Showing 36001 words to 39000 words out of 111837 words

Chapter 13 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

komawa wajen boka, domin a shagalar da ita ga barin yin addu'a, saboda ta haka ne xa su samu damar cinta da ya'ki.


wannan karon magaji suka aika don yaje ya kar6o musu maganin, cikin farin ciki ya kar6i aiken, a ranshi ya fad'a banxa ta fad'i xan je na shana son raina


kai tsaye gidan magajiya ya xarce, don ya dad'e yana son samun kud'i,don ya hole son ransa, amma hakan ya ci tura, saboda rashin kud'in da ya baibaye shi.


yana fi to ya shiga gidan, ya iske magajiya a xaune kan kujera, tana faman busa sigari,tana ganin shi ta mi'ke tana farin ciki, tasan duk lokacin da magaji xai xo da kud'i yake xuwa, d'aki ta shigar da shi ta bashi lemo da abinci, sai da ya ci ya 'koshi sannan ya fara mata magana.


"Uwar shagalallu 'yar duma-dumar yarinya nake so yau a nan xan huce gajiyata"


busa sigarin da ke hannunta ta cigaba da yi, sannan ta kalle shi tana juya idanunta.


"duk 'yan matana basa nan sun fita, amma idan xaka iya jira sai ka jirasu har su dawo, amma fa ka tabbatar kaxo da wadataccen kud'i"


"Haba uwar daba, kin san idan ba nida kud'i babu abinda xai kawo ni gidan nan, aljihuna a cike yake"


zama yayi har sai da 'yan matan suka dawo, ya gama duk abinda xai yi, da yamma li'kis ya koma gida, suna ganin shi suka ri'ka murmushin farin ciki a tunanin su, yaje ya isar musu da sa'kon da suke so.


xama yayi ran shi a 6ace, kamar wanda wani abu ya same shi, tambayar shi innah karime ta fara yi


"lafiya naga kaxo ranka ba walwala, me ya faru"


idanun shi ne suka firfito waje, alamar rashin gaskiya ya baiyana a fuskar sa.


"wlh innah tun da na fita nake ta yawo a garin nan, kudin da ku ka aikeni da shi, sun fadi gaba d'aya,kuma ban san ya aka yi ba".


dafe kirji tayi tana duban shi.


"sun fad'i!!! kana hauka ne kaje ka xubar mana da kud'ad'e haka"?


"kaddara ce innah, wlh bansan lokacin da suka fadi ba nima, kawai gani nayi babu kud'in a aljihuna"


"karya kake yi tsohon munafuki, ko dai kaje ka bawa 'yan mata kud'in, don nasan yanxu abinda kasa a gabanka kenan"


Habi ce ta le'ko da kai daga d'akin.


"A'a innah karime kada ki yi wa jikana sharri,wane mata yaje yana rabewa kud'i, bana son irin wannan maganar ehe"


ganin bala'in da Habi take mata ne, yasa ta yi shiru saboda tasan tsiyar Habi ta fi tata.










*Jeeddahtulkhair*😘
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*




*Masoya na tafi Kwana da kwanaki ko cigiyata Ma ba a yi ba na gode, kuma Duk nayi fushi da ku*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


3⃣9⃣




Washe garin ranar Asabar suka yi shirin xuwa yawon neman asirin da suka saba, ba su yi wa kowa sallama ba suka kama hanyar Zuwa Dan batta, babu abinda xuciyar su ke musu saka face sharrin da xasu kulla don kawar da Ammi da yayanta Daga doron kasa Domin su samu Farin ciki da Jin dadi na har abada.


