Showing 87001 words to 90000 words out of 113545 words

Chapter 30 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

Sallamar
da aka yi duk ta dawo da hankulansu bakin ƙofar
musamman ganin yanda wuri ya ɗauki guɗa.
Hafsat ce ta soma shigowa sai Kausar, bayansu kuwa
Ramlatu.
Wani irin miƙewa tsaye Hajiya Zeenatu ta yi a matukar
gigice. Babu chanjawar da za ta yi ta kasa ganeta tsabar
tsantsar tsanar da ta yi mata. Ido waje ta ke duban
Ramlatu, daga kan kafafunta har zuwa dukkan gaɓoɓinta
babu inda ba ya rawa. Ba ta ƙara razana ba sai da ta ji
muryar wata na fadin.
"Ƙaraso ciki ki zauna, Amaryar Husseini. Lale lale da
kyakkyawar halittarnan."
Wani ihu Hajiya Zeenatu ta kurma kafin ta yi tsalle da
nufin isa ga Ramlatu.
Caraf aka damƙe hannunta, ta dubeshi tsakar ido ya yi
mata wani kallon banza, kallo na tsana da ya jima yana
dannewa. Idanun Hajiya Zeenatu ya yi wani mugun
kaɗawa. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. Wani irin
uban zufa ya haɗemata duk da iskar da fankokin ke
bayarwa. Yarfar da hannunta ya yi. Bai kuma yi wata-wata
ba ya dauketa da mari hagu da dama. Kallo daya idan ka
yiwa fuskar Hussein za ka fahimci tsantsar ɓacin ransa.
Abu ne da ya jima yana dannewa. Hannunsa har rawa yake
sadda ya ke nunata da yatsa yana magana.
"Ko a mafarki! Kar ki ƙara tunanin cutar da matata!"
"Hussssseiin.." Ta furta da rawar murya ga hanjin cikinta
da ta ke jin sun dunkule wuri guda. Idan ba ta yi ƙarya ba
ma, ta ji fitar tagwayen tusa daga jikinta.
"Yes, Hussein ne. Wanda kika kashewa rayuwar shekaru
biyar! Kika raba shi da asalinsa! Ki ka tauye kuruciyarsa
don kafirin zuciya da zalunci irin naki! Idan ke
mahaukaciya ce da ba ki gano kuskurenki ba, kika
daukemu shashashai ki ka ci gaba da yin yanda ki ka so
da tunanin kin ci galaba ko kuma tunanin ni Hussein ina
sonki, kin yi ƙarya. Kin manta yanda muka hadu kuma
muka rabu a farkon haɗuwarmu? Har tunaninki ya ba ki
damar hango ni matsayin masoyinki? A'a, kin yi kuskure!
Dama wannan ranar nake jira. Na auri mafi soyuwa a
wurina da iyayena, mafi ƙi a wurinki sannan na yar da
ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda! Ko ba komai yanda
kika tako garinmu kika daukeni cikin dangina, hakanan na
dawo."
"Hussein! Karya ka ke! Karya ka ke wallahi! Ni za ka ci wa
mutunci?! Ka san irin son da nake maka?! Ka rasa wa za
ka auro sai wannan baƙar ashanar?"
Nan fa ta tubure ta dinga maka ashariya, wani marin ta ji,
wannan karon ba Hussein ba ne. Dada ce da fuskarta ta
gama jiƙewa da ruwan hawaye.
"Rufemana baki! Makira azzaluma kawai! Kina zaton
wawaye ne mu! Allah Ya isa tsakaninmu da ke! Alhakinmu
da kika ɗauka na tsawon wannan lokacin sai Allah Ya
sakamana walla.."
Kuka ya ci karfin Dada har muryarta na shaƙewa, kusan
ma da yawa hawayen suke yi musamman don tausayin
Dadar wacce ta yi uban jinya da Hussein ya ɓace kafin ta
samu waraka amma fa koyaushe cikin kuka ta ke da
addu'a. Ramlat ita kanta kukan ta ke yi sosai, daidai
sadda Hussein ya zura hannu a aljihu ya fiddo takarda ya
kama hannun Zeenatu ya damƙamata.
