Showing 81001 words to 84000 words out of 111837 words
Chapter 28 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
kirata sbd ta tsani tsayawa tayi doguwar magana da namiji indai ba yayanta bane.
Gyaran murya yayi sannan ya fara magana.
"maganar dama xamu yi dangane da sabuwar yarinyar nan da aka kawo"
Shiru yayi yana kallonta, muryarta a shaqe ta amsa masa da to malam, gabanta ba karamin faduwa yake yi ba, saboda bata sani ba ko wani ne ya hadawa nauwar sharri basu sani ba.
Katse shirun da tayi yayi
"ya naga kamar kin tsorota ki saki ranki ba komai bane ya faru, ni dai babban fatana kiyi min alkawarin xaki fada min gaskiyar Al'amari bana son karya, ko ki fada min abu ba dai-dai ba"
"nayi maka alkawari malam"
Cikin nutsuwa yake mata magana yadda zata fahimce shi.
"Menene alkarki da nauwar"
Cike da mamaki ta dago Kai saboda bata fahimci abinda yake nufi ba.
"okay naga kamar tambayar ta dan yi miki nauyi ina nufin ya ku ke da ita "
"yar kanwar babana ce"
ta amsa masa a takaice
"Masha Allah, naji tace min a kano take haka ne ko"
"Eh gaskiya ne abinda ta fada maka"
Biro da takarda ya dakko tsareta da ido yayi yana kallonta.
Kwarjinin sa ne ya kamata don haka tayi hanxarin kawar da kanta.
"shikenan naji, yanxu ina so ki bani address din gidan ku saboda ina so zan ga mahaifin ku, xamu tattauna da shi a kan lamarin karatun ku"
Ajiyar zuciya tayi, sannan ta fara kwatanta masa gidan shi kuma yana rubutawa, bayan ya kammala rubutawa ne, ya umarce ta da ta koma Aji.
Tana tafe tana wasu-wasi a ranta, anya ba sharri xa a je gida a hada musu ba, kafin ta isa Aji wani axababben ciwon kai ya rufeta, sauri tayi ta shiga Ajin don idan ta kara mintuna a hanya xata iya faduwa.
Wajen xaman su ta nufa, cike da damuwa ta samu guri ta xauna, cikin kulawa nauwar take tambayarta
"lafiya naga duk kin canja, ko dai wani abin ne ya faru da mu"
Ganin hankalin duk yan ajin ya dawo kanta kowa ya kasa kunne yana jira yaji gulma, don haka ta yiwa nauwar alama da ido da ta tsaya xata fada mata, idan ido ya bar kansu.
Wata hirar suka shiga yi, don su 6atar da tunanin masu kallon su, hakan ne yasa kowa ya mayar da hankali kan karatun sa, fakar ido tayi ta fara gayawa nauwar yadda suka yi da principal.
A tsora ce ta dubeta, "me yasa xaki bashi address shikenan fa mun shiga uku duk motsin da muka yi yanxu xai iya xuwa gida ya fada tunda yasan gidan mu,nifa dama naga ya sa mana ido da yawa, duk motsin da muka yi a makarantar nan idon shi a kan mu,idan ni har na fara jin na tsani makarantar ma wlh, gaskiya da kin sani kince kin manta address din gidan naga yadda zai yi"
Harararta saimah tayi
"lallai ma yarinyar nan kuruciya na damunki, idan nace na manta ai sai yace na raina masa hankali na sake janyowa kan mu wata masifar, ni dai gara da na fada duk abinda zai faru ya faru. ai dai baxa a kashe mu ba ko?"
"hmm saimah kenan ko bakin a kashe mu ba ai a saka mu bakin ciki, da asarar hawaye"
Har aka tashi hirar da suke yi kenan, hankalin su a tashe suka koma gida, suna shiga soro saimah ta fara kuka, dakin mama ta shiga tarar da ita tayi ta kishingida tana hutawa, fadawa jikinta tayi tana kuka, cikin kulawa ta fara tambayar autarta abinda ya faru da ita. kukan da take yi ne ya hanata magana, don haka ta juyo ta fara tambayar nauwar, cikin nutsuwa tayi mata Bayanin abinda ya faru.
