Showing 69001 words to 72000 words out of 111837 words
Chapter 24 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
kin isa sokoto LaFia*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣3⃣
Sashin su ta nufa tana kuka, Duk maganganun da Abban nauwar ya fada mata sun dagula mata lissafi, fadawa kan katifarta tayi tana kuka, a daidai wannan lokacin ne habi ta shigo dakin samunta ta yi a wannan halin, cikin nuna damuwa take tambayarta.
"lafiya na ganki haka innah me ke faruwa? "
Cikin karfin hali ta dago ta dubeta
"Habi muna cikin masifa a gidan nan dole sai mun tashi tsaye a kan mudi, abinda muke masa ya fara cika Shi, dole ne mu koma wajen gobe da Nisa ya sake sabon lae Idan ba haka ba kuma xa a yi babu mu"
Cikin mamaki habi ta dubi innah
"hmm dama ai nasan xa a rina wai an saci xanin mahaukaciya tunda tsohon banxan nan Yaxo ai nasan baxa a kulla abin arxiki ba, Yanxu dabara ta rage namu mu shirya Kawai gobe mu wuce mu nemi mafita "
Hirar da suka rika yi kenan har xuwa lokacin da magaji ya dawo Daga yawon sa ya tarar da su yayi suna tattaunawa, wajen xama ya samu suka fara xayyana masa yadda suka yi da Abban nauwar.
"Dama ai Kune baku fahimci inda aka dosa ba Amma ni na dade da gane cewa halayyar mutumin nan ta canja,tunda wannan tsohon tsiyar Yaxo ya lalata mana xama, idan fa bamu yi da gaske ba xamu rasa wannan gidan, da dukkan abinda muke son mu mallaka a rayuwa"
Cikin nutsuwa habi ta dube Shi
"gaskiya ne magaji Yanxu ya Kake ganin xa a kulla wannan tafiyar? "
Gyara xama yayi ya dubeta.
"gobe da sassafe Ku bani kudin mota Ku kwatanta min wajen da bokan yake xan je muku, xa a sake kulla musu wani bala'in da basu isa su kauce masa ba"
Farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu Jin an ambaci xa a kulawa Abban nauwar masifa, haka suka cigaba da hirar sharrin da xasu yi suna ta Farin ciki abin su.
Bayan fitar innah karime Daga dakin Abban nauwar kuwa, kur'ani ya jawo ya shiga karantawa yana addu'ar Allah ya bashi kariya Daga dukkan abinda xai same Shi.
Yana kammala addu'ar wani Bakin ciki ne ya mamaye xuciyar sa, tunanin nauwar da Amminta ne ya xiyarci xuciyar sa, ji yake kamar xuciyar sa xata tsage saboda takaicin halin da ya jefa su a ciki, wayarsa ya jawo ya kira baffan shi, hawaye na kwarara a fuskarsa yake masa magana, bayan sun gaisa ne yake fada masa abinda yake damunsa, rarrashinsa ya shiga yi.
'kayi hakuri Mahmud Insha Allah suna kyakkyawan hannu babu abinda xai same su, ka Kwantar da hankalinka tunda muna addu'a Allah baxai toxarta mu ba, fatana dai ka rika hana idonka bacci kana fadawa Allah nima xan taya ka da addua "
Sallama suka yi ya kashe wayar, Kwantar da kanshi yayi bisa kujera ya lumshe ido a Yanxu babu abinda yake muradin gani sama da iyalinsa, wata kaunarsu ce ta mamaye masa xuciya, ji yake Duk abinda ya faru tamkar mafarki.
A daren gaba daya bai runtsa ba salloli ya rika yi yana add'ar Allah ya bayyana masa iyalinsa har xuwa wayewar gari.
Bayan ya kammala shiryawa ya fito don tafiya aiki, a falo ya Samu su innah karime suna ganin shi suka xube har kasa suna gaishe Shi, ko kallonsu bai yi ba ya wuce, bayan ya Kai Bakin kofa ne ya juyo ya kalle su.