"Meye wannan?! Me kake nufi? Dama ka kawo ni cikin
danginka don ka ci mutuncina? Me ka ke son ka cemin?"
Tana maganar tana jijjiga takardar yayinda take kuka har
da majina. Ɗigon tausayinta ba wanda ya ji don dama
kowa da tabon shekarun da ya yi cikin zulumi da kewar
Hussein a zuciya.
Wani irin tsalle ta daka da zummar shaƙo wuyan Ramlat
sai dai tuni matan suka damƙe ta, Hussein shi kallon
mamaki ma ya tsaya yi mata na irin wannan ƙarfin halin
wai ɓarawo da sallama. Zagi take ƙudundumawa tana
kiran sai ta hallaka duk wanda ke shirin rabata da farin
cikinta.
"Modibbo ya yi gaskiya! Dama ya ce kar na zo! Kar na zo!
Ba sona ku ke yi ba! Ashe da gaskiyarsa! Wallahi Hussein
ka yi kaɗan! Zamanmu har abada ba na ƙare ba ne! Yanzu
aka fara!"
Gaba daya Hajiya Zeenatu ta birkice, fuskarta kace-kace
da hawaye ga majina tana aikin jansa. Idanunta yanda ya
rufe har ba ta san me ke fita daga bakinta ba.
Kowa a dakin ya shiga salati jin sunan da ta ambata.
Hussein ya ma kasa magana sai murmushi, ga duk wanda
ya gani kuma zai fahimci na zallar takaici ne kawai. Dama
shi kadai ya zarga, duk kuwa da bai gama tabbatar da
hakikanin lambar wayar da ya ɗauka a wayarta ba tunda
ba shi da lambarsa, amma daga kiran da ya yi sau daya
da kuma muryar da ya ji, jikinsa ya ba shi tare suke komai.
Hannu kawai ya harɗe a kirji bayan ya ja baya ya ci gaba
da kallon diramar da kowa ya ke jin sunan wanda ta
ambata, babu wanda ya zata. Dada kuka sosai ta ke yi don
har numfashinta na sama, wannan ne yasa AlHassan
janyeta zuwa ɗaki don kwantarmata da hankali. A hankali
Hussein ya juya zai fice, wannan yasa Hajiya Zeenatu bin
bayansa fuuu bayan ta ture duk wanda ke gabanta. Koda ta
kalli Ramlatu, wani banzan kallo kawai ta watsamata na
za mu haɗu sannan ta yi gaba don tasan ba damar taɓa ta
yanzun. Hafsat ta yi caraf ta dauki jakar Hajiya Zeenatun
ta buɗe ta cusamata takardar da Hussein ya bata wanda
ta yi wurgi da shi a tsakar ɗakin sannan ta bi bayanta da
sauri.
AlHassan dake ɗakin tare da Dada jin ƙugin tashin mota
ya mike da sauri ya fito. Ganin babu Hussein a falon yasa
da sauri ya fita.
"Kar ka sake ka budemishi gate!"
Ya fadi da ɗan ƙarfi yanda Maigadin zai ji kuma da
harshen fulatanci. Nan da nan Maigadin ya fasa. Hussein
ya ci burki, ita kuwa Hajiya Zeenatu dake bubbuga gilashin
mota tana bin motar don ya saurareta, itama ta tsaya cak.
Hafsat wacce tuni ta jefamata jakarta tana tsaye kallon
dirama da ƙarfin hali irin na Zeenatu. Daidai sadda
Hussein din ya fito daga motar. Hajiya Zeenatu ta cakumi
wuyan rigarsa bai yi wata-wata ba ya hankaɗata. Sai
yanzun ya tuna da akwatin kayanta da ke boot din motar,
tun a can gidan ya nunamata za su kwana biyu gidan
Dada, don haka ta haɗo komai na kayanta. Ya buɗe ya
fiddo akwatin kafin ya ja hannunta tana binsa ta na
magana kamar zautacciya.
"Hussein ina sonka! Ban taɓa son wani namiji dagaske ba
sai kai! Ka yimin rai kar ka rabu da ni! Kar ka manta da
dukiyarmu, na tuba ka yafemin don Allah."
