Showing 42001 words to 45000 words out of 113545 words

Chapter 15 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

jin tsanar
Hussein tsagwaronsa a fili da ɓoye. Miƙewa ya yi ya dauki
waya ya danna kira direbansa.
"Kana ina?"
Daga can aka ba shi amsa kafin ya dora.
"Ka fiddo mota, fita zamu yi."
Daga nan a gaggauce ya dauki hula ya rufe kansa ya fita
yana zuba sauri.
***
Ramlat bakinta ya yi mata nauyi, ta kasa ba Hajiya
labarin abinda ya faru. Damuwar da ke kwance samam
fuskarta yasa Hajiya ta fahimci ba lafiya. Ganin ta shige
daki sai ta mara mata baya.
"Ke mene ne wai? Shi Kawun ne ba ki samu gani ba ko
wani abin ne ya faru da Husseinin?"
Girgiza kai ta yi. Tunanin ta faɗa ɗin ya rinjayi komai, ko
ba komai Hussein na bukatar addu'a, don haka ta karya
bille ta labartamata duk yanda suka yi da Kawun. Hajiya ta
saki salati.
"Ni Rabi wannan rayuwa da ban mamaki. Ban taɓa jin
labari makamancin haka ba tunda uwata ta haifeni. Kai.."
Hajiya sai ta soma hawaye, ita kanta tausayin Hussein ke
ɗawainiya da ita. Hatta da abokin haihuwartasa ma
tausayinsa take ji. Miƙewa ta yi tana jan hanci.
"Addu'a zamu dage da yi, ke kanki yanzu ki dage da
addu'a don mutum idan aka ce mugu ne komai ma zai
aikata. Bari na kira Malam na faɗamasa, shima ya tayamu
da addu'a."
Daga nan Hajiya ta fita ta bar Ramlat da tarin damuwa.
Dakyar ta iya mikewa ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar
isha'i, zaman dirshan ta yi saman dardumar jefi-jefi tana
sharar hawaye.
Addu'a sosai ta yi kafin ta miƙe ta nufi gefen gado ta
zauna. Hayaniyar su Affan ta ishe ta don haka ta kora su
waje. Waya ta ɗauka ta hau kan whatsapp, babu alamar
Hussein ya hau. Yau ɗaya ta ɗaura ɗamarar kiransa. Don
haka ta sauka ta danna masa kira. Wayar a kashe.
Damuwarta madadin ta ragu sai ta ƙaru, ganin dukan na
nema ya yi mata yawa, sai ta miƙe ta koma falo ta yi
jugum. Ba jimawa Hisham ya kirata. Ta ɗaga.
"Antinmu shiru, ina jira na ji yanda ku ka yi."
Ta haɗiye hawayenta da ɓacin rai. Komai ba ta ɓoyewa
Hisham ba, ya dinga salati da salallami karshe dai ya
kwantar mata da hankali.
"Kar ki sanya damuwa a ranki Ramlat, in sha Allah kamar
yanda kika ce toh hakan ne, Allah Ya fi su. Mu dage da
addu'a."
Ta amsa da toh. Kamar ta tambayeshi ko sun yi waya da
Hussein sai ta share.
***
Washegari haka ta shirya ta fita wurin aiki ranta a jagule.
Ga wayar Hussein da ke a kashe. Ta gwada kira har cikin
dare don tsautsayi amma ba ta shiga. Tuƙi ta ke kusan ba
za ta ce a cikin hayyaci ba. Don haka ba ta kawo da cewar
an basu hannu ba sai da ta ji wani ruɗaɗɗen Hon daga
bayanta. Hakan ya fusata ta, ta madubi ta ke duban mai
shi. Ido da ido suka kalli juna, yana cin magani. Wannan
karon ba Tinted glass din a motar da yake. Yanda ya
ɗaure fuska ba alamun fara'a ya fi komai ruguza lissafinta.
Asalima ba wani wawan overtaking da ya yi ya kaɗa
hancin motarsa sai da ya daskarar da ita ya jazamata
ɗaukewar numfashi na ƴan dakiku.
