Showing 81001 words to 84000 words out of 113545 words
Chapter 28 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
yi. Ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turare.
Hajiya Zeenatu ta ƙuramasa idanu, kananun kaya ya
sanya. Rigar da ya sanya milk mai gajeran hannu sai blue
jeans. Tsayawa suffanta kyawun da ya yi mata ta sani
ɓata baki ne, mijinta kara kyau ya ke koyaushe da kuma
ƙuruciya musamman gashinsa baƙi siɗik da ya kwanta a
sumar kansa irin na Bafulatanin Yola wanda ke kara fiddo
da zahirin waye Hussein. Ta shagala a kallonsa da jin wani
irin tashin hankali da kishin zuwan da za su dinga yi Yolan
yanzu, tana da tabbacin idan matan Kano ba su yi nasarar
raba ta da shi ba, to wadannan kyawawan matan na
fulanin Yola za su iya rinjayar zuciyarsa. Hakan tunaninta
ke ba ta. Har ya kammala ya ɗaura agogo ta shagala a
tunani.
"Muje mu ci abinci, su na jiranmu." Ya fadi ba tare da ya
kalleta ba, jin shirun sai ya ɗaga kai yana dubanta. Ta
shagala a tunani, sai da ya ɗan yi tafi kusa da ita sannan
ta yi firgigit.
"Um, am..me ka ce?"
"Tunanin me kike? Nace mu je mu ci abinci daga can zan
biya wurin Dada sai na wuce Airport."
Ta yamutse fuska.
"Sai zuwa anjima zan ci, yanzu bacci nake ji."
Ya ɗan ɗaga kafaɗa.
"Ok. Bari naje, idan kin yi nisa a baccin ba sai na tasheki
ba. Zan wuce."
"Allah Ya kiyaye hanya."
Ya fice yana mai amsawa da wani irin nishadi a ƙasan
ransa.
A falon ya yada zango, yana cin abinci su na hira da
AlHassan da Kausar duk akan tsarin bikin.
"Yanzu kenan ita kadai za ta zauna a gidan? Yaushe
Amaryar za ta zo nan? Don naji ana cewa tare duka za su
shiga dakunansu."
Kausar ke neman sani.
"Asabar za su zo. Ke dama ai yanzu ba zancen zuwanki
Kano saboda matarnan. Su Hafsat dai da saura sai su je."
AlHassan ke maganar. Kausar ta jinjina kai.
"Allah Ya kaimu."
Shi dai Hussein loma kawai ya ke, yana kammalawa ya
mike ya gyara bakinsa. Koda ya shiga munshari Hajiya
Zeenatu kawai ke yi. Ya ja mata kofar bayan ya dauki
abinda zai dauka yana tsakin takaicin aurenta. Tare da
AlHassan suka shiga gidan Dada. Kullum ta gansu sai ta ji
kamar an yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi. Tana tare da
su Baba Yakura yan Maiduguri da ma sauran yan uwan
mahaiyarsu. Aka gaggaisa kafin ya yi musu sallama da
zummar wucewa Kano.
"Allah Ya kaika lafiya Ango. Mu dinma ai yanzu zamu
wuce. Kai dai tunda a jirgi ne za ka riga mu sauka."
Ya yi murmushi jin abinda Gwaggo Lubabatu ƴar abokiyar
zaman kakarsu ta bangaren Uba da ke Mubi ke fadi, ya yi
addu'a akan Allah Ya kawo su lafiya sannan aka kara yin
sallama ya tafi.
***
CIKAR BURI..
Gidan cike yake da yan uwa da aboka arziki, tun safe ake
shige da fice na dora sanwa. Dangi an cika a madafi ana
aiki ana kwasar hira. Fuskar kowa ka gani cike da farin ciki
musamman Hajiya da har kwalla sai da ta yi don kuwa
sun debemata kewar Abba. Cikar da suka yi ya motsa
zuƙatan mutan gidan da tunanin Abba, bikin ganinsa suke
yi tamkar na wata budurwa ba bazawara ba. Ƴan Daura da
yawansu sun zo hakanan kafatanin mutan gidan Hajja su
na nan. A bangaren Baba Dakta ma, hatta Kanwarsa
Hajiya Nabila da yan uwan Umman Amrah duk sun hallara.