Murmushi tayi
"to ke Auta menene na tada hankali kiyi kuka indai kin san kina yin abinda ya kai ki makaranta wannan ai ba abin tashin hankali bane"
Turo baki saimah tayi
"ni dai naji tsoro wlh saboda mutumin mugun dan sa ido ne , kuma xan fadawa Abbah ko yayi sallama kada ya fita ya gan shi ya kyale shi ya gaji da tsaiwa ya tafi"
Dariya sosai tasa mama
"sai ki fada masa shi kuma ya daka ta taki ku rika shirme, kinga ku tashi ga abincin ku can na hada muku, ku je ku dauka kuma kuna ci ku fara Karatu "
Tashi suka yi suka shiga kitchen suka dauki abincin suka fara ci.
Magariba na yi aka dawo da Ammi daga gidan magani, yau ko gardama bata yi ba da xa a shigo da ita gida, wani magani aka basu aka ce a daren ake so a bata tasha.
Abba na shigowa ya kira mama da sauri taxo ta rike Ammi mika mata maganin Abba yayi inda ya fada mata abinda xa a yi da shi.
Da sauri ta shiga ta dakko kofi ta fara jika mata, mika mata tayi ba tare da gardama ba ta karba ta kafa kai ta shanye.
Mama ce ta fara magana
"Gaskiya sauki ya fara samuwa, tunda har tana karbar magani tasha da kanta, lallai ba abinda ya fi karfin Allah "
"Ai insha Allah komai yazo karshe wannan ma cewa yayi tasha asirin da ya rike mata baki ya hanata magana xai warware da yardar Allah"
Tana kammala shan maganin ta ajiye kofin gefe guda.
Bata fi minti biyar da shan maganin ba, ta fara wani amai wanda sai da ya tsorata kowa a gidan, allurai da gashi ta shiga amayarwa, bayan ta gama kuma ta fara aman jini, A firgice yayan nauwar ya fita ya kira likita, magani ya bata sannan aka kara yi mata allurar bacci don ta huta sosai.
*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
Yau shafin gaba daya naku ne masoya Almajira na hakika iya wuya ana mugun tare*
Rahinatu Ibrahim (maman sadiq)
Hajiya Amina
Maryam (maman surayya)
Sharifa Niger
Firdausi Biu
Nanah Hauwa
Hadiza Ahmad
sa'adatu M shehu
maman Mahmoud
khadeejah sabo Abdullahi
maman Yakura
Maman Ahmad
Amrat makeover
Binta muhd
nusaibat muhd
maman imam
Bahijjah gora
Aysha Sulaiman Ahmad
Shatu Yusuf
Maryam elladan
Khadija Yusuf unique
Maryam B sadeeq
Amina H alkasim
Hajiya maryam Hassan
maman Anwaar
*Baxan iya lissafa sunayenku gaba daya ba na gode da kulawar ku Allah ya bar kauna*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
7⃣4⃣
Bayan an samu kan Ammi tayi bacci ne, shimfida Abba yasa aka yi masa, su nauwar suka kewaye shi suna hira, tashi saimah tayi tsaf daga wajen xamanta ta dawo kusa da Abba, ranta babu walwala take kallon shi, tambayarta ya shiga yi.
"lafiya Autar Abbah ko Autancin ne ya tashi "
ya karasa maganar yana dariya.
Bata rai ta sake yi taki magana, nan da nan idanunta suka kawo ruwa ta hau murxa ido, cike da kulawa ya sake tambayarta.
"Ki fada min abinda ke damunki ko kuma na kyale ki, bana son sakarci"
Share hawayen tayi ta sake duban shi.
"Abba dama principal din mu ne yace xai xo wajenka "
"Au dan wannan abin shi ne xaki rika kuka to ki Kwantar da hankalin ki babu komai"
Yana rufe baki yaro ya shigo tare da sallama, gaba daya suka mayar da kallonsu gare shi.
