Showing 54001 words to 57000 words out of 111837 words
Chapter 19 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
a matsayin ka na Babban mutum Kazo gidan mata masu xaman kansu kace xaka nemi aure. wannan ai kuskure ne, hausawa sun ce kwarya ta gari tana ragaya, Yanxu ka daga mata kafa ta biyaka kudinka a hankali
tunda dama bariki ta gaji haka, garin banxa ne ya tafi a faraufarau din Wofi, don haka sai ka rungumi na Annabawa"
Duk mutanen da ke wajen babu wanda ya goyi bayan a Kai Amarya wajen yan sanda,Kowa hakuri yake bawa Alhaji talle Sannan suka saka shi a gaba ya fita ya bar gidan"
*****************
Yau da sassafe baffan Mahmoud ya shirya xuwa wajen dansa,saboda ya dade bai xo wajen Mahmoud ba, shi ma kuma gaba daya ya dauke kafarsa Daga Dan batta, baya xuwa baya yi masa aiken komai.
kasuwa ya shiga Don siyowa yan jikokinsa mangwaro da gyada, bayan ya siya ya nufi Tasha don Hawa motar Kano.
Cikin kankanin lokaci suka shigo Kano inda ya samu adaidaita sahu ya kawo shi gidan Mahmoud.
A Bakin kofa ya iske mai gadi yana ganinshi ya tsugunnah har kasa ya gaishe Shi ya karbi kayan da ke hannunsa ya yi masa rakiya har cikin gida.
Sallama suka rika yi a Bakin kofar falon babu wanda ya amsa musu,duk da cewa suna Jin hayaniyar jama'a, sai da aka dauki mintuna Sannan innah karime ta fito, tana ganin baffan ta hade rai kamar Wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa, har kasa ya tsugunnah xai gaisheta, dakatar da shi tayi.
"bana bukatar gaisuwarka tauraruwa mai wutsiya ganinka ba alkhairi ba, wane munafuncin ne kuma ya kawo ka, Tunda Muka zo garin nan saboda kana ji da kininbibi baka biyo mu ba sai Yanxu, to me kaxo yi? "
Kansa a sunkuye ya bata amsa
"dama naxo naga wannan yaron ne da yayansa saboda na Kwana biyu ban gansu ba, Sannan kuma ina so Habi ta koma dakinta saboda Yanxu ina dan fama da rashin lafiya, bana samun mai kulawa da ni"
Wata shu'umar harara ta watsa masa
"to naji abinda ka fada, kana ta xuba kamar wani Dan Kanya, ina san ka sani Habi baxa ta koma cikin wahala ba, muna nan muna Jin dadin rayuwar mu, Allah ya kashe ya bamu, don haka ba inda xata je muna nan a tare"
Shigewa tayi daki ta barshi tsugunne, bayan lokaci kadan sai gata da tabarma da abinci watsa masa tabarmar tayi, shi kuma abincin ta ajiye masa shi.
"ga tabarma nan ka xauna kafin Dan naka ya dawo, don baxa ka shigar mana daki ba ko da wata jarabar kaxo mana, wannan abincin kuma kaci dama nasan shi ya kawo ka sbd an dade ba a hadu da shinkafa ba"
Shigewa daki tayi ta rufo kofa ta bar Baffa xaune yana hawayen Bakin ciki, da bai san innah karime ce mahifiyarsa ba, da cewa xai yi ba ita ta haife shi ba, saboda yadda take nuna masa kiyayya kirikiri.
Maigadi ne ya ganshi yana kuka don haka ya nufo wajen sa da sauri ya fara bashi hakuri.
" kayi hakuri baba, Wlh da xan fada maka irin abubuwan da suke faruwa a gidan nan da kayi mamaki, ka share hawayenka komai ka barwa Allah xai yi maka magani"
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
09077389712
5⃣3⃣
Share hawaye yayi ya dubi mai gadi
"na gode Malam Ali Insha Allah baxan Kara tayar da hankalina a kan haka ba."