Wannan karon da alamun karaya sosai a muryarta, shi
kuwa shareta ya yi bai ce uffan ba har sai da ya fidda ita
daga ƙofar gidan gaba ɗaya. Daidai sadda Rasheed ya
dawo gidan don ya ɗan fita. Ganinta ya gane abinda ke
faruwa don yana sane da shirin Amininnasa. Akwatin ya
diremata ya dubeta a wulaƙance.
"Sai ki kama hanya ki bar garinnan idan kinga dama, idan
ba ki gani ba ki zauna ki ƙara gwada kashe Ramlat ki gani
ko zan bar ki da rai."
Daga haka ya juya ya dubi Buzun maigadinsu mai jin
fulatanci, cikin fulatancinsa wanda ya ɗan farfaɗo ya ba
shi umarnin koda wasa kar ya bari ta shigo gidan. Daga
nan ya komai ciki tare da Rasheed.
"Na dauka wurin Kawu za ka je. Shiyasa na fito don tsayar
da kai."
Alhassan ya furta yana dubansa. Ya shafi suma gami da
runtse idanu, radadi ya ke ji idan an ambaci sunan
Kawunnasu azzalumi kuma maƙiyinsu da har yau sun rasa
gane kan ƙiyayyarsa.
"Nan na so zuwa amma na fasa. Zan jira hukuncin Dada."
Daga nan ya shiga motar, AlHassan ya yiwa Rasheed ido
alamar ya bi bayansa. Ba musu ya zagaya gefensa ya
bude ya shiga. Kallonsa kawai ya yi bai ce uffan ba, bisa
umarnin AlHassan din ya bude masa ƙyauren ya fice. A
hanya suka ga Hajiya Zeenatu jaye da akwati tana tafe
tana waige. Ganin motarsa har hannu ta sanya da nufin
tsayar da shi, ya ƙarawa motar wuta gami da jan tsaki.
***
Tun faruwar wannan lamari, tsoron Allah ya ƙara shiga
zuciyar Ramlatu. Ta ƙara tsoron ƊAN ADAM tunda har
nasa bai kyale ba. Wane irin zamani ne wannan? Haka ta
yi ta tunani bayan ta koma sashinta. Waya suka yi da
Hajiya ta labartamata dukkan abinda ya faru. Salati Hajiya
ta sanya gami da ƙarawa, ba abinda ya girgizata sai na jin
sunan Kawun Hussein din da ya fito a maganar. Addu'a ta
yi gami da ƙara jan kunnen Ramlat akan addu'a da kuma
kiyaye Azkar safe da yamma. Daga bisani ta kira wayar
Amrah wadanda basu jima sosai da isa Kano ba. Nan ma
dai duk hirar suka yi.
"Wannan kaɗai zai nunamaki ba karamin matsayi kike da
shi a wurin Mijinki ba. Sai ki zage damtse ki kwantar da
hankalinsa a wannan gaɓa, kinsan ba karamin damuwa zai
shiga a kwanakinnan ba."
Wannan shi ne zancen Amrah, nan fa daga Rafee'ah ta
kirata, sai Maman twins can kuma A'isha. Kowa mamakin
jin abinda Hussein ya yiwa Hajiya Zeenatu ya ke yi, a gefe
guda kuma ana tayata farin ciki don zama da Hajiya
Zeenatu masifa ne.
Don kanta ta gaji da wayar ta ce musu chajinta ya ƙare ta
kashe. Miƙewa ta yi ta shiga daki, wanka ta ƙara yi, ta fito
ta zauna gaban madubi ta na kallon fuskarta da ta
mulmule ta kara kyau adalilin gyaran da ta sha.