"Me nayi masa?" Ta ambata a fili, da rawar jiki ta ja motar
bayan ta gaji da tsinuwa da zagin mutanen da hankalinta
ba'a kansu yake ba. Koda ta gangara sai ta nemi wuri ta
tsayar da motar. Hankalinta ya gushe na ɗan lokaci.
Tunaninta abinda ta yiwa Hussein, shi dai ta gani kamar
yanda ya gan ta amma ya kauda kai. Wannan abu ne da
bai taɓa afkuwa ba tsakaninsu. Ta ɗauki wayarta da karar
shigowar saƙo ya katsemata tunani, kuɗi ne har dubu ɗari
aka aikomata. Ta kai duba ga lambar mai account din.
Aliyu Dikkl. Hakan ta gani a rubuce. Ranta ya ƙara ɓaci, ga
babu lambar acc balle ta mayarmasa. Ta ja tsaki. Kai
tsaye ta ƙara kiran wayar Hussein, wannan karon ringing ta
ke yi sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Ta kuma kira nan
ma shiru, a karo na uku ma babu alamar za'a ɗaga. A na
huɗu sai ji ta yi an kashe wayar gaba ɗaya.
"Meke faruwa?" Ta ambata a fili. Kawai sai ta ji zuwa
wurin aikin ma ya fita a ranta, don haka ta ba kanta
mintuna kusan biyar a tsaye tana jin karatun Alkur'ani tana
hawaye kafin daga bisani ta samu ƙwarin gwuiwar da za ta
tashi motar. Gidan Amrah ta nufa, a hanya ta kira ɗaya
cikin abokan aikinta, Hindu. Uzurin rashin lafiya ta bayar
domin dagasken ba ta jin dadin zuciya da gangar jikin.
***
Amrah ta yi mata duban tsanaki bayan gama sauraron
dukkan bayanin Ramlat. Ita kanta kwallar ce ta cicciko
mata.
"Yanzu AlHassan ɗin bai shigo ba?"
Ramlat da kanta ke jikin kujera sakamakon zazzaɓi-
zazzaɓin da ta ke ji. Ta girgiza kai murya a dusashe.
"Mun yi waya da shi yanzu da zan fito, abin hawa ne ba'a
kammala gyara mishi ba, yana tunanin ma bar musu zai yi
ya biyo motar kasuwa."
"Kai! Wannan lamari akwai wata sarƙaƙiya a cikinsa
Ramlat. Sai dai kuma ki zauna don Allah ki yi tunani ko
dai akwai abinda ki ka aikata ga Hussein har ya ɗauke
maki wuta haka? Ni fa gani nake da walakin goro a miya."
Cike da damuwa ta ɗago ta zauna sosai tana duban
Amrah da ciki ke ƙara girma.
"Da ace akwai abinda nake jin zan ba dukkam girma da
kulawa bayan iyaye, ƴaƴa da ƴan uwa, wallahi ya biyo
bayan Hussein. Kin san ni, kin kuma san halina Amrah. Ina
son Hussein, son shi nake yi da ban san iyakarsa ba. Akan
me zan ƙuntata masa? Ni duka-duka ma yaushe rabon da
ko chatting nayi da shi balle haɗuwa face to face? Ban
sani ba, ban san me na yi ba. Ni dai babban burina koda
zai zama abu na ƙarshe da zan mishi, shi ne na sada shi
da ƴan uwansa da taimakon Allah."
Amrah ta jinjina kai, shakka babu Ramlatu na son Hussein,
so mai yawa. Tana tsoron tarihi ya maimaita kansa idan
har dangin uwa da uba suka dage mata akan auren
Chairman. Sauƙinta ma wannan karon su Hajiya na goyon
bayanta.
"Ko Hisham zan tambaya?"
Maganar Ramlat din ta maido ta hayyacinta. Gyada kai ta
yi.
"Ki tambayeshi tunda amininsa ne. Ba zai rasa abinda ya
sani ba."
Da haka ta danna wa Hisham kira. Yana ɗagawa suka
gaisa.
"AlHassan din ya iso kenan?"
Ya nemi sani.
"Aa, wannan tsakanina da Hussein ne."
"Ina jinki Ramlat."
Ta ba shi labarin irin sauyin da ya ke mata.
"Ko akwai wani abu da ya ce maka na yi mishi don Allah?"
