Showing 78001 words to 81000 words out of 113545 words
Chapter 27 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
ba anan
sai dai mu ji labarin ka tafi ko?"
Dariya ya yi.
"Ni na isa na shigo garin nan ban je na ga Hajiyarmu ba?
Aa sam. Wallahi yau nake cewa zan shiga zuwa yamma
haka."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya nunamana."
"Amin amin. Bari na bar ki kada na sa ki makara. Sai na
shigo din."
Ta amsa da toh gami da yi mishi fatan alheri, ya rufemata
murfin motar sannan ya wuce zuwa tashi motar. Ta ja
numfashi ta furzar, Hilal kenan, mutumin da ya kaunaceta
don Allah. Gaba daya ya sauya ya ajiye kumatu. Ga duk
wanda ya gan shi zai fahimci yana cikin jin dadi da
kwanciyar hankali. Wayarta ce ta yi ringing daidai sadda ta
ke kokarin hawa titi. Ba tare da ta duba ba ta daga gami
da karawa a kunnen da sallama.
"Ke da waye tsaye a titi?"
Tambayar da aka watsomata ba tare da an amsa sallama
ba yasa ta gane ko waye. A hankali ta ɗaga kai ta dubi
mirror, motarsa na nesa kaɗan da nata. Ta fi kyautata
zaton daga wurin motsa jiki ya ke. Murmushi ta yi daidai
sadda ta hau titi ta harba motarta.
"Ba ka da hurumin sanin da wanda nake magana. Kar ka
manta ban kai ga zama matarka ba."
"Hakane, ba ki kai ga zama ba. Amma kin manta cewa
haramun ne nema cikin nema? Ke musulma ce."
Dariya ya ba ta jin yanda ya zaƙalƙale. Yanda ta ke tafiya
a sannu, haka yake biye da ita da motarsa a sannun. Ta
kauda kai kamar ba ta san da shi din ba.
"Babu wanda ba ya kuskure."
"Haka kika ce? To naga kin ƙara tsayuwa da wani ɗan
iskan! Duk abinda na yi mishi, ke kika ja. Sannan lokacin
da za ki ajiye yawon gantalin aikinnan ya yi! Ba zan
lamunta ba."
"Wannan kuma ba ka da hurumi a ciki, ajiye aiki sai
lokacin da naga dama. Ka bar tada jijiyoyin wuya tunda
har yanzu aure bai tabbata ba tsakaninmu. Akwai sauran
lokaci."
Tana kaiwa nan ta katse wayar ta taka motarta, sai dai ba
ta je ko'ina ba ya zo ya gifta ta har yana kokarin buge wani
ɗan sahu. Bai ko tsaya ba ya yi gaba. Ta bi shi da kallo
tana dariyar farin ciki, ko ba komai ta san ta ba shi aiki.
Wannan nishadin yasa ta ware waƙar Breaker na Jarumar
Mata tana saurara har ta karasa wurin aiki.
Hussein bai kara kiranta ba kwata-kwata a wannan ranar.
***
Bisa umarnin Yayanta Munir, ta rubuta takardar barin aiki.
A wannan satin Rafee'ah ke zuwa ta kai ta gidan mai
gyaran jiki. Ya kasance Ramlat ba ta da lokacin kanta
balle na yara, ɗawainiyarsu ta koma hannun Hajiya da
direba mai safa da marwar kai su makaranta da daukowa.
Waya ba ta kara shiga tsakaninta da Hussein ba sai dai
kokari kawai ta ke yi itama don tana kewarsa. Ya aiko da
wani leshi mai tsadar gaske da kuma atamfofi har kala
uku suma masu tsada sai mayafai da jaka da takalma, sai
kuwa tsarka kala biyu da abin hannu duk na fitar biki. Ba
ɓata lokaci aka kai wurin dinki tare da wanda Munir ya
siyamata.
"Wai ke angonnaki yana zuwa hira kuwa? "
Ta dakatar da shafa man da take yi a jiki ta dubi Amrah
wacce ke zaune saman gado tana shayarwa. Taɓe baki ta
yi.