Da isar su tasha suka samu mota, ba tare da bata lokaci ba suka dauki hanyar garin Dan batta. basu fi rabin awa suna tafiya ba suka isa garin. A tashar garin motar ta sauke su don haka suka kama hanyar gidan boka don Ko gidan Baffa basu nema ba, suka wuce dan gudanar da abinda ya dame su. tafiya Kawai suke yi babu wanda yake iya cewa dan uwansa komai kasancewar dukkansu suna cikin damuwa da alhinin kudaden da suke batarwa ba tare da sun samu biyan bukata ba, isar su wajen ke da wuya suka tarar da kofar Bokan a kulle, mamaki ne ya kama su saboda tunda suke xuwa basu taba tarar da hakan ba. Don haka suka nemi wajen xama, suna jiran tsammanin ganin ta inda xai bullo.




Bai fi xaman awa daya suka yi ba, guguwa mai karfi suka ji ta tunkaro inda suke. Tsoro ne ya kama su,suka fara janye jikin su, wani irin gunji gami da gurnani guguwar ke bayarwa tare da dariya mai ban tsoro, ga wani haske mai cike da walkiya da yake tashi, matsawa suka fara yi, amma da sun matsa sai ta kara tunkaro wajen da suke.
Sai da ta xo daf da su wani hasken wuta ya bayyana


Mutum ne sanye da warki wanda aka hada shi da fatar damisa, hannunsa jere yake da guru da layu, gemunsa kuwa har jan kasa yake, ga wasa layu shirye a kugunsa da dantsen hannayensa idanunsa kuwa tamkar garwashin wuta, da dukkan alamu dai ba Bokan da suka sa ba xuwa wajen sa bane, don wannan na yanxu, ya fi wancan hatsabibanci, ja da baya suka shiga yi. cikin kakkausar murya ya daka musu tsawa
"Me ke tafe da ku"?? yana maganar wuta na fitowa daga bakinsa.


Cikin rawar murya innah karime ta amsa masa


"Dama wajen boka na innah Muka Zo sai kuma Muka tarar baya nan, dama.... Dama.......


Nuni yayi mata da hannunsa


"bana bukatar Jin komai Daga gareku"


Wani mudubi ya dakko a cikin wata salka ya mika musu, murmushi suka yi gami da gyada kai, alamun sun samu gamsuwa da aikinsa, hoton Ammin Nauwar ne ya bayyana da Abbansu da Duk yayansu gaba daya.


dago jajayen idanunsa ya yi, ya kalle su
"me kuke so a yi musu ? ya fadi maganar tare da fitar da hayaki daga bakinsa.
Muna hallaka mutum
Muna lalata shi
Muna raba soyayya, muna raba mutum da hankalinsa, muna tsinewa mutum.
Wannan duk aikina ne wanne Ku ka xaba a ciki ?


Innah karime ce ta dago da sauri ta kalle shi


Abinda muke so Allah gafarta ran boka, ita wannan matar tasa a haukatata, yar su kuma a sa ta shiga duniya Shi kuma wannan yaron nasu namiji a hallaka Shi, ta haka ne xamu samu mu mallake duk abinda muke so. Ko ya kika ce Habi ??


Tabbas xancen ki na kan tsari innah haka za a yi


Bushewa yayi da dariya an gama.


Wata laya ya dakko wadda ke kunshe cikin wani tsumma ya mika musu,da hannu biyu suka sa suka karba.


Ya xamuyi da ita Allah gafarta Malam?
Daka musu tsawa yayi tare da nuna su da hannu.
bana son yawan tambaya da karambani.


Wannan ku jefata a kogi, kuna jefawa xata haukace baxa ta samu sauki ba har abada, kafin ku isa gida yanxu xan tura uwar daji ta fara aikinta.
wannan kasar kuma Ku barbada ta cikin gidan muddin suka taka shi yaron kashinsa ya bushe ita kuma yarinyar ta yi bankawana da rayuwar gidan har abada.


Kudi suka mika masa, nuni yayi musu da hannu alamun baya bukatar komai daga gare su. Don haka suka tashi xuciyar su cike da Farin ciki.


Haka suka cigaba da keta dajuka da ciyayi a kan hanya suka ci Karo da Audu inda suka kwashe labarin duk abinda ya gudana tsakaninsu da boka, yayi farin ciki kwarai da gaske. ba tare da bata lokaci ba ya karbi layar don yaje kogi ya jefata su kuma suka wuce tasha don hawa mota.




