Showing 102001 words to 105000 words out of 113545 words
Chapter 35 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
ciki. Hannu kawai ya waremata ba
musu ta ƙarasa ta rungumeshi. Ya kuwa ɗagata cak yana
juyi da ita, dariya ta yi bayan ya sauketa ƙasa yana nishi da
riƙe ƙugu.
"Heart, kin fa ƙara nauyi."
Ta turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara, ya yi murmushi
da jan karan hancinta kafin ya rungumota ta baya.
"Albishirinki."
"Goro."
"Alhamdulillah, bisa la'akari da workkng experience dina
da kuma credentials, Yayanmu ya samarmin aiki a wani
Kamfanin gine-gine. Sosai su ka yaba da komai nawa "
Ta juyo ta ba shi kyakkyawan sumba a kumatu. Ganin ya
jefata da wani kallo ta kauda kai tana murmushi don har
sannan wani lokacin Hussein dinta kwarjini ya ke mata.
"Congratulation, Allah Yasa a fara a sa'a. Ya kara
daukaka."
"Ameen dearest one."
Daga haka ya jawota ya hau yi mata raɗa a kunne. Daidai
sadda wayarta ta yi ringing, kasancewar shi ne a kusa, ya
ɗauma, ganin baƙuwar lamba sai ya ɗaga kawai, bai kai
da sallama ba muryar namiji ya ratsa dodon kunnuwansa.
"Assalamu Alaikum, Adda barka da rana. Taheer ne."
Wani irin kallo ya ke bin Ramlat da shi, Ramlat gabanta ya
fadi, ta sani dai a dazun Taheer ya kira ya ce yana son
magana da Hafsat zai mata wani albishir, ta ce ya bari
idan ta shiga gidan sai ta kira. Shaf ta mance, kuma ba ta
samu shiga ba sakamakon wankin undies dinta da ta
tsaya yi. Jikinta ya bata akwai matsala. Ba ta gama
tantancewa ba sai da ta ga Hussein ya miƙamata wayar ya
kuma ƙuramata idanu. Ta karɓa da rawar hannu, gaba
daya ta ruɗe, tunda suka yi aure ba ta taɓa ganinsa a
wannan yanayin ba kuma ma adalilinta sai yau.
KARFEN KAFA Chapter 77
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
"Hello. Taheer ba..ta..ba ta kusa."
Daga yanayin muryarta ya fahimci akwai matsala, bai kara
magana ba ya katse wayar yana mai dana sanin kiranta
duk da irin gargadin da ta yi mishi akan muddin ba ita ta
nemeshi ba su yi magana da Hafsat, kar ya yi gangancin
kiran wayarta.
Hussein juyawa kawai ya yi ya wuce ɗakinsa, ta dage
goshi tana kiran sunan Allah, shakka babu laifinta ne ko
me ya faru. Ta saɓa umarninsa na hana Hafsat waya,
tunda yanzun ba amfani, abinda ya ke gudun, tana yi da
wayarta.
Ramlat ta numfasa, tunani take ta bishi ko ta kyaleshi
zuwa anjima kaɗan? Sai dai idan ta rabu da shi, tana
tsoron kada ya ƙi cin abinci alhalin daga yanayinsa kadai
ma ta fahimci ya kwaso yunwar.
Mikewa ta yi tsam ta nufi dakin. Ba ya nan, alamar an
kunna ruwa yasa ta fahimci yana banɗakin. Ta nemi wuri
gefe gadon ta zauna, ta ɗan jima zaune kafin ya fito ɗaure
da tawul a ƙugunsa sai karami a hannun yana share ruwan
gashinsa. Bai ko kalleta ba ya yi gaba zuwa gaban
madubin, da saurinta ta karasa ta bayansa, ganin abinda ta
ke shirin yi, wato rungumoshi, sai kawai ya juyo fuska ba
walwala hakan ya dakatar da ita, ta sunkuyar da kai har
idanun sun cicciko da kwalla.
"Don Allah ka yi hakuri, ba zan ƙara ba. In sha Allahu an yi
na farko da karshe."
Bai ce mata komai ba ya juya ya bar gaban madubin
bayan ya gama abinda ya kai shi. Ramlat jikinta duk ya yi
sanyi, ta sa hannu ta dauke hawayen da ya gangaro. Shi
kuwa gogan, yana kammala shirinsa cikin kananun kaya ya
feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, ya fice. Ta bi
bayansa da sauri ganin ya dauki mukullin mota, da wani
irin gudu da ba ta san ta iya ba ta rigashi isa da ƙofar ta
tare. Duban tsakar ido suka yiwa juna, kowannensu sai da
yanayinsa ya sauya. Ba tare da ta dauke idanunta ba ta ce.
