Showing 9001 words to 12000 words out of 111837 words
Chapter 4 - ALMAJIRA Document Complete book .txt
shekara da shekaru, d'aukar masa jaka suka yi don shigar masa da ita gida. da sallama ya shiga gidan, inna karime da Habi ya tarar suna aikace-aikace, tsugunnawa yayi cikin ladabi yake gaishe su, amma ko d'an kallo bai ishe su ba, cigaba yayi da gaishe su, tsawa inna karime ta daka masa, cewa muka yi bamu ji ba, xaka damemu da gaisuwa, me gaisuwarka xata yi mana ne? da xaka takura mana, shasha irin mugun Abu, tsayawa yayi yana kallonta har ta gama surutanta, sannan ya d'auki jakarsa ya nufi d'akin Habi, yana kusantar d'akin,Habi ta biyoshi da gudu, kada ka shigar min d'aki jinin annoba, ka dawo daga yawon iskancinka xaka shigar min d"aki, uwarka ka ajiye a ciki, matsa ka bani guri irin ba'kin hali. hawaye ya ji suna taho masa yasa hannu ya share, ganin cin mutuncin da Habi da inna karime ke yi, yasa ya fita soro ya xauna yana ta shar6ar kuka.
Bai jima da xama ba malam Audu ya shigo, yana ganin d'an nasa farin ciki ya kama shi, ga mamakinsa xai ga d'an nasa cikin walwala amma ina sai yaga sa6anin haka, 'karasawa yayi yana tambayarsa, mudi me yasa kake kuka, yaushe kaxo garin nan ban sani ba? kasa bashi amsa yayi sbd ba'kin cikin da ya cika masa xuciya.
cigaba yayi da tambayarsa. ka fad'a min me aka yi, me ya faru da kai?cikin kuka Mahmoud ke magana "Inna da gwaggo ne suka xageni" don wannan ma kake kuka Mahmoudu, ai idan da sabo ka saba da cin mutuncinsu, yi hakuri Mahmouduna insha Allahu duk wadanda suke takura maka, sai sun ci arxikina, kuma sai 'ya'yan da ake so sun xauna a 'kar'kashinka, hawaye ya shiga share masa kayi ha'kuri tallafi marayan Allah, ubangijinka na tare da kai,kuma bai manta da kai ba. duk abin nan da suke yi ashe a kan idon Inna karime ake yin sa, tsalle ta doka ta fara masifa, ba amin ba shanyayye, uwarsa ta shanyeka, shi ma ya shanyeka dole ka riqa sambatu a kansa, to bari na gaya maka, indai arxi'ki ne,mudi yayi bankwana dashi, sbd bai gaje shi ba, har malam idi (kakan Mahmoud)ya mutu jakinsa d'aya ko gona ba shi da shi. su isah sune masu arxikin gidan nan, dan malam Habu mai duba ya dade da fad'a min haka,Mahmoud kuwa................... sai dai ya ga ana yi, jinin matsiyata kawai
*jeeddahtulkhair*π
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*β»EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
ππππππππππ
*Ina taya yar uwa MARIYA BABA ABDULLAHI(baby fine) murnar fara littafinta mai suna KAXAMAR MACEππΏββ, yadda aka fara lafiya, Allah yasa a gama lafiya*
*wannan shafin gaba dayanshi sadaukarwa ne gareki ATIKAH TIJJANI ADAM, Allah ya bar xumunci da kaunar juna, ana tareπ€π―*
1β£5β£
*S*hiru malam Abdullahi ya yi, yana sauraren inna karime har ta gama fad'anta, wucewa tayi ta tafi gida, xuciyar malam kuwa, xafi kawai take masa kamar xata fashe, saboda aibata d'an marayan nan da take yi. umartar Mahmoud yayi da ya tashi su fita bakin kasuwa ya siya masa Abinci,saboda yasan ba shi da rabo a gidan, sannan yayi Al'kawarin mayar da shi gidan malam gobe, saboda xamansa a nan xai iya haifar da wata matsalar, Mahmoud bai musa masa maganar da yayi ba, saboda shi kansa ya san inna ba 'kaunar ganinsa take yi ba, nisa da ita shi xai 'kara masa kwanciyar hankali, kuma xai fi xama mafi alkhairi a gareshi.