Ammi ce kwance a kan gado idanunwanta na rufe ji take kawai kanta na juyawa, bata iya gane komai, addu'a ta shiga yi tare da karanta ayatul kursiyyu, wani duhu take ganin yana kusanto inda take, amma da ta karanta addua sai ya gushe, tana tsayawa sai ya kara kusanto ta, haka suka rika yi har xuwa lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, a cikin baccin taji kamar abu ya tsikareta don haka tayi saurin farkawa tare da ambaton Allah, duhun daxu ne ya kara dawo mata, juyawa kanta ya rika yi yawun bakinta ya kafe gaba daya ta kasa karanta komai, wata mata ta hango a cikin duhun ta kusanto inda take, idanunta jawur gashin kanta a tsafe, matsowa ta rika yi inda take tana kawo mata duka, da karfi taja hannunta ta danna mata wasu layu a baki, wani ihu Ammi take yi tamkar haniniyar doki tun daga lokacin bata sake sanin a duniyar da take ba.






*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*

*(Jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆






4⃣0⃣




Haka ta kasance cikin matsanancin hali har xuwa lokacin da su innah karime suka iso gidan, cikin gadara da nuna isa, suka tura kofar gidan danna kansu falo suka yi kawai ba tare da sallama ba. ihun Ammi suka ji yana tashi, cikin farin ciki suka karasa dakin da take tarar da ita suka yi kwance cikin mawuyacin hali, hada idanu suka yi suka tafa suka bushe da dariyar mugunta.


Guda habi ta shiga yi,
Alhamdulillah aiki ya biya,kwance gefen xaninta tayi ta fito da maganin da boka ya basu ta shiga barbada mata a jiki, nan da nan yanayinta ya sake sauyawa kamaninta gaba daya suka juye ta koma tamkar wacce ta fito daga jinsin shaidanu, ihu ta shiga yi tayo kansu a guje suka fice suka kulleta a dakin.


barbada maganin suka cigaba da yi a duk lungu da sako na cikin gidan,sannan suka koma dakinsu suka mayar da kofa suka kulle.


innah ce ta dubi Habi, "Allah ya amsa rokonmu xamu yi yadda muke so a gidan nan, wannan shekarar har aikin hajji sai mun je mun sauke farali"


"ai bokan nan karshe ne innah, ya iya aiki ga shi babu ko sisin mu sai riba da muka samu, jira nake yi yaran nan su dawo daga makaranta, su taka maganin nan, su ma tasu ta kare kowa ya huta, ni yanxu babban abinda ya dameni kada magaji ya dawo daga gantalinsa ya bi, ta kan maganin alhalin ba dan shi aka xuba ba, tashi mu fita mu yi gadin sa a waje kada garin neman gira mu rasa ido.


fitowa suka yi gaba daya,suka nufi kofar fita daga falon, xamansu ke da wuya Nauwar da fu'ad suka dawo daga makaranta, sallama suka yi musu amma ko yan kallo basu ishe su ba, don haka basu tsaya gaisawa da su ba suka nufi hanyar shiga cikin gida, tun daga bakin kofa suke jiyo ihu da haniniya kamar na doki, don haka suka saurara don jin ta inda ihun yake fitowa.


Nauwar ce ta dubi fu'ad
"ni fa ihun nan jinsa nake kamar daga cikin dakin Ammi yake"


tsayawa suka yi suka saurara sosai, sannan suka danna kansu falo,ba tare da tunanin akwai abin cutarwa a cikinsa ba, sai da suka kai tsakiyarsa, taji fu'ad ya saki wani ihu mai raxanarwa ya fadi kasa babu abinda ke fitowa daga bakinsa sai dafara, gigicewa Nauwar tayi ta rasa inda xata sa kanta, fadawa kanshi tayi tana kuka mai cike da ban tausayi.