Babu walwala a tare da shi yake musu magana.
"Daga Yau sai yau, kada na sake fitowa na ganku xaune a falo, bana bukatar na rika ganin ku a nan, Ina so ku taimaka ku rika nesa da ni, don halin Yanxu na tsane ku"
Yana kammala maganar ya fice don baya bukatar Jin amsar da xasu bashi.
Ba karamin tsoro Al'amarin Abban nauwar ke basu ba Sbd gaba daya rayuwar shi ta fara canjawa ya fara dawowa hayyacinsa, gaba daya sun kasa magana sai magaji ne ya yi karfin hali ya dube su.
"ba mu ga ta xama ba fa, Ku tashi mu tafi inda xai kawo mana mafita "
Idanun innah karime cike da kwalla ta dubi magaji,.
"ni Wlh baxan iya xuwa ko'ina ba Al'amarin yaron nan so yake ya saka ni hawan jini, Shi yasa hausawa ke cewa mai laya kiyayi mai xamani, yau naga sharrin xamani da idona"
Gefen xani habi ta fara kwancewa Kudi ta xaro ta mikawa magaji
"karbi wannan maxa ka tafi wajen gobe da Nisa ka xayyana masa halin da muke ciki, nima baxan iya xuwa ba dan Yanxu wani jiri ke dibana "
Karbar kudin yayi, a fusace ya fita ya bar gidan
Kai tsaye tasha ya nufa inda ya samu abin hawan da xai kai Shi garin Dan batta, tunanin muguntar da xai kullawa Abban nauwar Kawai yake yi har ya isa garin .
Bayan tafiyar magaji Farin ciki ne ya kama su innah karime Sbd xa a yi musu aiki ba tare da sun sha wahala ba, kiran wayar magaji suka yi inda suka Kara xayyana masa muguntar da xa a Kara shiryawa.
Har bayan sallar magariba suna tsimayin dawowar magaji Amma shiru ba labari, gaba dayan su tagumi suka xuba suna tunanin abinda ya hana shi dawowa a kan lokaci cikin damuwa habi ke magana.
"ni kuwa Ina Dan nan ya makale, yaro tun safe ya tafi yaki dawowa kamar an aiki bawa garin su Idan ya dawo sai na bata masa rai"
Ran innah a bace ta bata amsa
"ai dama nasan xa a yi haka magaji baya Jin magana, Yanxu haka gidan karuwai ya wuce ya karbe mana yan kudade yayi mana wayo "
"duk inda ya tafi ma xai dawo Amma sai ranshi ya baci "
Suna wannan halin ne suka ji ana buga musu kofar falo cikin gaggawa suka nufi kofar suna rige-rigen budewa, Jama'a suka gani a tsaye suna duban su, cikin jimami habi ta dube su lafiya bayin Allah na ganku kamar bakwa cikin nutsuwar ku"
Cikin karfin hali daya daga cikin su yake mata bayani.
"mu Daga garin Dan batta muke, Akwai daya Daga cikin fasinjojin da suka hau mota Daga garin nan to shi ne ya samu hadarin mota a hanyar xuwa garin, shi ne Muka Tambaye Shi ya bamu kwatancen gidan nan, Yanxu haka muna tare da shi a mota mun xo ne mu tafi daku a kaishi Asibiti "
Cikin tashin hankali su Inna suka fita Bakin kofar suna kuka suna Salati. Magaji suka tarar kwance cikin jini ko yatsansa baya matsawa a firgice suka kama hanyar xuwa Asibiti Don bashi agajin gaggawa.
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Wannan shafin gaba daya naki ne sarkin rigima HAFSAT ABUBAKAR SHAGARI kiyi yadda kike so da shi, na baki halak Malak kada ki bawa BABY😜*
6⃣4⃣
Isar su ke da wuya aka fara yiwa magaji gwaje-gwaje inda aka tabbatar musu da cewa kwakwalwar sa ta hadu da jini, sannan ya samu karaya a cinya da sauran sassan jikinsa, ya tabbatar musu da cewa idan ba a bashi agajin gaggawa ba xai iya rasa hankalinsa.
cikin tashin hankali suka kira Abban Nauwar suka shaida masa abinda ya same su.
