Showing 15001 words to 18000 words out of 113545 words
Chapter 6 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
yanda aka
kurantamana wannan mutumin ba haka muka riska ba.
Kinga yanzu wai yaronnan Dubai zasu wuce da shegiyar
yarinyarnan siyayyar kayan haihuwa? Ban isa na faɗi
aibunta ba zai hau ni da faɗa kamar shi ya haifen."
Tsaki Hajiya Zeenatu ta ja.
"Ke naki ai da sauƙi tunda ba mijin bane, ni ina miki
maganar duk aikin da nayi sai ya lalace. Duk abinda na
ɗauki niyyar na yi sai kiga an yi rashin sa'a a kai. Jikina ne
ke yin sanyi, amma ba zan karaya ba. Har abada kuwa."
Ta ƙarashe tana mai goge zufa sa'ilin da kwakwalwarta ta
tafi ga tunanin wani abu da ya kasance a can baya wanda
nan da nan ya jefamata tsoron da ta ke gujewa a zuciya.
"Toh wai me zai hana mu koma wajen Gora? Kamar dai
aikinsa ya fi na wannan buzun. Duk buge ce."
Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi.
"Kuma hakane, kin fadi gaskiya."
Cewar Hajiya Zeenatu cikin karaya, yanzun dai ta saduda,
banda ma asarar kuɗi, aikin ma da ta yi nema ya ke ya
rushe, nema yake ya zama tamkar ba ta taɓa yi ba. Ita da
kanta ta soma ganin sauyi acikin rayuwar Hussein. Ya rage
shakkarta.
Suka yi ta tattauna yanda zasu ɓullo wa matsalolinsu kafin
su yi sallama su rabu zuƙatan duk babu dadi.
***
BAYAN SATI ƊAYA.
Tun shigowarsu garin na Dabo tumbin giwa Fatima ke ji
kamar tayi fiffike ta yi ta zagaye gari tsabar farin ciki da jin
dadin yau ga ta a Kano. Da wayonta haka dai ba ta taɓa
zuwa ba. Don haka bakinnan nata a wangale ga hannunta
riƙe da cakulet tana sha.
Uban ya dubeta yanda ta hakimce gaban mota, duk son
uwar da haka, hakura ta yi don ba ta iyawa rigimar Fatima
wani sa'in, zamanta ta yi kusa da Hafsat da Dada.
"Wai nikam Fatima kodai a Kanon zamu bar ki ne?"
Fadin Kausar tana dariyar yanda yarinyar ta kifa goshi a
kan gilashi tana ƙarewa waje kallo.
Da wani ɗoki ta dubi Mamarta ta gyaɗa kai, yanda ta yi
duk sai ta ba su dariya.
"Allah Ya rayaki dai Fatin Biyu"
Dada ta furta da dariya. AlHassan wanda walwalarsa ta
ɗan ja baya tun shigowarsu garin sai a sannan ya ɗan saki
fuska. Autar Dada ta ɗan dunguro kanta.
"Ke da ace za'a bar ta kinga alamar ba za ta zauna ba?"
Aka dara. Haka suka yi ta hirarrakinsu har suka kai gidan
Kawunsu Modibbo.
Yana parking ya budemusu ƙofa kafin ya zagaya ya sa
yara su fiddo akwatunan. Ya ɗaure fuska ya sauya kamar
ba AlHassan ba mutum mai yawan fara'a.
"Zan je na dawo."
Abinda ya ce kenan, Dada ba ta yi mishi dole ba ganin
sauyinsa, ta kauda kai don tasan ba da son ransa suka
zaɓi kwana a gidan Modibbo ba madadin ɗaki a Hotel da
ya yi niyyar kama musu. Suna shigewa ciki shima ya ja
motarsa ya fice.
***
Kausar ce tsaye bayan ta dawo daga ɗakin Amarya tana
duban yanda Dada ta zage tana faman aiki tuƙuru a sashin
Hajja Fatuma. Tana kallon yanda jikokin Hajja Fatuma
suke yin yanda suka so babu mai kwaɓa balle magana,
yaranta mata na hakimce saman kujera suna hira da
sha'aninsu ita kuwa ta shiga cikin ƴan aiki ana gyaran kaji.