"Mutumin da ko waya ba ya kirana."
Da mamaki Amrah ta ce.
"Bana son sharri Ramlat."
Harararta ta yi.
"Kawai sai na zauna na kantara maki karya saboda ina
tsoronki ko?"
Murmushi Amrah ta yi. Nan ta kwashe duk yanda ake ciki
ta faɗamata har maganarsu ta karshe.
"Kai amma kin fadi mai zafi da yawa Ramlat, to ko za ki
rama ai kya bari ya zo hannu tukunna. Shima dai da alama
yana da zafin kishi tunda ya kasa nemanki har yau. Amma
kar ki kara tunanin wai ba ya sonki, wallahi Hussein na
miki son da ba ki san adadinsa ba. Da kansa fa ya je ya
fadawa Baba Dakta yana sonki da aure tun ma a lokacin
Chairman. Abinda kawai na kula, kamar yanda ya
faɗamaki, shi mutum ne da bai yarda da wata soyayya
kafin aure ba. Ya fi imanin cewa soyayya ta gaske tana
zuwa ne bayan an yi aure. Kuma kar ki yi mamaki, irin su
Hussein sun iya tattali da nuna kauna ga mace. Ina goyon
bayanki, idan ku ka yi aure ki nunamasa kefa mace ce,
amma ba wai ina nufin kar ki masa biyayya ba, aa, ki dai
ja ajinki yanda zai gane shayi ruwa ne. Ke ba yarinya ba
ce, na tabbatar kin gane me nake nufi."
Suka yi dariya gami da cafkewa don tuni Ramlat ta taso ta
dawo gefenta.
"Ai ko yanzu ya ganki ya san kin sauya. Kin kara kyau
gyaran jikin ya karɓeki. Duk inda kika gifta kamshi kawai
kike kamar mai wanka da turare. Nidai akwai tsarabar da
zan maki na kananun kaya, saura ki ƙi sanyawa."
Murmushi Ramlat ta yi, sai kuma ta ji zuciyarta na neman
karyewa.
"Allah Ya jaddada rahma ga Aliyu."
Ta furta a fili, Amrah ta amsa da amin. Nan kuma suka
shiga tuna baya, sai da Amrah ta ga dagasken Ramlat
kukan take son yi don idanun sun cicciko da kwalla, sai ta
share gami da sanyo wata hirar.
"Zan so naga yanda waccan bakar munafukar za ta yi idan
ta ji labarin aurennan."
"Ni kuma kinga tsoron ranar da za ta sani nake yi. Sai
kuma mamakin dalilin Hussein na ƙin ɗaukar mataki a
kanta. Idan na yi tunanin ko yana sonta dagaske, ba ki san
ya nake ji ba."
"Gaskiya da mamaki ace yana sonta, nidai jikina sai ya
bani kamar so yake sai ya nunamata ita din ba komai ba
ce kafin ya dauki mataki. Ai ko don yanda ta dinga kai
maki hari, ya cancanta dama Hussein ya aureki mu ga ta
tsiya."
Ramlat dai dariya kawai ta yi.
"Kin sanar da Muhibbat?"
"Eh na fadamata, ta ce za ta shigo ranar daurin auren
tunda dai wunin ma duk rana daya ce."
"Allah Ya nunamana."
Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido.
A daren bayan ta yo wa Amrah rakiya kofar gida don
Dahiru ya zo daukarta, sai ganin Hussein ta yi. Suka dubi
juna da Amrah da mamaki. Amrah ta murmusa.
"Kinga ɗan halak, ashe dai yana tafe."
Ita dai Ramlat mamaki ma ya hanata cewa uffan. Suka
karasa daidai sadda ya fito daga mota suna gaisawa da
Dahiru, daga nan ya amsa gaisuwar Amrah har da karɓar
Baby ya yi mata wasa sannan ya yi musu sallama ya shige
ciki ko inda Mutuniyartasa ta ke bai kalla ba. Ita ma ta
dauke kai ba ta damu ta gaidashi ba.