"Don Allah ka saurareni, nayi maka laifi ka yi hakuri ka
yafemin."
Kamar ba zai tanka ba sai kuma ya kare tamke fuska.
"Tun yanzu zan yi hukunci akan abu, ki nunan bai maki ba
har ma ki goyawa wannan abun baya, wane irin kallo kike
son na yi maki? Ke a yanzu sai dai ki ba wani labarin
abinda ya gudana tsakaninmu da uban yaronnan, duk
wannan ma bai min ciwo ba kamar yanda har kika iya
take umarnina. Ko ban hanaki ba, tunda har kika ga na
raba ta da wayarta kin san me nake nufi. Ban wuri na
wuce."
Maimakon ta matsa sai kawai ta noƙe kafaɗa gami da
marairaice fuska, kallonta kawai ya ke yi. Daga yanayinsa
ta soma fahimtar ya soma saukowa don haka ta sanya
dukkan hannuwanta ta rungumoshi ta kwantar da kai a
saman kafaɗarsa.
"Ka yi hakuri, na tuba ba zan ƙara aikata laifi irin wannan
ba. Please Haskena."
Shirun da ta ji har ta fidda ran zai sauko, ta soma kokarin
janye jikinta ya riƙo ƙugunta dakyau, fuskarsu ya haɗe
wuri guda yana bin karan hancinta da kallo kafin ya maido
idanunsa cikinnata.
"Kinsan ba na iya fushi da ke ko?"
Ta yi murmushi ta lumshe ido gami da gyaɗa kai duk a
lokaci guda, a hankali kuma ya shiga aikamata saƙo mai
kashe jiki. Karshe dai Hussein fitar da bai yi ba kenan,
dama sanadin bacin ran da yake ciki ne ya tilasta masa
son fita. Can ta janye jikinta ganin yanda ta matsu da jikin
ƙofa.
"What?" Ya fadi da dusasshiyar muryarsa. A shagwaɓe ta
amsa.
"Yunwa."
Ya yi murmushi gami da ɗaga rigarta ya shafi cikin.
Lumshe idanu ta yi.
"Allah Yasa mun samu ƙaruwa."
Ta harareshi da wasa kawai ta juya ta bude kofar, ya biyo
bayanta don shi kansa yunwar ke cinsa. Sai da suka
kammala ba cikinsu hakkinsa kafin kuma ya miƙe ya shiga
ɓangaren Dada. Ramlat dai jikinta ya yi sanyi don har
tausayin Hafsat ya kama ta, ta tabbatar yau kam Hussein
ba zai ɗagamata ƙafa ba.
Aikuwa hukuncin da ya dauka a kanta mai tsauri ne don
har makaranta ya ce ta zauna sai ya yi magana sannan ta
ci gaba da zuwa, amma fita dai ko nan zuwa farfajiyar
gidan ce ya hanata. Ya kuma rantse muddin ta kara
gangancin yin waya da Taheer sai ya saɓa kamanninta. Da
wannan bakin cikin ya bar Hafsat ya fice abinsa.
***
NIJAR-KANO
Sun ɗau hanya miƙaƙƙa daga Maradi don dawowa
Nijeriya, garin Kano. Zuƙatan kowannensu farin ciki ne
marar misaltuwa, duk da irin wata azaba da su ke ji a
tsakanin mazaunansu, hakan bai sa sun kasa yin murnar
samun nasara ba. Kowaccensu ta matse kwalin aikin da ta
karɓo a ƙasan ƙafafu, idan kuwa wuri ne mai gargada, sai
su yi maza su riƙe dakyau a hannunsu. Har suka isa Kano
tulun nan yana matse da su.
Gidan Hajiya Zeenatu aka soma zuwa, suka rabu da Hajiya
Batool direba ya yi gaba da ita. Ma'aikatan na ta kallon
Madam din tasu riƙe da kwali, abinda suke ta tunani bai
wuce ko meye a cikinsa ba. Ita kuwa tana shiga ɗakin ta
samu wuri mai kyau ta killaceshi. Yanzu gaba daya
tunaninta shi ne na tafiya Adamawa a gobe-gobennan,
don ta fi son komai ta yi shi da gaggawa sai dai kuma
yanda ta ke jin bayanta naaa azabar da radadi da ciwo,
dole sai ta ji sauƙinsa. Don haka ba ta zauna ba, bandaki
ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi. Sai dai koda zamanta wani
uban ƙara ta saki na azaba. Ranar dai wuni ta yi jiki ba
dadi don har da su zazzaɓi. Haka ta samu labari daga
Hajiya Batool, ita kam har wani ruwa ta ke fitarwa.