"wai ance ana sallama da mai gidan nan"
Gaban nauwar da saimah ne ya fadi, suka xaxxaro da ido tambayar yaron suka yi.
"jeka kace inji wa"
Fita yaron yayi ya tambaya sannan ya sake dawo wa.
"wai inji Malam musa"
Dafe kirji suka yi suna Salati.
"shikenan kashin mu ya bushe, Abba principal ne"
Kallon su Abba yayi
"wai kuwa anya yaran nan kuna da gaskiya, daga ji anyi sallama da ni duk kun tada hankalin Ku, ko dai laifi ku ka yi, Kai yaro jeka kace ina xuwa, dauki shimfidar nan ka kai ka shimfida masa kaji dan albarka"
Takalmansa ya dauka ya fita, hankalin su nauwar a tashe yake, saboda fargaba sun kasa ci gaba da magana sai addu'a suke yi Kawai.
Abba na fita ya tarar yaron yayi shimfida amma Malam musa principal na tsaye, da sallama Abbah ya karasa wajen tare da mika masa hannu, kasa mikawa Abbah hannu yayi saboda girmamawa, cike da ladabi ya tsugunnah har kasa ya gaida shi.
Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa.
"Sannu da xuwa Malam, bismillah ga guri nan xauna"
Xaunawa yayi suka sake sabuwar gaisuwa.
"ya kokari Malam ya dalibai "
"dalibai alhamdulillah Alhaji"
Gyara xama principal yayi ya dubi Abba.
"Dama xuwa nayi mu gaisa sannan mu tattauna a kan daya daga cikin yaranka "
Gaba daya Abba ya bashi hankalinsa sannan ya bashi amsa da.
"Ina saurarenka Malam, da fatan dai ba wata fitinar suke aikatawa ba, don tunda Ku ka yi magana da su cewa xaka xo,suka kasa xaune suka kasa tsaye duk hankalin su a tashe yake saimah har da kukanta "
Murmushi Malam yayi sannan ya fara bayani.
"babu komai Alhaji alkhairi ne ya kawo ni, kuma ina fatan baxa a juyar da bukatata ba"
Cike da kulawa Abba ya bashi amsa.
"mu dama kullum alkhairin muke jira, sai dai mu yi addu'a Allah ya hada mu da shi a duk inda muke "
Ba karamin dadi principal yaji ba da kalaman Abba, wannan dalilin yasa ya saki jiki sosai ya fara bayyana masa abinda ya kawo shi.
Gyaran murya yayi sannan ya dan rusunar da kansa.
"Dama naga iri ne a gidanka, wato daya daga cikin dalibaina wadda saimah ta shaida min cewa yar kanwarka ce ita na gani na yaba da hankalinta da irin tarbiyyar da ku ka bata, shi ne naxo tambaya idan babu wata magana mai karfi a kanta sai na fito"
Shiru Abba yayi yana naxarin maganar principal, sai da ya nisa sannan ya bashi amsa
"Eh tabbas babu wata magana a kanta, kuma naji dadi da kaxo gida ka same ni muka yi magana, saboda wasu malaman idan suna son yarinya baxa su nemi magabatanta ba sai dai su rika tsare yarinya a Makaranta suna soyayya da ita, daga haka idan aka samu akasi sai kaga yarinya ta lalace, gaskiya naji dadi sosai da wannan tsarin naka, amma akwai wani hanxari ba gudu ba, kamar yadda saimah ta fada maka cewa yarinyar nan yar kanwata ce haka maganar take, Mahaifinta baya kusa ya tafi kasar waje Karo Karatu, kaga baxan yanke hukunci a kan xan baka ita ba, sai naje na shawarci yarinyar da mahaifiyarta sannan a samu babanta a yi masa magana, abinda muka yanke ni kuma xan same ka na fada maka."
"wannan gaskiya ne Alhaji, to Allah yayi mana jagora."
