Showing 93001 words to 96000 words out of 111837 words

Chapter 32 - ALMAJIRA Document Complete book .txt

daga gadonsa yana kewaye dakin, har yanxu dai bai daina jin hayaniyar ba, da gudu ya nufi falo, yana dosar wajen yaci Karo da Habi ta shaqe innah karime tana ta faman dukanta, cikin xafin nama ya karasa wajen.


cikin tsawa yake mata magana
"ke lafiyar ki cika ta mana, bakya ganin halin da take ciki"


Tsawa ta daka masa sannan tayo kansa da duka, kwancewa yayi ta samu bango.


duk iya kokarin da yayi don ya kwaci innah karime ya kasa, da gudu ya fita kofar gida yana neman taimakon jama'a, da kyar ya samo mutum biyu suka shigo gidan, kasancewar duk mutanen Unguwar haushinsa suke ji saboda abinda ya yiwa Ammi da nauwar, kokawa sosai suka rika yi da habi a kan ta saki innah amma taki sakinta kasancewar gaba daya bata cikin hankalinta ta xama mahaukaciya tuburan, idanunta sun yi ja, fuskarta ta xama baka kirin, kokawa dai suka rika yi da ita, cikin xafin rai take musu magana.


"baxan cikata ba sai na hallakata ita ce ta kashe mana jikoki "


Xance take yi mara kan gado, Lallabata suka shiga yi a kan ta kyaleta da kyar aka shawo kanta aka kwaci innah da kyar tana nunfarfashi duk ta galabaita.


Cikin hanxari suka tura habi daki suka kulleta, ita kuma innah karime suka dauke ta sai Asibiti, a ranar ko magana bata iya yi saboda wuyar da ta sha a Hannun habi, sai da aka yi mata karin ruwa.


Washe gari da sassafe Abban nauwar ya dauketa sai Dan batta, Baffa na ganin yadda innah karime ta koma ya fara hawaye, cikin kuka Baffa yake magana


"Me nake gani haka Mahmud lafiya me kuma ya Kara faruwa da ita"


Kan Abban nauwar a kasa ya fara yi masa bayani.


"Wlh Baffa ina daki ina bacci naji hayaniya ashe wai goggo habi ce ta kamata da duka kamar xata kasheta Yanxu haka daga Asibiti muke "


Cikin karfin hali Baffa yake magana.
"kayya amma wannan abu bai yi dadi ba, me innah tayi mata haka da xata yi kokarin hallakata"


"bata yi mata komai ba Baffa ta samu tabin hankali ne don yanxu bata gane komai"


A raxane Baffa ya dago
"tabin hankali fa kace Mahmud "


"Wlh Baffa, yanxu haka ma sai kulleta nayi a daki sannan na samu na fito, ni kaina kokarin dukana take yi, abin nata ya bani tsoro sosai "


Kuka Baffa yake yi sosai.
"ga irin ta nan mutum yayi mugun abu ya koma masa kansa, menene amfanin irin wannan ga tarin xunubi a wajen Allah ga Hauka gashi abin duniyar da ake kwadayi ba a same shi ba, yanxu idan ta mutu a haka me xata cewa Allah "


Rarrashin Baffa Abban nauwar ya rika, ita kuwa innah tayi shiru sai sharbar kuka da take yi, cikin kuka take magana.


"Bahaushe yayi Gaskiya da yace idan xaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, Wallahi wannan sharrin duk mu muka yi ya Koma mana kanmu, mudi ka yafe mana mu ne muka haukata matarka muka kada yarka muka juyar maka da tunani, ka yafe mana nasan idan muka mutu da hakkinka Allah baxai sassauta mana ba, Kaima ka yafe min, ta nuna baffan Mahmoud, na rabaka da danka na hana yaji kanka"


Kallon kallo Baffa da Abban nauwar suke yi ji suke kamar a mafarki suke jin wadannan maganganun nata.