Wannan shi ne kadai karar da zaa yiwa Hajiya mace mai
son mutane da kuma zumunci. Don sun shaida, Hajiya ko
ba ta je sabgarka ba, to hannunta zai je. Ba ta gajiya da
kyautatawa hakanan marigayin Mijinnata. A ganinsu
wannan ce karar da zaa yi.
Kowa ya bude baki ya ga cikar gidan cewa ake, har ma da
auren Ramlatun, shima ya yi albarka kwarai. Duk wannan
shagalin da ake, Ramlat na can tare da Amrah da kuma
Rafeeah a gidan kwalliya. Dama tun ana gobe daurin aure
suka je aka tsaramata lalle a ƙafa da hannu na gani na
fada. Hakanan duk a ranar aka yi mata kitso sirara.
Maryam Cutie ce gwanar kwalliyar, tsayawa faɗin irin
kyawun da ta yi ba'a cewa komai. Kasancewar Maryam
kawar Rafee'ah kuma ba ta da matsala ne yasa ba su wani
jima su na roƙo ba ta amince za ta bisu har Adamawa don
yiwa Amarya kwalliya ta musamman. Ba ta samu matsalar
hakan daga mijinta sosai ba don shi mutum ne mai
fahimta hakanan sanin da ya yiwa Rafee'ah da mijinta ne
yasa bai yi ja in ja ba.
"TubarakAllah Masha Allah."
Amrah ta fadi tana kallon Ramlat baki ya ƙi rufuwa tsabar
kyawun da ta yi mata. Ko aurenta na farko ba ta tsaya ta
nutsu an mata kwalliya kamar hakan ba. Murmushi Ramlat
ta yi jin yanda su ke koɗa ta. Farin leshin wurin Muniru ta
sanya an mata dinkin gown. Maryam Cutie ta yi mata
dauri na gani na fada a karshe ta yafamata gyalen kamar
yanda ya dace .
"Ke Ramlatu, kinga yanda kika sauya?"
Rafee'ah da ke tsaye gaban madubi tana dauri ke fadi, ita
da Amrah suma duka Maryam ta fito da fuskokinsu ba
laifi.
"Ya isa kar ku cinyeta."
Fadin Maryam tana dariya. Hotuna ta shiga yi mata tana
mai yin alfahari da baiwar iya kwalliya da Allah Ya ba ta.
Ta tabbata fuskar Ramlat ko kasar waje za ta a haka, to fa
za ta ciri tuta.
Sai wuraren sha biyu suka kama hanya zuwa gidan, ita dai
Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, fatanta Allah Yasa wannan
ya zama aure na karshe a gareta wanda mutuwa ce kawai
za ta raba. Allah kuma Ya ba su zaman lafiya.
Koda suka shiga gidan nan ma haka yan uwa suka yi caa
ana ta koɗa kyawun da Amarya ta yi, kunya ta kamata
ganin Hafsat diyar Dada, sai a sannan ta kula da zuwan
yan Adamawan. Hafsat ta ja hannunta zuwa can falon
Abba na baya da aka kai su, suka karasa ta durkusa ta
kwashi gaisuwa.
"TubarakAllah, Amaryar Hussein kyakkyawa da ita." Matar
ta fadi da hausarta da ba ta fita sosai. Ita dai Ramlat
kanta a kasa tana murmushin jin kunya. Sai da Hafsat ta
sanya ta zauna ta dinga daukarsu hotuna kafin a karshe ta
yi musu sallama ta fito tare da Hafsat. Nan fa Hafsat ta
shiga cikinsu aka dinga raha kamar dama can an shaku
sosai. Su Nusaiba duk sun zo, daga mai goyo sai mai ciki.
Suna zaune a daki sai ga Salma da Bilkisu, dama
Hunainah ita kam tun safe tana gidan, ko sadda suka shigi
tana kwance ta yi rashe-rashe a saman gadon suna
kwasar hira da kanwar miji kuma aminiyarta A'isha.
