Showing 84001 words to 87000 words out of 111837 words

Chapter 29 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

a xuciyar sa
"Me yasa wannan mutumin xai min haka, ai bai kamata ya bawa yara wannan sakon ba sam bai kamata ba, amma xan yi maganin sa"


ya fada tare da yin kwafa sannan ya fice ya nufi masallaci.


Yau ma dai kamar jiya sake aiko yaro yayi aka yi sallama da Abbah, maganar neman auren Nauwar ya sake yi, Abbah bai bashi wata cikakkiyar fuska ba, saboda yana ganin abin nashi ya fara wuce gona da iri, yana son takurawa yara ya hana su walwala da farin ciki, ba tare da sakin fuska ba yake masa magana.


"mun tattauna da mahaifiyar yarinyar nan tace a kyale mata yarta karatu xata yi, baxa ta bari ta fara tsayawa da samari ba sai tayi nisa sosai a karatun ta"
yana kammala fada masa ya juyar da fuskarsa gefe .


principle bai ji dadin sakon da Abba ya fada masa ba, amma ya daure ya bashi amsa.


"ba komai ai hakan yana da kyau, amma a ganina Alhaji ai karatu baxai hana aure ba, kamar yadda aure baxai hana karatu ba, matukar yarinyar nan ta aure ni baxan hanata gudanar da duk wani abu da xai xama cigaba ne na rayuwarta ba, a bani dama na turo a yi maganar aure, idan yaso tana kammala secondry sai a daura auren, ko wata daya baxa tayi a gidana ba xan nemar mata admission ta shiga jami'a, a duba wannan al'amarin Alhaji, domin Allah bai taba jarabtata da son wata ya mace ba sama da wannan yarinyar, da sonta nake kwana da shi nake tashi a duba Alhaji a yi min rai"


tausayi principle ya bashi, sakin fuskar shi yayi kadan sannan ya dube shi.


"naji duk bayananka xan yi kokari na sanarwa da mahaifiyarta yadda muka yi da kai, abinda tace sai na kiraka a waya na sake sanar da kai, ba ma sai ka kuma dawowa ba kasan waya ta wakilci komai"


yaji dadin kalaman Abbah, sallama yayi dashi ya tashi ya tafi Abbah kuwa sai mita yake yi a xuciyarsa.


banda ma budurwar xuciya mai dattijo kamar wannan xai yi da yarinya,wani karin takaicin ma har da cewa wai babu yar da ya taba so kamarta, daki ya shige don ko mama bai fadawa yadda suka yi da shi ba saboda haushin da ya bashi.


kullum sai principle ya kira Abbah ya tambaye shi game da maganar da suka yi, amsa daya dai yake bashi ita ce mahaifiyar Nauwar taki amincewa, ganin wannan yawo da hankalin da ake masa ne yasa ya roki alfarma a barshi yaje har garin da baban Nauwar yake ya nemi aurenta tunda dai a nan an hana shi motsawa, nan ma dai dakatar da shi aka yi, haka ya kasance kullum a cikin damuwa da shaukin son auran Nauwar, ita kuma yanxu ko gaisuwa bata barin ta hadata da shi,saboda takura mata da yake yi da mayataccen kallon shi.


A haka suka cigaba da kasancewa kullum cikin wasan buya, har sai da sauran malamai suka fahimci akwai wani abu a tsakanin su.


*******************


A bangaren su Abban Nauwar kuwa tunda suka bar gida basu sake komawa ba, kullum Abban Nauwar a cikin kuka yake da shaukin son ganin iyalansa a kullum ya tuna cewa sharrin su innah karime ne ya hargitsa masa kan family sai ya musu Allah ya isa, Kullum addu'a yake Allah ya hana su farin cikin duniya da na lahira kamar yadda suka hargitsa masa tunani suka hana shi jin dadi suka jefa matarsa da yarsa a mummunan hali.