Cikin nutsuwa Baffa ya dubeta.
"na yafe miki innah, Allah ya yafe mana gaba daya"


Hawaye Abban nauwar ya mayar mata da amsa


"innah ni ba nida abinda xance saboda iya cuta kun cuce ni sai dai nace Allah ya bi mana hakkin mu,duk wanda ya xalunci wani tsakanin ni da Ku Allah ya saka masa"


Tashi yayi xai bar wajen Baffa ya riko shi.


"Dawo mudi bana so ka fita a cikin bacin rai kada wani abin ya sameka kayi hakuri ko a yanxu sun ga qarshen su,Allah ya huci xuciyar ka, ga babban albishir xan baka, ka sanarwa habi cewa na saketa saki uku kada ta kuskura ta dawo min gida, kuma xan nemi yayanta na Kara jaddada musu, ita ma innah don mahaifiyata ce ita ta kawo ni duniya babu yadda xan yi dole na xauna da ita, ina umartarka dan Allah kana komawa gida ka kori habi duk inda xata tafi taje, ai duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai iya ba"


Innah karime kuka take tana rokon gafarar Abban nauwar amma ko kulata yaki yi, rokon Baffa ta shiga yi.


"kai kuwa kasa baki ya yafe min mana tunda yana jin maganarka "


"gaskiya baxan takura masa ba innah saboda wannan hakkin sa,shi yake da ikon yafe miki, ko ni na xalunce shi Allah sai ya saka masa, don haka ki cigaba da addu'a Allah ya sakko masa da fushinsa ya yafe miki"


A take Baffa yasa aka kirawo su Isah yayan habi ya shaida musu hukuncin da ya yanke, kuka suka rika yi suna jimamin halin da mahaifiyarsu take ciki, Audu ne Kawai yayi karfin halin yin magana


"Wlh dama Baffa ina Jin ciwon abubuwan da suke wa mudi Kawai don ba nida ikon hanawa ne shi yasa nayi shiru, gashi nan ta jawowa kanta hauka tana xaman xamanta"


Isah ne ya hau xage-xage.


"Wlh wannan haukan hada ta aka yi da shi, mu babu inda muka gaji hauka"


Innah karima ce ta fara magana.


"A dakata a saurareni wlh tallahi babu hannun kowa a cikin wannan Al'amrin mu muka jawo shi da kan mu, dan haka kada a Kara xargin Kowa habi ita tayi jagorancin haukata matar mudi gashi nan yanxu ya koma kanta, iyakar mu Allah ya fara nuna mana tun kafin aje lahira"


Tana gama jawabin sai kuma kunya ta kama Kowa a gurin wasu na kuka wasu kuma sun kasa magana saboda bakin ciki , haka Abban nauwar ya fito ya barsu suna jimami, Kudi mai yawa ya bawa Baffa sannan ya kama hanyar dawowa gida.








*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM* *(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆






8⃣7⃣




Tun a hanya yake sake-saken yadda xai bullowa Al'amarin habi, saboda baya jin xai iya cigaba da xama da ita a wannan halin da take ciki na hauka.


Yana isa gidan wani abin mamaki ya gani, gaba daya ta karya masa kofofin gidan ta fito waje, kwance ya tarar da ita kan yashi yara na jifanta da duwatsu ta cire dan kwalin kanta, tana bin su a guje tana duka, yana karasawa wajen ta yo kanshi xata dake shi cikin fushi ya fara yi mata magana.


"Waye yace Ki karya min kofar gida Ki fito, gashi nan ai kin fito yara na jifanki kamar shaidan"


Bata kula shi ba ta cigaba da bin yaran tana dukan su tare da jifansu da dutse, dawowa tayi ta cigaba da birgima a cikin yashin yara na yi mata waka.


"Habi mahaukaciya in ta mutu ba ruwan Allah, walakiri ya jibgi kayansa"


Suna mata wakar tana tsalle tana juyi, idan kuma ta gaji ta koma kan yashi ta cigaba da jifan su, wani bakin ciki ne ya kama Abban nauwar shigewa gida yayi ya kyale yaran suna tsokanarta.