Juyawa ta yi ta koma sashin Amarya dakin da suka sauka.
Nan ta tarar da Hafsat tana sauyawa Fatima sutura zuwa
na bacci, a gefenta Rasheeda ce, ɗiyar Amarya da zasu yi
sa'anni da Hafsat. Su dai kam dama jininsu ya hadu don
har chatting suna yi. Ganin yanda Kausar ta shigo fuska a
ɓace yasa Hafsat gane inda zancen ya dosa.
"Anti kin ce ta zo ta ci abinci?"
Sai a sannan ne ma ta tuna abinda ya kai ta wurin Dadar,
ta ja guntun tsaki.
"Kinga halin mantuwa ko?"
Miƙewa Hafsat ta yi a fusace, ita kam yau sai ta taho da
uwarta don ba bauta ta zo ba.
Za ta fice Kausar ta riko hannunta. Ta dubi Rasheeda.
"Don Allah kirawo Dada."
Rasheeda ta mike ta fita. Ta riga ta san komai dangane da
irin tsangwamar da Dada ke sha a wurin Hajja da Modibbo
mahaifinsu har ma da wasu cikin ƴan uwansa. Ta kuma
rasa dalilin wannan ƙiyayya, a ganinta abinda ya wuce ya
riga da ya wuce.
"Kai Adda, nidai wallahi da kin bar ni na je, na gaji da
wannan abu. Tun zuwanmu awa nawa yanzu ace Dada ko
abincin kirki ba ta ci ba? Daga zuwa gaishesu ta dawo sun
haɗata da aiki don rashin tausayi, kuma shi ne ita ta
karɓar? Nidai sai na gayawa Hamma.."
"Kul! Kar ki soma. Kinsan dama ba da son ransa aka yi
wannan tafiyar ba, abin ya zo mishi ne a ba yanda ya iya.
Yanzu kika kirashi tayar da hankalinsa kawai za ki yi kuma
ranmu ya ɓaci. Ke dai ki bi gargadin da Dada ta yi maki a
rabu lafiya. Gasunan dai kinga su Hanifah duk suna zaune,
nima ban ishesu kallo ba tunda a cewarsu ina auren
AlHassan."
Yamutse fuska Hafsat ta yi.
"Wallahi Adda, Adda Hanifah ƙarya take. Son Hamma take
yi kamar yanda ɗan adam ke son rayuwarsa. Ai inada
labarin komai, kuma ma.."
Sai ta yi ɗif, sai yanzun ta ke tuna katoɓarar da ta yi, ta
ɗan datse harshe da haƙori ta yi shiru. Dada da ke tsaye
bakin ƙofa ta ƙaraso ta bata rankwashi a kai, ita kuwa
Kausar dariya ma ta yi. A saninta ko giyar wake AlHassan
ya sha ba zai auri Hanifah ba. Har abada ya tsani zuri'ar
Modibbo. A wani ɓangaren kuma itama ta san da wannan
soyayyar ta Hanifah ga mijinta, takan ga kiranta sau tari a
wayarsa, bai yi saving lambar ba, amma ita tana da
lambar a wayarta. Allah Ya hana bincike, shiyasa ba ta
zurfafa ba. Sai kuma sanin da ta yiwa Modibbo na bala'in
son kansa da kuma ƴaƴansa, wannan ne waekness dinsa.
Duk abinda yaransa ke so koda ba ya son abin, zai yi
yanda zai yi ya nemamusu farin ciki. Wannan ya yi sanadin
lalacewar wasu a yarannasa.
"Ke za ki biyewa wannan shashasha har ki wani tsaya
zurfafa tunani? Kin yarda da abinda ta ce kenan?"
Dariya Kausar ta yi tana girgiza kai.
"Ko kadan." Suka ɗan dara, Hafsat ta turo baki.
"Toh nidai gaskiya Dada ba zamu yarda da wannan aikin
da kike fita ba, idan kika ci gaba zan kira Hamma."
Dada ta yi murmushi cikin harshen fulatanci ta amsa.