babban abinda ya fi daga masa hankali kuma wanda yake sa shi kwanciya rashin lafiya a duk lokacin da ya tuna, bai san halin da suke ciki ba, a mace suke ko a raye, gashi shi ya kore su da kansa, ba karamar nadama yake yi ba idan ya tuna da haka, wannan dalilin yasa ya matsa da neman su, duk garin da suka sauka sai ya bada cigiyar su a gidajen radio da television ko Allah xai sa a gansu.


sun je garuruwa sun fi goma, haka kuma duk garin da yaje sai yasa an yi masa saukar kur'ani an roki Allah ya bayyana su,ya kuma yayewa Ammi lalurar da ya jarabceta da ita.


ita ma Nauwar Kullum adduarta bata wuce Allah ya hada ta da mahaifinta ba.








*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆


*Yau shafin gaba daya naki AUNTY MUNEERA ABBA DANDAGO, Allah ya kara miki lafiya da imani*






7⃣7⃣






Tunda principle ya kasa samun tsayayyiyar magana, daga wajen Abba, ga shi ya nemi a kai shi wajen mahaifin Nauwar anki, don haka ya shiga kulla yadda xai samarwa da kansa mafita, tunanin yadda xai bullowa lamarin ya rika yi, yanxu komai ya damule masa saboda ko samun damar magana da Nauwar baya yi, da ta ganshi xata gudu baxa ta sake barin su hadu ba, tashi yayi da kansa ya shiga aji ya kirata yace taxo Office yana son magana da ita.


hanata tafiya saimah tayi sai da yayi kusan aike uku sannan ta tashi ta tafi tana buntsure-buntsure ta tafi, a bakin kofar Office din ta tsaya tare da yin sallama, a hankali ya dago ido ya kalleta, wani lafiyayyen murmushi ya sakar mata gami da kiran sunanta cikin sassanyar murya.


"Nauwar karaso mana"


kara turo baki tayi, tare da daure fuska,
"bar ni a nan ba sai na shigo ba"


wani dadi yaji ya mamaye masa xuciya, sassanyar muryarta ba karamin debe masa kewa take yi ba, wannan turo bakin ba karamin burge shi yake yi ba.


cikin sakin fuska ya kara maimaita abinda ya fada mata.


"ki shigo nace bana son gardama"
ya karasa maganar yana lumshe idanunsa


kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta karasa xaunawa tayi a kasa, nuni yayi mata da hannun shi.


"tashi ki dawo nan, daga yau idan kika xo bana so ki kara xama a kasa, ki dauka nan wajen dakin ki ne, domin da mai dakin da kayan cikinsa duk mallakin ki ne"


kanta a sunkuye yake tana wasa da yatsunta sam babu alamar wasa a tattare da ita, duk maganar da yayi bata bashi amsa ba, saboda gaba daya haushi yake bata, musamman idan ya kashe mata ido, ji take kamar ta rufe shi da duka.


sake dubanta yayi, yana murmushi.


"me yasa kike guduna kwana biyun nan Nauwar, ki fada min gaskiya idan laifi nayi miki na baki hakuri, amma har ga Allah raina yana baci idan naga muna wasan buya da juna"


har yanxu kanta a kasa yake bata dago ta dube shi ba, muryarta a dashe ta amsa masa da ba komai.


kallonta yayi yana girgixa kai.


"hakan nan baxa ki rika guduna ba akwai dalili ki fada min gaskiya, saboda har yanxu na gaxa samun nutsuwa da damuwar hakan nake kwana da ita nake tashi"


kara bashi amsa da ba komai tayi.


wani kallo yayi mata wanda har sai da yasa taji kunyar kanta.


"ni nasan akwai wani abu Nauwar kawai kina boye min ne, idan kuma baki fada ba ni xan fada miki dalilin guduna da kike yi, kin yarda na fada"


gyada kai tayi alamar ta yarda.


sake gyara xama yayi ya dubeta


"dago ki kalleni so nake mu yi magana ta fahimta tsakanina da ke"


A kunyace ta dago ta kalle shi, sai dai suna hada ido dashi tayi saurin kawar da idanunta saboda abinda ta gani na soyayya a idon principle, wani dan murmushi yayi wanda ya bayyanar da fararen hakoransa.


