Showing 66001 words to 69000 words out of 113545 words

Chapter 23 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

yi ba. Da sauri ta ɗago kan Hussein ta na
shafa fuskarsa da duka hannuwanta biyu. Kukanta bai
tsaya ba hakan ya jawo mata rawar murya.
"Husseini, kai ne? Dagaske kai ne tsaye a gabana? Allahu
Akbar."
Kawai ta kara ƙarfin kukanta. Ya ja hannunta suka zauna
saman kujera, ya zame hannunsa guda cikin nata. Ya
shiga sharemata hawaye.
"Ni ne Dada, Hussein dinki ne. Na dawo gareki Dada. In
sha Allah ba zan ƙara nesanta kaina da ke ba. Ki yafemin,
wallahi ba ni da laifi."
Ta shiga girgiza masa kai amma ina! Ta kasa magana don
kuka sai kuma ta shiga dariya da hamdala.
"Yaya Hussein?" Hafsat ta fadi a hankali bayan fitowarta
daga ɗakin hayaniya ta ƙi ƙarewa. Ta ƙarasa itama ta rike
hannunsa, kallonta ya ke yi da mamaki kafin ya yi ƴar
dariya ya dubi Dada.
"Auta kenan?"
Ta yi murmushi kawai, ba ƙaramin mamaki ya yi ba.
"Shekaru bakwai fa Husseini, jiya ba yau ba. Tun kana da
shekaru ashirin da takwas muka rabu da ganinka."
Hawaye Dada ta share tuna irin jinyar da ta yi adalilin
rashinsa.
"Ya isa kukan please Dada. Mu godewa Allah tunda
yanzun ya cika buri."
AlHassan ya furta don har ga Allah ba ya son ganin ana
kuka, musamman ma kukan Dada.
Nan fa aka shiga nan nan da Hussein, abinda ya fi so a
baya, wato fura da kuma dambun shinkafa, shi Dada ta sa
Hafsat ta yi. Dakyar Hussein ya rarrasheta akan a bar
Dambun dare ya yi sai zuwa gobe.
Bayan sun gabatar da sallar isha'i suka zauna zaman hira.
Shiru ya yi yana jin AlHassan na waya da su Hajiya yana
sanarmata cewa sun sauka lafiya. Bayan ya kammala ne
aka shiga hira. Tiryan-tiryan AlHassan ya ba Dada labarin
komai tun daga farko har ƙarshe. Dada kuka ya dawo
sabo. Takaicinta yanda matar ta ɓatawa ɗanta
ƙuruciyarsa.
"Me ka ke jira ba za ka saketa ba Husseini?"
Murmushi Hussein ya yi gami da ɗan matsa ƙafar Dada
kaɗan.
"Komai yana da lokaci My Dada, ki kwantar da hankalinki."
Ba haka Dada ta so ba, sai dai kuma ba ta tsoron komai
tunda ta san ki mene yanzun da asiri a ciki. Da yardar
Allah kuma hakan ba zai ƙara faruwa gareshi ba.
Tahir dai kallonsu yake kawai, ya lura da ɗan sauyin da
Hussein ya soma gwadamishi tun da ya ji alaƙarsa da
Kawu. Bai yi mamakin komai ba don ya san dama za'a
rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Shi kam yana tunanin
fasa tafiya Kano da zai yi a goben sai zuwa jibi duk kuwa
da irin wayar da Kawun ke dokamishi akan ya dawo.
Washegari da safe dangi suka cika ganin Hussein, Gwoggo
Karime har da kukanta, takanas ta tahowa da Hussein
lafiyayyen farfesun da ta girka da hannunta. Hakanan
shima Kawu Adamu, hatta da sauran yaran Inna da ke a
Adamawa da yaran Hajjo sun zo ganin Hussein. Gida ya
cika ana murna, ya yi mamakin yanda suka sauya. An sha
hira kamar ba gobe. Fatima tunda ta gane dan uwan
mahaifinta ne ta maƙale masa, wannan kaunar nata da ya
soma yi tun bai san dangantakarsu ba yana nan daram a
ransa sai ma ƙaruwa da ya yi. Kowa ya yi Allah wadai da
Hajiya Zeenatu, har da masu kuka.