Shiru ya biyo baya kafin Hisham ya ce.
"Ya Salam!"
Jin haka ta gyara zama tana kallon Amrah don dama a
speaker ta sanya. Suka nutsu.
"Meyafaru?" Ta tambaya kirjinta na dukan uku-uku.
"Ki yi hakuri, ina ga wannan laifina ne, yanda na ɓata
kuma ni zan gyara. Kar ki damu don Allah. Zan kira ki
anjima ko kuma ince zai yi kiranki da kansa. In sha
Allahu."
Daga haka ya katse kiran. Suka dinga mamaki. Tunanin
Ramlat me Hisham ya faɗawa Hussein?
"Hisham ya san batun aurenki da Chairman?"
Amrah ta nemi sani. Maganar Ramlat ji ta yi kamar an
sokamata mashi a ƙahon zuci don haka maimakon amsa
sai ta harareta ta ja guntun tsakin da ya ba Amrah dariya.
"Allah Ya ba ki hakuri. Mancewa nayi fa."
Ta cije lebɓa gami da girgiza kai ba ta ce komai ba.
***
MISALIN ƘARFE SHA ƊAYA..
Rubutu yake kamar wani Mango Park ba ya ko kallonsa,
Hisham ya ƙuramasa idanu da mamaki. Ya sauya kamar
ba Hussein din da ya sani ba.
"Malam ya ina magana ka kyale ni? Ba ka ji me nace ba?"
Ya ɗago ya dubeshi, ya ji, dukkan wani labari da ya ba shi,
ya ji ba wai bai ji ba. Sai dai duk da hakan shi bai ga ta
inda zai fara rage KISHIN Ramlat da ya ke ji ba. Ya soma
yarda da abinda ya ƙaryata da gangan, ba kuma ya son
sanya ta a matsala. Wannan ne dalili sauyawar sai dai ya
ji wani sanyi kaɗan a maimakon tsananin zafin da ya
ɗauka a farko duk akan lamarin aurenta da Chairman.
"Kunne ke ji, kuma na saurareka. Ka yi kokari."
Harara Hisham ya watsamasa yana danne tausayinsa.
"Shi ne za ka share ni? Nima fa takanas na taso don
wanke laifin Ramlat amma ina da abin yi ai. Aikina na
baro na zo."
Wannan ne karon farko da ya yi murmushi daga jiya zuwa
yanzun, Hisham yana da raha. Ko ya ya ka zauna da shi
sai ya sanyaya ranka.
"I'm travelling to London."
"For what?!"
Yanda Hisham ya nemi sani a hargitse, hakan ya ba
Hussein mamaki har ya kalleshi, ganin ya zaro ido sai ya
buɗe tafukan hannu gami da ɗaga gira cikin dakiya.
"Me akai na razanar? Tafiya ce kawai ta 3months."
"Gwara da Allah Yasa na zo." Hisham ya faɗi a fili kuma a
hankali. Da ace ba su haɗu ba ba zai sani ba kenan. Lallai
dole su yi komai cikin gaggawa.
"Me ka ce?"
Hussein ya tambaya. Girgiza kai ya yi.
"Ba komai. Yaushe za ku wuce?"
Damuwa ƙarara a fuskar Hussein sai dai ba ƙaramin
ƙoƙorin dannewa ya ke ba.
"Ba na jin za mu wuce satinnan. Ya dai danganta da
samun Visa."
Ya faɗi a sanyaye.
'Innalillahi wa inna ilaihir raajiu'un!'
Hisham ya ambata a zuciya gami da mikewa.
"Ok ok, Allah Ya nunamana. Bari na wuce sai mun haɗu
anjima."
Hussein ya bishi da kallo har ya fita. Abinda ya kawo a rai
shi ne damuwa ce tsantsa na ganin za su yi nesa da juna.
