Showing 30001 words to 33000 words out of 113545 words
Chapter 11 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
kanta take yi cikin lamuran Hussein
dumu-dumu. Idanunta ga cicciko da kwalla, ta sharesu. Ya
dace ta yi baya-baya da shiga shirginsa tun kafin ta yi
nisan da ba ta jin kira a sha'aninsa. Ko babu Hajiya
Zeenatu, Hussein ya fi ƙarfin ajinta. A ganinta, wutsiyar
raƙumi ta yi nesa da ƙasa.
Haka ta wuni cike da kasala, sai dab da Magriba sannan
ta fito ta faɗa kicin, kunu ta dama, ta zubawa Hajiya wacce
ke azumi cikin flask mai riƙe zafi. Dama ta iske tuni an yi
Ƙosai. Wannan tasa ta haɗamata da lemun zoɓo da ya sha
kayan ƙamshi.
Sai da ta tabbatar ta haɗa komai saman darduma kafin ta
koma ɗaki, alwala ta ɗauro. Wayarta na kyallin shigowar
saƙo don haka ta duba.
*"Thank You."*
Abinda ya turomata kenan. Murmushi kawai ta ɗan yi ta
shimfiɗa darduma.
Misalin ƙarfe takwas da rabi suna zaune a falo tare da
Hajiya, kallon Tarkon Ƙauna suke a tashar Arewa24. Gaba
ɗaya hankalin kacokan yana kan talabijin, sallamar Baba
Maigadi ta ɗauki hankulansu. Suka amsa. Saƙon Ramlat ta
yi baƙo yake tafe da shi. Nan da nan ta ɗaure fuska, tana
da tabbacin Chairman ne don dama Kawu yace ta zuba
idanun ganinsa a satinnan.
Umarnin Hajiya ta bi kawai ta miƙe ta shiga ɗaki, Hijabin
sallarta ta zura ta fita. Kamar dai yanda ta tsammata hakan
ce kuwa, yana tsaye ya sha wata narkakkiyar shadda da aka
yi mishi aiki a jiki. Ƙaton tumbinsa shi za ka soma haskowa
kafin ma ka kai ga ganin komai.
"Mtsw." Ta ja guntun tsaki tana jin kamar ta juya, dolenta ta
daure ta ƙarasa. Ganinta ke da wuya, ya ƙara daidaita
tsayuwarsa yana mai ƙuramata idanu ga wani haƙoransa da
suka bayyana shi a dole murmushin ƙauna ya ke.
"Ranki ya daɗe Ramlatu."
"Ina wuni."
Ta gaidashi ciki-ciki.
"Lafiya kalau Hajjaju. Wato sai kika ganni kwatsam. Wallahi
kasa hakurin na soma kiranki nayi saboda jina nake kamar
na shiɗe jiya tsabar tunaninki da ya.."
"Ina mai neman alfarmar ka tafi kai tsaye ga abinda ya
kawoka, komai nawa nakan ba lokaci muhimmanci. Da ace
dai ka sanar da ni zuwannaka tun wuri zan fi samun
sukunin tsakurar maka mintoci kaɗan daga lokutan da nake
sa shi. Yanzu dai akwai abinda nake yi ka katsemin hanzari.
Amma bari na ƙara faɗamaka haƙiƙanin abinda ke zuciyata
dangane da kai. Inaga hakan zai taimaka wajen ganin ba
mu shiga haƙƙin juna ba."
KARFEN KAFA Chapter 53
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Chairman Dikko wanda ya zubamata idanu kamar ya
haɗiyeta tsabar so, ya jinjina kai gami da gyara tsayuwa.
"Na ji abinda kika ce, ko daga yanda kika tarbeni nasan me
kike nufi, kar ki manta kin faɗamin ai tun kafin na tako nan.
Amma Hajiya Ramlatu, duk wasu bayananki ba zai sa ni
Dikko na haƙura da ke ba, ina sonki, wani irin so da rabona
da shi tun a kan Mairo uwargidata. Don haka zan jure
dukkan ƙiyayya, na rantsemaki da Allah kika shigo gidana
ba za ki ƙara marmarin fita ba saboda daɗin da zan jiyar da
ke. Ga kuma madarar ƙauna."