Wasa-wasa zazzaɓi ya tsananta ga Hajiya Zeenatu, har
washegari da ta ke fatan tafiya Adamawa, abin ya gagara.
Dakyar ta iya daukar waya ta kira likitanta. Har gidan ya zo
ta kira Emma a waya ta ba shi iznin a shigo da shi. Ya
karasa har dakinta, ya yi mata allura. Koda wasa ba ta
bari ya san ɗaya ɓangaren na ciwonta ba, yana
kammalawa ya fice abinsa. Aikuwa wani wahalallen bacci
ya yi awon gaba da ita.
Ta fi awa hudu tana bacci, kafin ta farka, ba laifi ba kamar
sadda ta kwanta ba, kusan ma babu zazzabin sai uban
gumi da ta ke yi. Wayarta ta jawo, ta bude rututun
missedcalls da ta gani na Manajanta mai kula da shagon
gwal-gwalanta. Kafin ta gama shanye mamakin, wani kiran
ya ƙara shigowa. Ta ɗaga da saurinta.
"Hello! Hajiya, gobara! gobara ta cinye shaguna har da
namu! Ga wuta har yanzu an kasa tsayar da ita!"
Daga jin yanda ya ke zancen a matukar rikice ya ke don ba
laifi shima yakan haɗa da nasa jarin ya juya. Wani irin
miƙewa tsaye da Hajiya Zeenatu ta yi, sai ga ta a kan
ƙafafunta, jikinta ko'ina ya ɗauki rawa, shi kenan dukiyar
da ta ke taƙama da shi yanzun kaɗai a duniya.
"Me ka ke cewa Bala? Me kake nufi wai?!"
Inaa! babu kwakkwarar amsa, tana ta hello amma kamar
babu service ga kuma hayaniyar jama'a ta cika wurin. Ai
ko mayafi ba ta tsaya ɗauka ba, mukullin motarta kawai ta
ɗauka ta fito hankali tashe. Ma'aikatan na ganinta suka
nufota.
"Hajiya lafiya?"
"Ba za ku gane ba! Yi sauri budemin gate! Gobara a sabon
gari!"
Hakan da ta fada duk sai suka fahimci inda zancen ya
dosa tunda duk sun sani tana da shago a sabon gari,
wato dai an samu matsala, da sauri Emma ya karbi
mukullin ya ce ta bari ya kai ta ba ta da nutsuwar yin tuƙi.
Ba musu ta miƙa masa jiki na rawa ta koma mazaunin
kusa da direba. A hanya kamar za ta yi tsuntsuwa, duk irin
gudun da Emma ke shararawa ba ta gani. Tuni ta nemi
ciwo ta rasa.
Cunkoson ababen hawa da na yan sanda har ma da
motocin kashe gobara, ya sa dole Emma sai wuri ya samu
ya ajiye motar suka karasa da kafa. Hajiya Zeenatu na
ganin yanda shagon ya ƙone ƙurmus babu abinda ya bari
kawai sai ta faɗi yanke jiki ta faɗi. Nan fa mata da maza
aka yi kanta, bakinta tuni ya karkace tana fidda yawu,
idanunta kuwa kamar mai harara garke. Emma da ma
wasu aka taimaka wurin daukarta zuwa asibiti, Manaja ya
yi danasanin kiranta a waya sai dai hakkinta ne ta sani.
Kusan ma akwai wadanda sai da suka sume, wasu kuwa
banda kuka ba abinda suke yi kama su yi hauka.
Asibiti kai tsaye Emma ya wuce da Hajiya Zeenatu cike da
tashin hankali, Likitan dai da ya zo mata dazun, Dakta
Salisu, wurinsa suka je. Ya yi matukar mamakin ganinta a
cikin wannan yanayin, anan Emma ya labartamasa komai.
Nan da nan likitoci suka rufu a kanta sai dai kuma sun
makaro, Hajiya Zeenatu an samu ta ɗan dawo daidai
amma fa ta hadu da shanyewar ɓarin jiki hakanan tana
magana a jagwalgwale miyau na kwaranya ta gefen bakin.
Banda hawaye ba abinda ta ke yi, ba abinda ke yawo a
ranta sai kudirinta na zuwa Adamawa. A yanda ta ke jinta,
ko a wane hali ta ke sai ta je. Sai ta samu Hussein ko ta
halin ƙaƙa.