Cikin kuka innah ta karbi wayar take masa magana.
"ka taimaka mudi kaxo iftila'i ya afkawa magaji, Kansa ya hadu da jini yanxu haka Muna Asibiti muna bukatar kudi kafin ma likita ya kalle shi ya fara bashi magani"
cikin rashin nuna kulawa ya mayar mata da amsa.
"yanxu ina Office ki jira na tashi xan xo Insha Allah"
fashewa tayi da kuka ta fara yi masa magiya.
"yanxu har sai ka tashi sannan xaka xo ka same mu, baxa ka tausaya wa yaron nan ba, bai san fa inda kansa yake ba"
kashe wayar yayi ya barta tana sambatu.
har bayan sallar magariba babu Abban Nauwar babu dalilinsa, gaba daya ya manta da wayar da suka yi da su innah karime don shi tuni ya shige ya tafi gidan malam Abdullahi don karbar maganinsa.
gajiyar da suka yi da jiransa ne yasa Habi ta tashi ta nufi gidan, bude dakuna ta shiga yi, don dibar wata kadara ta siyar ta nemarwa jikanta magani, gidan ta shiga lalubewa bata samu komai ba, don haka ta yanke shawarar balle mukullin dakin Abban Nauwar ta dauki kudi, ciki hanxari ta balle kofar ta kwaso kudade masu yawa ta nufi asibitin.
Tana isa ta biya duk kudaden da ake bukata aka fara bawa magaji agajin gaggawa, Bayan ya kammala duba shi ne ya tabbatar musu da cewa ko magaji ya samu lafiya ya rasa wani bangare na hankalin sa, a ranar Kwana suka yi suna kuka Suna tsinewa Direban da yayi tukin ganganci ya illata musu da.
Abban nauwar na dawowa gida ya tarar da barnar da habi tayi masa, Kai tsaye wajen mai gadi ya nufa cikin tsawa yake tambayar sa.
"waye ya shigo ya bincike min daki ya kwashe min kudaden da aka bani ajiya "
Cikin tashin hankali mai gadi yayi dube Shi.
"Wlh babu wani Bakon fuska da ya shigo gidan nan, Kawai baba habi ce ta shigo ita ma kuma bata dade ba ta fita "
Gyada kai yayi gami da tsaki Sannan ya fice daga gidan ya nufi Asibiti, tarar da su ya yi sun xuba tagumi GA kuma jakar Kudi a Hannun habi, cikin hanxari ya fixge jakar ya fara xaxxaga musu masifa.
"Haba baba a wane dalilin xaki shigar min daki Ki daukar min kudin da aka bani amana abinda kika yi ya dace kenan, na farko dai ke ba gadona kike dashi ba ballantana kice xaki fara Karbar rabon Ki, daga Yau kada ki sake yi min irin wannan, saboda bani na aike Shi Yaje yawon iskanci ba mota ta buge Shi"
A fusace ya shiga office din likita inda ya shaida masa irin barnar da habi tayi masa, ya kuma roke Shi ya bashi wani bangare na kudin da suka kawo masa.
Ba musu ya xaro ya bashi"
Bayan Abban nauwar ya tafi ne likitin Yaxo ya same su ya sanar da su yadda suka yi dashi, tsine masa suka shiga yi suna aibata Shi, daga karshe ya shaida musu cewa gobe xai sallame su kasancewar babu ragowar kudin Su a hannunsa.
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da Jin kalaman likita Sbd ba su da kudin da xasu nemawar wa magaji magani, gashi jikinsa ya Kara rikicewa baya gane komai sai xage-xage da yake yi, a ranar hana su bacci yayi saboda xafin ciwon da ya addabe Shi.
