Showing 18001 words to 21000 words out of 113545 words

Chapter 7 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

ƙasarnan don asirinki ba zai je
ko'ina ba sai tonu! Ita dai yarinyar da na gargaɗeki a
kanta, ita ce silar rushewar dukkan ayyukanki! Ke kuma
Batulu! Nan ba da jimawa ba, ɗanki zai zo da batun ƙarin
aure! Auren da zai rushe duk wani asiri da kika yi
tsakaninsa da matarsa! Anan ne duk abinda kika binne zai
fito fili muraran!"
"Ƙarya kake! Wallahi ƙarya kake! Dama na faɗamaki kar
mu zo wurinsa!"
Hajiya Batool ke maganar jikinta har yana ɓari, fuskarnan
wacce man bleaching ya maida jawur, sai ƙara kyalli take.
Ita kuwa Hajiya Zeenatu idanun kamar an watsa barkono.
Ba ta san hawaye ke fita daga idanunta ba sai da ta ji
suna kokarin shigewa bakinta. Shi kuwa Gora banda wata
shegiyar dariya ba abinda yake yi don ko kaɗan kalaman
bai ɓatamasa ba, ya saba ganin irin wannan hauka da
jahilcin na mata.
Tsawa Hajiya Zeenatu ta dakawa aminiyarta ganin gaba
ɗaya ma ta ƙi maida hankali ta nutsu su nemi mafita. Ita
da take da tashin hankalin rasa miji irin Hussein ba ta yi
gigitar da Hajiya Batool ta yi ba. Ta sa mayafi ta sharce
gumi idanunta a kansa.
"Mun tuba, wallahi mun tuba ba zamu ƙara saɓawa
umarninka ba. Ka taimakemu Gora, a wannan gaɓar idan
ka ce za ka bar mu, ba wanda zai tsira."
Ya ci gaba da kallon ƙasar da ke shimfiɗe gabansa yana
ƴar dariya gami da gyara hannun babbar rigarsa.
"Akwai tsada..."
Bai ma kai ga ƙarasawa ba duk suka tari numfashinsa.
"Zamu biya ko nawa ne, wallahi ko duka abinda muka
mallaka ne."
Ya jinjina kai, kaf ba wacce bai san halinta ba a cikinsu.
Yana da karatun kowaccensu don tun ana damawa da su
a siyasa da bariki yake tare da su. Maida hankali kan ƙasa
ya yi can kuma ya ɗago ya dubi Hajiya Zeenatu. Yanzu da
ace zai faɗi ainahin abinda ya gani, toh ya tabbatar
kuɗaɗen da suka Kaɗaita masa ba zai samu ba, gwara ma
Hajiya Zeenatu akwai sakin hannu, anan ne suka sha
bamban da aminiyarta da ta kasance marowaciya.
"Aikinku zai yiwu, sai dai dama ai na riga da na faɗamaku
akwai kashe kuɗi. Batun kuma shi mijinnaki ina tabbatar
maki ba zai haɗu da ɗaya cikin ƴan uwansa ba. Sai dai
kuma ki kara kiyayewa ga barin kowace mace shiga
rayuwarsa. Idan na ce kowacce, ina nufin hakan!"
Ya fadi kai tsaye, kusan bayanai biyun ƙarshe da ya yi sun
kasance abinda ya hanga ɗin.
Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi, nan kuma Gora ya shiga
lissafomata abinda za'a siya. Da ta gaji ta bude jaka ta
fiddo bandirin ɗari biyar sabbi har biyu ta ajiye a gaban
buzunsa.
"Gashinan, na bar maka wuƙa da nama, duk abinda ya
kamata nidai a yimin don Allah. Sannan idan da hali a
yiwa ita yarinyar turen aljanu su zama silar ajalinta. Nidai
ko haukatamin ita ne don Allah a yi Gora."
Wani murmushi Gora ya yi ya sa hannu ya dauki kudin
gami da faɗin.
"An gama! Kedai kawai ki sha kuruminki."
Daga haka ya juya ga Hajiya Batool wacce ganin irin
yanda ya kwantar da hankalin Hajiya Zeenatu da bayanan
gamsuwa da kuma karfafa gwuiwa, itama sai ta ji nata ya
kwanta. Nan ya shiga kora mata karya da gaskiya itama ta
hau ta zauna ta cikashi da kudin. Kafin dai a bar gidan
Gora an shirya, dariya ake yi har yana neman su ba shi
haɗin kai yanda suka saba.
"Alƙawari ne mun yi maka, zamu cika mu ziyarceka da
zarar aiki ya kammalu." Cewar Hajiya Zeenatu da take ji
kamar an mata albishir da mutuwar ɗan uwan Hussein.
Wata dariya suka yi tare kafin su fice. Sai a sannan
hankulansu ya kwanta.
***
BAYAN KWANA UKU.
Tun wuraren biyu na rana ta samu kira daga Alhassan
(wanda tuni ta sauya mishi suna daga mutumin mall zuwa
Alhassan kamar yanda ta ga username ɗinsa a
WhatsApp). Sanarmata da batun zuwansu da iyalinsa ya
yi, wannan tasa bata zauna ba, ita da Hajiya da Ladidi
suka shiga kicin don yin kayan maƙulashen tarbar baƙi.
Suna tsaka da aikin sai ga Zulaihat da Rafee'ah, mamakin
irin wannan garar da ake shiryawa ta kamasu.
"Baƙi za ku yi ne Hajiya?" Cewar Zulaihat tana duban kajin
da Ramlat ke soyawa.
"Au, ashe mu ba zamu ci daɗi ba kenan sai zamu yi
baƙi?"