Nan kuma Dakta Salisu ya ba Emma umarnin sanarwa
mijinta da yan uwanta, Emma nan take ya sanarmasa
cewa Ogansu ya rabu da ita. Dama kaf dinsu sai da ya
bisu da alheri kuma ya yi musu sallama da zummar ya tafi
kenan. Ba su ji dadin hakan ba amma sun mishi murnar
rabuwa da muguwar mata irin Hajiya Zeenatu, ko ba
komai sun jima da sanin munanan ɗabi'unta da yanda
Ogansu ke shakkarta.
Ba wacce ta fado a ran Emma sai Hajiya Batool, ya san
matar aminiyar Madam ce, don haka ya fice daga asibitin
ya nufi gidanta.
Hajiya Batool na zaune tana jin wani mugun farin ciki
yanda ɗanta ya kira waya yana sanarmata da cewa a
gobe-gobennan zai taso saboda kewarta da ta cikashi,
kuma a shirye yake da bin umarninta, dama ita kiranye
aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kudin sabulu,
ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri
wacce take so. Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga
don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji
wayara kashe.
Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo
tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya
Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan
sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki.
Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta kaɗu sosai. Ba shiri ta
ce ya je za ta leka asibitin. A yammacin ta je, ta yi
mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki.
"Zeenatu! Ke ce haka?"
Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta
wanda maganar ba ta fita sosai ta ce.
"Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein."
Hajiya Batool ta girgiza kai ta riko hannunta.
"Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi
maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama,
za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein."
Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai bakin cikin
abinda ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da
tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar.
Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon
Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da ɗanta zai yi,
haka kawai maimakon ta tayata farin ciki sai ta ji hassada
da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu
ita kuwa babu ɗaya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi
tasiri ba sai ta je ta barbaɗawa Hussein hodar da Buzu ya
ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya Batool ta fice daga
asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai
Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin
rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi.
***
ADAMAWA
Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada
zango a ɓangarensu, wannan karon ma an musu tarba sai
dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya
yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan
gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu.
"Sharrin shaiɗan ne, ku yafemin domin Allah. Itama
Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu."
Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan, ko ba komai har da
rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa
jagorancin wani ɗan uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran
ƙarfe, suka ɗunguma har iyalin Kawun, a yammacin zuwa
gidan Dada.
***
Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke
kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi
sakamakon raɗan da ya ke mata a kunne amma hakan ya
gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai yi aune
ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama
leɓensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami
da kama baki.
"Aush!"
Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar
nauyi, da kaɗan ta wuce gwuiwarta. Gashinta wanda tuni
ta warware kitson yana tufke a baya.
"Sorry." Ta fadi tana ɗaga yatsunta bayan ta ja baya sosai
tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi leɓensa ya manna
mata harara.
"Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki."
Ta narkar da fuska.
"Haba don Allah Haskena, kai ɗin ne ka ƙi hakuri ka bari
na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin
za ka fara zuwa aiki. Don.."
Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa
da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya
jingina jikin kofar.
"Za ki fito ki same ni, na san maganinki."
Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta
ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar kaɗan-
kaɗan ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone.
Shi kuwa gogan yana shirin komawa ya zauna, aka
kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da
umarnin shigowa.
Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a
tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta
ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki.
"Dada ce ke kira."
Ya gyaɗa kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na
dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya
ga waɗanda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne
yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan
ta mishi bayanin komai. Wannan yasa ba ɓata lokaci,
AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu.
"Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?"
"Toh."
Ta amsa ba tare da ta buɗe ƙofar ba. Ya gyara zaman
brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙaƙe na maza na
yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da
motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa
baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu
amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman
maza da mata. Haka kawai ya ji gabansa ya fadi da sauri
kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan
kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya
zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya
gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin
da ya shiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar
jikinsa gaba daya ta tashi tsabar ɓacin rai, yayinda
idanunsa suka kaɗa, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa
kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin
yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Surajo ya
mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar
dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai
hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin
idanunsa.
"Me ya kawo shi nan?"
Baffa Surajo ya dafa kafaɗar Hussein kafin ya ja hannunsa
ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda
girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya
ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar.
"Ya isa ɗana. Ya isa."
Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin
tsawa ya dakatar da shi.
"Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!"
Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen
falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar
zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi
tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah
ne Mai shiryarwa.
Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har
ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein.
"Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da
iyalinsa baki daya, ka tuna, idan shi ne ya yi mana laifi,
iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu."
Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi
zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan
ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin
kunya, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira?
Allah Ya tsaremu.
"Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har
da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita
ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a
zuƙatanmu, sai ya kasance ni abin ya zame min ciwo
domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin
tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da
mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba.
Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa
daga wannan bakin cikin na ci gaban da Amina ta samu
ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu,
ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na
yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da
murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa
musamman da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya
dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A
wannan halin