Ya dafe kai da hannu. Shi kansa damuwar ce ke cinsa,
tunanin tafiya ya bar Ramlat da Chairman kan ci masa
tuwo a kwarya. Sai dai ya tabbatar furta wata kalma a
kanta zai zama kamar barazana ga rayuwarta. Hajiya
Zeenat ta sha faɗamasa gami da cin alwashin kashe duk
wata mace da za ta shiga rayuwarsa. Ba a bayan idanunsa
ba, a gabansa ta ke faɗi ya na kuma ji a jikinsa fiye da
hakan ma za ta aikata. A hankali ya ɗauki waya ya kunna
Data wacce rabonsa da whatsapp tun ranar da Hajiya ta
kwace wayar. Saƙonni suka shigo har da nata. Ya shiga ya
karanta. Gaisuwar safe ce ta mishi gami da tambayar ko
lafiya. Ya dinga binyana karanta hirarsu da bai fi a ƙirga
ba. Murmushi sosai ya ke yi san nan ya bude hotonta yana
kallo. Ya kai kusan minti biyar ba'a hayyaci ba, tashin
hankalinsa ya ƙaru. A hankali ya rufe hoton ya aikamata
saƙo.
-* "Ki sa ranki Hussein ɗan uwanki ne. Ya na buƙatar
addu'arki a duk inda zai je. Akwai wani duhu da na kasa
fita, ke na gani kin fitar da ni kin sadar da ni da haske. Ina
fatan mafarkina wataran ya tabbata. Ban ce ina sonki ba,
ban kuma ce ina tsananin kishinki ba, amma ina roƙonƙi
akan kar ki yi garajen aure. Nemi zaɓin Allah. Ke ba
yarinya ba ce. Ina miki fatan alheri koyaushe." *_
Ya aikamata ya kashe datar, dakyar ya ci gaba da abinda
ya ke ransa a jagule.
***
Kawu Modibbo tsaye a tsakar falonsa. Safa da marwa ya
ke yi yana ƙarawa. Babu wani cikin iyalinsa da ya yi
ƙoƙarin dosar inda ya ke, Amarya kanta haƙura ta yi da
kwanan ta koma sashinta ta kwana.
-* "Kamar wuta da ruwa, haka ta ke barazana ga ayyukanka.
Na sha faɗanaka, ba kai ɗaya ke aikin ba, akwai masu yi.
Naka kan rinjayesu ne wani lokacin, kamar yanda nasu kan
rinjayi naka aikin. Ina tsoron shaida maka muddin ba'a
kawar da yarinyarnnan ba, aikin shekara da shekaru zai
lalace. Za'a rasa dukkan wata nasara a kansa. Abubuwan
da ka ke gudun afkuwarsu a rayuwarka, za su afku!" *_
Waɗannan jawabi na Tsoho, shi ke yawo a kwanyar Kawu
Modibbo suka kuma hanashi sukuni daidai da sakan.
Daren jiya kasa runtsawa ya yi balle har ya samu damar
baccin. Idan komai ya lalace, hakan na nufin bayyanuwar
komai.
"Lokaci ya yi da za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da ke
ZEENATU."
Ya furta a fili kafin ya samu wuri ya zauna kamar kayan
wanki.
***
ƘARFE BIYU...
Ta karanta saƙon Hussein sau ba adadi, sai dai ba ta
fahimci komai ba. Cewar ba ya sonta ba kuma ya kishinta
wannan ya haifar mata da matsananciyar damuwa. Kukan
da ta yi ya jazamata tsananin ciwon kai. Hajiya na ganin
haka ta tsorata, abinda ya faɗo a ranta kada ace wani
mummunan abin ya sami Ramlatu sanadin wannan yaro,
bayan ta taimaka mata ta sha magani ta shiga tofe ta da
addu'a. Ummi kam su na Islamiyya ba su da labarin wainar
da ake toyawa.
Wuraren ƙarfe huɗu da mintuna ne. Wayarta ta yi ƙara,
dakyar ta iya ɗagawa. AlHassan ne.
"Na shigo Kano, ina hanyar gidanku."
Ta amsa da toh, a daddafe ta miƙe, babu laifi kan ya
daina sarawa. Ta shiga ta yi brush ta kama ruwa ta yi
alwalar jiran la'asar. Fitowa falon ta yi bakinta duk jikinta
ya yi mata nauyi. Hajiya na zaune tana amsa waya.
"Ita Ramlatun?!"
Hakan da Hajiyar ta faɗi ya ɗau hankalinta, ba ta katse ta
ba har ta kammala wayar.
