Showing 45001 words to 48000 words out of 113545 words

Chapter 16 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

Kai tsaye ta wuce rumfar Malam Bello
inda anan ne yawanci Kawunnan ke zama a sha hira kuma
a tattauna matsaloli. Da yake rana ce, aikuwa ta ci sa'a
ganinsu a rumfar. Su biyar zaune, Kawu Bello, Kawu
Sunusi, Kawu Jamilu, Haruna sai Usman.
Kawu Bello na ganinta ya haɗe gira, ta ƙarasa ta zauna
aka gaisa.
"Sai kuma kika ji an turo kuɗin Ramlatu ko?"
Kawu Usman ya furta yana washe haƙora da duk goro ya
ɓata. Ta haɗe gira.
"Na ji Yaya, sai dai sam ba'a kyauta ba. Ba ku yiwa yarinya
daidai ba. Kada ku manta Ramlatu ba yarinya ba ce yanzu,
addininta ya ba ta damar zaɓen miji a karon kanta. Idan
ma ku ka dauke batun ta, na tabbatar ku kanku ba ku tsaya
wani dogon bincike a kan mutuminnan ba saboda.."
"Saboda yana da kudi ko? Haka kike so ki ce! Wato mu
gamunan mayun kudi? Rabi yaushe kika sauya haka? Kina
son ki nunamana ke da Khalid ku ka haifi Ramlatu?"
Kawu Bello wanda tun zuwanta ya ke a fusace shi ne ya
hau wannan kumfar bakin. Hajiya ta ɗago ta dubeshi don
tuni ta soma hawayen idanun sun ƙanƙance.
"Ba iko nake nunamaku da Ramlatu ba, amma fisabilillah
duk irin munin ɗabi'u mutuminnan da na lissafamaku a
baya bai hana kun murzawa idanunku toka ba kun ba shi
damar ya turo kuɗi. Wannan auren ba zai taɓa yiwuwa ba
idan har ina raye, ku gafarce ni amma Ramlatu ba za ta
auri Chairman ba."
"Yanzu na fahimci inda Ramlatu ta ɗauko kafiya da taurin
kai. Ashe ba a ƙasa ta kwasa ba, a nono ta tsotsa. Wato
yanzu da babu ran Malam shi ne ki ka samu kwarin
gwuiwar cin karenki babu babbaka Rabi. A baya ke yarinya
ce mai takatsantsan da ɓacin ran ƴan uwanki, amma
saboda kin haifa, kina kuma taƙama da dukiyar marayun
yaranki da ubansu ya bari, shi ne za ki wulaƙantamu. To
gwara da aka yi yunwa ai halin kowa ya fito."
Sosai kalaman Kawu Haruna sun soki zuciyar Hajiya
kamar mashi, ta kalleshi ta kasa magana. Sai Kawu Usman
ya sa baki
"Ni abinda ban gane ba Yaya Bello, kai da bakinka ka
tabbatarmin da yardar Ramlatu a auren wannan mutumin,
yanzu kuma sai na ke jin sabon labarin da ya sha bamban
da wanda na sani. Wato dai dole ne za ku yiwa yarinya?
Wannan ai ba girmanmu ba ne."
Ya fadi a sanyaye amma ransa a ɓace, haka yake mutum
mai hakuri da gudun duniya. Sai a lokacin Kawu Sunusi ya
tanka ta hanyar zubawa Usman daƙuwa.
"Ka ci ƙaniyarka Usmanu, mu sa'anninka ne da za ka yi
fito na fito da mu? Ai ko Murja ba za ta yi mana haka ba."
Kawu Usman jin Kawu Haruna yana sanya Yayarsa ciki ya
sa shi jan baki ya yi shiru sai dai ya rantse ba zai ƙara sa
hannu a cuci yarinya ba.
"Aa Haruna, zancen Usmanu gaskiya ne, ni kaina ai shi
Bello cemin ya yi da amincewar yarinya aka yi komai. To
ba za ta saɓu ba, ke Rabi ki je. Ni da kaina zan yi kiran shi
Dikkon na ba shi hakuri. Ita Ramlatu ta je ta ciro kudin ta
turomin da hannuna zan ba shi."