Sallama suka yi sannan Abba ya kira su nauwar suka dauke shimfidar da suka xauna, tun daga waje suke tambayar Abba amma yaki basu amsa yace ba maganar su bace.
dakin mama ya shiga ya sanar da ita yadda suka yi da principal, cikin farin ciki mama ta bashi amsa
"wannan a ganina ai ba wani abu bane, samun yarinyar nan ya kamata kayi ka tambayeta idan xata amince da shi, kaga duk lokacin da aka samu babanta ko mahaifiyarta taji sauki sai a sanar da su abinda ya faru, amma bai kamata kayi shiru da bakinka ba"
Shiru yayi na dan lokaci Sannan ya sake dubanta.
"shikenan xan yi tunani xuwa gobe abinda na yanke sai na mata magana "
Tashi yayi ya nufi dakinsa don yin bacci
*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Yau ma dai shafin naku ne masoya Al-majira, ina matukar jin dadin yadda ku ke kaunar wannan littafi ana mugun tare*
Hafsat muhd ibrahim
Nana Aysha mahmud
zainab Niger
7⃣5⃣
Da gudu su Nauwar suka bi bayan Abba, a hankali suke masa magana
"Abbah sannu da dawowa"
cikin sakin fuska ya amsa musu.
"yauwa sannun ku yayan Abbah, ya kamata ku tafi ku kwanta gobe akwai xuwa makaranta idan kuma ku ka makara ba ruwana, sai malam ya xane ku ina gida ban san an yi ba"
saimah na dariya take magana.
"ai mu yan gatanka ne Abbah babu mai dukan mu in dai kana nan, tunda muna da kai ba mu da matsala"
murmushi yayi, har sai da wushiryarsa ta bayyana.
"To Allah yasa rakiya tayi tsawo tsakanina da ku, Allah kuma yayi muku albarka"
amsawa suka yi da Ameen, shigewa daki yayi suka bi bayan sa, cike da mamaki ya juyo ya dube su.
"ya naga kuma kun biyo ni, ku da nace ku tafi ku kwanta"
"hira muka xo xa mu yi da kai Abbah mu bama jin bacci" saimah ta fada tana murmushi.
sake matsawa tayi kusa da shi.
"yauwa na manta ban tambayeka yadda ku ka yi da principle ba Abbah, har yanxu fa a tsora ce muke hankalin mu ya kasa kwanciya, dan Allah ka fada mana abinda yaxo yi Abbah"
cike da kulawa ya bata amsa.
"Ba laifi ku ka yi ba, dan haka ku daina tayar da hankalin ku"
"nasan ba mu yi laifi ba Abbah amma tabbas principle baxai xo gidan nan haka kawai ba akwai dalilin da ya kawo shi, ka taimaka ka fada mana Abbah dan Allah"
gyara xama yayi ya mayar da kallensa gare su.
"ina so ku tattara min hankalin ku sannan duk abinda xan fada bana so naji shi a makaranta ku ja bakinku ku yi shiru, sirri ne tsakani na da ku"
da sauri suka bashi amsa.
"Babu mai ji Abbah xamu rike wannan sirrin"
gyara murya yayi sannan ya fara fada musu.
"principle din ku shi yaga ke Nauwar, ya nuna ta da hannu sannan ya cigaba da magana, yace yana son hada xuri'a da mu"
A firgice ta dago.
"ni kuma Abbah?"
cikin kulawa ya dube ta.
"eh ke yace yana so, amma ban amsa masa ba nace sai na shawarce ki abinda kika ce shi xa a yi, dan ni baxan miki dole ba, shi yasa nace ya saurare ni xan fada masa yadda muka yi"
saimah ce tayi sauri ta karbi xancen
"Abbah principle fa kace, tsoho ne fa yarsa ma ta girme mu Allah, tabdi ni dai gaskiya Nauwar kice bakya son shi"
dakatar da ita Abbah yayi.
"Ba na hanaki wannan shirmen ba saimah idan kika kara magana xan kore ki"
kan Nauwar a sunkuye ta kasa bada amsa saboda mamakin yadda aka ce principle yana sonta, ashe duk kulawar da yake bata ba ta banxa bace akwai abinda yake nufi, shiru tayi tana naxarin maganganun Abbah, shi ya katse mata shirun da tayi ya cigaba da magana.