"Wai ke ba Angonnamu kenan ba? Shi ne ko gaisuwa."
Dahiru ya fadi cike da zolaya. Ta harareshi don dama sun
saba.
"Ban ga damar gaidashi din ba."
Ya daga kafada.
"Ai shikenan. Mu dai maza ba'a ja mana aji."
"Ko?" Cewar Amrah cikin son a tuna baya. Ya yi dariya
kawai ya bude motarsa ya shiga.
"Allah Ya bamu alheri Amarsu. Sai da safe kafin wannan
Madam din ta ɓallomin ruwa."
Dariyar suka yi kawai, ta bude gidan baya ta ajiyewa
Amrah ledarta. Ba ta juya ba har sai da ta ga sun ja mota,
ta koma ciki tana son ganin yanda za su kwashe da
Gogannata.
A hankali ta ke takawa tamkar mai tafiya akan ƙaya,
murmushi kawai ta ke zabgawa tana duban sararin
samaniya wanda taurari da kuma watan na Rajab da bai fi
kwanaki shida da bayyana ba. Hakan na nunk da
kusantowar da wata azumin Ramadan ke ƙara yi. A
hankali kuma ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da tafiya har
ta kusa barandar da za ta sada ta da falonnasu. Yanda ta
ganshi a tsaye hakan ya dauremata kai, ta yi zaton yana
ciki su na gaisawa da Hajiya, ko kuwa dai ya shiga ne ya
fito? Oho. Ba ta da tabbaci, ganin kallonta kawai ya ke yi
sai ta sunkui wa kai, koda ta karasa har za ta gifta sai
kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, don haka sai ta tsaya
ta gaishe shi.
Maimakon ya amsa kawai sai ya kuramata idanu, idan ya
ce ba ta sauyamasa ba, to ya yi karya. Ta wani cicciko ta
yi haske, kamshi ke tashi kawai a jikinta. Ramlat ta ji
shirun ya yi yawa don haka ta ɗan ɗago kai. Nan da nan
ya daure fuska ya hadiye murmushin da ya yi niyyar
suɓucemasa. Ya wayance da ɗan jan karan hancinsa da
jan hancin kamar mai mura.
"Am...Meyasa ki ke giftawa cikin maza da uban
ƙamshinnan? Koda ace babu maganar auren wani a kanki,
kina sane da cewa haramun ne ko?"
Kanta a kasa ta yi murmushi a kasan ranta ta ce.
'Ka ji da masifaffen kishinka.'
"Ni ko fita ba na yi yanzu."
"Ko? Meyasa na ganki a waje? Idan mijin Amrah ne,
mijinki ne?"
Ta ɗago ta dubeshi sai ma ya ba ta ƴar dariya. Maimakon
ta ba shi haushi sai ta burgeshi, kawai sai ya jingina kai
jikin gini yana kallonta. Ganin haka ta hadiye dariyar.
"Allah Ya huci zuciyarka."
Lumshe ido kawai ya yi ya bude.
"Matso, magana za mu yi."
Ba musu ta dawo ta tsaya daga gefensa. Kamar ta ce
masa su nemi wurin zama amma kawai sai ta share.
"Kamar yanda na san cewa kin sani, yana da kyau na kara
faɗamaki da bakina. Bayan aurenmu Adamawa zan kaiki.
Kano sai dai mu zo ziyara. Abu na biyu babu batun aiki, ko
a Kanon ko a Adamawa. Ba zan jure ganin ina fita nema,
matata na fita ba. Kar ki ce za ki haɗa kanki da Zeenatu,
wannan daban take hakanan tsarin rayuwarta daban da
taki. Ina fatan kin fahimta?"
Ramlat da ta kasa haɗiye kishin Hajiya Zeenatu, ta gyada
kai, ciki-ciki ta amsa.
"Na ji."
Jin yanayin sauyawar muryarta ya sanya shi ɗan matso da
kai kaɗan yana murmushi, cikin rada-rada ya ce.
"Mece ce damuwarki? Hajiya Zeenatu ko kuma maganar
aiki?"