Kawu Jamilu ke maganar a daure, kasancewar shi ne
babbansu a wurin don daga Kawu Yakubu sai shi, kuma
bai fiye magana ba sai ta ɓaci wannan yasa suke ɗan
shakka-shakkarsa. Kawu Bello ya soma share gumi, babu
abinda ke ba shi tsoro sai yanda zai yi ya biya kuɗaɗen da
ya ci na Chairman. Ƙananun filaye har biyu ya siya ba tare
da sanin ƴan uwannasa ba. Wannan tashin hankalin ya sa
ya kara magantuwa.
"Haba Yaya, ka mance da auren Ramlatu na baya? Ka
mance irin tijarar da ta yi mana? Yanzu Rabi ke har kin
mance kina ɗauremata gindi?"
Hajiya wacce ta ke jin ya zamemata dole ta koma wajen
Malam Mu'azzam ƙanin babansu na Daura ta yi shiru ba ta
ce masa uffan ba. Suka ci gaba da ja in ja, daga ita har
Kawu Usman ba wanda ya ƙara tankawa. Kawu Jamilu ya
kafe lallai a mayar da kudi yayinda Bello da Haruna suka
ce sam ba zai yiwu ba. Wannan ne karon farko da suka yi
mishi musu a rayuwa. Ko ba komai shima Haruna ya ci
rabonsa. A karshe dai Hajiya ta mike ta wuce sashin Hajja
ina ta tarar da Zulaihat zaune su na tattauna maganar.
"Aa, kenan dagaske dai Uwani ta ke za ki zo?"
Hajiya ta harari Zulaihat wacce ita kuma yanda idanun
Hajiyar ya yi ja ya ɗaga hankalinta. Ta koramusu duk
yanda aka yi. Hajja ta yi salati.
"Ke Rabi! Ban ce ki bari zan je na same su da kaina ba?"
Hajiya ta girgiza kai.
"Ki bar ni kawai Hajja, ni yanzu gobe ma Daura na nufa
zan je na sami Baba Mu'azzam da kaina mu tattauna."
"Hakan ya kamata ki yi tun farko ba yanzu da muka dawo
ba. Meyasa tun acan shi ba ki mishi bayani ba sai yanzu
da ki ka je kike kokarin rushe zumuntarku da ƴan uwanki."
Hajiya ta kalli Mahaifiyarta da mamakin furucinta, ga dai
Hajja girma ya ja amma kyawun jikinta yasa ta ke nan
ƙyam da ita tubarakAllah.
"Ƙarya na yi kike kallona Rabi? Meyasa za ki tunkare su, ni
ban isa ki zo ki fara shawarta ta ba shi ne za ki yi gaban
kanki. Yanzu idan wannan ya haɗaku rikici fa? Mun cika
alƙawarin da muka ɗaukarwa Babanku kafin rasuwarsa na
ganin zumuncinku ya kara ɗanko?"
Hajja ta karashe gami da fashewa da kuka. Hankalin
Hajiya da Zulaihatnya tashi, suka shiga ba ta hakuri da
neman gafara, dakyar ta sauko ta kuma yi mata fada
sosai.
"Idan irin haka ta faru ba'a yanke hukunci cikin fushi.
Hakuri ake yi da kuma kai zuciya nesa."
Ta amsa da toh tana sharar kwalla.
***
Zufa sosai ya shiga ketowa Halima, kirjinta na dukan
tara-tara. Da gaskiyar ƴar uwarta da ta taɓa gargaɗinta
akan son abin duniya.
_*"Watarana idan ba ki yi hankali ba Halima, son kudinki zai
kai ki ya baro. Kuɗi sheggun abu ne da idan har ka sa a
ranka za ka aikata komai don ka same su, toh ina mai
tabbatar maki cewa wataran za su yi sanadin rushe
rayuwarka." *_
"Kin yi shiru Halima."
Hajiya Batool ta faɗi tana murmushi yayinda Hajiya
Zeenatu ke kallonta cike da nazari tana shakkun ko za ta
yi musu abinda suke so.
"Ba fa a kyauta za ki yi wannan aika-aikar ba. Hajiya
Zeenatu za ta dauki nauyinki ki je duk ƙasar da kike so ki
rayu cikin aminci da walwala. Za kuma ta ba ki gida da
mota mallakinki. Ke ba wannan ba, duk abinda kike so za
ta yi maki. Kawai ke dai ki aikata abinda muke sonki da
shi."