"Amarya Ramlat. "
Bilkisu ta fadi tana yamutse fuska musamman jin bakin
cikin ganin Hunainah ta riga ta zuwa. A ranta ta ce 'Cusa
kai.'
Ramlat ta gaidata da murmushi saman fuskarta. Ta
mance rabon da ta sanya Bilkisun a idanu, gaba daya ta
kara wani fari fat sabida shafe-shafe ga wani uban ƙiba da
ta ke narkawa, ita kuwa Salma har tambarin baƙi-baƙi ya yi
mata a fuska. Ramlat ta ja hannun Yasmeen suna
gaisawa, yarinyar yanzu ta bar sakewa sosai kamar a baya
don dif haka uwar ta raba ta da gidan. Yanzun ma da biyu
ne zuwannata, ba ta san mijin Ramlatun ba. Ko a hanya
suna ta gulmar abin suna dariya don har Salma na fadin
Allah Yasa wani Alhajin ne mai mata uku da katon tumbi.
A jikinsu ba su taɓa kawo wai matashi mai jini a jika zai
aureta ba musamman idan an san wacece ita.
"Murja da Fareeda ma suna tafe, Hilal ya fadamusu tunda
ke ba ki iya gayyata ba."
Ramlat ta dubi Amrah, Amrah ta kanne mata ido don ta
san gulma ce.
"Ayya, ban yi zaton za su zo bane. Allah Ya kawosu lafiya
kuwa. Ina murna."
Bilkisu ta taɓe baki ita kuwa Salma murmushi ta yi ta dora
kafa daya kan daya tana girgizawa. Sai dai kyakkyawar
budurwar da suka gani da aka kirata da yar uwar mijin
Ramlatun duk sai suka soma shan jinin jikinsu. A hankali
Salma ta yi magana saitin kunnen Bilkisun.
"Anya wadannan mutanen su na da labarin wace ce
Ramlat a baya?"
Bilkisu ta ce "Oho musu, nikam daga suturar jikin yarinyar
kamar dai ba karamin mutum shegiyar ta kwaso ba. Ai
kuwa ƙafata ƙafarsu har Adamawan naje na ƙarewa
danginnasu kallo sosai."
Salma da takaici da bakin ciki ya cika zuciyarta, ita kasa
magana ma ta yi. Shekararta sama da ashirin da biyar
yanzu amma ko auren fari ba ta yi ba, ga Ramlat har ta
kara samun wani ɗanɗasheshan. Don jikinta ya fara ba ta
hakan. Burinta yanzu a daura auren ya shigo ta karemasa
kallo.
***
Yana kishingide saman kujera a gidan Hisham wanda ya
shiga wanka, hotunan da Hafsat ta hankaɗomasa ta
whatsapp ya ke aikin kallo, sosai ya yi zooming hoton
Madam din tasa ya kasa kauda ido. Murmushi ya ke yana
jin soyayya mai tsafta na kara mamaye ko'ina na zuciya
da kwakwalwarsa.
Ba zato ya ji an fisge wayar, ya dan dago a ɗan razane
don sam bai ji tahowar Hisham din ba. Hisham wanda ke
daure da tawul ya ja tsaki.
"Aikin banza, sai afkin karewa mace kallo amma ba a iya
tattali ba. To ka tashi, yanzu Yayanmu ya kira ya ce sun
iso, ka tarbo su suna waje."
Hussein ya mike zaune gami da dan dafe kai kafin ya mike
ya ja guntun tsaki yana gyara zaman rigarsa ta shadda
fara ƙal sai dai babbar rigar na ajiye bai sanya ba.
"Ka ci gaba da shiga rayuwata. Kuma ma meyasa ya
kiraka bai kira ni ba?"
"Ganin dama."
Daga haka Hisham ya yi ciki da wayar Hussein din a
hannunsa don ya shirya, Hussein ya bishi da harara don
sosai ya ragemasa nishadi, a bakin gate ya ci karo da su.
Ganin wanda bai zata ba sai kawai ya tsaya kamar wani
gunki baki a bude.
"RASHEED?!" Ya furta kai tsaye kafin da azama su yiwa
juna wata wawuyar runguma da bubbuga gadon baya ana
dariya. Can ya sakeshi suka kara cafkewa su na dariya.