washe gari da sassafe Baffansa ya had'a masa kayansa,bayan sun karya kumallo, ya shiga d'akin inna ya gaisheta sannan ya sanar da ita cewa yau xai mayar da Mahmoud makaranta, ko tanka masa bata yi ba, haka ya gaji ya mi'ke.
kai tsaye tasha suka nufa inda suka samu motar da xata kaisu har cikin birnin kano, basu dad'e suna tafiya ba,suka iso gidan malam, malam Audu yayi mamakin ganin Mahmoud da wuri haka, a xaton shi xai dad'e bai dawo ba, saboda yadda yaga Mahmoud d'in na d'okin xuwa gida, kuma ga shi ya dad'e rabonsa da gidan, amma sai ga shi ya dawo a washe garin da aka kaishi, gaisawa suka yi da mahaifin Mahmoud, tambayarsa malam Audu ya fara yi, lafiya dai ko malam Abdullahi? lafiya amma ba lau ba, kasan sha'anin gyatumata da abokiyar xaman mahaifiyar mudi, basa 'kaunar yaron nan, basa son ganinsa ko kad'an, kuskure kad'an xai aikata su fara aibata shi da xagin mahaifiyarsa,duk da cewa tana kabari bata san abinda ake yi ba, wannan dalilin yasa na tattaro shi na dawo dashi, saboda tunda yaron nan yaje ba shi da kwanciyar hankali nima haka, ko d'aki ba a barshi ya shiga ba, a soro ya 'kare xamansa har na dawo dashi. Shiru malam Audu yayi har sai da Baffa ya kare maganarsa, gaskiya ne gara da ka dawo da shi d'in, ka 'kara ha'kuri malam Abdullahi wata rana sai labari, irin wadannan yaran da ake wulakantawa su Allah ya fi axurtawa, kuma ina son ka bar min yaron nan kada ya 'kara xuwa ganin gida har sai ya mallaki hankalinsa ya xama saurayi, amsa masa yayi da to Allah yayi mana jagora, hannu ya mi'ka masa suka yi sallama sannan ya tafi, zuciyarsa cike da farin cikin karamcin da malam Audu yake masa.
*****************
kwanci tashi asarar rai, yau ga shi Mahmoud ya kammala karatunsa na secondry, inda Mahmoud yake da shekara ashirin a duniya, kasancewar Mahmoud dalibi mai 'kwaxo, shi ya bashi damar samun shiga gasar da gwamnatin kano ta sanyawa daliban da suke da haxa'ka, don d'aukar nauyinsu, su yi karatu a 'kasashen waje, Allah ya bawa Mahmoud sa'a inda ya kasance d'aya daga cikin dalibai biyar da suka samu nasara, aka d'auki nauyin karatunsa a 'kasar sudan, farin ciki gurin malam Audu kuwa abin baya misaltuwa, ji yake kamar d'ansa ne na cikinsa ya samu wannan damar, ana saura kwana biyar su tafi, malam Audu ya umarce shi da yaje 'Dan batta ya yi wa mahaifinsa sallama, haka kuwa aka yi, ya shirya ya tafi don yi musu sallama.
wannan karon kasuwa ya je ya tarar da Baffan nasa, don baya son ya same shi a gida, ya 'kara cin karo da wulakancin inna karime, malam Abdullahi yayi farin ciki da ganin Mahmoud, sannan ya ji dad'in albishir d'in da yaxo masa da shi, albarka ya shiga saka masa, sannan ya yi masa fatan samun nasara a rayuwar karatunsa, yayi masa nasiha sosai a kan kula da addini da barin rud'in xamani. umartarshi yayi da su je gida ya yi wa su inna da gwaggonsa sallama, bai musa wa mahaifin nasa ba suka tafi, suna yin sallama suka tarar ba kowa a tsakar gidan, don haka suka nufi d'akin mutan gidan, sallama suka 'kara yi musu amma babu wanda ya amsa, sai kallon sama da 'kasa suke yi wa Mahmoud duk a tunaninsu ya xama d'an iska, malam ne ya fara magana, dama sallama yaron nan yaxo yi miku, jibi xa su wuce 'kasar sudan, gwamnati ta xa6eshi cikin yaran da xasu je su karanta harkar lafiya a can, Habi ce ta yi masa wani kallo mai cike da alamomin tambaya, sannan Inna karime ta d'ora da jawabi,da gwamnati ta xa6e shi sai akai yaya?dama indai kaga tururuwa ta fara fiffike ai ta tasarwa lalacewa, yanxu yawon iskancin ya cigaba har sudan to Allah ya kyauta, ni dai jikokina baxa su xama bayin turawa ba ina nan tare da su, ina ganin fad'i tashin da suke yi, kai kuma umma ta gaida Ashsha, mu ma mun huta da jaraba. ba wani fatan alkhairi da inna ta yi masa, haka nan ya fito ya barta, yayi sallama da Baffansa ya dawo gidan malam, dan ko kwana Baffansa hana shi yayi saboda halin Inna.