Halima da jikinta ke kakkarwa ta sharce gumin da sanyin
Ac bai sa sun fasa zuba ba. Duban Hajiya Zeenatu da
Batool take kamar wasu zakuna wanda kwakkwarar
numfashi idan ta fitar bai musu ba za su tashe ta daga
aiki yanzun. Ta yi shiru tana nazarin kudaden da kuma
sauyin rayuwar da za ta samu.
_*"Abu ne da kika jima kina nema, kullum kina cikin kallon
hotunan ƴan film da yaran masu hannu da shuni kina
kwaɗayin ki samu fiye da haka. Lokaci ne ya yi Halima,
mene don ki kashe rai ɗaya tilo kin gudu? Nawa aka yi?" *_
Nan da nan ta samu wani irin sukuni a ranta. Da murmushi
ta ɗago ta dube su wannan karon. Wannan ya sa suka dubi
juna su ma suka murmusa.
"Hakan na nufin kin amince?" Cewar Zeenatu.
Ta gyada kai tana dariya.
"Ɗari bisa ɗari na amince Hajiya, na tsani Ramlatu sai dai
ban zaci zan iya kasheta ba, amma yanzu yanda nake ji
zan mata duk abinda ya kama idan har hakan na nufin
samun ɗaukaka ta a duniya. Na dai so ace tana raye za ta
ga yanda Halima za ta zama, amma ba komai, yaranta za
su gane mata."
Ta ba su dariya sosai har da cafkewa. Sai kuma aka shiga
tattauna yanda za'a yi komai kuma a darennan. Ta yi shiru
tama sauraronsu tana gyada kai. A karshe ta ce.
"Na amince. Duk yanda ku ka ce zan bi na yi."
Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.
"Yauwa ƴar gari, yanzu bani lambar ita Ramlat din. Ki
tabbata kin isa wurin kafin ta je."
"An gama ranki ya daɗe." Tana kai wa aya ta ciro waya ta
ba ta duka lambobin Ramlatu guda biyu sannan suka
Hajiya Zeenatu ta ba ta kudi har dubu ɗari wai ta ɗan
taɓa. Wannan ma ya ƙara zuzuta Halima. Ta fice da
murnarta da kuma ɗaukar ALWASHI.
***
Hajiya da Zulaihat suka zauna saman kujera, Ramlat ta
fito daga ɗaki da sauri. A farko ta yi zatom shiriritar Ansar
ne da ya ke batun dawowarsu. Lokacin ƙarfe shida na
yamma, don haka ba su yi wani dogon zance ba sai da
aka idar da Magriba.
Zama suka yi Hajiya ta ba Ramlat labarin duk yanda aka
yi.
"Ai yau ba gobe ba, ki je ki fiddo kuɗaɗen nan ki kawo su
kwana a hannuna. Da kaina zan koma na kai wa Yaya
Jamilu."
Ramlat kamar ta rungume Hajiyarta don dadi, ta dinga
godiya da addu'a. Murmushi kawai Hajiya ta yi.
"Shikenan ma kinga sai ki ragemin hanya."
"Kai Maman Twins, nan da nan ba mota zan ɗauka ba."
"Haba ƴar Hajiya ƴar gatanta, daure don Allah muje da
mota kinga ko yaya kika ɗan ragemin zai min sauƙi."
Ramlat ta yi murmushi.
"Baƙonmu ya zo?" Hajiya ta tambaya.
"Eh tun ɗazu, yanzu ma nake shirin zuwa na kirashi mu yi
magana. Wallahi duk ya matsu."
"Wa kenan?" Zulaihat ta nemi ba'asi.
Nan Hajiya ta labarta mata, sosai ta ji ya ba ta tausayi.
Ramlat ta mike ta yiwa AlHassan iso, suka gaisa da Hajiya
da kuma Zulaihat, a karshe suka yi mishi addu'ar Allah
Yasa a dace da abinda ake nema ya yi ta jin dadi da
godiya. Bayan fitarsa Ramlat ta bi bayansa gami da ba
Zulaihat hakuri kan yanzun za ta dawo. A harabar gidan
suka zauna saman kujera. Ya gyara zaman gilashinsa yana
dubanta.
