Showing 1 words to 3000 words out of 113545 words
Chapter 1 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
KARFEN KAFA Chapter 41
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rfaida Umar
Assalamu alaikum. Ina gaida kowannenku. Allah Ya bar
zumunci🤩🤩🤩👏
Katafaren wurin hawa biyu ne, na farkon kayan snacks ne
kala-kala, saman kuwa wurin siyar da ice-cream ne
kowane irin ɗanɗano. A farfajiyar wurin kuwa kaji ne
manya gashin inji ake siyarwa. Kai tsaye saman ta haye ta
nufi wurin masu kula da wurin, ƴanmata da samari ne ƴan
ƙarya a wajen, basu ko tsonemata ido ba, burinta ta yi
abinda ya kawo ta ta bar wurin, sai dai tsayuwarta ba
jimawa kamar ance ta waiga, ido huɗu suka yi da juna,
daidai sadda ta fito daga wata ƙofa. Kallon mamaki da
tsana ta ke yiwa Ramlat har ta ƙaraso inda take a matuƙar
fusace.
"Ke! Wai ke wace irin mayya ce?! Duk yanda na kai ga
nesantaki da mijina hakan bai isheki ba? Wannan wane
irin bibiya kike mishi?!"
Ba Ramlat ba, gaba daya mutanen wurin suka maida
hankali ga Hajiya Zeenat dake tsaye tana cika da batsewa.
Ramlat ta kai maƙura da irin wannan cin mutuncin da
Hajiya ke mata. A yau ta ji shirun ya gagareta don haka ta
watsamata banzan kallo sama da ƙasa.
"Daga ke har mijinnaki ba ku isheni kallo ba. Kuma ma
banda abinki Mama, ai matar da ta yarda da kanta a
zuciyar mijinta, ta kuma yarda da mijinnata, babu wata
ɗiya mace da za ta razanata balle har ta damu kanta.
Sa'arki ɗaya, ba zan iya haɗa miji da sa'ar uwata ba, da
babu abinda zai hana ni auren mijinki ko don na nunamaki
bambancin aya da tsakuwa!"
Hannu Hajiya ta ɗaga da zummar marinta, caraf ta riƙe
hannun tana murmushi kafin ta yarfar.
"Kin yi kaɗan Mama. Mari wata dai ba Ramlat ba."
Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta kama hanyar barin
wurin, tana jin Hajiya na kwalawa Maigadin wurin kira, har
suka kusan cin karo da Ramlat, tana sauka yana hawa, ta
kuma ji sadda ta ke bada umarnin koda wasa ya ƙara bari
ta shigo wurin ya tabbata ranar barin aikinsa kenan.
Ranta a tsananin ɓace ba ta ko kallon gabanta sosai, ba
ta yi aune ba ta yi karo da mutum, tsantsin tiles da ya
kusan kifar da ita yasa ta saurin riƙe kafaɗarsa da dukkan
hannuwanta. Ƙamshin tsadadden turarensa ne ya kashe
dukkan wata lakar da ke jikinsa. Ko sakan ba ta yi ba ta
saita kanta gami da kauda hannunta a jikinsa, kallon kallo
suka yi. So yake ya tambayeta dalilin ɓacin ranta, amma
ganin wacce ke saukowa tana haɗa matattakala bibbiyu
zuwa uku yasa shi yin shiru.
"Dama na faɗa! Yarinyarnan karuwa ce! Karuwa ce! Kun
gani ko? Kun ga kalar iskancin da ta ke yi a jikin mijina
ko?!"
Samari da ƴanmatan da aka bari a sama tuni suka
garzayo ta jikin gilasai suna kallon ƙasan. Wadanda basu
taɓa ganin mijin Hajiyar ba sai a sannan suka ganshi,
ƴanmata ido ya soma wani kakkarwa, basu taɓa zaton
haka mijin Hajiyar yake ba. Wasu kuwa suna ganinsa a
wurin don mafi akasari don shi suke takowa su zo, amma
basu taɓa kawowa a ransu mijin wannan uwar matar ba
ce.
Ramlat ta dubeshi da idanunta wadanda ɓacin rai ya
sauya, gani take ya kamata ta rama abinda Hajiya ke
mata. Babu ruwanta da abinda zai biyo baya, idan har
hakan zai baƙantawa Hajiyar to a wurinta daidai kenan.