Bude masa kwanon abincin yayi
"kaci abincin nan baba kada ya huce"
Kallonsa yayi ya girgixa masa kai, "bana sha'awar komai Malam Ali Bakin ciki ya gama cika min cikina"
Tausayin baffan Mahmoud ne ya kama mai gadi
"kayi gefe da komai baba Insha Allah komai mai wucewa ne"
Hawaye Baffa ya cigaba da sharewa saboda kukan ne Kawai xai saukaka masa damuwar da yake ciki. Duban Malam Ali yayi
"wai ni ina matar gidan nan da yaranta ne Malam Ali tunda naxo fa banji motsin su ba, ko sun tafi unguwa ne"
Shiru Malam Ali yayi ya rasa amsar da xai bawa Baffa,saboda Idan ya fada masa basa nan ba karamin tashin hankali xai shiga ba, Don haka ya ki bashi amsa ya kawo masa wata hirar. Duk da wannan dabara da Malam Ali ya yiwa Baffa sai da ya sake maimaita masa irin wannan tambayar, dabara ce ta fado masa yace sun tafi Makaranta, haka suka xauna har wajen sallar La'asar suna hira suna jiran dawowar Abban Nauwar.
Bugun kofa suka ji dan haka Malam Ali ya tashi Don bude kofar, Habi ce tare da magaji suka dawo daga unguwa, tana ganin Baffa tayi turus taja da baya
"me xan gani, mafarki nake ko idona biyu"
Magaji ne ya karbi zancen idon ki biyu Don haka sake bude su Idan Kina ganin mafarki kike yi"
Wucewa magaji yayi ya shige daki ko kallon Baffa bai yi ba, ballantana ya samu arxikin Gaisuwa.
"Lallai annoba ta xiyarce mu har gida, me kuma kaxo yi nan gidan Malam, me yasa Kai ba kada hakuri ne, duk kokarin da yaron nan yake yi a kanka sai ka biyo shi har gida maula,salon ka zubar mana da mutunci ya gaji da kulawa da mu, gaskiya Malam baka kyauta mana ba wlh"
Sakin baki Malam Ali yayi yana ganin ikon Allah tunda yake bai taba ganin irin wannan rashin da'ar ba sai yau.
Hawaye ne ya cigaba da sauka a fuskar Baffa, saboda Bakin cikin da ya mamaye xuciyar sai da yayi da na sanin xuwansa gidan , ga Shi bai samu ganin Wadanda Yaxo dominsu ba, tashi yayi ya saka takalminsa xai fita ya bar gidan, da sauri maigadi ya tare shi yana bashi hakuri, Amma Sam yaki hakura ya fita.
Tare shi yayi yasha gabansa.
"kayi hakuri Baba baxan bari ka fita ranka a bace haka ba, Yanzu xamani ne na lalura idan wani abin ya sameka fa, kayi hakuri ka jirayi xuwan mai gidan, tunda domin shi dama kaxo, kaga ba dadi idan baka hadu da shi ba"
.saboda kukan da Baffa ke yi ya kasa magana ma gaba daya, baki ya cigaba da bashi amma yaki komawa cikin gidan, suna tsaye a wannan halin suka ji karar mota, saurin waiwayawa mai gadi yayi da sauri
ya tafi bakin motar ya tsugunnah..
"Sannu da xuwa ranka ya dade, Ga Baffa nan Yaxo tun daxu yake jiran xuwanka"
Da hanxari Abban nauwar ya fito daga motar ya fito, wajen Baffa ya nufa, Tsugunnawa har kasa yayi
"Sannu da xuwa baffana"
Kukan da Baffa ke yi shi ya hana shi amsa sallamar, shirun da yaji ne yasa ya dago kai don ganin halin da yake ciki.
Hawaye yaga na sauka a kan kuncin Baffa
Tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa "lafiya naga kana kuka baffana, me yake damunka ko jikin naka ne"
"ka Kwantar da hankalinka Mahmoud lafiyata kalau kukan Farin cikin ganinka nake yi shi yasa".
Murmushin karfin hali yayi ya sake Duban baffanshi
"nasan ba haka bane baffana Kawai ka Boye min ne saboda kada na shiga damuwa amma a xahirin gaskiya Akwai abinda yake damunka"
"na fada maka babu komai Mahmoud"
Kiran Malam Ali yayi ya fara tambayarsa abinda ya faru da baffanshi, bayani yayi masa dalla-dallah, a fusace ya wuce xai shiga gidan.