washe gari da asubar fari malam ya raka shi gidan gwamnati inda a nan ne xa a kaisu Abuja su hau jirgi, daga nan kuma su wuce sudan, malam yayi masa nasihohi masu ratsa jiki,sannan suka yi sallama dukkansu suna Hawayen rabuwa da juna.
*jeeddahtulkhair*π
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRAH*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeeddahtulkhar)*
*β»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
ππππππππππ
*Wannan shafin d'ungurungum sadaukarwa ne, gareku yara manyan gobe,ku yi yadda kuke so da wannan page, jeeddah ta baku shi halak malak FATEEMAH MUKHTAR LAWAN & FATEEMAH TIJJANI ISAH FAGGE (AMATURRAHMAN) ina yinku, ina sonku, muna mugun tareπ€ Allahu ya raya mana Ku a tafarkin sunnah, Allahu ya kareku daga dukkan abin 'ki, ya tsareku daga sharrin mai sharri*
*Baxan gushe ba ina mi'ka Godiya a gurin ki sisterna UMMIEY XEE ABAKSON, Allah ya 'kara d'aukaka da basira, jeeddah na godiya da kulawar ki gareta, kuma tace ana mugun tare*π€
1β£6β£
Da misalin 'karfe biyu na rana suka isa garin Abuja, tuni dama jirginsu ya yi ready, su kawai ake jira, don haka suna xuwa suka hau suka wuce sudan.
Sun sauka a garin MADANY a wata unguwa da ake kira RIYAD, inda a nan ne makarantar da xa su yi karatu take, ba tare da 6ata lokaci ba aka basu d'akin Kwana, sannan aka kawo musu abinci kala-kala, kowa sai da ya ci ya ture. Washe gari da wuri suka fita i xuwa d'akunan karatunsu, yana isa aji ya tarar har malamin ya iso, don haka yana shiga ya samu guri ya xauna, ana cikin karatun ne wata kyakkyawar yarinya ta shigo,taku take yi cikin nutsuwa, sanye take da had'ad'iyar doguwar riga,duk sai kallo ya koma kanta, malamin yana ganinta ya fara murmushin farin ciki, magana ya fara mata da harshen larabci *"HAYYAKILLAH"* Ma'ana ranki ya dad'e, ita ma da larabcin take magana d'an rusanawa tayi sannan tace *" SABAHUKAL AJMAL"* ma'ana barka da asubah, tambayarta ya fara yi *"LIMAXA TA'AKKARTI YA REHAB"* saboda me kika makara Rehab, sai a nan muka ji sunan yarinyar Rehab, sunkuyar da kai tayi sannan ta bashi amsa da cewa, *" ANA MASHGULAH LIXA TA'AKKARTU"* amsa mata yayi da *"MASHI, IMSH WA TAJLISI*" OK je ki xauna.
cikin nutsuwa take takawa har ta isa gurin da xata xauna, sannan aka cigaba da darasi, da misalin karfe 10:00 aka 'kare karatun, tunda dama lecture d'in 8:00-10:00 ne, don haka kowa ya wuce hostel, shi kuwa Mahmud ya samu bakin wata bishiya ya fara bitar karatunsa.