Ta juyo da zummar harararsa, sai dai ganin irin kusancin
ya kai har fuskarsu na dab da haɗewa yasa ta saurin ja
baya tana maida numfashi. Shi kansa sai da ya ji wani yarr
tun daga yatsar ƙafafunsa zuwa kwakwalwa. Ya sauke
ajiyar zuciya.
"Ina iya tafiya?" Ta nemi sani a gaggauce.
"Kin gaji da ganina? Sati nawa ba ki ganni ba?"
Baki sake ta dubeshi. To ma duka-duka yaushe suka hadu
a titi ya cashe mata? Sai kuma ta juya kanta kawai tana
duban yatsun kafafunta.
"Shikenan, zan kiraki a waya. Kina iya tafiya."
Ta amsa da toh sannan ta nufi ciki.
"Ba ki ji ba."
Ya katse ta, ta ciji lebban bakinta don ita kam ba ta son
kallonnasa, ta daure ta juya. Murmushi kawai ya yi mata.
Sai aikin kallo, ta gaji da rashin maganar ta juya abinta
zuwa ciki.
Yau kam duk juyinta tunanin Mijinnata ne, ta yi mamakin
sauyinsa amma ta fi kyautata zaton kawai kewarta da ya
yi ne ya chanja shi. Koda ta kammala shirin kwanciya, ta ji
bai kira ba sai ta yi zaton ya yi bacci. Da Asuba bayan ta
idar da sallah, ta zare wayar a chaji. Ga mamakinta
missedcalls har biyar duk na Hussein sai saƙon da ya turo.
Ta bude.
_*Kin kyauta kenan?*_
Ta yi murmushi, Hussein rigima kenan. Ita shaf ba ta
tsammaci zai kira ba tunda har goma ta wuce ga kuma
bacci na cin idanunta don kwanakinnan ba ta fiye samun
yi sakamakon sammakon zuwa wurin gyaran jiki da ta ke
yi. Madadin ta ba shi amsa sai kawai ta share ta jefa
wayar gefen gado sannan ta fita gaida Hajiya. Koda ta
dawo, biyawa ta yi ta tashi Ummi da Ansar su yi sallah. Ba
ta ci wuya ba suka tashi domin sun riga sun saba. Kamar
yanda ta yiwa Hajiyar, hakanan su ma suka shiga suka
gaisheta.
Ƙarfe takwas a gidan Hajiya Bingel Sudan ta yi mata, ta
yarda sosai da gyaran matar don ta san ta kan gyara.
Duka-duka ba a sani jima da farawa ba amma gaba daya
ta sauya, sai dai ba laifi Yayyunnata mata sun kashe kudi.
Koda ta koma gida ta iske kaya jibgi a falo, ashe kasuwa
su Maman twins suka je. Tarkacen kayan kicin ne kala-
kala da Munir ya bada a siya. Babu laifi kullum kudinsa
daɗa albarka ya ke yi. A bakin Rafee'ah ta ke jin zancen
furnitures, wai Baba Dakta ya ce komai da ya danganci
wannan a barshi a hannunsa. Ta kara jinjina riƙon zumunci
da kuma abota na Baba Dakta wanda bai taɓa bari sun
koka da rashin Abba ba.
"Kai wannan Jug din ya yi kyau. Ga azumi ya taho, har na
hango bakin Hussein yana kwankwaɗar lemu."
Rafee'ah ke maganar tana dariya, gaba daya suka sa
dariyar har Ramlatu.
"Ke dai Rafee'ah ban san sadda za ki girma ba. Yara uku
amma har yanzu da sauranki."
Rafee'ah na dariyar furucin Hajiya, Maman Twins ta ce.
"Ai da alama sai Baban Abba ya rangaɗomata kishiya."
"Shi ya isa? Taɓdi! Ai shiyasa ko magana ya dauko nake
katseshi da cewa ko gidanmu daya tal na tashi na gani.
Soyayya tun na yarinta har girma don haka kada ma ya
fara."
Daƙuwa Hajiya ta mata.