_*Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane
so da kuma ƙiyayya .*_
Ta tuna kalaman Hussein, a hankali ta ci gaba da murza
man a wuri guda na fatar hannunta. Kenan yana nufin ita
ɗin ya ke so? Ita ce abar sonsa? A abinda ya faru, zallar
ƙiyayya ta gani ya nunawa Zeenatu yayinda ita duk wani a
wurin zai shaidi yana sonta. Wannan tunanin ya janyo ta
sunne kai tana murmushi, murmushin da ya fito tun daga
ƙasan ranta. A hankali ta ɗago kai ta dubi madubi, ba zato
ta hangeshi tsaye jikin ƙofar ɗakin. Ta yi sauri ta kauda
kai. Kasa motsi ta yi gaba ɗaya don ba halin ta miƙe
sakamakon guntun tawul dake jikinta. Tunaninta ma tun
yaushe ya ke tsaye a kanta. A hankali kuma ta ga ya juya
ya fita bai ce uffan ba. Ta dafe kirji gami da sauke ajiyar
zuciya sannan a gaggauce ta mike bayan ta fesa abinda za
ta fesa. Ko ba'a faɗa ba, mijinnata yana tattare da
damuwar da ya ke buƙatar kulawarta. Ta gama gane irin
ɗaukar da Hussein ya yi mata kamar yanda ta soma
amanna da zancen soyayyar da ya ke magana bayan aure.
Riga da siket ta sanya na atamfa, ta yi ɗaurinta tsaf
sannan ta fesa turare ta fita gabanta na faɗuwa. Fatanta
Allah Yasa ya huce. Koda ta fito ana kiraye-kirayen sallah,
har a sannan ba ta samu tsarki ba. Ba ya falon amma ya
ajiye wayoyinsa da agogo, wannan ya sa ta fahimci alwala
ya shiga don haka itama sai ta koma ɗaki don kunya ta ke
ji ya fahimci halin da ta ke ciki. Tana ji sadda ya fice daga
falon sannan ta fito. Mintuna kaɗan bayan idar da sallah
sai ga Hafsat tare da Kausar. Fatima ta ruga a guje ta
rungumeta yayinda Hafsat ta karasa ta ajiye kwandon
abincin hannunta saman tebur. Zama suka yi aka gaisa.
Nan kuma aka shiga maida zance.
"Nifa Adda Amal ba wanda ya bani mamaki sama da
Kawu. Wallahi ban san rashin kaunar da yake yiwa
iyayenmu da mu ya kai girman hakan ba. Ai shiyasa yau
nima na rama a kan ɗansa, ya kirani har ya gaji ban ɗaga
ba, karshe ma na aikamasa da zazzafan saƙo. Rasheeda
fa ki ga ta kasa zama ma a gidannan ta tafi gida Adda
Fati saboda kunya da kuma bakin cikin abinda Babansu ya
aikata. Anti Amarya ma wai mijin ya kira ta je can yana
nemanta."
"Toh ke Hafsat ai dole, amma bana goyon bayan ki
wulakanta Tahir tunda ba shi ya yi maki ba. Asalima ke da
bakinki kin faɗi irin zafin da ya ke ji na yanda Uban yake
hana su zumunci da mu."
Kausar ke maganar kafin ta maida hankali ga Ramlat.
"Kinga shawarar da zan ba ki,wallahi ki tashi sosai ki riƙe
mijinki hannu bibbiyu. Kar ki ga kin rabu da Hajiya Zeenatu
ki ɗauka shikenan, ba ita kaɗai ce mayya me kwacen miji
ba musamman ma a garinnan. Mijina gashinan har yau
ban gama fidda ran watarana ba zai ƙaromin abokiyar
zama ba don yanda ƴanmata da zaurawa ke farautarsa
tamkar nama."
Suka yi dariya. Kausar ta girgiza kai ta nuna Hafsat da
yatsa.
"Ba abin dariya ba ne, ke ai kin san komai. Ke za ki ba da
labari, ko ƙawayenki na makaranta ba sai da na takamusu
burki da zuwa gidana ba?"
Dariyar dai Hafsat ta ƙara, ita kuwa Ramlat sai ta ɗan
tsunduma tunani, wato dai bayan wani yaƙin akwai wani,
amma bai kai wancan ba. Motsin bude kofarsa ce ta
sanya su jan baki su yi shiru don ɗazun dama sun baro shi
ya shiga bangaren Dada, tare yake da AlHassan. Zama
suka yi Hussein na mai kama hannun Fatima da ta yi
tsalle ta faɗa jikinsa. Da wani murmushin samun nutsuwar
zuci da gangar jiki adalilin nasiha da ban bakin da
Gwaggonninsa suka yi mishi. Ramlat ta gaida AlHassan ya
amsa fuska a sake.