Murmushinta da ba kowa ke ganin irinsa ba ta jefamasa
gami da yi mishi kallon da sai ka rantse wani masoyinta
ne take tare da shi. Shi kuma har sannan ɓacin ran abinda
Hajiya Zeenatu ta yi bai sakeshi ba, fuskarsa a ɗaure. Sai
dai ganin irin murmushin da Ramlat ke mishi, bai san ya
akai ba sai ya tsinci kansa da maidawa kura aniyarta.
"Ka yi hakuri Heart, ko ma mene zan jure a kanka. Kar fa
ka yi tunanin zan bar ka a kowane yanayi, wallahi ta yi
kaɗan ta firgitani. Soyayya kuma yanzu muka fara. Ina jiran
kiranka."
Tana kaiwa nan ta ɗaga yatsunta biyu tana murmushi ta
bar wurin, Hajiya Zeenatu ta kunduma ashar gami da ɗaga
ƙafa da zummar bin bayanta, caraf ya riƙe damtsen
hannunta.
"Ba girmanki bane!"
Abinda ya fadi kenan cikin sanyin muryarsa kuma ƙasa-
ƙasa yanda ita ɗaya ce za ta ji, samari da ƴanmata wurin
da abinda Ramlat ta yi ya burgesu suka hau tafi da ihu har
da masu fiito. Baƙin ciki da takaici ya sa Hajiya watsawa
mijinta kallon banza da jajayen idanunta, ta yi rantsuwa
akan sai ta kashe Ramlat da hannunta. Hussein sai ya
raina kansa a hannunta. Ga mamakinta kamar karamar
yarinya ya shiga jan hannunta suka fita daga wurin ya
cusata a motarsa, fitowa ta yi ya dubeta.
"Ina za ki?"
Wani banzan harara ta watsamasa da ya sanya shi
rudewa. Ya kasa magana sai faduwar gaba.
"Ki yi hakuri."
Bakin ciki bai bar ta ta yi magana ba, ta rasa wannan
wane irin aiki ne, wani sa'in ya yi tasiri a kansa, ya dinga
shakkarta, wani sa'in kuwa sai ka rantse babu ko ɗigon
asiri a kansa.
"Ai ba kai ka kawoni ba! Ka motarka ka bar wurinnan tun
kan na yi maka abinda za ka yi nadamarsa!"
Kamar wanda mahaifiyarsa ke ba shi umarni, ya bude
gidan gaba ya shiga. Gilasan duk a sauke.
Kallonsa Hajiya Zeenatu ke yi har ya tashi motar,
fuskarnan ba'a sake ba kuma ba'a ɗaure ba, duk iyakar
nacinta ta kasa gano kalar rikiɗewar da maganganun
Ramlat ya jefashi ciki. Idan ta tuna ranta baƙi yake, komai
dangane da Ramlat take da buƙatar sani. Wannan kuma
ba zai mata wuya ba, ta ci alwashin rusa dukkan farin
cikinta koda za ta rasa dukkan abinda ta mallaka. Jikinta
ke ƙara ba ta ita ce yarinyar da Isuhu da Gora suka yi mata
gargaɗi a kai.
Har ya bar wurin ba ta fasa kallonsa ba kafin a rikice ta
shige nata motar ta bar wurin. Kai tsaye gidan Hajiya
Batool ta nufa.
***
"Me na faɗamaki?! Ke kin tsaya kan lallai ba za ki bar
garinnan ba da hannunki za ki ɗauki mataki a kan yarinyar!
Ai wallahi Zeenatu ji nake kamar na ɗaukeki na jefa a
wuta tsabar haushin da kika bani!" Hajiya Batool ke zuba
wannan ruwan masifar kamar ta ari baki. Dama cike take
da ɓacin ran yanda tana wankan magani a tsakar gida
Maigadinta ya ganta, takaicin ya ɓatamata aiki ne yasa ta
sallameshi ta kuma yi mishi gargadi mai girma akan
yunƙurin tona asirinta.
Hajiya Zeenatu ta share hawaye.