Ya ƙarashe da wata shaƙiyiyar dariya. Ta bishi da kallon
tsana, ta sauke idanunta kirjinta na ƙara zafi. Kasa cewa
komai ta yi har ya kammala sumbatunsa, karshe ta
dubeshi.
"Dare ya fara, na kuma gaji da tsayuwar."
Ya sauke ajiyar zuciya gami da duban agogo.
"Wallahi ban san lokaci ya ja har haka ba, amma nidai don
Allah ki ƙara dubawa tunda dai su Kawu sun riga da sun ba
ni ke. Kinga kuwa babu abinda zai hana aurenmu, ki
sanyawa ranki salama ki yi tunanin alherikan da ke jiranki a
gidana."
Ta ƙara ɗaure fuska, ba ta bari sun yi doguwar sallama ba
ta juya ta nufi ciki. Ba jimawa da shigarta sai ga Baba Mai
gadi da ledoji har uku shaƙe da kaya, da sauri ta karɓa da
zummar maida mishi, babu shi babu motarsa.
"Ai ina ce miki ya wuce, ba ki ji ba."
Faɗin Baba Maigadi, cike da takaici ta dubeshi.
"Don Allah Baba kar ka kara amsar saƙon wannan
mutumin."
Baba ya ɗan yi shiru, ita kanta Ramlat din sai ta ga rashin
kyautatawa tunda dai Baba Maigadi ba ruwansa da
alaƙarsu. Juyawa ta yi ta koma ciki.
"Wai ke wannan kumburin da kike yi, ba fa wanda ya matsa
akan sai kim aureshi."
Hajiya ta furta tana dubanta. Ramlat da tuni idanunta sun
cicciko da kwalla ta amsa.
"Ni Hajiya abinda ke tayarmin da hankali, bai wuce yanda
Kawu ya yi saurin aminta da shi ba. Fisabilillah babu bincike
babu komai? Ni nasan waye Chairman, ba abinda suka sani
a kansa."
"Ke wa ya faɗamaki ana dogon bincike akan mai muƙami ko
dukiya? Hum, Ramlatu a zamaninnan ba'a wannan. Bar
ganin Yayyuna ne, amma na fi ki sanin halinsu. Ke dai ki
dage da addu'a, muddin kuma kina son ki shafe maganarsa
toh wallahi ki watsar da komai ki fiddo mijin aure. Shi ne
kwanciyar hankalinki da namu baki ɗaya. Ai kin dai ji abinda
Uwani ta faɗamaki. Yanzu da ace kin tsaida hankali wurin
ɗan uwan mijinnata ai da yanzun sai dai wata maganar ba
wannan ba."
Ramlat kirjinta ya yi nauyi, ta share hawayen da ya soma
sauka saman fuskarta. Miƙewa ta yi ba ta ko yi marmarin
ganin abinda ke cikin ledojin ba ta faɗa ɗakinta. Gefen
gado ta zauna gami da zabga tagumi. Tana cikin tsaka mai
wuya, ita ta sani. Wanda ta ke masifar so kuma ta ke jin za
ta iya aura bai san ma tana yi ba. Runtse idanunta ta yi
tana mai sa hannu ta dafe kanta.
"Ya Allah!" Ta furta a fili, fuskar Hussein kawai ta ke gani
cikin ƙwayar idanunta. Ta buɗe idanun, tuni sun kaɗa sun
yi jazur. A hankali ta kai duba ga hotonsu na Family,
Abbanta ta ƙurawa idanu. Take dukkan wani faɗi-tashi da
aka yi akan zancen aurenta da Aliyu ya faɗomata.
Murmushi ta yi da ya fi kuka ciwo, soyayyar Abbanta ya
mamaye zuciyarta, yanzun komai ya zama tarihi. Abba ya
bar ta da kewa ta har abada, hakanan Aliyu.
Ta tsinci kanta a sabuwar rayuwar da ba ta san abinda zai
haifarmata a gaba ba.
***
ADAMAWA
Misalin ƙarfe biyu da mintuna na ranar Talata, Rasheed ne
zaune yana faman haɗa gumi ga idanunsa da suka kaɗa
suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin ɓatan amininnasa
ya matuƙar girgiza shi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Ya furta a fili, Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da
ke raƙuɓe a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada.
Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci.
"Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina
duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sannan
meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo da talabijin ba?
Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin
ganoshi."
AlHassan ya jinjina kai.