Washe gari da sassafe ya kawo musu takardar sallama,suna kuka suna rokon ya tausaya musu Amma likitan ya kekashe kasa ya kore su.
Gida suka dawo kai tsaye dakin su suka shigar da magaji suka Kwantar da shi, ihu Kawai yake yana xagin su innah karime, hayaniyar da Abban nauwar Yaji ne yasa ya fito a lokacin yana daki suna tattaunawa da Hamdan dangane da batan su nauwar,tunda suka bata yake xageye duniya yana neman su Amma ba Labari, gaba daya suka fito don ganin abinda ke faruwa, dakin suka shiga inda suka tarar dashi hannunsa Rike da kansa yana kuka yana xage-xage.
Su habi na ganin su suka Mike suna kuka
"ka tausaya mana Alhaji ka duba halin da yaron nan yake ciki "
Sbd takaici Abban nauwar kasa cewa komai yayi, sai Hamdan ne yayi musu magana.
"Indai xalunci abin yi ne ku cigaba wannan kadan Ku ka gani daga cikin irin sharri da Makirci da ku ke kullawa, kun kashe kun haukatar kun tarwatsa rayuwar iyalin da suke cikin Farin ciki, ta Yaya xaku ga daidai a rayuwar Ku, wannan so mun tabi ne, baku ga komai ba sai nan gaba"
Kuka su habi suke yi suna rokon a taimaka a mayar da magaji asibiti, cikin takaici Abban nauwar ya dube ta.
"ba wani abu da xan iya yi masa Sbd bani na aike Shi Yaje inda abin ya same Shi ba, ko kafar nan xata rube kansa ya lalace ba ruwana, sharrin da ku ka shuka ne, Ku ka fara girbar irinsa."
Yana kammala maganar suka fice suka koma daki, cigaba da tattauna maganar Nemo su nauwar suka yi, inda suka tsayar da matsaya cewa xasu sake fita nemo su gobe Sannan kafin ya tafi ya yanke shawarar korar su innah karime Daga gidan.
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣5⃣
Bayan fitar Abban nauwar daga dakin su Inna karime kuwa,duk jikin su yayi sanyi ganin yadda ya canja taku gaba daya, ya daina saurarar su ya yanke duk wata alaka da su, sannan ya daina jin nauyin su duk abinda ya fito daga bakin sa baya jin kunyar fada musu, Habi ce ta katse musu shirun da suka yi.
"Gaskiya sai mun canja taku innah, wannan yaron yana son jefa mu a wani hali, kin ga duk makircin da muke shiryawa kokarin warwarewa yake yi, mu koma tamkar bola a cikin gidan nan, duba kiga irin bakaken maganganun da ya fada mana Yanxu, duk rashin Lafiyar nan da yaron nan yake yi yaki tausaya masa, Wallahi wata rana tsaf xai Kore mu"
Gyara xama tayi ta sake duban innah karime ta cigaba da magana.
"Yanxu wata Shawara nake son mu tattauna a kanta, me xai hana mu yiwa xulai yar gidan kawuna waya ta dawo gidan nan da xama ta jawo mana hankalin sa da kwalliya da kisisina, sannan kafin taxo sai taje ta shirya jikinta da magani ta yadda yana mata kallo daya xai haukace da soyayya, Kin san xulai yarinya ce wayayyiya tasan salon janye hankalin da namiji, mu yi duk kulle-kullen da xamu yi, mu cusa ta har sai yaron nan ya mutu a kan sonta, kin ga mu kuma mun samu damar da xamu dada bajewa sosai a gidan nan babu wanda xai tsangwame mu, sbd Idan bamu yi haka ba akwai matsala Kin san dai baxai ta xama a haka aure ba. Gashi Yanxu duk abinda muke yi so yake ya tashi a banxa Amma idan Muka biyo ta wannan hanyar akwai yiwuwar mu ci nasara. ko ya kika gani?"
Murmushi innah karime tayi ta bata hannu suka tafa.