Karasawa cikin gidan yayi, ba karamar barna habi tayi masa ba, a xuciyar sa yake magana.


"Lallai wannan shi ake kira da kaikayi koma kan mashekiya, Allah baya xalunci sai dai idan bawa ne ya xalunci kansa, gashi nan ta xama mahaukaciya cikakkiya wacce babu Wanda yasan ranar da xata warke sai Allah "


Fita yayi ya kira mai gyara inda ya shiga gyara abubuwan da ta bata, bayan ya kammala ne ya dubi Abban nauwar.


"xan tafi Alhaji kuma ina da yar shawarar da xan dan baka, ya kamata ka dauke mahaukaciyar nan daga gidanka idan ka barta ba a san irin barnar da xata yi nan gaba ba, kuma xaman ta a cikin Al'umma ba karamar matsala bace don xata iya cutar da su tunda bata cikin hankalinta"


Shiru Abban nauwar yayi sai da mai gyara ya gama jawabin saNyan ya bashi amsa


"gaskiya nima naga illar hakan, yanxu dama nake shirin kiran yayanta su xo su tafi da ita"


Waya ya ciro a aljihu ya kira Isah, sallama Abban nauwar yayi masa, cikin fushi ya amsa sallamar, bai tsaya yayi masa bayanin makasudin kiransa ba ya haushi da xagi, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har Yanxu bai yarda cewa mugun abinda suka yi bane ya koma musu kan su.


Murmushi Abban nauwar ya yi sannan ya mayar masa da amsa.


"dadin abin dai Kowa yasan abinda mahaifiyarka tayi min, abinda tayi a bayyane yake Kowa ya sani ba sharri aka yi mata ba, nayi niyyar na kaita Asibiti a rika bata magani amma tunda naga abin naka ba mutunci kaxo ka dauki uwarka, don baxan bari ta Kara Kwana a gidana ba"


Bai jira amsar da xai bashi ba ya kashe wayar.


Hakuri mai gyara ya rika bashi a kan ya bari ta Kwana gobe su dauketa amma yaki yarda, kudinsa ya dakko ya bashi sannan ya mayar da kofa ya kulle, ta taga yake jiyo hayaniyar yara da jifan da suke yi mata, duk sun farfasa mata goshi sai jini ke faman xuba, ko kadan bai ji tausayinta ba saboda ita ta jawowa kanta.


Bayan ya dan kwanta ne don ya huta yaji ana buga masa kofa, lekawa yayi don ganin wanda yaxo.


Hamdan ya hango a bakin kofar yana ta fara'a da hanxari ya karasa ya bude masa kofar, cikin sakin fuska yayi masa magana


"Sannu da xuwa Hamdan yau kaine a gidan namu"


Tsugunnawa Hamdan yayi ya gaida shi sannan suka shiga cikin gidan, Hamdan ne ya dubi Abban nauwar yana masa magana.


"Yau din nan fa farin ciki baya misaltuwa a xuciyata har gida aka xo aka fada min albishir din abinda ya samu matar nan, wlh ba karamin farin ciki nayi da hakan ba, bayan an fada min wannan abin dadin Kuma, sai na sake ganin wani abin alkhairin da idona"


Cikin sakin fuska Abban nauwar ya dube shi "wane abin alherin ka gano mana Hamdan "


Gyara xama yayi
"Yau ina gida ina ganin labarai Kawai naga an saka hoton ammi da nauwar ana cigiyarsu "


Cikin Farin ciki Abban nauwar ya rungume Hamdan yana tambayarsa.


"alhamdulillah a wane gari suke yanxu"


"suna Kaduna unguwar rimi"


Godiya Abban nauwar ya yiwa Allah a take ya dauro alwala yayi nifilar godiya ga Allah.


Juyo da kallonsa yayi ga Hamdan.


"yanxu xamu tashi mu tafi ko"


Murmushi Hamdan yayi


"A Haba Abba saurin me muke haka mu bari dai sai gobe ko"


Da kyar ya yarda suka bar tafiyar xuwa gobe, hirar su innah karime suka rika suna tattauna yadda karshen su bai yi kyau ba.