Yana cikin karatun tunanin Baffansa da na malam ya fad'o masa,sai ya tsinci Kansa yana mai hawaye, har yanxu yana jin xafin rabuwa da malam da Baffansa, saboda sun bashi kulawar da baxai iya mantawa da su a rayuwarshi ba, yayi xurfi a cikin tunanin Baffansa har ya manta da abinda ya kawo shi gurin, sallamar da ya ji an yi masa, ita ce ta dawo da shi daga tunanin da yake yi, da sauri ya juya ya fara share hawayen da ke sauka a kan kuncinsa,Rehab ya gani a bayansa, yayi mamakin ganinta, da abinda yasa taxo wajen shi, tunda yasan shi ba kowa bane a ajin, tambayar shi take *"LIMAXA RA'AITUKA TABKEE?*" murmushi yayi sannan ya girgixa kai alamar ba komai, matsa masa tayi da tambayar abinda yake damunsa, sai da ta matsa masa sosai, sannan ya fad'a mata yana tunanin Baffansa ne, tausayi ya bata, sannan tayi masa nasiha da ya tsaya ya yi karatunsa ta dauki alkawarin xata ri'ka taimaka masa da duk abubuwan da yake bu'kata, godiya mai yawa yayi mata sannan ta tambayi sunanshi ya bata amsa da "Sunana Mahmoud Abdallah", ita kuma tace sunanta Rehab Abu Fu'ad, kuma ta fad'a masa gidansu yana bayan makaranta, sun dad'e suna tattaunawa a kan matsalolin rayuwar duniya da yadda ya kamata su tsaya su fuskanci karatunsu, a 'kan'kanin lokaci suka saba da juna, saboda Mahmud mutum ne Wayayye ba shi da duhun kai, hakan yasa ya shiga ran Rehab suka xama kamar dama sun Dad'e da had'uwa, sai bayan magrib suka gama karatu, Mahmoud ya yi sallama da ita, har sun rabu ya kama hanyar xuwa d'akinsa ta biyoni shi, sunansa ta kira, ya juyo da fuskarsa ya amsa mata, alfarma ta nema a gurinsa a kan ya shirya su je gidansu ya ci abincin dare a can.
'Kin amincewa Mahmoud ya yi sai da 'kyar, ya yarda suka tafi gidan tare.
Bakin mota suka je,bud'e masa ta yi ya shiga sannan suka tafi.
Wani katafaren gida suka tarar, kana ganin yanayin ginin xaka tabbatar da cewa gida ne na masu arxiki, tsayawa siffanta yadda gidan yake ma xai iya xama 'kauyanci, saboda duk inda ake Neman Had'uwa gidan ya gaji da Had'uwa.
Horn tayi mai gadi ya 'karaso da sauri ya bud'e mata gate ta shiga.
Parking tayi, sannan ta umarci Mahmoud ya fito daga mortar, sannan suka shiga cikin gidan.
falon gidan suka nufa, sallama Rehab tayi, sannan ta yi wa Mahmoud magana da ya 'karaso.
Cikin nutsuwa ya bud'e 'kofar falon ya shiga, mahaifiyar Rehab ya gani xaune a kan kujera, jikinta lullu6e da laffaya da ganinta kaga dattijuwa mai addini, har 'kasa ya tsugunnah ya gaisheta cikin harshen larabci *"'DABA LAILUK*" (barkanki da dare)amsa masa tayi da *"KAIFUK"* (ya kake) murmushi yayi ya amsa mata da *"ALA MA YURAM"*(ina lafiya) tambayarsa tayi da *" MIN ANTA YA SHAB"* (daga ina kake d'an saurayi) xai fara magana kenan Rehab ta shigo hannunta d'auke da abubuwan sha kala-kala, ita ce ta cigaba da bayani a madadin Mahmoud, mamanta tayi farin ciki da shi, kuma ta yaba da Hankalinsa da nutsuwarsa, umartarshi ta yi da ya tashi yaje ya ci abincin da aka kawo masa.
Abinci kala-kala aka kawo masa wad'anda bai saba cin su ba, wasu kuma ma bai ta6a ganin irinsu ba, LUXX ne da ADAS Adas d'in Anyi masa jellof,sannan ga KIBDA ga kuma IDAMUSSAMAK, ga kayan shaye-shaye kala-kala.
Kad'an ya caccaki abincin ya tashi, kasancewar bai saba da cin su ba.
Yana gama ci ta nemi da yaje ya gaisa da Habbobanta (kakarta) nan ma da karamci aka kar6eshi.
Har bakin gate ta rakoshi sannan aka sa driver ya mayar da shi har hostel.