"Nema ne da muka jima mu na yiwa Hussein, yanzu sai
abin kusan muke tunanin ya zo ƙarshe idan har yana raye
kuma yana hannun matarnan."
Ya ba ta labarin duk yanda suka yi da Rasheed abokin
Hussein, ya ƙara da fadin.
"Don Allah my sis idan har da wani abu sa kika sani game
da matarnan kar ki ɓoyemin. Jikina yana bani ɗan uwana
yana raye."
Tausayi sosai ya bata don har idanunta suka cicciko da
kwalla. Ta sharesu.
"Ka kwantar da hankalinka, labari ne mai tsawo kamar
yanda na faɗamaka. Shakka babu nasan inda Hajiya
Zeenatu ta ke kamar yanda na sani cewa Hussein yana
tare da ita tsawon shekarun da ku ke nemansa."
Ai wata irin zabura da Alhassan ya yi ya mike tsaye sai da
ya razanata.
"Dagaske kike?! Hussein na hannunta?! Ya akai kika san
Hussein din?! Tashi muje ki kai ni wurinsa don Allah."
Jikinsa har rawa yake yi, ga mamakinta ma hawaye ya
soma. Dakyar ta kwantar da hankalinsa.
"Don Allah ka zauna mu yi magana. Idan har daga jin
wannan ka shiga ruɗani, ta ya za ka iya amsar dukkan
labarin da zan ba ka?"
Hakan da ta faɗi sai ya koma mazauninsa yana jero
hamdala ga UbangijinSa. Lallai kukansu ya zo ƙarshe.
Hawayen Dada zai daina zuba.
"Mami! Mami!!"
Suka dubi yaran, AlHassan na ji kamar ya zanesu don sun
katsemishi hanzari. Wayarta ce su ke kokarin miƙo mata.
Ta karɓa tana fadin mene.
"Kira aka yi kuma an miki saƙo."
Fadin Ummi, ta karba ta basu umarnin su koma ciki. Har
za ta ajiye wayar saman cinyarta, ta hangi suna kamar ma
Hussein a karshen saƙon da aka turo wacce lamba ce.
"Yi hakuri don Allah." Ta faɗi a gaggauce, hannu na rawa
ta buɗe.
_*"Za su kashe ni. Ramlat ke kaɗai za ki iya taimakamin. Ki
zo ki cece ni. Hussein." *_
Ta karanta ya fi sau uku, hannunta na rawa, wani saƙon ya
ƙara faɗowa. Adireshin wurin da yake ne kawai.
"Wai meye haka? Innalillahi." Ta furta tana mai mikewa da
fashewa da kuka. Da sauri AlHassan ya karɓi wayar don
dama ba a nutse ya ke ba. Yana karantawa ya dubeta.
"Hussein ɗina zaa kashe?! Su waye? Taho mu je!!"
Duk a hargitse ya yi wannan kalamin, ya nufi motarsa
amma mukullin na ɗaki, don haka a guje ya koma ciki har
yana mance ɓangarensa a gidan yana faɗawa falon
Hajiya, ganinsa a rude yasa Hajiya miƙewa tare da
Zulaihat.
"Lafiya?" Suka nemi sani. Maimakon ya amsa sai ya kasa
don haka ya fice, Allah Ya taimaka ya gane dakin, ya shige
ya dauki mukullinsa a aljihun kayan da ya fidda. Su Hajiya
tuni sun fito harabar gidan inda Ramlat ke safa da marwa
cike da tashin hankali tana kuka kamar ranta zai fice.
"Meke faruwa?" Tuni AlHassan ya tayar da mota yana
mata horn. Ta dubi su Hajiya.
"Za su kashe Hussein."
"Ki taho mu je ko?!"
Tsawarsa ta sa duk suka dubeshi, su Hajiya na ta salati
gami da fadin.
"Kai Hassan kar ka yi tuƙi a wannan yanayi! Ka tsaya!"
Amma ina! Ramlat ba ta ƙarasa rude ƙofar ba ya ja, Baba
Maigadi tunda ya ga an tayar da mota ya tsaya bakin
gate, ganin ya taho kawai sai ya buɗe masa.