"A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka
watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kaina ban yarda cewa
Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu
nemeshi ba, sai dai ba wani labari."
Rasheed ya runtse idanu cike da ɓacin rai, ransa na suya.
"Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke
zargi?"
"Babu."
Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya
manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a
ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji
na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu.
Bai bar gidan ba sai da ya ci abinci, nan ma kawai cusawa
yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa
biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da
alhinin ɓatan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya
musu sallama ya bar gidan.
Ranar dai ya tayarmusu da alhinin Hussein, wunin ranar
sun yi shi sukuku ba daɗi idan ka cire Taheer da bai san
me ake ba.
Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma ta kaunaceshi, sai
dai abin ya faskara.
***
KANO
Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara
rungume wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da
cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo ɗaya za ka yiwa
yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba
ƙaramin daɗi ya yi mata ba.
"Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka
san daɗin da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai
ma kwallon shege ne!"
Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce.
"Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka ɗaga ƙafa, wani
ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce
muddin ta faɗo hannunka. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa
makwaɗaitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin
dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma
ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata
kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka."
Jin haka daga can ɗaya ɓangaren, Chairman ya shiga zuba
godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu,
har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin
saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan
wayar. Duban mijinta ta shiga yi tana murmushi sosai,
ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san
ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake
amsawa na Hisham game da kasuwanci na haɗin gwuiwa da
suke son yi.
Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, ganin irin kallon da
ga ke jifansa da shi yasa shi fadin.
"I will call you back." Daga nan ya katse wayar.
"Lafiya?"
Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai.
"Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yallaɓaina."
Ɗan murmushi ya yi bai ce uffan ba.
"Amm, dama ina son zuwa asibiti."
Ya dubeta.
"Meke faruwa?"
Cike da ƴar damuwa ta ce.
"Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga
yawan kasala."
Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya yi sai bai
mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da
murmushin da ya fi kama da yaƙe.
"Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya."
Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta.
"An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa
mu ji alheri."
Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya
maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya buɗe yana
kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa
irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai.
Abu daya ya tuno da ya ji ba dadi, wato dai rabon da ya ga
Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto.
"Wannan kuma wacece?"
Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi
tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa,
cikin faɗuwar gaba ya ƙirkiro ƙarya ya shirgamata.
"Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?"
Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya
dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.
"Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma."
Ya gyaɗa kai kawai.
***
"Wai wa ya faɗamaki ina sonsa? Ni wallahi ban taɓa
sauraronsa ba."
Ramlat ke faɗi a gundure, gaba ɗaya zancen Chairman ya
isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce.
"Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da hakan sai ki
daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta
kawai ki faɗamasa."
Cewar Rafee'ah.
Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son
maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba.
"An faɗamaki Baba Daktan shima zai saurareta ne idan ba
wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki
faɗa tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban
Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani
ba na tarihinsa."
Wannan karon ma shiru ta yi, Ramlat ta yi dana sanin
dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba
abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da
zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin
Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da
ke gabanta, yanzun kuma ta zo ta iske yayyunnata, sun
sanyata tsakiya kowanne da kalar nashi zancen.
Tsam! Ta mike tsaye ta kwashi tarkacenta na ofis da
zummar wucewa.
"Au, mu za ki yiwa rashin ta ido? Don ana faɗamaki
gaskiya?"
Ta kasa ba Anti Zulaihat amsa, cike da damuwa ta dubeta
kawai.
"Wuce abinki, ke kika sani. Rayuwarki ce."
Ta furta a zafafe, Ramlat ta ciji lebbanta tsabar takaici,
karshe ta yi gaba zuwa daki tana ji Hajiya na fadin su bita a
sannu.
Ruwan ma kasa watsawa ta yi don haka ta bi lafiyar gado ta
kwanta, a hankali ta shiga fitar sa hawayen baƙin ciki.
Kewarsa ta ke ji kamar ta yi me, ga wani irin sonsa da ke
nuƙurƙusarta, kwana biyu ba su yi magana ba, bai ganta
online ba kuma bai nemeta ta waya ba. Wannan yasa ta
ƙara tabbatarwa ita kaɗai ke haukan sonsa. Ta kai minti
goma sha biyar a haka ba ta iya ko motsawa ba, tausayin
kanta take ji, da ace su Ummi na gidan, ko ya ya zasu
ɗebemata kewa, kiran sallar Magriba ce ta tasheta. Ta faɗa
banɗaki ta kama ruwa ta yi alwala.