"Wannan bala'i da me ya yi kama, yarinya ta zamemin
ƘARFEN ƘAFA? Yarinyar da a haife a haifi wanda ma ya
girmeta balle ita? Wallahi ina kara fadamaki kowane gari
zan je tunda har aka tabbatarmana sai ya aureta toh za ta
biyoshi tunda mayya ce. Abu ɗayan dai shi ne mafita, na
kasheta da hannuna ko kuma na gallabi rayuwarta ta
yanda na lahira ma sai ya fi ta jin dadi. Batool ina son
Hussein fiye da yanda nake son rayuwata, ba irin mazan
da ake dandanawa bane a kyale, kuma wallahi wallahi ko
zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu."
"Au kin ma san sunanta ashe?"
Ta gyada kai.
"Har inda take aiki na sani, zan kuma ci ubanta."
Hajiya Batool ta jinjina kai cike goyon bayan aminiyarta.
"Duk abinda ya dace ki aikata ki yi idan har zai nesanta ta
daga Hussein. Amma kafin komai, ki soma yi mata
kyakkyawan gargadi, idan ta ji shikenan, idan kuwa bai
samu shiga ba sai ki aikata yanda kika so."
Da haka suka ci gaba da saƙe-saƙensu akan Ramlat.
***
Ramlat kuwa, wani wurin ta nufa ta yi musu siyayya, ko
kusa ba ta ji ko ɗarr da abinda ta aikata ba asalima wani
irin murmushi da dariya take ita kadai a mota cike da
nishadi. Ko ba komai yau ta rama abinda Hajiya Zeenat ke
mata akan zargi da baƙin kishi irinnata. Da wannan
nishaɗin ta isa gida, Hajiya sai da ta kasa hakuri ta
tambayeta. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta sanarmata duk
yanda lamuran suka faru. Baki sake Hajiya ke dubanta.
"A'a Ramlatu, kar fa ki jajiɓomana abinda ya fi ƙarfinmu.
Ke ko tsoro ba kya ji."
Taɓe baki ta yi haɗe da murmushi tana kokarin kai tsokar
nama bakinta.
"Hajiya kar wannan ya dameki, daidai nake da ita tunda ita
ba ta da hankali. Ni wallahi ban yarda da ita ba ma."
Jinjina kai Hajiya ta yi.
"Ba dai ruwanki da ita, idan ta yi miki sanadin aiki ai ta
gama da ke tunda ta san inda kike aiki."
"Da yardar Allah ba ta isa ba."
"Ai shikenan."
Faɗin Hajiya ta ƙara da addu'ar neman tsari, Ramlat ta
amsa da amin gami da lumshe ido kadan tana tuno da irin
kallon da Hussein ya ke jifanta da shi, kallon da ya nemi
rikitata ta kasa abinda ta ci burin aikatawa, taimakon Allah
ne kaɗai yasa ta ƙarasa jawabinta ta bar wurin. A gefe
guda tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, ta kuma
ƙudurta taimaka mishi da addu'a don hankalinta bai
kwanta da Hajiyarsa ba.
Misalin karfe sha daya na dare, tana kwance Affan a
gefenta ya yi bacci, ita kuwa tana kan whatsapp suna hira
da Amrah tana bata labarin abinda ya faru yau suna dariya
har Amrah ke gargaɗinta akan irin wannan gangancin
acewarta irin su Hajiya ba haka suka tsaya ba. Dawowar
mijin Amrah ne yasa suka yi sallama ta ɓige da kallon
status. Da sauri ta mike zaune tana ƙara kallon sunan
Mutumin Mall kamar yanda ta yi saving lambarsa. Status
ya dora na wata yarinya kyakkyawa da ba ranar ta soma
ganinta ba.
"Dama yana whatsapp ban taɓa lura ba?"
Ta fadi a fili kamar mai jiran amsa daga wani ko wata.
Kallon hoton yarinyar ta shiga yi tana murmushi.
"Fatima." Ta furta a fili sannan ta yi screenshot. Hoto na
gaba ne ya kusan zautar da tunaninta, ji ta yi cikinta ya
murɗa, ta ajiye wayar ta faɗa banɗaki sannan ta fito. Gumi
na tsastsafomata ta ƙara ɗaukar wayar tana dawo da
hoton baya ta kalla.