"Ungo nan! Kin isa ki ja da ikon Allah? Yau Isma'il ya so
aure ai kuwa baki isa ki hana ba. Ba gwara kishiyar ciki ba
da a yi maki ta waje ba?"
Nan fa aka shiga hirar kishiya, Maman Twins na fadin ita
kam tana ma ji a jikinta Baban Twins aure yake son yi
tunda ginin da ya fara na bangare biyu ne. Ita dai Ramlatu
ta yi shiru kawai tana duba kaya, idan abin ya ba ta dariya
ta dara. Can kuma maganar ta dawo kanta.
"Kedai me kishiya irin Zeenaru take ko wa? Wallahi sai kin
tashi tsaye da addu'a. Azkar safe da yamma kar ki bari ya
wuceki. Ni na ji dadi ma tunda ba wuri daya zai haɗaku
ba."
Ta dubi Maman Twins.
"A ina kika ji?"
"Ni ya fadawa. Na fi zaton akwai dai abinda ya ke nufi a
kan matar, amma bari mu zubawa sarautar Allah ido. Ke
dai kamar yanda Uwanin ta fada, ki zage damtse da
addu'a. Ya sanar da ni ma zuwan matar Hassan da wasu
cikin yan uwansu, amma ba gidansa za su sauka, masauki
zai kama musu. Ba yanda ban yi ba da shi akan ya bari su
zo nan yace babu komai."
Hajiya ke zancen ita dai ba ta da labari ma sai lokacin. Sai
kuma suka koma batun rakiyar Adamawa, su na tantance
wadanda ya kamata su je.
"Bilkisu fa? Ke an fadamaki Bilkisu za ta shiga sabgar
Ramlat?"
Rafee'ah ta tambaya da mamaki jin Maman twins na batun
Bilkisu.
"Toh aikuwa za ki sha mamaki tunda Munirun da kansa ya
sanarmin cewa za ta je. Kuma ita ta amsa da hakan."
Hajiya ta fadi. Nan dai Maman twins aka hau rantsuwar
gulma ce kawai za ta kai ta. Haka suka yi ta tattaunawarsu
abin gwanin sha'awa. Aisha ciki ya soma nauyi ba kasafai
ta ke fitowa ba.
***
WASHEGARI...
"Ki soma shirya kayanki. Tafiya ta zo."
Hajiya Zeenatu ta dubi mijinnata gabanta ya fadi.
"London ko ina?"
Ba tare da ya dubeta ba ya ce.
"Adamawa kafin London. Ai na faɗamaki zamu je yan
uwana su ganki ko?"
Ta dan yi shiru tana tuna wayar da suka yi jiya da daddare
da Kawu Modibbo. Gargadi ya yi mata a kan zuwa
Adamawa don a cewarsa ya zo garin, bai kuma ga wata
alama da ke nuni da cewar ta samu karɓuwa ba, asalima
labarin da ake shi ne, asiri ta yi ta rabashi da mahaifarsa.
"Kin yi shiru."
Hussein ya furta gami da ɗan riƙo yatsun hannunta yana
murmushin yaudara. Ta bishi da na yaƙe.
"Hum, kana ganin ba ni da matsala da su? Za su karɓe ni
da hannu bibbiyu?"
Hussein ya ci gaba da bin ta da kallo, abinda ya ke zargi
ya kara tabbata. Jiya ya ji tana waya kuma tsaf ya ji me
tace. Sai dai bai gama fahintar waye ke tare da ita a
danginsa ba, ko ma waye dai ya lura sun jima su na tare.
Zai bi ta sannu har wayarta ta fado hannunsa ya dauki
lamba.
"Kamar kowane dangi, akwai masu murna da ci gaban
mutum da ma wadanda ba su yin farin ciki. Ba zan rantse
maki cewa duka dangina su na sonki ba Zeenat,
musamman abinda ya faru tsakaninmu wasu su na daukar
alhakin ki cewa ke ce silar komai. Amma bangaren yan
uwana kuma shaƙiƙaina, ba ki da wata matsala. Don haka
ki kwantar da hankalinki. Ban taɓa fadamaki ba saboda
bana son sanyaki cikin wani hali. Amma yanzu ya zama
dolena na faɗa don kar ki ga wani abu a wajen wasu ki ji
ba dadi. Ba zaman kowa kike ba face ni."