"kada ka mutu fu'ad ka barni dan Allah ka tashi ka taimakeni dan Allah kayi magana"
da taga alamar dai baya cikin hayyacinsa nan da nan ta fita ta kira mai gadi aka saka shi a mota suka tafi asibiti.


da isarsu aka fara duba shi, aka bashi taimakon gaggawa ya fara farfadowa farin ciki ne ya cika xuciyarta sai a lokacin ta tuna bata ga Amminta ba, don haka ta dauki waya ta fara kiranta, wayar na ta ringing amma an ki dauka, sai da tayi mata missed call wajen goma ba a amsa ba, don haka ta fara kiran Abbanta ta sanar da shi halin da ake ciki, ba tare da bata lokaci ba ya dakko mota ya biyo su asibitin, a lokacin da ya iso jikin fu'ad ya kara tsananta ko hannunsa baya iya dagawa, hankalinsa ya tashi sosai, babu abinda yake iya yi banda hawaye.


tambayarta ya shiga yi ina Amminta da su innah karime


cikin kuka ta fada masa cewa Amminta ta tafi unguwa, su Innah karime kuma suna nan amma basu taho tare da mu ba.


A fusace ya dauki key ya fita don yaje ya same su ya ci musu mutunci, yana isa gidan ya tarar da su xaune sun baxa tabarma suna cin abinci, ko sallama bai musu ba ya hau yi musu fada.


"yanxu dan Allah innah ya kamata a ce fu'ad yana cikin wani hali kun kyale shi daga shi sai yarinya a wajensa babu wanda xai bisu yaga halin da suke ciki, ya dace abinda kuka yi.


innah ce ta karbi xancen


kayi hakuri Alhaji, abinda xan fada maka ba mai dadi bane kuma shi ne dalilin da yasa bamu bi yarinyar nan asibiti ba, sbd idan muka tafi tare da ita mu ma abin xai iya ritsawa da mu.


cikin mamaki ya dubeta
"wane abu ne ya faru, da har ku ke tsoron kada ya ritsa da ku?


hawaye innah karime ta shiga sharewa
"wlh Alhaji yarinyar nan makiyiyarka ce bata kaunarka bata kaunar ganin cigabanka da farin cikinka, guba ta bawa yaron nan yaci ya shiga wannan halin da yake ciki.


kallonta yayi idanunsa cike da kwalla, guba fa kika ce innah, anya Nauwar xata bawa fu'ad guba kuwa, yarinyar nan tana son dan uwanta da yawa fa.


wlh ba karya nayi maka ba Alhaji guba ta bashi, tunda ka kyaleta tana xuwa makarantar yahudawa komai ma xata iya aikatawa.


Falo ya shiga ya fada kan kujera ya rika kuka tamkar karamin yaro, sai dai har yanxu xuciyarsa bata gama yarda cewa Nauwar ce ta aikata wannan danyen aikin ba.


daurewa yayi ya tashi ya tafi asibitin sai dai yana dosar kofar dakin ya jiyo kukan Nauwar da mai gadi, da sauri ya karasa inda suke ya tarar da Nauwar kwance kan gawar fu'ad tana kuka mai cike da ban tausayi, cak ya dauketa yayi jifa da ita gefe guda ya shiga dukanta ta ko'ina, har sai da likitocin suka shigo suka karbeta.


tambayarsa suke yi, lafiya Alhaji, kawai nuna ta yake da hannu ya kasa magana sai kuka da yake yi


cikin kukan yake fada musu cewa ita ce ta kashe shi.


ita ma Nauwar din kukan take yi, kamar ranta xai fita.
"wlh bani na kashe shi ba Abbah"


mamaki ne ya kamasu don su kansu maganar bata bi jikinsu ba, daya daga cikin likitocin nan ya dafa kafadarsa
"Alhaji kabi abin nan a hankali a yi bincike don wannan yarinyar da gani baxa ta aikata haka ba"


ture hannunsa yayi,"kaga dakata malam, ba a shedar dan yau, baxan kyale maganar nan ba dole a dauki mataki"


wayarshi ya dauka ya kira yan sanda a mintunan da basu wuce biyu ba, yan sanda suka xo suka yi awon gaba da Nauwar don a gudanar da bincike.