Ita ce ta dinga yi mishi kwatance, sai dai kafin su kai
wurin saƙo ya ƙara faɗowa.
"Dakata!" Ta faɗi da babbar murya. Ya ci wawan burki yana
jin wani irin mutuwar jiki, idanunsa da yake gani dishi-
dishi a dalilin faɗuwar gilashinsa a ƙasan ƙafafunsa, ya
ƙuramata su.
"Sun kashe shi?" Yanda ya yi maganar a sanyaye yasa ta
dubansa da nata idanun da suka yi kaca-kaca da hawaye.
KARFEN KAFA Chapter 59
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


"Aa, ba kisa ba ne."
Ta miƙa masa ya shiga karanta saƙon.
"_*Muddin ki ka sake ki ka zo da wani ki tabbatar babu
abinda zai hana mu katse numfashin Hussein a doron
ƙasa. "*_
"Ka bar ni na je ni kaɗai kar su kashe shi."
Ta faɗi da gaggawa, da sauri ya ja motar ya gangara gefe.
"Kinsan me za'a yi? Sauka ki shiga adaidaita sai na bi
bayanki."
Ta gyada kai sai kuma ta dube shi.
"Toh kuɗin.." Ba ta karasa ba ya hau laluben aljihu, ya zaro
kudin da bai san nawa ba ne ya miƙamata. Har ta sa kai ta
fita, ta leƙo.
"Ka kira Hisham ka sanarmasa, ka kuma ba shi
kwatance."
Daga haka ta wuce da sauri, Allah Ya taimaka ta samu
abin hawa da wuri. Tana shiga yana biye da ita, lokaci
guda kuma ya kira Hisham ya sanarmasa komai. Hisham
wanda dama hankalinsu ke a tashe sanadiyyar kiran da
Hajiya ta yi mishi kan Ramlatun da Hassan. Da gaggawa
ya amsa da cewar yana nan tafe da hukuma. Daga haka
AlHassan ya kashe kiran.
***
Hisham ya gwada kiran wayar Hussein sai dai duk
wayoyinsa a kashe. Wannan ne ya sanya shi ruɗewa, ya
kuma gasƙata maganar Ramlat haka yake. Da sauri ya
mike ya zari mukulli. Aisha ta tare shi tana kuka.
"Don Allah kada ka je kai kaɗai"
Ya kama gefen fuskarta.
"Please ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba abinda
zai faru. Ba ni kadai zan je ba, zan biya wurin ƴan sanda."
Daga haka ya samu ta gyada kai gami da yi mishi fatan
nasara. Hisham koda ya fito bai tsaya ko'ina ba sai
babban hedikwatar ƴan sanda na Bompai. Shiga ya yi kai
tsaye ya yi report. Kallonsa sosai Sajan ya yi.
"Me ce ce shaidarka?"
Ya riƙe goshi.
"Saƙo suka yi mata, kuma ƙanwata ce."
"Ina saƙon?"
Hisham kamar ya shaƙe shi ya amsa.
"Na faɗamaka ba ni suka aikawa ba, ita da aka aika wa
tana can ta kama hanyar zuwa ita kadai ba tare da wani
ba. Don Allah ku taimakamin."
Har Sajan zai magana sai ga D.P.O ya shigo.
"Meke faruwa ne?" Hisham ya dubeshi, baki sake D.P.O
ke dubansa.
"Aa, Hisham Muhammad, me ka ke yi anan? Lafiya
kuwa?"
Hisham wanda mamakin ganin yayan marigayin abokinsa,
Safwan ya kamashi, a gefe guda wani farin ciki marar
misaltuwa ya shige shi. Nan ya ba shi labari a gaggauce.
D.P.O Musa ya yi salati.
"In sha Allahu za ta kuɓuta, amma na fi tunanin it is just a
trap. Gwada kiranta ka ce ta dakata kar ta ƙarasa."
Jin haka Hisham ya shiga kiran Ramlat amma ina! Ba ta
ɗaga ba. Wannan yasa D.P.O ya ba sajan umarnin maza a
ɗauki mota a je. Ba shiri suka dunguma suka fita Hisham
na mishi godiya.