Ranar dai har dare bai samu kansa ba sai dakyar. Hajiya
Zeenatu ta kira sai hakuri ya ba ta ya nunamata ana ta
tambayarta da son ganinta.
"Ko na biyo hanya gobe na zo?"
Ya yi murmushin mugunta jin irin wannan wauta daga
matar da ta kusa dosar shekara hamsin.
"Aa Hajjaju, ki yi zamanki, idan zan ƙara zuwa sai mu
dawo tare. Dawowar dindindin."
Wannan amsar ya ba ta sai ta ɗan yi turus, a karshe dai ya
yi mata dabara ta sake kafin su yi sallama.
Ƴan Maiduguri labari ya riskesu su ma sai murna. Hussein
ya san zama bai gan shi ba, zaga dangi ya zamar masa
dole.
***
BAYAN SATI BIYU..
KANO
Ta fito daga motarta a farfajiyar asibitin Baba Dakta.
Amrah aka yiwa aiki sakamakon faɗuwar da ta yi a
bandaki da ya jazamata naƙudar dole, cikinta bai jima da
shiga wata na takwas ba, an ciromata Baby Boy. Yaron sai
ka rantse ya shiga watansa tara cif sannan ya fito duniya.
Ta zagaya ɗayan gefen ta ɗauki kwandon abincin da ta
kawomusu Da ka ganta za ka fahimci tana cike da farin
ciki. Tun da ta ji labarin auren da Chairman zai yi na huce
haushi take jin ta kamar an mata albishir da gidan aljanna.
Yanzun ta kara tabbatarwa babu abinda zai ƙara haɗa ta
da shi. Ta sha adonta cikin laffaya dark brown mai adon
milk flowers a ƙarshensa. Fuskarta babu wani heavy make
up, hoda kawai ta shafa sai man leɓe mai danƙo. Ga duk
wanda ya ganta sai ya ƙara kalla, Allah Ya ba Ramlat ƙira
mai kyau, sai ka rantse ba ta taɓa haihuwar ko ƙwai ba
ballantana ɗan mutum. Da wannan takun ta ƙarasa cikin
asibitin zuwa dakin da aka kwantar da Amrah. Ta murda
kofar da sallama ta shiga.
Umman Amrah na zaune gefe tana kurɓar ruwan shayi, ta
karasa suka gaisa. Amrah na bacci. Ajiye kwandon ta yi ta
ƙarasa ga gadon Babyn, murmushi kawai ta ke yi tana
ƙaremishi kallo, duka-duka yau kwanansa hudu a duniya.
"Ki ciro shi mana Ramlat, ke da ɗanki."
Ta juyo tana dariya kadan.
"Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana
juyewa zuwa kamannin Zaituna."
Umma ta yi murmushi.
"Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke."
Ta jinjina kai.
"Naga kin warware sosai yanzu, ko don kin ji labarin auren
Chairman ne?"
Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke
ranta kenan sai ta sa dariyar.
"Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da
alaƙaƙai."
Dariya sosai ta ba Umma.
"Kai Ramlatu ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka
ƙare da Kawunnaki?"
Ta ɗan taɓe baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu
Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe
dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce.
"Yanzu ki ka zo?"
Muryar Amrah ta katse su. Suka dube ta.
"Yanzu na zo, sannu ya jiki"
Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri
Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya
bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo.
Umma kuwa ta gyara shimfidar ta kwantar da ita.
Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa
wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai
iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa
meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama
saddaƙarwa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana
ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta
A'isha da ta taɓa ce mata gani take kamar Hussein ya fi
ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali
ta sa bayan hannu ta share kwallar da ta cika idanunta.
Muddin zai faɗomata a rai to fa sai ta ji kwalla.
Wayarta ta ɗauki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar
yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da
haɗuwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da
aure don haka ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a
kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa
Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa
a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da
Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin
Hisham ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa
Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya
nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya
yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan
saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham bai hana ta
kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin
babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana
ta hakura ta ba Baban Hanif dama.
Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta
ɗaga ba. Ya ƙara kira ta ɗaga. Bayan amsa sallama ta ba
shi uzurin tuƙi dole ya hakura.
***
"Shi kika tsayar kenan matsayin miji?"
Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya faɗi, kanta a ƙasa
yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da
gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta haɗiyi miyau, ta
hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta
yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan
karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi.
"Eh Baba."
"Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana son
jin wata magana ta ɓullo daga baya."
A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai
sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu.
Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta
kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun shekara da
shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon
yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.
"Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan
har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya
turo magabatansa. Allah Ya zaɓamaki abinda ya fi alheri."
Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta
mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan
daman, koda ta isa gida ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba.
Hajiya ta yi murmushi.
"Yaron ya san abinda ya ke yi da alama, kuma ko ba
komai ɗan babban gida ne tunda Kakansa ma abokin
Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu
Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke
a dadinki ma tunda ba gida daya zai haɗaku ba da
matarsa."
Ramlat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron
Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana
ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba
iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare.
A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a fusace, suka
dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan
zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa.
"Lafiya kake kuwa?"
Ya yi kwafa.
"Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan
zama a gaban mota ta kama Hunainah da duka."
"Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki.
"Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu.
Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma,
yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni
kuwa na kora ta gidansu ba zan iya ba."
"Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake
ciki?"
Munir da har lokacin bai huce ba yana aikin karkaɗa
mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya.
"Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun,
kuma na kora ta gidansu na sake ta."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa?
Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba
Muniru! Ai idan rai ya ɓaci, hankali ke dawo da shi."
Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin da Bilkisu ke
yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi
faɗa ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da
Bilkisu kafin ransa ya ɓaci. Ganin bai samu goyon baya ba
haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai
duk kanwar ja ce, sai dai ɗan saukin da ya samu jin cewar
Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a
washegari.
***
Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi
ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai
tsaye cikin fawwalawa Ubangiji lamarinta ta ba shi damar
yi mata zaɓi a wannan karon.
"Idan har shi ka zaɓarmin Baba, na amince zan zauna da
shi kuma ba zan ba ku kunya ba."
Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka
karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya za ta ji. Da
wannan suka ajiye maganar.
"Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta
furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta
dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan
idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi.
"Ba zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai
bar wa Allah zaɓi, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne
daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif
shikenan."
"Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?"
Ta hadiyi miyau a kokarinta na danne damuwarta.
"Koda ya dawo mene ne haɗina da shi? An faɗamaki
kalmar so ta taɓa shiga tsakaninmu?"
Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat.
Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya
nemanta.
"Amma sai naga kamar yana sonki."
Ta girgiza kai.
"Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani
amfani."
"Ai shikenan. Allah Ya yi maki zaɓi na alheri."
Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba.
***
BAYAN KWANAKI UKU...
BAZATA.....
Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani
littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar
Nene ta ke yi sosai har ɗankwalinta na zamewa. Tana
sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau.
Ummi da su Ansar suna farfajiyar gidan su na wasa, sai ji
ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro
can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba
Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman
ɗan kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar ɗauko
mayafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan
yunƙurinta.
"Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?"
Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke
tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon
kallo da Ramlat yasa ta katae tambayar. Ramlat da sauri
ta fada daki don ɗauko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya
sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta
ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita
ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa.
"Dama za ka dawo ɗannan? Ni na ɗauka kuma sai dai mu
bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya
gama jajensa."
Dariya ta ba shi.
"Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya ban sanar maku
batun zuwana ba."
"Ba komai ai."
Nan kuma aka shiga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki
Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin
ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana
nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya
ƙasa-ƙasa ya ce.
"Kin fi koyaushe kyau."
Ta ɗan dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana
murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri.
Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa
maimakon ya karɓa sai ya ɓige da tambayar Hajiya.
"Na yi zaton zan tarar an yi bikin Ramlat."
Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar
mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki
sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da
Chairman.
Bai katse ta ba har ta kammala.