"Dayake shi ya haifeni ko? Banda abinki Hafsatu, ni da
gida ɗan uwana? Wa ya fadamaki abinda na yi faɗuwa
ce? Babu, zumunci na sadar kuma Allah zai duba."
Ita dai Hafsat ta ja hannun Fatima suka fice zuwa falon
Amarya. Banda Dada ta tilastamata kuma tana son zuwa
gurin Rasheeda, ba abinda zai sa ta tako ƙafarta Kanon, a
yanzun ma ji take da ace akwai wasu ƴan uwannasu can
za ta yi tafiyarta.
Da yammacin ranar AlHassan ya iso ƙofar gidan
Modibbo, waya kawai ya yi ya ba Hafsat umarni fitowa
tare da Fatima su yawata. Da wani irin ɗoki Hafsat ta mike
ta shirya Fati suka fice ba su ko tsaya sallama da kowa ba
banda Adda Kausar da suka faɗawa ta sanar Dada.
Fuska ta daure ganin yanda Taheer ɗa ga Hajja Fatuma
ya tsuramata idanu yana kallo. Bafulatanin usuli wanda
daga ka ganshi ka ga jinin Mamman Gidado.
Dagasken gaske tana lura da yanda yake wani safa da
marwa a sashin Amarya wanda hatta da Rasheeda sai da
ta nuna mamakinta a fili, acewarta abu ne mai wahala ka
ganshi a sashin nasu.
Har ta isa ta buɗewa Fatima gaban mota ta shiga itama ta
bude gidan baya ta faɗa babu walwala. Alhassan ya
dubeta yana murmushi sadda ya ja motar.
"Ke kuma ke da wa?"
Turo baki ta yi.
"Bakomai."
Ya taɓe baki. Ko me ya faru ai su suka sani, shi dai kam
dama bai nunamusu yana son zuwan ba.
"Daddy ina zamu je?"
Cewar Fatima a ɗokance. Ya ja kumatunta da murmushi.
"Surprise ne."
Ya yi ta biyemata su na surutu har suka iso tafkeken
shagon na A&Z.
Hafsat sai a lokacin ta saki ranta, suka fito suka jera
ciki. Da ka gansu ka san jini ɗaya ne.
Kai tsaye suka hau sama, ma'aikatan sai kallon AlHassan
suke yi kusan a mamakance. Duk a zatonsu Mijin Madam
ne, ganinsa da budurwa ya ba kowa mamaki, har da
samari da ƴanmatan da suka mayar da wurin wajen
zuwansu. Shi kuwa Alhassan wayar da aka kirashi ce ta
sanya shi ba Hafsat kudade tare da ba ta umarnin ta
suyamusu duk abinda ya dace, yana jiranta a waje.
Sauri yake sosai yana son barin hayaniyar cool music da
ke tashi a wurin ganin Director ɗinsa na wurin aiki ke kiran.
Magana ce za su yi mai muhimmanci. Karo ya ci da ita
sadda ta sanyo kai nan take wayarsa ta faɗi, ya ɗago ita
kuwa ta matsa baya gami da fadin.
"Yi hakuri fa."
Ɗagowar da zai yi sai da ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Ba
don ace tare suke tafe da mijinta Hussein ba, kuma yana
cikin mota sanye da kananan kaya, madadin wannan da
ke sanye da shadda blue, za ta rantse shi ne tsaye.
Murmushi ya yi mata da nunamata ba komai kafin ya yi
gaba. Har tana tuntuɓe haka ta juya ga mararta da ta cika
taf da fitsari, haka ta karasa ga Hussein wanda ya
juyamusu baya yana kokarin rufe motar. Ganinta a gigice
yasa shi dubanta da mamaki.
"Lafiya?"
Dafashi ta yi gami da riƙe kai.
"Lafiya, a'a ba lafiya, muje don Allah. Jiri nake ji shiga mu
tafi."