Sai da ta idar da sallah kafin ta ninke Hijab ta fice zuwa
falon. Wannan karon ta yi ƙoƙarin saita zuciyarta ta ƙaƙalo
walwala, suka ci gaba da hira da ƴan uwanta kamar wani
abu bai faru ba. Tattaunawa ce game da bikin da ya taso a
Daura, wanda zasu tafi dukkansu don karshen sati ne. Su
ma basu ƙara tayar da batun Chairman ba.
Sai bayan sun bar gidan, Hajiya ta shige daki don watsa
ruwa, itama ta faɗa nata ɗakin da niyyar hakan.
Ganin hasken shigowar saƙo bai sa ta yi wani rawar ƙafa
ba, hakan ya faru ba adadi a yini biyunnan, sai dai daga ta
duba, saƙon Muhibbat ne ta ke gani, wani lokacin Hilal, wani
lokaci kuwa saƙon kamfanin layukanta. Tunanin hakan yasa
ta ƙin daukar wayar har sai da ta fito daga wanka ta gama
shafe-shafenta ta shirya cikin riga da wando na bacci. Ta
dora rigarta na sallah ta shimfida darduma. Sai da ya idar
da sallar Isha'i ta yi duk abinda ya dace sannan ta ƙara
samun nutsuwa.
Kai tsaye ta nufi wurin wayar, sunan da ta gani a saƙon ya
sa ta jin nauyi a ƙafafunta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a
ciki, haka ta buɗe bayan ta zaune gefen gado.
*Na lura kina da kishi, wato don ban nemi ki turomin
hotonki ba ne yasa ki ke shan ƙamshi ko? Oya, a turomin
yanzu. Happy?*
Lumshe idanu ta yi tana murmushi.
*Ya ya zan yi in misalta soyayya..? Ya ya zan yi in fasalta
soyayyaa..? Ita ce ba'a siye da kudi duk dukiyaa..Ita ce
mai gida na mulki shi ne zuciyaaa..Ta sanya mai ƙarfi ya
sunkuyaa..ya zubda hawayen idaniyaaa..!* Umar M
Shareef
Hoton ɗan aljan mai murmushi kawai ta tura mishi. Aka yi
sa'a ya hau online. Ganin ya buɗe ta yi saurin kife wayar ta
runtse idanu kamar yana gabanta, kirjinta na wani dukan
tara-tara. Jin ƙarar shigowar saƙo yasa ta karkata wayar a
hankali kamar marar gaskiya ta duba.
*"Please." *
Don ƙara tabbatarwa ta ƙara murza idanu ta duba, roƙonta
fa ya yi? Anya? Kuma akan hotonta? Ina Hajiyarsa?
Duk wannan tambaya ce da babu mai amsamata sai shi,
har abada kuma ba za ta tambaya ba. Ta jingina kanta
jikin gado tare da miƙar da ƙafafunta.
*" Angel ɗina ya hana ni aikawa kowa hotona. "*
Ta ba shi amsa duk kuwa da cewa ba ta ji dadin amsar
ba, sai dai ta lura idan ta biyewa kanta, za ta iya tona
asirin zuciyarta har ya gane inda ta dosa.
Ya buɗe, kusan mintuna biyar shiru, goma, sha biyar, duk
shirun ne, shi bai sauka online ba kuma bai ce uffan ba.
Ramlat dai har bacci ya soma fisgarta babu amsa daga
Hussein. Don haka ta ajiye wayar ta mike ta kakkaɓe
shimfidarta ta kwanta. Ta soma addu'oin kwanciya bacci
kenan wayarta ta yi ringing. Da sauri ta kai idanunta,
lambar da ta gani ya hargitsa kwanyarta, miƙewa zaune ta
yi b shiri. Sai da ta kusan yankewa kafin ta samu nutsuwar
ɗagawa. Leɓɓan ke rawa, zuciyar na ƙara ƙaimi wurin
bugu sai dai lanƙwasa harshen har ta iya haɗa kalma
kwakkwara ta gagara.
'Haka so yake?' Ta jefawa zuciyar tambaya. Ta san ba
wannan ne farkon soyayyarta ba, wanda ta shimfiɗa a
baya ya girmi wannan. Sai dai wannan shigarsa da
tasirinsa mai sauri ne kuma mai sanyaya zuciya da ruhin
ma'abocinsa.