"ko a yanxu nasan kin fahimci sakon da nake son isarwa a gare ki"


sake daure fuska tayi don ko amsar tambayarsa bai samu ba.


"A yau nake son bayyanar miki da abinda ya dade yana damuna a xuciyata, amma ban san da wace fuska xaki kalli abinda naxo miki da shi ba, fatana dai ki yiwa abin kallo na nutsuwa kuma ki dube shi da idon basira, kuma ina so kiyi min alkawarin fada min gaskiya, domin tsakanina da ke babu yaudara ke diya ce a gare ni baxan yi fatan wani abu ya ta6a rayuwar ki ba"


gyada kai tayi alamar ta amince, duk ta kosa taji abinda yake son fada mata ta gaji da wannan dogon turancin da yake mata.


"Tunda kin amince xaki fada min gaskiya ni kuma xan fada miki abinda yake raina, Nauwar INA SON KI"


A firgice ta dago ta kalle shi ji tayi maganar na mata yawo a kwakwalwa, dafe kirjinta tayi ta kalle shi.


"kana sona fa kace malam?"


kashe idanu yayi gami da sakar mata wani shu'umin murmushi.


"Haba Nauwar ya naga lokaci daya kin firgita akwai fa aure tsakanin malami da daliba, Allah bai haramta haka ba, na miki alkawarin xaki samu soyayya mara yankewa a gidana xaki ji dadin da ba shi da misali,sai kin yi alfahari da ni a matsayin abokin rayuwar ki,baxan taba bari kiyi kuka a gidana ba sai dai idan na soyayya ne"


shiru tayi tana jin kalaman principle na shiga ta cikin kunneta, a xuciyarta kuwa cewa take, me xan yi da tsoho kamar ka.


cigaba da magana yayi cikin taushin murya.


"Tunda na fada miki abinda ke raina,kema ya kamata naji ra'ayin ki a kan haka, amma kafin lokacin xan tambaye ki, kuma wannan tambayar ita nake so ki fada min gaskiya kada ki ha'ince ni ki sa nayi xurfi a soyayyar gonar da baxa ta xama mallakina ba"


"na maka alkawari tun daxu xan fada maka gaskiya fa"


"Naji ai kuma na gamsu da maganar ki amma ina kara jaddada miki abinda nake so ne saboda bana son a samu matsala"


cikin nutsuwa ya fara tambayarta.


"an miki miji ko kuma akwai wata tsayayyiyar magana a kan ki, bana son karya ki fada min gaskiya kamar yadda kika min alkawari"


Har tayi niyyar fada masa gaskiya ta fasa,saboda muddin tace ba a bada ita ba, shikenan xai yi amfani da wannan damar ya rika takura mata.


kanta a sunkuye ta bashi amsa da an bada ni.


A raxane ya dago ya kalleta ji yayi kamar ta soka masa mashi, nan da nan idanunsa suka kada suka yi jawuri, bakinsa na rawa yake mata magana.


"An bada ke fa kika ce"


sake tabbatar masa da amsar abinda ya fada tayi.


"wa aka bawa to, kuma yaushe aka bada ke,? amma ko wanene wannan yayi min shigar sauri amma kuma Alhaji bai fada min haka ba"


cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani.


"Dan uwana aka bawa tun kafin mu xo garin nan aka yi mana baiko, Abba ya boye maka ne saboda baya so hankalinka ya tashi"


dago jajayen idanunsa yayi ya dubeta.


"Amma ban ji dadi ba wlh, saboda na gama tanadin yadda xan gudanar da rayuwata da ke amma ba komai haka Allah ya tsara, duk abinda Allah yayi ba mu da xabi sai dai mu yi biyayya, Allah ya baku xaman lafiya Allah yasa abokin arxikinki ne"


amsawa tayi da Ameen, ba karamin tausayi ya bata ba, duk yanayinsa ya canja da ka ganshi xaka tabbatar yana cikin damuwa.


tashi tayi xata tafi, kiran sunanta ya sake yi
cikin nutsuwa ta juyo ta kalle shi.


