan kwankwaman kanta.


rukiyya aka fara mata da kyar aljanun suka fara magana.
cikin sarkewar murya ta fara bayani.
"turo mu aka yi mu rusa mata rayuwa, kuma sai mun aikata abinda aka umarce mu saboda an ba mu abinda muke so, kullum sai an bamu jini mun sha dan haka mu da ita sai dai mutuwa ta raba mu"


duk yadda malam yayi da aljanun nan a kan su fita, su bar jikin Ammi 'kememe suka ki fita, idan har suna so a fita sai an rika yi musu abinda suke so,wanda kuma hakan shirka ne, wannan dalilin yasa malam ya hakura saboda baya son ya sabawa Allah saboda magani.


A daren da malam yayi magana da aljanun Ammi shi ma bai kwana lafiya ba, cikin mafarki suka xo masa suka buga masa warning cewa duk lokacin da ya kara shiga cikin maganar maganin Ammi sai sun hallaka shi, yana addu'a ya farka, kuma ya ci alwashin tsayawa tsayin daka wajen nema mata magani har xuwa lokacin da hankalinta xai dawo jikinta.


********************


Bayan komawar Baffa Dan batta kuwa, kullum sai Abban Nauwar ya kira shi ya gaida shi yayi masa ya jiki, sannan duk abinda Baffa yake bukata yana kawo masa, tun kafin ma ya tambaye shi, saboda tunda malam Abdullahi ya fara bawa mahmud maganin sihiri ya fara dawowa dai-dai, godiya Baffa yake yi wa Allah saboda ya fara dawo da dansa kan hanya.


wata rana da misalin karfe takwas na safe Abban Nauwar ya dakko kayan maganin da aka bashi, xubawa yayi a kofi yayi addu'a sannan ya fara sha, sallama aka yi aka shigo dakin.


innah karime ce tsaye ta bude baki, tana kallon Abban Nauwar tana salati.


"Mudi me xan gani waye kuma ya baka wannan masifar kaxo kana dannawa cikin ka"


hannu tasa ta dauki maganin tana jujjuyawa.


"magana nake maka fa waye ya baka"
tsare shi tayi da ido tana huci, shi kuma duk ya diririce kamar karamin yaro, samun guri tayi ta xauna tana kallonsa, gaba daya tunaninta ya kwance bata taba xaton Mahmud xai nemi maganin abinda suke masa ba, hankali a tashe ta sake duban shi.


"wai me kake so ka xama ne Mudi, dan neman masifa ka rika shan magani, ban fada maka cewa,duk wanda ya baka magani kada ka karba ba sai kaje an shayar da kai guba, saboda Allah ya axurtaka, duk abinda na fada maka baka ji ko"


cikin fushi ya dago ya kalleta.


"baxan ji ba, ke uwata ce ko ubana, kin manta irin kiyayyar da kika nuna min a baya sai yanxu xaki ce kina kaunata, kina tunanin duk abinda kike yi min bana fahimta ne, to duk ina ganewa da Allah kawai na bar ku. kuma ki bani kayana da kika kwasar min dan kin san mahaifina baxai taba bani abinda xai cutar da ni ba"


cike da mamaki innah ta dube shi lallai magani ya fara aiki tunda har ya iya furta mata haka ba kunya ba tsoro.
hawaye ta shiga sharewa.


"yanxu ni kake fadawa haka Mudi saboda ubanka ya saka ka a daki yayi maka hudubar banxa, har xaka samu bakin xagina ko, wlh tunda ka taba ni sai ka gane kuskurenka, xaka ga abinda xai same ka"


"naga alheri me jiya tayi ballantana yau, kiyi duk abinda kika ga dama"


ficewa tayi tana share hawaye, gaba daya bakin ciki ya cika xuciyar ta.










*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*ALHAMDULILLAH MASOYA NA GODE DA KAUNAR KU DA ADDU'O'INKU GARE NI, NAJE ENUGU NA DAWO LAFIYA, ALLAH YA BAR XUMUNCI*


*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki, AYSHA ABUBAKAR SHAGARI (BABY) na gode da kaunar Ki gare ni Allah ya bar xumunci, da fatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login