Su biyu ne cikin shigar ƙananun kaya iri ɗaya sai
bambancin kala. Ɗaya yana sanye da farin t-shirt, ɗayan
kuwa sky blue ce. Banda hakan da kuma farin gilas din da
ya ɗaya ya sanya a idanunsa, za ta iya rantsewa ta ƙara
duk na hoton mutum ɗaya ne. Kuma nan take za ta ce
HUSSEIN ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton ne yasa ta
yin salatin da ba ta shirya ba.
"Idan kana raye Hussein, ina riƙon Allah Ya bayyana mana
kai. Ƙwaƙwalwa da zuciya ba zasu taɓa yarda cewar ba ka
tare da mu ba."
Cikin sauri ta yi screenshot na hoton sannan ta yi cropping
ta yanke wurin rubutun mai kama da cigiya kafin ta yi
saving, hannunta har rawa yake yi. Tana so ta ce mishi ta
san inda dan uwansa yake amma ta fi son ta tabbatar da
zarginta. Tana son Hussein ya yi ido hudu da hoton ta ga
yanayin da zai faɗa. Anan ne za ta san yanda za ta ɓullo
ta faɗawa mutumin mall inda ɗan uwansa yake. Dama ita
sam ba ta yarda da Hajiya Zeenatu ba, yanzun kuma ta
ƙara tabbatar da zarginta. Ta kara komawa kan Status din,
ga mamakinta ya cireshi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, tunda
dai ta yi screenshot ai shikenan.
A daren dai baccinta ragagge ne, ita kanta ba ta san inda
za ta ƙara haɗuwa da Hussein ba balle har magana ta
haɗasu na dogon lokaci sai dai hakan bai karyamata
gwuiwa ba. Ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba.
***
Tuƙi yake amma murmushi yake yi akai-akai, daki-daki
yake tuna kalamanta da irin kallon da ta jefeshi da shi,
koda ace bai kai zuciyarta ba, ba ta da masaniya akan
tasirin da ya yi mishi.
Ya ɗan kalli garin yanda ya yi luf luf, yammaci ne kuma
babu rana dalilin damina da ke kokarin shigowa, wurare
da dama a garin Kano ya samu labarin an yi ruwa. Bai
tsaya ko'ina ba sai a wurin Gym dinsu. Ya fito sanye da
wandonsa three quarter sai rigarta marar hannu sai baƙar
jaka da ya rataya a kafaɗarsa. Da wannan ya nufi ciki inda
nan ya tarar da Hisham ya dage sai ɗaga ƙarfe ya ke. Suka
yiwa juna dariya gami da cafkewa.
"Shegen sama! Ban tsammaci ganinka nan kusa ba ai. Ka
biyewa aure ka soma ajiye tumbin."
Dariya Hisham ya yi yana tsane gumi da ɗan ƙaramin
towel.
"Ba'a magana kai kam, aure ƙarshe ne. Wallahi ba don kai
ba bazan fito ba don bani da niyya, sai gashinan ka
shanyani sai yanzu."
Zama Hussein ya yi yana gyara ɗaurin igiyar fararen
canvas ɗinsa.
"Yi hakuri. Ban kyauta ba kam."
"Ina jinka, ya akai?"
Hussein ya ɗan yi shiru don bai san ta inda zai fara ba,
can dai ya numfasa.
"Za ka tuna yayar Madam dinka da na kai gida?"
'Anzo wajen.' Hisham ya ayyana aransa, murmushi ya yi.
"Yes, Antinmu Ramlat."
Ya gyada kai yana shafa suma,
"Ita, sun samu matsala da Madam ɗita. Ina kuma tsoron
kar ta yi mata sanadin aiki da ma abubuwa da dama.
Nasan halinta da baƙin kishi."
Cikin rashin fahimta Hisham ya ce.
"Yimin dalla-dalla."
Tun farkon ganinsu da Ramlat har zuwa abinda ya faru a
A&Z bai ɓoyemishi ba. Hisham dai ya cika da mamaki,
diramar ƙarshe ta ba shi dariya sosai ya kuma yi mamaki
don bai zaci Ramlat din za ta aikata ba. Ɗaukar ta ya ke
matsoraciya kuma shiru-shiru marar son hayaniya.