Kiran sunan shi Baffa yayi
"kada kace xaka yi tashin hankali a kan wannan abin, kamar yadda na barwa Allah Kaima kayi hakuri ka barwa Allah, innah mahaifiyata ce baxan iya bari ka yi mata abinda bai kamata ba, kayi hakuri ka kyale su Duk abinda mutum yayi Dan kansa"
Dawowa yayi ya Rike hannunsa suka shiga cikin gidan.
Ko sallama bai yi ba, yasa kafa ya doki kofar falon, yana shiga falon su innah karime suka Mike suna masa Sannu da xuwa
"Barka da zuwa Alajin Allah Ashe har ka iso" bai basu amsa ba ya wuce sashinsa
Mamaki ne ya kama baffan Mahmoud wai Mahmoud din da aka tsana ne har ake kiransa da Alajin Allah~ Lallai duniya ba gaskiya"
Suna shiga daki ya kunnawa Baffa AC ya shiga kitchen da kansa dan hada masa abinci, bayan ya kammala ya kai shi bandaki ya umarce Shi da yin wanka.
Yana fitowa ya bashi kaya na alfarma ya saka Sannan suka fara cin abincin suna yi suna hirar Yaushe gamo. A cikin hirar ne ya jefo masa tambaya
"wai ni ina matar gidan nan da yayanta ne tunda naxo fa banji motsinsu ba, na tambayi mai gadi yace suna unguwa, gashi har kusan karfe takwas basu dawo ba, kuma ban ji kayi cigiyarsu ba, anya lafiya kuwa Mahmoud"
Wannan tambayar ba karamin tayar masa da tabon da ke ransa tayi ba, sunkuyar da kansa yayi saboda ba shi da amsar da xai bawa Baffa, hawaye ne suka rika sauka a kan kuncinsa.
cikin tashin hankali Baffa ya dube shi lafiya kake kuka, ko dai sakin yarinyar nan kayi.
inda inda ya fara yi, saboda gaba daya ya mance inda su Nauwar suke ya manta da rayuwarsu tunda suka tafi bai sake tunawa da su ba.
ganin kukan da yake yi ne, yasa Baffa ya kyale shi da maganar ya kudurce a ransa washe gari xai samu mai gadi ya tambaye shi abinda ke faruwa.
kwana Baffa yayi yana tunanin su Nauwar,shi kuma mahmud na jin xafin abinda ya yiwa su Nauwar, amma kuma baxai iya yin komai a kai ba.
Washe gari da sassafe Baffa ya fita wajen mai gadi, samun shi yayi yana laximi don haka ya jira shi ya kammala sannan suka gaisa
"dama xuwa nayi mu tattauna dangane da matar gidan nan tunda naxo ban ganta ba banga Nauwar da fu'ad ba, na tambayi wannan yaron ya hau kuka ya kasa bani amsa, ko dai sakinta yayi, shi ne yake boye min, dan Allah kada ka rufe min komai ka fada min gaskiyar wannan al'amarin.
shiru mai gadi yayi na wasu yan lokuta sannan ya dago ya dubi Baffa.
"tunda ka roke ni na fada maka gaskiya Insha Allah xan fada maka baba, babu abinda xan boye maka"
"Abubuwa da dama sun faru a gidan nan wanda nasan baka sani ba, kuma ba a sanar da kai ba, amma ina rokonka dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka bata ranka dangane da abinda xan fada maka"
tsayawa yayi yana sauraren sa.
"Baba Allah ya yiwa fu'ad rasuwa sakamakon rashin lafiya"
dafe kirji Baffa yayi" subhanallah yaushe, wlh basu fada min ba"
Ai har an dan kwana biyu "baba
kwalla Baffa ya shiga sharewa
"kayi hakuri Baba addu'a xaka yi masa Allah ya gafarta masa"
addu'a Baffa ya shiga yiwa fu'ad yana roka masa rahma. tambayar mai gadi ya shiga yi
"to ina matar gidan da ragowar yaran gidan?"
kamar mai gadi baxai bashi wannan amsar ba, amma saboda ya yi masa alkawarin fadar gaskiya, sai ya danne xuciyarsa ya fara yi masa bayani
"uwar yaran ta haukace, shi ne mai gidan nan ya kore su"
mikewa Baffa yayi yana salati, nan da nan kansa ya rika juyawa, ya fadi kasa sumamme.
*Jeeddahtulkhair😘*

addu'a Baffa ya shiga yiwa fu'ad yana roka