"kije kiyi shawara kin ji ko, kuma kiyi addua abinda kika yanke sai ki fada min, baxan miki dole ba duk abinda kike so shi xa a yi"
tashi suka yi suka fita daga dakin, suna shiga dakin su saimah ta fara masifa.
"lallai ma principle din dan rainin hankali ne, duk xaurawan garin nan ya rasa wacce xai ce yana so sai ke yar karama, wlh kada ki yarda kawata"
wani hawayen takaici ne ya xubo wa nauwar.
"ni gaba daya maganar ma mamaki ta bani ban taba xaton wannan maganar xata fito daga bakinsa ba,dadi daya naji da Abbah bai amsa masa ba,amma da ya amsa da haka nan xan karbe shi ko bana son shi, saboda baxan iya watsawa Abba kasa a ido ba"
"lallai da sauran ki yarinya yanxu da ya amsa masa sai ki karbe shi a haka ko bakya son shi, lallai ma"
"to ya xan yi kawata baxan iya ketara umarnin Abbah ba"
matsawa kusa da Nauwar saimah tayi.
"yanxu kin san yadda xa a yi"
dago idanu tayi ta kalleta, sai kin fada.
"Mu daina sakar masa fuska gaba daya, daga gaisuwa shikenan"
hannu ta mika mata suka tafa.
"haka xa a yi kawata"
bayan sun kammala hirar ne suka kwanta basu jima ba bacci yayi awon gaba da su.
yau ma kamar kullum da sassafe suka kammala shirin makaranta, yau Abba ne ya kaisu da kanshi, bai bari sun hau abin hawa na haya ba, Aji suka wuce inda kowa ya dauki alkur'ani ya fara karatun haddar da xa a karba bayan axahar, tunda principle yaga xuwan su Nauwar ya fara kewaye makaranta duk don ya leka aji ya gano ta yaji sanyi a ransa.
saimah na ganin xai leko ta window xata sa Nauwar ta buya a cikin hijabi duk don kada ya samu damar ganinta, ya leko ya fi sau biyar amma bai samu nasarar haduwa da ita ba, sake xagayo wa yayi ya tsaya daidai window din da xai hango su, a lokacin su kuma sun shagala da karatu, kiran su yayi duk su biyun suka fito tsugunnawa suka yi a gabansa tare da gaishe shi.
fuskarsa a sake ya amsa
"yau dai baku xo makaranta da wuri ba ko, kuma, nasan ke kika sa Nauwar ta makara don ta fiki himma"
kansu a kasa suka bashi amsa.
"da wuri muka xo malam"
"shikenan naji ku tashi ku tafi aji, idan kun je gida ku gaida babanku ku ce yau xan dawo mu karasa magana a kan gonar da na gani ina so "
tashi suka yi, ya bi Nauwar da wani mayataccen kallo, ba karamin burge shi take yi ba, yanxu babban burinsa bai wuce yaga Allah ya mallaka masa ita ba.
saimah ce ta dubi Nauwar, "kawai fa dan ya ganki ne ya kira mu dan rainin hankali a yau din nan nake so mu yi wa tufkar nan hanci, mu fadawa abbah gaskiya ya dakatar da shi, don baxai hana mu sakewa a makarantar mu ba"
Har suka shiga Aji saimah na mita saboda abin principal ya fara bata haushi.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki yar uwa aminiya, kuma abokiyar fadana, AYSHA SABO ABDULLAHI (maxumunciya) na baki wannan page kyauta ba dan halinki ba, kiyi yadda kike so da shi*
7⃣6⃣
Su saimah na isowa gida suka ci karo da Abbah xai fita masallaci hannun shi rike da tasbaha yana ja, da sauri suka karasa kusa da shi.
"yauwa Abba yau ma principle ya sake bamu sako mu fada maka, wai ya maganar gonarka da ya gani yana so, yace kuma xai xo yau ya ganka"
mamaki ne ya cikawa Abbah xuciya, ya ma kasa basu amsar abinda suka fada masa.
"to naji ku tashi ku tafi, Alllah ya kawo shi lafiya"
jujjuya maganar ya rika yi