"Mamaki nake."
Hisham ya fadi yana ci gaba da dariya gami da riko
hannun Hussein da ke binsa da kallo kamar ranar ya soma
ganinsa.
"Wai meye hakan?"
"Um um, amma fa duk da bansan wannan Madam din
taka ba, gaskiyar magana ta ɗauki hanyar da ba zai ɓullar
da ita ba. Kishi ko hauka? Ba ta san yanzu kai ya waye
ba? Nikam Ramlat ta burgeni wallahi, wannan ma.."
"Nima ban ce ba ta kyauta ba, amma na fi ta sanin
matata. Idan a kan kishi ne komai ma za ta aikata. So
nake ka ja mata kunne don Allah, ta nesanta kanta daga
inda zasu haɗu balle har wani saɓanin ya ƙara shiga
tsakaninsu."
"Abinda ban gane ba, tausayinta kake har kake son ba ta
kariya ko kuwa tsoron Madam dinka kake?"
Hussein ya yi shiru bai amsa ba can kuma ya dubeshi.
"Alaƙar da ke tsakaninta da matarka na duba, amma fa
zahirin gaskiya ba ta kyauta ba. Ko ba komai dakyar na
shawo kan Madam ta fahimci dagasken ba komai
tsakanina da ita. Kar ka ƙara cewa ina tsoron matata." Ya
ƙarashe cike da rashin gaskiya, shi kansa ya sani yana
shakkar Hajiya Zeenatu.
"Kuma dagasken ba komai tsakaninka da Ramlat?"
Gabansa ya fadi, ya kauda kai daga duban Hisham gami
da ɗan murmusawa.
"Yarinyar kallonta nake kamar irin Boss ɗin nan, komai ta
yi dariya yake ban, tana burgeni. Amma ban taɓa son wata
irin son da na yiwa Hajiya ba,har gobe bana jin akwai
wacce za ta kai Hajiya a zuciyata."
Ya ƙarashe da wani irin rauni na zuciya da gangar jiki, a
karon kansa yake ji kamar ba hakan bane, amma a wani
ɓangaren na zuciyarsa ji yake kamar ana ƙara tabbatar
mishi da cewa eh! Ba shi da kamar Hajiya Zeenatu.
"Owk!" Abinda Hisham ya ce kenan, ya ji kuma ba don ya
yarda ba. Ya hango abubuwa da dama a saman fuskar
abokinnasa. Can ya ƙara karambanin watsamasa tambayar
da ya taɓa kwatanta yinsa bai ji da dadi ba.
"Kai wai yaushe za ka kaini na gaida Mummynmu ne?"
Kamar walkiya, ya nemi annurin fuskar Hussein ya rasa,
kamar wanda ya haɗiyi garwashin wuta, haka fuskarsa ta
soma wani ja-ja ga gumi da ya soma tsirfowa saman
goshinsa. Miƙewa ya yi kamar wanda aka mintsila ya
dauki jakarsa. A ruɗe Hisham ya miƙe tsaye ya riƙe mishi
kafaɗa ya fisge har hannunsa na bugun wani ƙarfen motsa
jiki, koda da zafi, bai ji ba. Yatsa ya shiga nunawa
Hisham. Ya soma magana da muryar da ta ɗauki hankulan
jama'ar wurin.
KARFEN KAFA Chapter 41
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
"Kar ka ƙara! Wannan ne gargaɗi na ƙarshe da zan maka!
Bana so! Har abada banda kowa a duniyata sai Hajiya
Zeenatu! She meant everything to me! Ita kadai ce
dangina. Ka rike wannan ka ji?"
Ya ƙarashe a sanyaye, abin mamaki hawaye ya shiga
fitarwa, a hankali ya juya ya soma taku ya bar Hisham
tsaye a wurin baki a bude. Ga mamakin Hisham da
mutanen wurin, faduwa ya yi. A guje suka yi kansa,
Hisham ya tallafoshi, idanunsa a rufe sai numfashi yake
fitarwa sama-sama
"Hussein, me ya yi zafi haka? Ka yi hakuri don Allah."