Hussein dai abin ya dauremishi kai, zai yi musu abin
mamaki Hajiya ke roƙonsa ya bar kowace magana a gefe
su wuce su koma gida. Ba ta da lafiya. Dole ya shiga
motar bisa umarninta itama ta shige. Ba ta samu nutsuwa
ba sai da ya doshi gate, sai dai kafin ya kai ga fita jikinsa
kawai ya yi wani irin la'asar yayinda ya ji kirjinsa na dukan
uku-uku, ya kalli bayansa ta mirror. Bai ga kowa ba face
wani matashin da ba zai fi shi a shekaru ba, tsaye jikin
mota ya juyamusu baya yana amsa waya.
"Ya kake tafiya kamar ba ka so? Ka yi sauri don Allah."
Maganar Hajiya ta dawo da shi nutsuwarsa, ya ɗan ƙara
ƙarfin gudun.
"Wai meke faruwa? Naga lafiya muka shigo wajennan."
Girgiza kai ta yi tana share gumi.
"Nima dai ban sani ba. Watakila plantain da kwai da na ci
ne ya ɗan juyamin ciki."
"Kuma kika ce jiri?"
Ta ja guntun tsaki ganin zai ƙureta, ita dai yanzu ta fi
kaunar a kyaleta tayi tunani mai kyau. Wannan ya nuna
twin brother din Hussein ya zo Kano kenan? Lallai dole ne
ta hana Hussein zirga-zirga. A farin farko dai za ta bincika
ta ji dalilin zuwansa, idan har zama ne na dindindin, barin
Kano na har abada ya gansu ita da mijinta koda ba ya so.
Haka ta yi ta tufka da warwara, Allah-Allah take su isa
yanda za ta samu damar yin tunani mai kyau.
Shi kuwa AlHassan koda ya gaji da gaisuwar da wasu
daidaikun ma'aikatan masu wucewa suke mishi sai kawai
ya shige cikin motarsa ya zauna ya ci gaba da wayar. Har
su Hafsat suka fito ɗauke da ledoji yana waya. Hayaniya
kwakkwara hanasu ya yi, kusan har ya soma tuƙi suka yi
tafiyar mintoci yana waya. Can dai ya katse ya ajiye, da
murmushi ya dubesu.
"Sorry, ban kyauta muku ba ko?"
Fatima ta turo baki ta gyaɗa kai. Dariya ta basu.
***
"Hajiya Ramlatu, ina son ganinki."
Shi ne abinda ya ce kenan bayan ta saka wayar a kunne.
Ramlat ta ajiye kan wayar ranta na zafi, tsabar raunin
hankalin Chairman ya soma isarta, tana kallon abin kamar
da biyu yake yi.
Ta mike ta gyara zaman naɗin laffayarta ta tabbatar
ko'ina na jikinta ya ƙara rufuwa ruf sannan ta ƙarasa ciki.
Kallon haramun dai bai fasa ba don haka ta daure fuska.
"Gani Yallaɓai."
Ta faɗi a ladabce cikin basarwa don yanzu ta bar ganin
ƙima da mutuncinsa.
"Amm..yanzu a kan aiki muke don haka ba zan ce komai
ba. Sai dai idan ba damuwa ko za'a yimin iznin zuwa
gida?"
'Anzo wurin.' Ta fadi a ƙasan ranta. Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai..."
"A'a kinga Ramlat, ba batun nayi hakuri bane. Tsakani da
Allah ba zan iya ba. Na fadamaki yanzun muna bakin aiki
ne, magana ce kuma zan zo muyi ta fahimta."
Shiru kawai ta yi, ganin ta ƙi ce mishi uffan ne ya sa shi
magana.
"Zan ba ki daga nan zuwa Monday, please ki yi tunani mai
kyau. Ki sani, koda ace a baya sharri ne a zuciyata, yanzun
babu ɗigon wannan Ramlatu. Wallahi babu."
Yanda yake magana kamar wani yaro sai ma ya so ba to
dariya, ita dai ba ta ce komai ba.
"Shikenan kina iya tafiya."
Ta juya ta fice ba ta ce mishi uffan ba, Chairman ya bita
da kallo kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya.
Sanin gidansu Ramlat abu ne mai sauƙi a wurinsa, sai dai
ya fi kaunar bi ta hanyarta ko don ya goge wannan kallon
girma ya faɗin da ta ke yawan jifansa da shi. Ko ba komai
dai da gaskiyarta. Da niyyar cuta ya zo sai soyayyarta na
gasken ya sauya komai.