"Lafiya lau Amarsu, ya kwanan baƙunci?"
Ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Bai wani jima ba
AlHassan din, bayan fitar su Kausar don ta je ta harhada
kaya su tafi gida, ya ɗan yiwa Ramlat har ma da Gogan
yar nasiha akan zamantakewa sannan ya yi musu sallama
ya miƙe ya yi gaba. Shima Hussein ya miƙe ya dubeta,
duban shauki da kauna.
"Ban mintuna kaɗan, zan je na dawo."
Ta gyaɗa kai.
"Allah Ya dawomin da kai lafiya."
Ya ɗan tsaya ya dubeta na sakanni, kamar ya yi tsokana
kawai kuma ya murmusa cike da jin dadin addu'ar ya fice.
***
Kawu Modibbo gumi kawai ya ke sharcewa, labarin komai
ya riskeshi daga bakin jama'a, hakan yasa don ya tabbatar
ya umarci Anti Amarya da dawowa. A bakinta tana kuka
cike da takaicinsa ta sanarmasa duk yanda aka yi ta kara
da fadin.
"Mece ce ribarka idan ka cutar da ɗan ɗan uwanka? Abu
ɗaya da wannan zuri'a ta yi maka da sunan laifi, ba za ka
iya tunawa ba saboda babu shi. Babu dalilinsa. Ka ji
tsoron Allah tun lokaci bai ƙuremaka ba, ka tuba ka je ka
nemi gafararsu."
Tana kaiwa nan ta bar shi da shi da Uwargidansa Hajiya
Fatuma wacce ita kanta jikinta ya yi mugun sanyi. Ta san
ba su kaunarsu saboda bakin cikin daukakar da suka
samu, amma ba ta taɓa tsammanin mijinnata zai aikata
wani abu makamancin wannan ba. Tambayoyi ne birjik a
kwakwalwata na yanda akai ma ya san matar Hussein, har
ta soma tunanin ko shi ne ya haɗa auren amma babu mai
ba ta amsa, mai amsawar ba ya a hayyacinsa. Ta kara
dubansa yanda ya ke faman sharce gumi sai ta kula har
wani hawaye ya ke fitarwa, na nadama ne ko akasinsa, ba
ta da masaniya.
"Ku harhaɗa kayanku, gobe za mu koma Kano."
Ta bishi da kallo har ya shige ɗaki, ranta ya ɓaci, wato dai
ba shi da niyyar aikata abinda Anti Amarya ta ce? Ta
girgiza kai don ba ta jin zata ɗara ko nan da can ba tare da
ta nemi gafarar Dada da yaranta ba na irin kiyayyar da ta
musu kuma ta tara yaranta su nema su ma.
***
Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan, a lokacin
Ramlat har ta gaji da zaman jiransa ga yunwa. Ƴan
Maiduguri sun shigo sun mata sallama kasancewar da
Asuba za su tafi. Ta sha nasiha sosai sannan suka bar
sashinta.
Ta ƙarasa ta nufeshi da zummar karɓar ledojin hannunsa,
hannunsu ya haɗu wuri guda, ta ji wani yarr, da sauri ta
janye ta yi gaba zuwa cikin falon ta ajiye saman tebur. Shi
kuwa dakinsa ya shige, har ta kammala jera kayan abincin
da ruwa bai fito ba. Can kuma ba jimawa sai gashinan,
daga shi sai jallabiyar maroon. Ko ba'a faɗa ba wanka ya
yi don ƙamshi kawai ke tashi a jikinsa. Kauda kanta ta yi
tana mamakin ma kunyarsa da ta ke ji, ta yarda dai mazan
ma suna suka tara don Hussein wani kwarjini yake mata.
Tana zuba abincin amma a jikinta ta ke jin ya cika ta da
ido yana kallonta, gaba ɗaya sai ta rasa sukuni. Ta saci
kallonsa, ita ɗin kuwa ya ke kallon babu ƙakƙautawa. Ta
gama zubamishi ta ajiye a gabansa, tana shirin zuba nata
ya damke hannunta. Kallonsa ta yi. Murmushi ya
sakarmata.