"Maida ni gida." Abinda ya iya fada kenan cike da wata
iriyar kasala. Jama'ar na ta yi mishi sannu, wani ya riƙe
jakar yayinda Hisham ya saƙalo hannun Hussein a
wuyansa suka nufi motar Hussein din. Sai da ya zaunar da
shi kafin ya koma da sauri shima ya dauko tarkacensa ya
zuwa a aljihu suka bar wurin. Yau ne zuwansa gidan
Hussein karo na farko, dakyar yake mishi kwatance
wannan karon muryarsa ta bude ba kamar ɗazun ba kamar
yanda idanunsa suka bude sosai. A gaggauce Maigadin ya
bude ƙyaure ganin motar maigidan, Hisham ya tura hancin
motar ya faka.
Hajiya Zeenatu na zaune a falo tana amsa waya ta ji
sallamar da ba muryar mijinta ba. Turus ya yi kamar yanda
itama ta yi tsaye tana dubansu.
Ganin yanayin Hussein ya sa ta ƙarasawa da sauri.
"Habeebee meke samunka? Kai kuma waye?"
Hussein ya zauna ya amsa.
"Hisham ne."
Ta dubi yanayin Hussein din sannan ta dubi Hisham wanda
ke gaidata. Ta amsa fuska na yabo ba fallasa ganin irin
duban mamakin da ke saman fuskarsa. Ya riga ya gane
matsayinta wurin Amininsa don tun shigowarsu idonsa ya
kai ga makekan enlargement din da ke dauke da
fuskokinsu. Daga irin rikon da ta yiwa Hussein kadai ya ci
ace duk mai hankali ya gane alaƙarsu.
'Taɓ!' Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa. A ƙarshe ya
daure ya ɓoye mamakinsa ya saki fuska. Zai ba ta bayanin
abinda ya faru ne ya ji Hussein ya tareshi cikin rawar
murya.
"Amm..dama kaina ne ke ciwo da jiri, ganin ba zan iya
tuƙi ba yasa nace ya kawoni. Kiyi hakuri idan ganinsa ya
ɓatamaki rai."
Sai lokacin ta wayance gami da sakin fuska
"Haba kai kuwa, mene abin ɓacin rai don abokinka ya
kawoka? Wani zubin kamar yaron goye idan ka fadi wani
zancen. Sannu, zauna mana bari na kawomaka ruwa."
Hisham ya girgiza kai yana dariyar yaƙe.
"A'a ba komai tafiya zan yi, nima yawa Amaryar na jirana."
Suka yi dariya, ya yi mata sallama sannan ya fice cike da
tsantsar mamakin wacce ya gani matsayin matar
abokinsa.
"Akwai wata a ƙasa." Abinda ya ce kenan bayan fitarsa
daga gidan. Jikinsa ya ba shi akwai wata a ƙasa.
Har ya koma wurin Gym ya dauki motarsa ya yi gida, bai
bar tunanin lamarin Hussein da matarsa ba. Da ma duk
abinda ya faru tsakaninsu.
***
"Wai mene ne?"
A'isha ke tambayar Hisham cike da damuwa ganin yanda
yake mata Safa da marwa a tsakar falon, idan kuma an
ɗan jima ya ce "Taɓ!"
Ya dubeta sai ya kama hannunta suka zauna.
"Ba komai Princess, kar ki damu. Amm..please kiramin
Antinmu a waya ki ban."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Wacce a ciki?"
"Ramlat."
Nan da nan tunanin A'isha ya tafi wani bigiren, murmushi
ta yi don gani take fatanta ne zai tabbata tsakanin abokin
mijinnata da Yayarta. Ta mike ta nufi ɗakinta ta dauko
wayar kai tsaye ta dannawa Ramlat kira.
Bayan ta ɗaga sun gaisa ta sanarmata saƙon Hisham
sannan ta miƙa masa.
"Ranki ya dade Antinmu."
Daga daya bangaren Ramlat ta ɗan yi murmushi mai
sauti.
"Angon ƙanwata fatan kuna lafiya?"
"Lafiyarmu kalau, don Allah alfarma nake nema a wurinki."
"Toh wace iri?"
"Ina son idan kin samu lokaci ki zo gidana ko kuma na
sameki wurin aiki wata ƴar magana zamu yi mai
muhimmanci."
Shiru ya