Nan da nan idanunsu suka kada kuma kamar wadanda ke
shirin kuka. Tabbas sun yi masifar kewar juna. Bai ma ga
sauran yan uwansa uku da ke tare da su ba sai da ya
gama gaisuwar da Rasheed. Najib, Faruk da kuma Khalil
duka Yola idan ka cire Faruk da ya zo daga Mubi.
"Allah Ya isa, ban yafewa matarnan."
Rasheed ya fadi sadda suka nutsu suka zauna a falo.
Murmushi Hussein ya yi.
"Ka bar damuwa da ita, ta kusa zama tarihi. Momi ta zo?"
Rasheed ya jinjina kai. Yana nufin mahaifiyarsa, Hajiya
Binta.
"Yes tare muke, tana can Yola wurin Dada."
Haka suka yi ta hirarsu cike da nishadi, shi dai Hussein
bini-bini zai duba agogo. Ganin lokacin sallah na ƙaratowa
ya dubesu.
"Ya kamata mu hanzarta wuce masallaci ko?" Lokacin
sallah ya gabato."
Me zasu yi ba dariya ba.
"Lokacin sallah ko lokacin daura aurenka? Kai Malam ba
ka da kunya wallahi."
Faruk ya fadi yana dariya.
"Bar shi kawai, ai idan bai yi hakan ba bai cika sabon
shiga ba."
Hussein dai har ga Allah sun soma ba shi haushi, dagaske
so yakeya ga an hanzarta an tashi an tafi.
"Na rantse zan muku ƙofi yanzun nan ku ga maciji."
Ya fadi yana mai mikewa tsaye suka yi dariya sosai shi
kuwa ya shiga zura babbar riga yana mai tafiya gaban
madubin dake falon yana gyara zamanta. Karshe ma hular
ya dauka ya shiga gyaramata zama yana ji AlHassan na
cewa su tashi don da alama Angon zai iya ficewa ya bar
su. Nan kuma wadanda ba su da alwala duk suka dora
sannan aka kama hanya bayan Hussein ya feshe dukkan
jiki da turaruka masu tsada da kamshi har kala uku.
Bababn burinsa Ramlat ta zama mallakinsa kafin kowane
irintsautsayi ya gifta da ba ma ya fatansa.
***
Misalin karfe biyu da mintuna, dubban jama'a suka shaida
daurin auren HUSSEIN AMINU GIDADO da RAMLAT
KHALID MU'AZZAM akan sadaki har dubu ɗari wanda nan
take aka damƙawa Babanta Dakta matsayinsa na
waliyyinta.
Bakin Hussein ya ƙi rufuwa, sosai daurin auren ya tara
mutane. Hilal kansa sai da ya halarta, duk da Hussein ya
san shi, haka suka gaisa faran-faran suka yi hotuna. A
karshe aka dunguma gaida iyaye.
***
Babu damar sallah a wurinta sakamakon tana fashinsa, sai
dai ta yi sujjadar godiya ga Allah kuma ta yi addu'a sosai.
Bayan ta mike ne Amrah ta ba ta tissue.
"Don Allah kar ki ɓata kwalliyar mana."
Ta karba tana goge hawayen.
"Kukan munafunci ne kawai, mace sai ka ce yau aka taɓa
dauramata aure. Aure na uku?"
Bilkisu ta fadi da dariyar kissa, Hafsat jin ta ce aure na
uku yasa ranta ya ɓaci, dadinta Hussein bai ɓoyemusu
komai na labarin Ramlat ba. Dama tun zaman Bilkisun da
irin kallon da suke jefamata ita da abokiyar rakiyarta ta ji
sun ba ta haushi.
"Ko aure na nawa ne ai aure ne. Duk wacce ta san me ta
ke yi dole zuciyarta ta karye a wannan rana, ko bakomai
ta san nauyin da Allah Ya ɗoramata."
Maganar Hafsat ta zo wa su Bilkisu a bazata, wato dama
sun san komai? Nan da nan ransu ya kara yin baƙiƙirin
musamman Murja da Fareeda da basu jima da shigowa
ba, suma dai ganin kwakwaf dinne.