*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*


*JEEDDAH TIJJANI*

*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*




*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*wannan shafin gaba daya naki ne halak malak kiyi yadda kike so da shi AYSHA AHMAD SANI (YAR LONDON) ana mugun tare*




4⃣1⃣








Tun a motar take ta rusa ihu, ita kam yanxu ji take kamar Allah ya dauki ranta ta bi fu'ad ta huta da bakin ciki da kuncin rayuwar da take ciki. suna isa police station din aka fito da ita daga motar suka shiga ciki domin a fara gudanar da bincike.


kuka take yi mai ban tausayi, cikin rarrashi da lallabawa yan sandan ke yi mata magana, "ki kwantar da hankalinki indai babu hannunki a cikin kisan yaron nan xaki fita,kiyi shiru ki daina kuka, yanxu xamu tura wakilin mu Asibitin su tabbatar da cewa guba aka bashi,ko mutuwar Allah da Annabi yayi, baxa mu yanke miki hukunci ba tare da mun bincika gaskiya ba.


kalaman dan sandan su suka kwantar mata da hankali ta ji sanyi a ranta, sannan aka umarci wata yar sanda ta shigar da ita jail


kukanta ne ya kara tsananta, yau ita ce a cikin mummunan matsayi, kuma da sa hannun mahaifinta aka kawota, yanxu tasan babu wani gata da ya rage mata, banda na Hamdan, tasan da yana gari da duk haka bata faru ba, don baxai taba barinta a cikin mawuyacin hali ba. ji take kamar ta bar duniyar ta huta da bakin cikin rayuwa.


bayan yan sanda sun tafi da Nauwar, Abbanta ya cigaba da kiran yan uwa da abokan arxiki yana sanar da su mutuwar fu'ad da abinda ya faru da Nauwar, amma babu wanda ya yarda da maganarsa, saboda yanxu kowa ya fahimci halin kunci da su Nauwar ke ciki ita da mahaifiyarta, kafin a dauki gawar likitoci suka tabbatar masa da cewa yaron ba guba ya sha ya mutu ba, kawai lokacinsa ne yayi, amma duk da haka yaki amincewa don haka suka kyale shi ya dauki gawar don xuwa a yi mata suttura.


bayan komai ya lafa hankali ya kwanta, mahaifin Hamdan yaje ya same shi don su tattauna a kan abinda yake faruwa da Nauwar, amma gaba daya ya birkice masa yaki xancen, sai hakura yayi ya kyale shi. A kullum su innah karime sai kara hura wutar bala'in suke yi suna dada xuga shi, wannan dalilin yasa bai sake komawa ta kan xancen Nauwar ba, ko abinci ba ya kai mata, sai dai yan sandan su ji tausayinta su bata, sai da tayi kwana 5 a hannunsu ba tare da ya waiwayi inda take ba.


A ranar da fu'ad xai cika kwana bakwai da rasuwa manyan unguwa da baban Hamdan suka hadu suka xo wajensa, domin samarwa Nauwar mafita, a bakin gate suka tarar da shi yana kokarin fita da mota, don haka suka dakatar da shi, bayan sun gaisa suka fada masa abinda ke tafe da su, sai da yayi kamar baxai saurare su ba, ganin yadda suka xo da yawa ne yasa suka yi masa kwarjini ya tsaya.


falo ya shigar da su, suka fara yi masa bayani


"gaskiya Alhaji abubuwan da suke faruwa a gidan nan basu kamace ka ba, ya xa ai a ce yaro ya rasu ka dorawa karamar yarinya laifi kace ita ta kashe shi, kuma likitoci sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login