"Ke da kanki ki ka ba shi Dikko damar turo kuɗi? Yaya
Bello ya shaidamin ai sun ma gama magana ya turomaki
kudin aurenki ta akawun dinki da ki ka aikamasa."
Dafe kanta ta yi tana salati, kirjinta na bugu da sauri-sauri.
"Ni kuma Hajiya? Wallahi ban.."
Ɗif ta yi, sai lokacin ta tuno da kuɗin da ya turomata
account. Ranta idan ya yi dubi ya ɓaci. Ta faɗawa Hajiya
gami da nunamata sannan ta ƙara da faɗin.
"Amma wallahi ban san inda ya samu lambar account
ɗina ba. Ban sani ba. Me ake nufi da ni wai?"
Ta karashe hawaye na son zubomata. A fusace Hajiya ta
mike tana faɗa.
"Bari na je gidan! Ba su suka haifarmin ke ba don haka ba
zan zauna rayuwarki ta ƙare haka ba Ramlatu! Idan shi
Munirun ya kasa ni zan je na same su."
Daga haka Hajiya ta faɗa ɗaki ta bar Ramlatu da ruɗewa
da kuma hawaye. Waya ta ɗauka ta kura Zulaihat ta
sanarmata komai, itama hankali a tashe ta ce za ta je can
gidan su Dada kar abin ya ɓaci. Hajiya ta fito ta kama
hanya ta fita.
Mintuna talatin bayan fitar ta sai ga kiran AlHassan yana
shaidamata zuwansa ƙofar gidan. Ta mike ta shiga ciki ta
gyara fuskarta da ta kumbura. Dole haka ta haƙuranta fita
hakan. Tuni an gyaramasa ɗakin Muniru na baya, ta yi
mishi iso ya shiga yana bin ta da kallo.
"Lafiya dai ko?"
Ta yi murmushin yaƙe.
"Lafiya kalau. Sannu da zuwa."
Ya amsa karo na biyu, shi ba wannan ya ke da muradi ba.
Labarin Hajiya Zeenatu da adireshinta ya ke da buƙata.
Abinci ta kawomishi ta kuma ce ya yi hakuri har su yi
sallah tukunna. Daurewa ya yi ya amsa da toh sannan ta
fice.
***
"Rai kan ga rai?" Hajiya Zeenatu ta faɗi tana murmushi
da wani irin mamaki shimfiɗe a fuskarta tana duban Kawu
Modibbo da ke zaune a ofishinta na A&Z. Ya share goshi.
KARFEN KAFA Chapter 58
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


"Kin san dai ruwa ba ya tsami banza. Kamar yanda kin
sani, na sani, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo. Toh idan ba
mu yi dagaske ba, asirinmu na dab da tonuwa."
Nan da nan ta haɗe rai.
"Me kake nufi?"
Kawu Modibbo ya gyara zama yana mata kallon ƙyar.
"Wata yarinya ta zo min da zancen da ya rushe dukkan
walwalata. Tana ƙoƙarin shaidamin cewar ta san inda
Husseini yake, duk da ba ta fito fili ta yi bayanin komai ba,
amma daga yanda ta ambaci shi Hassan ta alaƙantashi da
Husseini shakka babu akwai babban al'amarin da ta sani."
"Ya sunanta?" Hajiya Zeenatu ta nemi sani a hanzarce
yayinda kirjinta ke bugu, tana tsoron kar hasashenta ya
zama gaskiya. Sai dai abinda ta guda shi ya faru, sunan da
ta ke fatan kar ta ji, shi dai ta ƙara tsinkaya daga bakin
Kawu Modibbo.
"Ramlatu ta ce sunanta."
Wani miƙewa da Hajiya Zeenatu ta yi sai da shi kansa
Kawu ya ƙara tsorata. Jikinta ya shiga rawa nan da nan
idanunta suka kaɗa.
"Baƙa ce, ba ta da jiki sosai kuma.."
"Abinda ya tunkaro mu, ya fi ƙarfin mu tsaya ɓata lokaci a
kan suffantawa ba. Ki faɗi kai tsaye idan kin santa."
Ya faɗi cike da ƙagara. Ta haɗiyi miyau tana goge gumin
goshi.