"Muje falo ga Angon ya zo."
Fadin Muhibbat da ta shigo, ta ja hannun Ramlat suka
fice, Aisha kam ji ta yi kamar ta goya Hafsat don dadi,
balle kuma Rafee'ah da ke dariyar shaƙiyanci. Sosai
Hafsat ta burgesu don kanta a waye yake ba karya. Ai su
Bilkisu na jin haka suka bi bayansu rii duk domin su
ganewa idonsu Angon Ramlatu. Ai kuwa sun yi
kyakkyawan gani da ya birkita tunaninsu.
KARFEN KAFA Chapter 71
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Yana durkushe gaban yan uwan Ramlatun ana kwasar
gaisuwa, sai ga Amaryar. Nan da nan tsofaffi aka sjiga
guɗa da kirari. Ya kasa kauda idanunsa a kanta, ita kuwa
ganin irin kallon da yake mata babu kunyar ido yasa ta yi
ƙasa da idanunta.
Tsakiya aka zaunar da ita shima ya zauna, yan uwa aka
baibayesu mai hoto ya shiga aikin dauka. Kirjin Hussein
banda bugu da sauri babu abinda ya ke yi, ji yake kamar ya
ja ta ya sanya a babbar riga ya gudu da ita. Sai da aka
kammala hotunan har da mutan Adamawa sannan Ango
da tawagarsa suka fice.
Murja da Fareeda dai fasa yinin aka yi aka dunguma aka
tafi yayinda Bilkisu ta daure suka zauna. Amma Salma
rantsuwa take yi da ƙarawa cewa asiri ne kawai aka yiwa
Hussein domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa,
ko makaho ya shafa Hussein ya san ya wuce aurar Ramlat
duk da dai itama ba baya ba.
***
Sai wuraren bakwai na dare sannan jama'a suka soma
tafiya, wadanda suka rage da zasu je Adamawa ba su da
yawa. Ramlat ta yi ɗai-ɗai saman gado tana hutawa duk
ta gaji don yau ba karamin zirga-zirga ta sha ba a cikin
gidan kawai. Kowa ya zo sai an kirata an ɗauki hoto,
wannan zamani na hoto har haushi ya ke ba ta.
"Ke kinga mutuniyarki ko? Ta kasa ɓoye abinda ke cikinta?
Kai Allah Ya rabamu da hassada mugun ciwo."
Amrah ke zancen ganin duka na dakin babu bare, daga su
sai Nusaiba sai Aisha sai kuwa Hunainah dake sallah.
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ni mamaki ma abin ya dinga ban, ta madubi fa ina kallon
yanda suke hararata amma da mun hada ido sai su
basar."
"Ke wa ya taɓa samun daukaka idan bai hadu da yan
hassada ba? An fadamaki tsakani da Allah za ta je
Adamawarnan? Ni wallahi ban san sadda Bilkisu za ta
sauya ba. Gaba daya a farko kamar ba za ta yi ba." Fadin
Rafee'ah wacce ke shan wani youghurt da ƴan Yola suka
kawo.
"Dama DAN ADAM ance mai wuyar gane hali." Aisha ta
furta.
Haka aka yi ta hira, har zuwa sadda Hafsat ta shigo da
sauri ta hau kan gadon gami da sanyawa Ramlat waya a
kunne. Ta kalleta kafin ta tambayi waye cikin rada-rada ta
ce.
"Angonki."
"Assalamu alaikum."
Ta ji muryarsa sadda ta rike wayar sosai a kunnen, amsa
sallamar ta yi.
"Shi ne kika kashe wayarki ko? Gaba daya kin sa na rasa
nutsuwa."
Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuna ashe fa tun a wurin kwalliya
ta kashe wayar ba ta ƙara bi ta kai ba.
"Ina neman afuwa."
"Naji, amma yanzu ki fito ina mota. Gaisawa kawai zamu
yi."
"Ka..."
Bai bari ta kai aya ba ya katse wayar, dole ta cire ta
miƙawa Hafsat da hankalinsu gaba daya ba ya kanta. Ta
matsa kusa da Amrah ta mata raɗa. Amrah ta murmusa.