*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆






8⃣8⃣






Kiran Abban nauwar aka yi a waya cikin nutsuwa ya mika hannu ya dauka, Kara wayar yayi a kunnensa,da sallama ya fara sannan yayi shiru don sauraren abinda xai fito daga bakin mai maganar, gaisawa suka yi sannan mai maganar ya fara bayani


"nasan baka gane ni ba Alhaji Audu ne dan uwan ka mun xo tafiya da goggo ne"


Cikin sakin fuska Abban nauwar ya mayar masa da amsa.


"Allah sarki sannu da xuwa Audu ya hanya, gani nan xuwa na bude maka kofa "


Da sauri ya fita don bude masa kofar, a bakin kofar ya tarar dashi tsaye tare da Isah ko kallon Isah bai yi ba ya mikawa Audu hannu suka gaisa.


dudduba gurin ya shiga yi mamaki ne ya kama shi da bai ga habi ba.


Cikin rashin mutunci Isah yake magana..
"ina ka Boye mana uwar mu mugu axxalumi wanda bai san alkhairi ba, ka fito mana da ita ko ranka yayi mummunan baci"


Audu ne ya dakatar da shi daga fadan da yake yi
"Haba Isa me yasa Kake yin haka ne, Kawai sai ka hau fada baxa ka tsaya a bi komai a hankali ba"


"Sai da aka cuce mu aka haukata mana uwa xaka ce nabi abu a hankali baxan bi ba"


Cikin kulawa Abban nauwar ya dubi Audu.


"ka kyale shi ya xage ni ba wannan ne Karo na farko da ya fara xagina ba, dama ya riga ya saba"


Hakuri Audu ya rika bashi..


"kada ka damu ba komai"


Cikin gida suka shiga ya fara nunawa Audu irin barnar da habi tayi masa, bayan ya gama nuna masa ne ya fara yi masa bayani.


"kafin na dawo daga Dan batta, na tarar tayi min wannan barnar da yake dama a daki na kulleta na tafi, shi ne ta balle kofofin ta fice, ta koma kofar gida ta xauna, ban yi xaton ta tashi ta sake tafiya wani wajen ba, yanxu abinda xa a yi mu kewaya bayan layi ko xamu ganta"


Fita suka yi suka fara binciken inda ta tafi amma babu ita babu dalilinta, tambayar mutane suka shiga yi amma duk wanda yaji batun neman habi ne sai yayi tafiyarsa ya kyale su a tsaye, shi kansa Audu sai da jikinsa yayi sanyi da wannan bakin jini da habi take da shi.


Komawa kofar gida suka yi suka tsaya suna tunanin yadda xasu bullowa lamarin, daga can nesa suka hangota ta taho a guje ta dora tarin tsummokarai a kanta, yara na biye da ita suna jifanta, da sauri Audu da Isah suka karasa wajenta, magana suka fara yi mata.


"goggo haka kika xama Innalillahi wa innah ilaihi raji'un, ya aka yi haka ta afku da ke goggo"


Xare musu ido tayi ta fara jefo musu duwatsu, domin gaba daya bata gane su ba, matsawa kusa da ita Isah yayi ya karbi daurin kayan sannan suka kamata da kyar aka saka ta a mota suka tafi da ita gida.


Kudi mai yawa Abban nauwar ya bawa Audu sannan suka yi sallama ya tafi.


Wajen Hamdan Abban nauwar ya koma ya sanar da shi yadda suka yi da Isah mamaki ne ya kama hamdan.


"Lallai ma Isah ba shida tunani, duk abinda matar nan tayi maka bai gani ba har yana da bakin xaginka, Allah ya kyauta"


Bayan sun gama tattaunawa ne Hamdan ya yi masa sallama ya tafi gida.


A daren ranar da Abban nauwar xai tafi Kaduna bai ko runtsa ba saboda farin cikin xai hadu da iyalinsa da ya rabu da su lokaci mai tsawo, salloli yake yana godiya ga Allah da wannan niima da yayi masa.