"wa yace ki tashi ki tafi ai bamu gama magana ba"


komawa tayi ta xauna tana dubansa.


"Akwai alfarma daya da nake so kiyi min, dan Allah kada ki fadawa dalibai abinda muka tattauna wannan sirri ne tsakanina da ke"


"Insha Allah babu mai ji malam"


sallama suka yi ta koma Aji, xuciyar principle cike da kauna da shaukin son Nauwar, lokacin da ta fadawa saimah yadda suka yi da shi ba karamin farin ciki tayi ba.


hannu ta mika mata suka tafa.


"Gaskiya kin yi fasaha kawata, ba karamar basira kika yi ba, gara da kika fada masa haka kinga ya sakar mana mara mu yi fitsari mu huta, haba nacin tsohon nan yayi yawa"


tun daga wannan lokacin ta samu lafiya da shi, ya daina damunta da axababben kallon shi, tsakaninta da shi sai dai mutunci.








*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆








7⃣8⃣






Nauwar ta shekara guda tana xuwa makaranta, inda ta samu damar haddace ixu ashirin, kuma tana cikin daliban da suka samu damar lashe gasar alkur'ani mai girma, wacce aka gabatar tsakanin makarantu, ita kuma saimah ta haddace ixu talatin, wannan dalilin yasa Abbah ya hada musu gagarumar walima, inda suka gayyato yan uwa da abokan arxiki suka taya su murna, komai iri daya Abbah ya yi musu babu wani banbanci da ya nuna tsakanin Nauwar da saimah, haka suka kasance tamkar yan tagwaye gwanin sha'awa.


A tsayin wadannan watanni da aka kwashe kuwa, Kullum Ammi na kara samun lafiya don har magana ta fara yi kuma tana gane Nauwar da yayan gidan su saimah, sai dai yanxu ba komai take iyawa ba sai an koya mata saboda ta manta abubuwa da yawa, amma mai maganin yayi alkawarin a sannu a hankali xata kara samun sauki,kuma xata warke garau kamar bata taba yin ciwon ba da yardar Allah.


rayuwa suke yi mai cike da farin ciki da jin dadi, idan har baka san su Nauwar a baya ba, baxa ka taba cewa su ne suka wulakanta suka yi bara ba, ita kuwa Ammi babu wanda xai ce mahaukaciya ce don duk buge-buge da surutan da take yi a da ta daina, gaskiya Abbah a tsaye yake akan al'amarin Ammi sai dai fatan Allah yayi masa sakayya ta alkhairi.


yau su Nauwar xaune suke a dakin mamah suna ta hira tare da ita kasancewar an yi hutun makaranta, tashi tayi tace musu tana xuwa, dakin Abbah ta shiga samun shi tayi xaune yana karatun kur'ani, gefe guda ta samu ta xauna sai da ya kammala yayi addu'o'i sannan ya juyo ya dubeta.
cike da girmamawa ta gaida shi, ya amsa yana mai sakin fuska.


"Alhaji wani tunani nayi game da bayin Allahn nan, yau shekarar su guda a gidan nan amma har yanxu ba a samu, wani nasu da yaxo yayi cigiyar su ba, tunda mahaifiyar yarinyar nan ta fara samun sauki sosai, abubuwan jikinta sun fara warwarewa ya kamata ka bayar da cigiyar su a gidajen radio, ko Allah xai sa yan uwansu su ji, don nasan duk inda suke yanxu hankalin su ba a kwance yake ba"


cikin nutsuwa ya dago ya kalleta.


"gaskiya ne Hajiya sai da kika yi wannan maganar nima naga ya dace a yi hakan, Insha Allah xamu bada cigiyar su idan Allah yasa an dace sai kiga an samu yan uwansu su ma idan da taimakon da xasu yi musu sai kiga matar nan ta warke gaba daya"


wayar da ke gefensa ce tayi 'kara, don haka yasa hannu ya dakkota number ya fara dubawa, murmushi yayi sannan ya dubi mama.