*jeeddahtulkhair*π
Ina yinku masoyana, dan Neman 'Karin bayani 08094136204
[9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: ππππππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
*β»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
ππππππππππ
*Baxan manta da 'kaunarki da kulawarki gareni ba, ina godiya da yadda kike nuna tsantsar kauna gareni, ina alfahari da karamcinki gareni,don haka wannan shafin gaba d'ayanshi sadaukarwa ne gareki, yar uwata MARYAM SANI LAGOS, jeeddah ta baki shi kyauta, kiyi yadda kike so da shi, ina yinki kamar yadda kike yi na*
*jinjinar ban girma gareki my lovely Sister NASEEBAH I UBAH (NASIBAH GAWO)Allahu ya bar xumunci da 'kaunar juna, Allah ya 'kara miki basirah da hasken makaranta, jeeddah tace ana tareπ€*
1β£7β£
Dakinsa ya shiga xuciyarsa cike da farin cikin karamcin da Rehab da iyayenta suka yi masa, tsintar kansa ya yi cikin tunaninta, sai ya zamto duk bugun da zuciyarshi za tayi sai ya tuna da ita, haka ya kasance har zuwa lokacin da bacci yayi awon gaba da shi. Bayan yayi sallar asubah, yayi addu'o'i ne ya 'kara mayar da kanshi ya kwanta, kasancewar ba shi da lecture din safe, nan ma dai xuciyar shi yaji tana tuna masa Rehab, shi kansa abin ya fara bashi mamakin yadda ya canja lokaci guda, tunda yake a tarihin rayuwarshi bai ta6a tsintar kanshi a son wata yarinya ba, amma sai ga shi yanxu, dare d'aya ya fara son wadda ta fi 'karfinshi. shawarwari xuciyarshi ta shiga bashi, a kan ya furta mata so, wata xuciyar kuma tace ya kyaleta kawai, saboda ba lallai ta amsa tayinshi ba. yanke shawarar sanar da ita ya yi don ya jarraba damarsa ko xata amince da shi. agogon da ke manne a bangon d'akin ne ya buga, shi ne ya katse masa tunanin da yake yi, 'karfe goma dai-dai ya gani, don haka ya mi'ke ya fara shirye-shiryen tafiya makaranta. cikin mintunan da basu wuce biyar ba, ya kammala shiryawa, kulle d'akinsa yayi ya fice.
'Dakin karatu ya nufa ya samu guri ya xauna ya fara d'aukar darasi, bayan an gama ne ya fito inda ya saba xama, don yayi karatu, bai dad'e da fara karatun ba, ya gano Rehab daga nesa tana masa murmushi, da fara'arta ta 'karaso wajen da yake, gaisawa suka yi sannan suka fara hira gami da karatu kamar yadda suka saba, bayan sun gama ne, suka yi sallama xasu rabu kenan Mahmoud yake sanar da ita halin da ya tsinci kanshi a ciki, ta yi farin cikin jin wannan magana daga gareshi, saboda ita kanta ta yaba da hankalinshi da yanayin tarbiyyar da yake da ita, da kuma addininshi, don haka basu samu wata matsala da junansu ba, suka fara soyayya mai tsafta da ban sha'awa, suka xamto tamkar "yan uwa.
A lokacin da suka shiga level 400 Mahmoud yake sanar da Baffansa cewa ya samu matar aure kuma abokiyar karatunsa ce, Baffa yayi farin ciki da wannan maganar, kasancewar duk 'yan uwansa sun yi aure, shi kad'ai ne ya rage a 'kasa saboda yana karatu, addua mai yawa yayi masa da fatan Alkhairi.
bayan sun yi magana da baffa ne ya nemi Rehab a kan ta sanar da iyayenta maganar aurensu,tunda dai suna son juna, da farko dai ta nuna 'kin amincewarta a kan baxa ta sanar da su ba, saboda ba lallai ne su aurawa Ba'kar fata 'yar su ba, kasancewar su larabawa ne, lalla6ata yayi a kan ta fad'a musu tunda suna addua insha Allah xasu amince da abinda suka xo musu da shi.
Tun da ta je wa da iyayenta maganar ta daina samun walwala da farin ciki daga garesu, saboda ita ce 'ya mace d'aya tilo a