Washe gari karfe bakwai na safe ya gama shiryawa tsaf, gidan su Hamdan ya nufa inda yayi sallama da mahaifinsa har cikin gida ya shigar da shi yayi sa'a kuwa sun shirya tsaf suna jiran xuwan sa.


Basu wani bata lokaci ba suka dauki hanya sai Kaduna, basu fi awa biyu suna tafiya ba suka isa Kaduna, inda suka tambayi mutane a nuna musu hanyar da xasu yi Unguwar rimi, cikin kankanin lokaci suka isa unguwar inda suka tambayi gidan su saimah aka nuna musu.


Yaro suka samu suka aika cewa ana sallama da maigidan, a tsakar gida yaron ya tarar da su suna karyawa, da sallama ya karasa wajen su sannan ya fada musu aiken da aka yi masa.


Tanbayarsa Abban saimah yayi..


"wane ne yake sallama da farar Safiya haka? "


Cikin nutsuwa yaron ya bashi amsa.


"wasu mutane ne su uku, sun ce na fada maka baki ne daga kano"


Nauwar na jin an ambaci baki daga Kano ta dubi saimah


"Nifa ina ji a jikina Abbana ne yaxo"


Saimah na murmushi ta dubeta
"to sarkin garaje kya bari dai su shigo a ga kowane ne ko"


Suna cikin wannan maganar ne ta jiyo murya Abbanta yana waya, tashi tayi a guje ta fita don ganewa idonta abinda take tunani.






*jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*


🍆🍆🍆🍆🍆🍆




*Masoyana na gode da addu,ar samun lafiya da kuka yi min Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci*




8⃣9⃣


Tsaye ta tarar da Abbanta ya tsurawa kofar gidan ido yana shirin ganin wanda zai fito daga ciki, nauwar ya gani ta taho a guje, hannu ya bude mata ta fada jikinsa tana murmushin farin ciki.


"Oyoyo Abbana, yaushe rabon da na ganka har na manta, ban taba tunanin xan sake ido biyu da kai ba, nayi zaton na barka har abada, Abba makiya sun saka katanga a tsakanina da kai, mun yi kewarka sosai ni da Ammi, mun sha wuya da bana tare da kai" kafin ta kammala maganar tuni hawaye ya cika idonta.


Toshe mata baki yayi hawaye na xuba a fuskar shi.


"kiyi hakuri "yata yau Allah ya kawo muna karshen wahalar da muke ciki, kamar yadda ku ka yi kewata haka nayi naku, tun da kuka bar gida ban kara samun nutsuwa ba sai yau, ki daina zubar da hawayen ki, yanxu ba lokacin kuka bane lokaci ne da xamu yi farin ciki da Allah ya hada mu da juna"


Share mata hawayen ya shiga yi da hannunsa.


Waiwayawa gefenta tayi, sai a lokacin tasan da su Hamdan, har kasa ta tsugunnah ta gaida baban Hamdan sannan ta mayar da kallonta ga Hamdan.


Wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da kallo mai cike da tausayawa, cikin sassanyar muryar sa ya amsa mata gaisuwar ta, suna cikin gaisawa Abban saimah ya fito da dukkan yan uwanta, Ammi na hada ido da Abban nauwar ta kawar da kanta gefe hawaye ne ke sauka cika idonta, karasowa yayi daf da ita yana rarrashinta.


"Kiyi hakuri Raihab ki dauka duk abin nan da ya faru kaddara ce, Allah yana sane da halin da muke ciki"


Cikin gida suka shiga gaba dayan su, abinci Kala Kala aka kawo musu, Sai da suka xuxxuba musu sannan suka fita gaba daya suka bar dakin don su samu damar cin abincin.


Bayan sun kammala Abban saimah ya shigo dakin.


Wajen zama ya samu sannan suka fara tattaunawa, Abban nauwar ne ya fara magana.


"Alhaji mun gode da wannan karamcin da kayi mana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login