***
KARFEN KAFA Chapter 47
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
LAMIƊO CRESCENT
"Ki soma faɗamin wannan ƙullen da kike yimin na mene
wai? Ina da aikin yi, kin hana ni fita."
Hussein ke maganar a tausashe da ɓacin rai saman
fuskarsa. Zeenatu dubansa take yi don ta rasa ma hanyar
ɓullo mishi. Ba ta son fitarsa, jinta take kamar wata
zararriya, gaba daya babu aikinta ɗaya da ya tafi daidai. A
baya ta rantse ba za ta bar garin Kano ba amma kam a
yanzun a shirya ta ke da yin nesa da duk abinda zai sa
Hussein ya suɓucemata.
"Tafiya zamu yi, Kano nake son mu bari."
Kallonta kawai yake yi cike da tunanin meke damunta har
haka. Dariya ta so kwacemasa don shi kansa yana
mamakin irin ƙwarin gwuiwar da ya ke samu na yi mata
jayayya akan duk abinda ya zartar a yanzun.
"Kinsan me kika ce kuwa?" Ya fadi kansa tsaye yana
kallonta har sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Dakyar ta
haɗiyi yawu.
"Me kake son ka ce? Jayayya za ka yi da ni? Ba za ki bi
ra'ayina ba?"
Ya yi shiru kawai yana kallonta da wani mamaki, wani
tsana yake ji kamar yana son tasomishi sai wata soyayya
da bai san mafarinta ba ta zo ta danne wannan tsanar.
Kauda kai ya yi gami da miƙewa daga saman gadon.
"Kiyi hakuri, abu ne da ba zan iyaba."
Daga haka ya faɗa banɗaki. A gigice Hajiya Zeenat ta
miƙe ta fice zuwa ɗakinta. Wanka ta yi a gurguje ta shirya.
Kamar yanda ta zata hakan ce, ya shirya da zummar zuwa
ofis. Bai yi mamakin shirin da ta yi ba illa murmushi da ya
yi, abin kam ya ba shi dariya. Wannan bibiyar bai san
kuma ta mece ce ba duk da a bayan ma tana yi mishi don
wani sa'in kamar daga sama haka yake ganinta a
ma'aikatarsu.
Ya shirya suka fita tare, ita ke tuƙi don a cewarta za ta
fita daga nan duba Hajiya Batool ba lafiya, bai damu da
gasken take ko a'a ba. Ya dai amsa zuciyarsa a ɓace.
***
Tuƙinta cikin nutsuwa take yi, yau gaba daya ta makara a
dalilin zazzaɓin da ya kama Ansar sai da ta kai shi asibiti
tukunna ta maida shi gida. Ta so ta ƙi zuwa sai dai
hakanan ta daure tunawa da aikin duba wasu files na Tax.
A harabar wurin parking ta ajiye motar ta ƙarasa ciki. Ko
zama ba ta kai ga yi ba wayar dake saman tebur ta ɗau
ƙara, tsuke fuska ta yi gami da jan tsaki ciki-ciki. Tun
sadda suka yi haka da Chairman ta ƙi jinin abinda zai sa ta
haɗu da shi sai dai ba yana ta iya. Wayar ta ɗaga da
sallama, ya amsa gami da ba ta umarnin ta je. Dire wayar
ta yi ta ajiye jakarta ta fita bayan ta gyara zaman hijabinta.
Yana zaune da manyan kaya har da babbar riga, idanunsa
sanye da gilashi yana danna laptop. Shigowarta yasa shi
kallonta.
'Ban yafe ba.' Ta furta a ƙasan ranta. A fili kuwa gaidashi
ta yi a ladabce, ya amsa yana wani washe haƙora. Bayan
gama jin dalilin da yasa ba ta shigo da wuri ba ya gangara
kan abinda ke cin ransa. Chairman ke kiran yana sonta,
dama tuni ta riga ta gane.