"Allah Ya kyauta." Shi ne kadai abinda ya furta. Daga
bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira
Dada a waya video call ya haɗa su suka gaisa, Dada
godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A
karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta karɓi wayar
ta shige dakin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance
saman gado.
"Mami, ga Dada."
Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin
mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba
Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi
ta fice daga dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse
kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga
hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow
guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai
take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan yasa ta
yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan
kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida
mishi.
Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a
wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta
bude.
_*"Wayartawa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka
yimin iyaka da HEART?" *_
KARFEN KAFA Chapter 66
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, takaici ya sa ta wurgi da
wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta
rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane
matsayi ya ajiye ta ba. Ta cije lebbanta tana karkaɗa ƙafa
daidai sadda Ummi ta faɗo ɗakin a guje.
"Mami, wai inji Uncle.."
Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar.
"Maza dauka ga ta can ki miƙa masa."
Ummi wacce ba shi ya aiko ta ba, ta girgiza kai sai dai ba
ta fasa ɗaukar wayar ba kazalika ta ci gaba da zancenta.
"Wai ki zo zai tafi."
Harara ta watsawa Ummin.
"Ki ce ba ki ganni ba."
Ummi ta bude baki.
"Mami kin fa hana mu.."
"Kika karasa sai na buge bakinki. Naji ba zan zo ba wuce
ki ban wuri."
Rai ba dadi Ummin ta fice, Ramlat ta sauke ajiyar zuciya.
Kwanciya ta yi sai dai karatun littafin da ta ke yi ma ya
fice a ranta. Ba zato ta ji muryar Hajiya.
"Ramlatu yaushe ki ka sauya? Baƙo ya zo domin ya
gaishemu shi ne za ki aikamasa mugun kalamai? Me kike
nufi da ba za ki je ba? Wani abun ya haɗa ku ban sani
ba?"
Jikinta sai ya yi sanyi, Hajiya ta ba ta umarmin fita, a dole
ta mike tana ba ta hakuri sannan ta gyara zaman hijabin ta
fice ranta na tururi.
Ba kowa falon sai wata ƙatywar leda a gefe, don haka ta
tsaya gami da juyowa da zummar komawa ciki, suka yi
kiciɓus da Hajiya. Harararta ta yi.
"Ki je yana waje tare da yara. Tsaraba ya kawomusu. Ki
mishi godiya don Dadarsa ta aikomin fura da nono."
"Toh." Ta amsa a ciki-ciki tamkar ba ta so sannan ta fice,
ita dai Hajiya bin bayanta da kallo ta yi da mamakin
wannan sauyi a fuska da gangar jikinta.
***
Yana zaune a mazaunin direba ƙafarsa ɗaya a waje, alewa
ce a hannunsa yana kokarin ɓarewa Affan. Ta kauda kai
daga kallonsa ganin ya ɗago nashi kan, kallonta yake da
murmushi a saman fuskarsa. Sai kuma ya miƙawa Affan
alawar ya dube su.
"Oya ku shiga ciki."
Dama haka suke jira musamman Ummi da ke rike da
ƙatuwar ledar kayan kwalam da ya damƙa mata su je su
sha. Ba ta son hararar da uwar ke watsomata wannan ta
sa ita ce farkon sheƙawa a guje sauran ma suka mara
mata baya.
Ta rasa dalilinsa na korar yaran don haka ta ja numfashi
ta furzar. Cikin dakiya ta dubeshi kirjinta na bugu da sauri-
sauri.
"Hajiya ta ce na kara miƙa mata godiya. Allah Ya saka da
alheri. Mun gode sosai da ɗawainiya."
Ya murmusa yana shafa sumar kai. A hankali ya kai hannu
ya bude dayan murfin na motarsa. Dubanta ya yi.
"Dan zagayo ki zauna ki ban aron koda mintuna biyar ne,
magana zamu yi."
Ta yi shiru ba ta tanka ba, karshe ma ta daure fuska don
ta san wani sabon rainin hankalin ne.
"Please." Ya furta a sanyaye, sai ta ji ba za ta iya jan musu
ba don haka ta zagaya ya bita da kallo har ta shigo ta
zauna. Shiru ya biyo baya har dai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login