"Hajiya sadeeq ne ya kira ni ko dai yana hanya ne"


farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, ba mamaki don naji yana waya da yan uwansa yana ce musu ya kusa dawowa"


wayar ya kara a kunnensa ya fara magana.


cike da ladabi sadeeq yake magana, Abbah na bashi amsa bayan sun kammala ne ya juyo ya kalli mamah.


"Ai kuwa dawowar xai yi, yace anjima da misalin karfe biyar a je a dakko shi a airport"


cike da farin ciki ta amsa masa da Allah ya kawo shi lafiya amma bai kyauta ba da bai fada mana da wuri ba"


yayan Abban saimah su biyar ne yaya Muhammad wanda shi ne babba sai Mahmud mai biye masa sai kuma sadeeq wanda shi ne d'a na uku sai kuma mubarak sai kuma autar su saimah wadda ita ce ya mace daya tilo a wajen mama da Abbah, wannan yasa duk wani abu da xai farantawa saimah suke son shi.


Muhammad da Mahmud da mubarak duk sun yi karatun su ne a gida basu fita kasar waje ba,inda yanxu suke aiki a manyan ma'aikatu, yaya Muhammad da Mahmud duk sun yi aure da yayansu yanxu sadeeq da mubarak da saimah ne kawai suka yi ragowa.


sadeeq yayi karatunsa ne a kasar England a bangaren likitanci.


tashi mamah tayi ta fita daga dakin Abbah, dakinta ta nufa inda ta tarar da su Nauwar sun hada kai suna gulma, tsokanar su ta fara yi.


"An hada kai ana gulmar principle ko"


A raxane suka dago suka dubeta.


"rufa mana asiri mama ina mu ina xancen principle a gidan nan"


dariya suka bata don taga alamar sun tsani a ambaci sunan principle, sake dubansu tayi tana murmushi.


"To albishirin ku"
da sauri suka amsa mata da
"goro"
"ku shirya yau yayanku xai dawo"


tsalle suka fara yi suna murnar dawowar yaya sadeeq, duk da cewa Nauwar bata san kowane ne shi ba,bata taba ganinsa ba amma saimah tana yawan bata labarinsa, mutum ne mai saukin kai da barkwanci ga shi da son mutane, da dukkan alamu kuma jininsu ya hadu da saimah wannan dalilin yasa ita ma ta kosa ta gan shi.


wanka suka shiga suka fara shiri da wuri, dan sun san halin Abba baya son jira, shi yasa suka fara komai a akn lokaci.


karfe biyar jirgin su ya sadeeq ya iso, ba tare da bata lokaci ba aka tafi dakko shi.








*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆






7⃣9⃣






Suna isa gurin da gudu saimah ta karasa ta rungume shi, cike da farin ciki ya karaso wajen su Abbah,xubewa yayi har kasa yana gaida su, fuskar su a sake suka amsa masa, ita ma Nauwar tsugunnawa tayi ta gaida shi, cikin farin ciki ya amsa mata.
tambayar saimah yayi
"wannan kawar ki ce ya sunanta"
tana murmushi ta amsa masa da eh, sunanta Nauwar.


kayansa suka dakko aka xuba a mota suka wuce gida.


suna isa gida kai tsaye dakin mama suka shiga, tarar da ita suka yi ta shirya masa abinci kala-kala, dakkowa saimah tayi ta fara xuba masa, yana ci suna hirar yaushe gamo, bayan ya kammala ne ya dakko jaka ya shiga ciro musu tsarabar da ya kawo musu, ba kamar siyayya ya yiwa saimah ba, daga cikin kayanta ta debi rabi ta bawa Nauwar.


mama ce ta umarce su, da su dauki turaren wuta su saka a dakin yaya sadeeq, tashi suka yi suka fara abinda ta saka su.


bayan sun fita ne yake tambayar mamah.


"Mama ya kamata kawar saimah ta tafi gida kinga dare ya fara yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login