"Ke ba yarinya ce karama ba, nasan kinsan me nake nufi
kike kaucemin. Wallahi na gaji, bani da burin da ya wuce
na aurenki a yanzu Ramlat. Don Allah kar ki ce za ki ƙi. Na
miki alƙawarin gidanki daban, ba zan haɗaki da matana
ba."
Ya kammala surutansa tana sauraro, ƙarshe ta soma da
ba shi hakuri.
"Inada wanda zan aura don har anyi magana."
Wata dariya ya kece da ita, hatta ita Ramlat sai ta ji
maganar nata banbarakwai, ta kara hade fuska.
"Haba Hajiya Ramlatu, yanzu fa na gama fadamaki ke ba
yarinya ba ce. Wane sokon ne zai yi gangancin tsallake
sati biyu ba'a ɗauka muku aure ba? A'a ban yarda ba
gaskiya. Nidai ki karɓi ƙoƙon barata ki ba address da kanki
a ganina zai fi mana mutunci."
Ta yi shiru, ya ci gaba da magiya kamar ba Chairman mai
cin magani a gaban staffs ba, haka ba don ranta ya so ba
ta mishi kwatance. Ranar kowa ya kalleshi yasan yana
cikin farin ciki marar misaltuwa.
Koda aka tashi, kai tsaye tsohon department din da take
ta ziyarta. Ta kuwa ci sa'a duk suna ciki, aka gaisa ba ta
ko bi ta kan Halima mai amsa gaisuwar ciki-ciki ba.
"Yanzun nake shirin shiga wurinki. Ƴar halak kin ƙi
ambato."
Ta kai duba ga Naja'atu Azare mai wannan batu, suka yi
dariya. Takardar gayyatar biki ta fiddo daga jakarta ta miƙa
mata. Murmushi sosai Ramlat ke yi har fararen haƙoranta
na bayyana.
"Kai na ji dadi sosai wallahi, ki ce abun ya zo. Allah Ya
nunamana, Yasa muna raye." Aka amsa da Amin.
Hira ta tsaya yi a karshe suka dunguma gaba daya matan
suka fita, Halima har lokacin fuskarnan ba fara'a.
"Wai ke me akai miki kike ta cin magani?"
Saudat ke tambayar tana dubanta.
"Ba komai, sai Allah Ya kaimu."
Daga nan ta yi gaba ta bar su.
"Wai nikam Ramlat kamar dai akwai wata a ƙasa
tsakaninku da Halima, na lura duk sadda kike wuri ba ta
fiye kaunar hakan ba." Samira ke wannan maganar tana
duban Ramlat. Ita kam murmushi kawai ta yi, tana ji suna
faɗin rashin kyautatawar Halima a lokuta da dama ita dai
ta musu sallama ta nufi inda ta yi parking. Idan da sabo ya
ci ace dama ta saba da halinta. Murmushi ta yi da wani
bahagon tunanin da saƙe-saƙen zuciya ke jefawa ɗan
adam ya ziyarceta, wato ace ta yarda da auren Chairman,
Allah Kadai Yasan irin kiyayyar da za ta fuskanta daga
Halima. Ba ma daga gareta kawai ba, har da yawa cikin
matan wajen.
***
Zaune gaban Boka Gora, Hajiya Zeenatu ce da Hajiya
Batool kowannensu rai a ɓace.
"Shekaru sama da goma muna tare da kai, kar ka yi mana
haka. Ka taimakemu ka kula da damuwarmu. Bamu da
wanda muke da shi da zai share hawayenmu face
kai." (Wa'i'yazubillah)
Gora ya yi wata dariya ta shaiɗanun da suka riƙa kafin ya
ɗaure fuska tamau. Ya kwalalo musu manyan idanuwansa
da suka sha kwalli.
"Kar ku rainamin hankali! Wa ya fadamaku zan kasa sanin
kun yi doguwar tafiya har wata ƙasa don a yi muku asiri?
Cin amanar da zai biyo bayan dukkan taimakon da na yi
muku a baya kenan! Yanzun da ku ka zo me kuke so nayi
bayan komai ya warware! Komai ya lalace! Ke Zeenatu! Ki
fara tattara kayanki ki bar