Wani dadi ya lulluɓeta, ta ji a duniyar nan ta kara son
Mijinnata. Ba ta sadda ta rungumeshi, ya runtse ido yana ji
kamar wuta ta ɗosana a fatar jikinsa.
"I love you."
Ta furta a hankali. Ramlat ce ta fado a ransa kafin ya ce.
"I love you too."
Da wannan ya shawo kanta ta mike har da batun za ta
shiga kasuwa ta soma siyan tsaraba. Ya fiddo kudi zai
karamata ta girgiza kai da binsa da hararar wasa.
"Ah haba, yan uwanmu ne fa. Rike abinka, da kudina zan
musu tsaraba."
Ya yi murmushi kawai. Yana binta da kallo, ya lura kwana
biyunnan kurajen nata da sauki sun fara mutuwa, ta dai ce
na gargajiya ta soma karɓa ta gaji da zirga-zirgar asibiti.
Shi dai ba abinda ya shafeshi. Kusantarta ne tuni ya bari.
***
RANA BA TA ƘARYA!
KARFEN KAFA Chapter 70
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Ana gobe ɗaurin aure tun da safe, suka bi jirgi zuwa Yola.
Awa biyu da mintoci ta kaisu. Kamar yanda Hussein ya
shirya, Kausar da AlHassan ne masu zuwa tarba. Kausar
tun da ta ga Hajiya Zeenatu ranta ke zafi dakyar ta iya
tankwara zuciyarta.
'Allah Ya isa.' Ta fadi a kasan ranta, Hajiya Zeenatu kuwa
wani dadi ta ji ganin irin tarbar da ta samu a wurin Kausar
duk da shekarun da ta ba ta. Suka dunguma a motar
AlHassan zuwa gida. Bai yi gangancin sauketa a gidan
Dada ba don ya tabbata Dada za ta iya kasa hakuri don ba
ta iya ɓoye abinda ke ranta ba wasu lokutan sai dai ya san
akwai ta da hakuri.
"Anan za ki zauna sai zuwa gobe idan an huta sai a leka
dangi. Hakan ma ina ce ya yi miki?"
Hajiya Zeenatu dake karewa dakin da aka ba su kallo ta
juyo tana dubansa fuskarta cike da damuwa.
"Yanzu dagasken a yau za ka juya? Gaskiya idan hakane
zan jira a gidannan zuwa sadda za ka shigo garin sai mu
leka dangin tare. Wallahi haka kawai na ke jin fargaba."
'Me akai da maza Zeenatu?' Ya furta a ƙasan zuciyarsa a
fili kuwa murmushi ya yi kamar gaske ya shafi gefen
fuskarta.
"Shikenan, yanda ki ka ce hakan za'a yi. Nima kin riga da
kinsan dalilin komawar, ban larasa handling komai a wurin
aikinmu ba ne, gobe juma'a in sha Allah da zarar na
kammala, Asabar da safe zan taho."
Ta gyada kai.
"Babu wata damuwa. Allah Ya kaimu."
"Amin. Amma toh ko bikin ba za ki leƙa ba? Na fadamaki
Cousin Sister ce a wurina."
Ta tuno da hakan don Kawu Modibbo ya fadamata zancen
bikin don shi ne silar zuwansa garin shima. Sai dai ya
gargadeta da shiga dangin gudun samun matsala don
haka ta girgiza kai. Shima Hussein kawai fada ya yi don ya
gwadata, amma tuni ya ji tana batun ba bikin da za ta leka
da wanda suka yi waya kwanaki.
"Ka yi hakuri dai, ka ga ba'a san ni ba. Zan jira har ka
dawo ka gabatar da ni a wurinsu."
Ya jinjina kai.
"Ba damuwa."
Daga haka ya rage kayan jikinsa ya shiga bandaki, can ya
fito, wanka ya