"gaskiya kan ki yana ja habi, kin yi babban tunani, yadda abin nan namu ya daina ci wannan ce kadai hanyar da xamu bi mu yake Shi, kin san tunda yayi wannan karatun na nasara baxai rasa bin mata ba, suna fara shakuwa xamu yi kokari a yi biki mu huta, dan naji yana shirye-shiryen tafiya nemo wannan mahaukaciyar Matar tasa, mu kuma indai muna doron kasa tayi bankawana da gidan nan sai dai su hadu a lahira "
A raxane habi ta dube ta.
"nemo ta yace xai yi"
"kwarai kuwa, daxun nan naji yana fadawa wannan munafikin yaron da ya tsani magaji"
Waya habi ta fara lalube "ai kuwa Yanxu xan kirata innah Kinsan ba a bori da Sanyin jiki"
Kiran wayar xulai tayi inda ta xayyana mata duk salo da kissa da makircin da take so ta yiwa Abban nauwar, har ya ji yana sonta, bayan ta kammala fada mata ta bata umarnin ta ranto kudin mota ta taho a ranar.
Bayan sun gama wayar ne xulai tayi wani tsallen Farin ciki ta fada kan gadon karfen da take, a tunaninta shekarar arxikinta ne ya kama, gidan wata yar bori ta biya inda ta bata kunshin wasu magunguna tace tayi wanka da shi, Sannan ta bata wani kwalli ta saka duk yadda xa a yi tayi kokarin yin ido biyu da shi Abban nauwar.
Cikin Farin ciki xulai ta fita Daga gidan yar borin ta kama hanyar xuwa Kano.
Da misalin karfe biyar na yamma ta iso gidan, habi ce ta Kai mata ruwa bandaki ta sheka wanka Sannan ta shiga dakin ammin nauwar ta dauko mata turarukan da take amfani da su, ta bata kayanta ta saka, bayan ta kammala aka umarce ta da ta fito falo ta jira yi dawowar sa, su kuma suka shige daki suna jiran Jin yadda xata kaya tsakanin xulai da Abban nauwar.
Horn din motarsa suka jiyo, da sauri habi ta sake fitowa ta fesheta da turare ta Kara gyara mata daurin dan kwali Sannan ta koya mata irin tarbar da xata yi masa a lokacin da ya shigo tana kammala koya mata ta Kara shigewa daki.
Da sallama ya shigo dakin tare da ambaton Allah saboda Malam Abdullahi ya jaddada masa cewa kada ya rika sake da addu'ar shiga gida da fita Daga gida, cikin kisisina gami da rangwada xulai ta karasa gare shi hannu ta kai xata rungume shi tare da Karbar abinda ke hannunsa, da hanxari ya ja da baya yana kiran Sunan Allah, ba karamin daure masa Kai abin yayi ba saboda duk a tunaninsa aljanah ce tayi shiga irin ta ammin nauwar, addu'a yake ta karantawa yana neman tsarin ubangiji.
Cikin kissa ta Kara kai hannu xata taba shi, Rike Hannun yayi gami da wanke ta da mari domin a Yanxu tsoro ya bar ranshi ko aljanar ce yana Jin xai iya bugawa da ita, ihu xulai ta saki ta sake binsa a guje xata rungume shi, babban burinta bai wuce su hada ido dashi ba maganinta yayi tasiri amma bata samu wannan damar ba, sa kafa yayi ya take ta ya wuce bangaren sa kulle kofa yayi, Sannan ya samu guri ya xauna yana mayar da numfashi.
Wannan Al'amarin ya daure masa Kai, Anya kuwa ba gamo yayi ba, bandaki ya shiga ya dauro alwala ya fara jera salloli bayan ya idar ya dauki al-kur'ani yana tilawa, tare da neman tsarin Allah ya Kare shi daga dukkan sharrin mai sharri.
Bayan komawar Abban nauwar daki ne habi ta fito a sanyaye ta karaso inda xulai take tana faman share hawaye, masifa xulai ta fara yi Mata.
"Haba Yaya dama Kin san wulakancin