"Tsinanniyar yarinyar da aka sha yimin gargaɗi a kanta
kenan! An tabbatarmin muddin ban nisanta Hussein daga
duniyarta ba, to shakka babu komai zai lalace. Kenan
yanzu ta gano dangin Hussein? Wannan mayyar ina ce?!"
"Mafita za mu nema. Kin sani, baragurbin kwai idan ya
fashe, yakan shafi kowa ba mutum guda ba. Za ki fi ni
shiga matsala. Kin san komai don haka a bar kaza cikin
gashinta. Tun lokaci bai ƙure ba ya kamata a ɗau mataki."
"Kasheta zan sa a yi."
Kai tsaye ta furta tana fidda hucin ɓacin rai. Kawu ya
dubeta sosai, duk da cewar yana shuka abubuwa a doron
ƙasa, bai taɓa tunanin ya kashe rai ba.
"Kina ganin hakan zai haifar da ɗa mai ido? Kisa na nufin
abubuwa da dama ciki kuwa har da rabuwarki da shi
Hussein don za ki ƙare a kur..."
"Dakata, ai ba ni zan kashe ba. Zan saka a kashe ne.
Mace ƴar uwarta zan saka, ita kanta ba za ta fahimci
komai ba. Na santa a bakin Dikko, mayyar kuɗi ce da za
ta iya aikata komai saboda shi. Don haka ka bar min wuƙa
da nama yanda ka ce, za ka sha mamaki nan da awannin
da suka rage kafin safiya."
Kawu ya jinjina kai, suka ƙara shawarwarinsu sannan ya
fice.
A gaggauce Hajiya Zeenat ta kira Hajiya Batool ta ba ta
labarin komai har shawarar da suka yanke.
"Wannan ya yi kuma ina goyon baya dari bisa dari. Gwara
tun wuri a yi ta kuma ta ƙare."
Da wannan suka yi sallama ta kira Chairman a waya. Cikin
gaggawa ta ce
"Ka turomin lambar yarinyarnan."
"Wa?" Ya nemi sani.
"HALIMA."
Dariya ya ɗan yi mai sauti, sanadin Halima ya san duk
wani tarihi na Ramlatu, duk da cewa ya san da biyu ta
faɗamasa, amma ya zamar masa tamkar ƙarin makaman
yaƙi a wurin iyayen Ramlatun har ya same ta. Sanadin
wannan ne ya sanya har holewa ya yi da ita na sati kafin
ya biya ta da maƙudan kuɗaɗen da suka kusa zautar da
ita.
"Wani abu ne ya taso?"
Ya nemi sani.
A ɓangaren Hajiya Zeenat ta ja tsaki.
"Wankim hula ke neman kai ni dare, turomin yanzu-yanzu."
Daga haka ta katse kiran ta kwashi tarkacenta ta fita. Ba
zai yiwu su tattauna da Halima a wurin ba. Hussein zai iya
shigowa kowane lokaci.


Tun kan ta kai motarta lambar Halima ya shigo. Kai tsaye
ta ɗauka ta kira bayan ta daidaita zama cikin mota ta rufe.
"Hello."
Halima ta furta.
"Kina magana da Hajiya Zeenatu mamallakiyar A&Z."
Hajiya Zeenatu ta yi shiru don ba ta san ta ya za ta soma
bayani ba. Ga mamakinta sai ji ta yi Halima ta ce.
"Lah, na san wurin ai ina zuwa lokaci -lokaci. Ai kin taɓa
zuwa inda nake aiki kwanaki can kika biya kudin haraji. Na
sanki sosai. Ranki ya dade, Allah Ya ƙara girma."
Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi, dagaske ba za ta samu
matsala da wannan ba. Don haka ta muskuta.
"Halima ina son ganinki, idan ba damuwa a yau kuma a
yanzu."
"Aa babu wata damuwa Hajiya, ki fadi inda zan zo na
sameki kawai."
Nan Hajiya ta yi mata kwatancen gidan Hajiya Batool. Ta
dinga amsawa daga bisani suka yi sallama bayan Halima
ta tabbatar mata yanzun za ta taho.
***
Hajiya ta isa unguwar Yakasai ranta a tsananin ɓace, ko
sashin Hajja ba ta shiga don tasan tsaf za ta hanata tada
kowace magana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login