***
Fili ne sosai na makarantar Gwamnati, unguwa ce mai
masifar shiru, sai a kwashi tsawon mintuna talatin ba ka
ga abin hawa ko ɗaya a wurin ba. Mai Adaidaita na ƙorafi
da tambayarta abinda ya kawo ta irin wannan wuri sai dai
ba ta tanka masa ba. Kiran Hajiya har da su Hisham da
Yaya Munir yana ta shigowa sai dai ba wanda ta amsawa.
Text ya faɗo ta yi saurin dubawa hannunta har rawa yake
sai dai ba ta fasa addu'a ba,ba ta fasa maimaita addu'a a
zuciyarta ba.
'ALLAHUMMA ANTA 'ADHUDEE WA ANTA NAASIREE, WA
BIKA UƘAATILU' (Ma'ana: Ya Allah Kai ne Majinginata,
kuma Kai ne mai taimakona, kuma da Ƙarfinka ne zan
yaƙesu).
_*"Mun hangoki, ki tabbatar da tafiyar mai napep ɗinnan, ki
tako ki shigo makarantar ke kaɗai. Ki tabbata kin kashe
wayarki." *_
"Tsaya! Ya isa. Anan zan sauka."
Yanda ta faɗa sai da ya tsorata mai napep din har ya juyo
ya dubeta, hasken fitilar motar bai sa ha ga fuskar sosai
ba. Ya ja ya tsaya ta sauka ta miƙamasa kuɗin.
"Chanji fa?"
"Na bar maka."
Ta faɗi ka tsaye, ya yi godiya ya kaɗa abin hawa ya juya
ya tafi yana waigenta da mamaki.
Ta ci gaba da addu'a tana dosar cikin makarantar bayan
ta kashe wayar gaba ɗaya. Mamaki da tsoro ta ke yi, me
zai sa a kama Hussein a kuma kwo shi irin wannan wuri?
Tafiya sosai ta yi har ta soma shiga wuraren ajujuwa.
***
AlHassan ya fito daga motarsa a hankali ya shiga takowa
zuwa cikin filin da duhu ya mamaye sai kadan daga
haskenfarin wata. A hankali ya ke tafe, madadin ya bi inda
Ramlat ta bi sai ya zagaya. Wayarsa a mota ya bar ta
gudun kada haskenta ya ankarar da su wanzuwarsa a
wajen.
***
Halima wacce ta ci riga da wando baƙaƙe ta kuma sanya
mask a gaba ɗaya fuskarta tana hango Ramlat. Yanda
Ramlat ke ƙara takowa haka kirjinta ke bugu fat! fat! Ta kai
duba ga mutumin da ta sanyawa baƙin kyalle ta rufewa
fuska gaba ɗaya. Cikin raɗa-raɗa ta ce.
"Ta taho, ka soma acting."
Ya amsa da "An gama!"
Halima ta ƙara lalubo aljihunta ta fiddo bindiga. Ta nufi
Ramlat.
***
Ramlatu dake cikin tafiya sai ji ta yi an rufe mata baki da
ƙarfi, ta shiga kokarin kwatar kai sai jin bakin bindiga ta yi
a saitin kanta.
"Ina Hussein yake? Na ji idan zai tsira ni ku kashe ni don
Allah amma kar ku kashe Hussein."
Daga haka aka soma tafiya da ita har inda wani mutum da
ta ga inuwarsa kadan sakamakon hasken farin wata, yana
ta walainiya da kai alamar ya jigata sosai a hannunsu.
"Ramlat." Ya faɗi da wani irin sanyi kusan kalar muryar
Hussein da ya yi haddarsa.
Kuka sosai Ramlat ta shiga yi. Za ta nufeshi Halima ta
ƙara yo baya da ita.
Juyo da Ramlatun ta yi, Ramlat ba damar gudu.
Hankalinta na kan Hussein yayinda idanun ke kallon
masheƙin da ke tsaye a gabanta.
"Mene ribarku idan kun kashe Hussein? Me ku ke da
buƙata?"
Wata dariya Halima ta yi kamar ta yara ƙanana, ta sauya
murya.
"Ubanki za mu yi! Ai ke muke nema! Ke kuma aka ce mu
kashe ba Hussein ba. Kai Gwaska!"
Tana fadin haka wanda ke zaune da ta yi zaton Hussein
ne ya miƙe ya yakice kyallen. Nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login