"Kar ki manta dai, yanzu miji ne a wurinki ba manemin
aure ba. Umarninsa za ki bi kawai. Ki je ba komai"
Ta mike ta gyara zaman dankwalinta ta yafa gyale sannan
ta fice. Tana jin yanda matan dakin suka dauki sowa
murmushi kawai ta yi ba ta ko juya ba.
A farfajiyar gidan ta ga mota sabuwa dal sai sheƙi ta ke,
ba ta yi zaton shi ne a ciki ba sai da ta zo giftawa ta ji ya
mata hon, hakan ya ba ta damar bude kofar don ba'a
ganin na ciki. Shi din ne zaune kuwa, ta shiga ta rufe
sakamakon AC da ke a kunne. Kamshin motar da
kamshinsa sun hadu da sanyi sun saukarmata da ni'ima a
zuciya. Ta dubeshi, ya cire babbar riga hakanan hular na
ajiye saman gaban motar.
"Ina wuni."
"Lafiya."
Ya furta tamkar ba ya so. Can ya ce.
"Ya gajiyar biki? Anya kin ci abinci? Sai naga kamar kin
faɗa."
Ita mamaki ma ya ba ta don haka ta kasa amsawa.
"Kin yi shiru."
"Uhm, na ci."
"Kin fa zama matata, amma na lura da ke tun dazu kamar
murmushin dole ki ke yi."
Yanda ya yi maganar kamar zai yi kuka yasa ta dubansa,
gaba daya ya juyo ya matsa dab da ita, ta ji nauyinsa, shi
kuwa hakan yake so dama, tun shigowarta ya ke kokarin
su hada ido amma hakan ya gagara. Za ta juya kai ya yi
saurin riƙo haɓarta ya karkato da kan. Ta dora hannunta a
saman nasa da zummar kautarwa. Sai dai ya rike hannun
tamau.
"Please ka sakarmin hannu."
Ta ci gaba da kokarin kwacewa don ba ta shiryawa hakan
ba. A hankali ya saki hannun.
"Na saki. Shikenan?"
Ba ta ce uffan ba.
"Ki je kawai, sai mun yi waya ko?"
Ta saci kallonsa, kamar dai fushi ya yi. To ita kuwa me za
ta ce? Ina sabon da za ta sake don ya rikemata hannu?
"Kin tsareni da ido, ba na kyaleki ba?"
Yanda ya yi furucin sai ma ya ba ta dariya, ta kauda kai
tana murmushi.
"Ni kike wa dariya?"
"Aa."
"Kin ma iya ki ci abinci, ni da ban ji ki ba kasa daurewa
nayi da komai har sai yanzu da na zo na ganki. Idan na
tsaya wassafa kalar farin cikin da nake ciki, zamu kwana
mu wuni a nan."
A hankali ya jawo hannunta mafi kusa da shi ya damƙe
cikinnasa. Wani yarr ta ji kamar yanda shi kansa sai da ya
ji wani shock. Ya ƙurawa lallen idanu.
"Allah Ya bani ikon riƙe ki amana Ramlat. Ya ba ni ikon yi
maki adalci a zamantakewarmu. Na san na ɓatamaki rai
da yawa, amma ki yi hakuri. Haka nake, ban yarda da
soyayya kafin aure ba, bayan aure ke kanki yanzu son zai fi
maki armashi a kowace tafiya. Abubuwa da yawa ba ma
sai na fada ba tunda ke ba yarinya ba ce ko?"
Ta saci kallonsa don gaba daya sautinsa ya sauya, gira ya
ɗaga mata yana jifanta da tattausan murmushi. Ta kauda
kai ta shiga kokarin zame hannunta.
"Na dauka zaman hakuri da biyayya kawai zamu yi ai
tunda cikinmu ba wani mai kaunar ɗan uwansa."
Ba zato ya fisgota kafadarsu na gogar juna kamar yanda
fuskokinsu tuni ya hadu wuri guda sai hucin numfashinsu
da ke gaurayewa.
"Kina da tabbacin bana sonki? If yes,