"Wannan ya yimin yawa. Zo mu ci tare."
Ya fadi yana matso da kujera daf da shi.
"Seat." Ya fadi a hankali yana dubanta ƙasa-ƙasa. Ba
musu ta zagayo ta zauna, ganin jikinsu na gogar juna ne
yasa ta yunkurin ja da baya, hannu ya sa da sauri ya
saƙalo ƙugun.
"Why?" Ya furta kamar mai raɗa a saitin kunnen. Ta yi
ƙasa da kai ba ta ce uffan ba. Ganin haka ya saketa ya
soma cin abincin yana haɗawa da sanyamata a baki.
Ramlat dai ta ga ta kanta, duk wannan yunƙurin da
alwashin da ta ci sai ta neme su ta rasa. Ita har wani
shakka-shakkarsa ma ta ji tana yi. Bayan sun ci ya ba ta
umarnin ɗauko ledojin da ya shigo da su, ta bude, kaza ce
sai lemuka. Ya ja plate ya ajiye, nan ta bude kazar ta zuba,
lemukan kuwa ta kai firij don akwai wani a ajiye. Koda ta
dawo nan ma ya dage sai dai ya ba ta, ta gaji da wannan
abin don haka ta ɗan yi kicin-kicin da fuska. Murmushi ya
yi.
"Oh, ashe fa kin ce ba zaman da ki ka shirya yi da ni ba
kenan ko? Sorry."
Ta ɗan harareshi da wasa, ya shafi fuskar.
"Ko me kika yi, kyau ya ke min."
Haka suka ƙarasa ci yana ta jan ta da hira. Falon ya koma
ya zauna bayan ya wanke hannu ya kuma rage hasken
fitilu. Ta kammala gyara wurin, sauran abincin ta sanya a
firij. Niyyarta ta shige ɗaki ta kwanta amma kaifin
idanunsa ya hana ta aikata hakan, dole ta dawo ta zauna.
Hankalinta ya rabu biyu, tana kallon talabijin, yayinda
Hussein ke afkin kallonta. Ta gaji ta juyo fuskarta na nuna
alamun gajiya.
"Me nayi don Allah?"
Yanda ta marairaice sai ta sanya shi ƴar dariya. Hannu ya
miƙamata. Ɗan harararsa ta yi.
"Gulma ce fa ba na so Heart."
Ta basar.
"Wace gulma kuma?"
Hannunta ya kamo ya murza cikinnasa.
"Har yanzu ba ki tabbatar da babu ƙiyayya tsakanina da ke
ba? To a tunaninki tun ma farko, don me na aureki?"
Ta rasa amsar ba shi, ita dai gani ta ke kawai rainin
hankali ne yasa shi aurenta. Yanzu kuwa ya gama wanke
kansa.
"Tunanin me kike ne? Na shayar da ke mamaki ko? Ni
yanzu damuwata kamar ma ke ce ba kya sona."
Ta kalleshi, ya wani yamutse fuska shi a dole damuwa.
Hannunta ya kai saman fuskarsa. Ta lumshe idanu sadda
ya shafa tun daga sumarsa har ya gangaro saman karan
hancinsa, yana tafiyar da hannun tana jin wani zuum a
gangar jikinta. Hannunta ta ke kokarin ɗaukewa amma ba
ta da wannan kuzarin. Tana ji ya maida yatsunta bakinsa,
ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya sumbata.
"Faɗamin meyasa ba kya sona? Tsakani da Allah nasan
muna da kyau. Haka Allah Ya haliccemu kuma mun
godemasa. Ba fa yabon kai ba."
Ta maze ta yi gyaran murya kafin ta amsa.
"Ka ɗauka kyau shi ke sanyawa a so mutum?"
Ya shafi sumar kai yana murmushi da dubanta idanun a
lumshe kamar mai gyangyaɗi.
"Kin ɗauka bansan rashin ra'ayin hakan ne ya bambanta ki
da sauran matan da ke sona ba?"
Baki buɗe ta ke kallonsa don ita mamaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login