"Kin yi shiru."
Ta dawo daga duniyar tunanin abinda ya yi mata nisa,
TAZARAR DA KE TSAKANINSU kamar tazara ƙasa da
sararin samaniya ne. Ɗumi ta ji a kumatunta, wani
ɗanɗano na gishiri ya sauka a leɓɓanta ta cije leɓɓan.
Kitt! Ta katse kiran, ba ta tsaya anan ba sai kawai ta kashe
wayar gaba daya ta jefa gefen gado. Kwanciya ta yi ta
runtse idanu, me ya rinjayeta har haka? Hussein fa?
Kamanninsa suka yi dirar mikiya cikin idanunta, tunaninta
ya ɗauketa ya cillar tun daga ranar da ta soma ganinsa
har zuwa yanzu da suke tare.
"Ka fi ƙarfina Hussein, Allah Yayemin wannan jarrabawar."
Ta furta a fili, ta yi addu'a ta kunna Mp3 Suratul Baƙara na
tashi a hankali tana bi. Tun tana tunani har bacci ya yi
awon gaba da ita.
***
"Baƙo?"
Ta furta a mamakince tana mai tsurawa Baba Maigadi
idanu, tana kyautata zaton kunnuwanta ne basu ji daidai
ba. Daga ita sai hijab saman rigar baccinta wanda ta dora
zani a samansa.
"Nima kaina nayi mamaki Ranki ya daɗe, sai dai kuma
kallo ɗaya na yi mishi uzuri."
Daga haka ya juya bai ƙara dogon jawabi ko ƙarin bayani
ba. Ta bi bayansa baki galala sannan ta ɗago idanunta ta
dubi agogo dakyau. Bakwai da rabi da safe.
'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'
Ta furta a zuciya, Hajiya ba ta kai ga tashi ba. Itama
baccin ta kasa, ta rasa ya za ta yi da ranta, babu jimawa
da fitowarta falo ta ji kwankwasar Baba Maigadi, ya kuma
isar da saƙo ya bar ta tsaye da mamaki da fargaba. Ta dai
daure ta yi shahada ta zura silifas ta fito. Fuskarta fayau
sai dai albarkacin ruwan alwala da ta yi yasa ya yi kyan
gani.
KARFEN KAFA Chapter 54
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Ido da ido suka dubi juna, daga shi sai riga da wando na
sport. Ya zura hannu cikin aljihun wando, idanun sun yi
luhu-luhu hakanan sun kanƙance, gashinnan a birkice
kamar yanda fuskarsa ta nuna. Ta kasa kauda idanunta
kamar yanda shima ya kasa kauda nasa, kirjinta lugude
yake kamar ana surfa gero. Ya tako har gabanta ya tsaya.
"Me na miki? Ki fadamin laifina, kiyi hakuri."
Ta lumshe ido ta bude don mamaki, sai a sannan ta samu
damar magana.
"Me ka yimin Hussein? Ba abinda ka yimin ni."
Ya girgiza kai, ta kalleshi sau daya ta kauda idanunta da
sauri.
"Kin kashe waya ba ki yimin magana ba, don nace ki turon
hoto? Wasa nake maki. Ki yi hakuri, na shiga rayuwarki da
yawa."
Ta girgiza kai, kamar yanda idanunsa ya kaɗa, haka nata
ya cicciko da kwalla.
"Ni wallahi ba abinda ka yimin, kuma maganar da nayi
wasa ce kawai nayi ba wai da wata niyya ba. Shi ne dama
ka doko sammako? Ka yi hakuri."
Ya yi shiru bai daina kallonta ba. Ganin shirun ya yi yawa
ta kara kallonsa.
Hussein tambayar kansa yake abinda ya ruɗashi, ya
hargitsa tunaninsa. Mene abin ɗaga hankali don Ramlat ta
kashemasa waya? Me ya birkita kwanyarsa har bacci ya
kauracewa idanunsa kamar yanda ya kasa bambance
daidai ko akasinsa? Hajiya Zeenat baccinta take sharɓa ya
fito, meyasa tunanin ta farka ta nemi ba'asi bai faɗomasa
a rai ba sai yanzun da ganin Ramlat ya