Dariya ta basu.
"A'a, amma dagaske naga kayan ne da yawa har da su
zoɓo da ginger. Duk na waye?"
Murmushi Hajiya ta yi.
"Ku tambayi ƙanwarku."
Ramlat ta sanarmusu batun zuwan Alhassan wanda suka
taɓa jin ta yi waya da su. Rafee'ah ta kama baki tana
dariya.
"Ah lallai, ki ce surukinmu ne zai iso. Kai abu ya yi kyau."
Yamutse fuska kawai ta yi kafin ta murmusa, ita dariya ma
suke ba ta idan suna haɗa ta da AlHassan. Ko za ta kwana
ta na faɗamusu zumunci ne kawai tsakaninsu ba yarda
zasu yi ba don haka ta ja bakinta kawai. Hajiya da su
Zulaihat suka koma falo, itama tana kammala suyar ta
haɗa chicken pepper dinta ta zuba yanda ya kamata, da
taimakon Ladidi suka kwashi kayan zuwa saman tebur.
Lemukan suka sanya a firij. Tana zama a falon ba jimawa,
wani tunani ya faɗomata a rai, cikin sauri ta mike zuwa
ɗaki. Wayarta dake hannun Ansar wanda ke kwance yana
buga game ta karɓa haɗi da faɗin.
"Kaima Monday ta zo ba zama za ka yi ba sai ka je
makaranta tunda ka warke."
Ya hau tura baki.
"Tashi ka je ga su Maman Twins da Anti Rafee.."
Ba ta kai aya ba, da murnarsa ya dira ƙasa ya fice.
Murmushi ta yi kawai. Abinda ya shigo da ita ta tuna
hakan yasa ta saurin kiran Hisham.
Bayan sun gaisa ya gama jan ta da tsokana yanda ya saba
sannan ta samu damar magana.
"Idan ba damuwa don Allah ka shigo gidanmu kamar
wuraren biyar haka."
"Toh Antinmu, ina fatan dai ba ƙarata Princess ta kawo
ba? Dagaske sharri take min."
Murmushi Ramlat ta yi, Hisham ba ya rabo da zolaya.
"Ni ba haka nace ba, abu ne mai muhimmanci akan
abokinka, sai dai duk abinda za ka gani kar ka yi magana.
Please."
"Shikenan, kar ki damu, In sha Allah zan shigo."
Daga nan suka yi sallama ta faɗa wanka. Koda ta fito, ba
kwalliya ta yi ba sai dai ta gyara fuskarta ta shafa hoda da
man leɓe. Ko ba komai baƙinta ne. Ta shirya ta fito falon
daidai sadda su Ummi suka dawo daga makaranta.
Dakyar Ramlat ta korasu islamiyya har Ansar don a farko
ganin iyayennasu sun so su ƙi zuwa.
Sai a sannan su Rafee'ah masu kwasar garar abinci suka
yi wa Ramlat kallon tsaf ganin yanda ta sh sutura mai
kyau. Ramlat ta yamutse fuska kadan.
"Ku faɗa kawai, abinda ku ke nufi ba shi bane."
Dariya suka yi.
"Kin ji yarinya da tsarguwa."
Fadin Zulaihat tana duban Rafee'ah. Taɓe baki Rafee'ah ta
yi, ita me za ta ce? Ta dai lura Ramlat ba ta kaunar
maganar aure don haka a yanzu nata mujiya. Aka bar
zancen aka faɗa labarin gidan Yaya Munir wanda a yanzu
don kansa ya zo ya samu Hajiya ya rantse rabawa
matansa gida zai yi. Wannan kalami ya sa su dariya
musamman Zulaihat abokiyar takun saƙarsa.
"Maganinsa! Tun farko nan ba na nunamasa hakan zai
fiyemishi ba amma ya nunan shi din gwani ne. Kuma
adali."
"Toh dai yanzu ko mene ai shikenan tunda ya riga da ya
faru." Faɗin Hajiya kenan.
Haka suka yi ta hira kafin a kira la'asar duk su mike don
ɗauro alwala. Wurare karfe hudu da rabi sai ga wayar
Alhassan, nan ta ƙara yi mishi kwatance, a ƙarshe ma ta
fita don tarbarsu.
Har suka ƙaraso idanunta na wani gefen, ya fito daga
motar sanye da dark blue din shaddarsa sai gilashin da ke
ƙaramasa kyau. Ya karya hula kamar Bakano.
Yarinya karama ta fito ta sha ƙananun kitso shuku a kanta,
an sanyamata ribbons masu kyau da ya ƙaramata kyau.
Ganin har da dattijuwar da nan take jikinta ya bata cewar
ita ce Dada, yasa ta ƙarasawa tana ƙara yi musu barka da
zuwa. Kausar da Hafsat sosai Ramlat ta burgesu, ta
jagorancesu har cikin falon Hajiya wanda aka ƙara
kimtsawa, Alhassan ne dai ya toge a farfajiyar gidan ya ƙi
shiga. Bayan sun zauna aka gaggaisa, can kuma ta shiga
daki ta kira Hajiya. Su Zulaihat ma suka biyo bayanta.
Dada ba ta jin hausa sosai, a haka dai aka gaggaisa,
wani abin Hafsat ce ke cin gyaranta.
"Kinga abin Allah mai haɗa zumunta."
Fadin Hajiya tana murmushi ganin yanda Fatima ta
maƙalewa Ramlat kamar dama can sun taɓa haɗuwa.
"A bar ki a nan za ki zauna?" Fadin Hafsat tana duban
Fatima wacce ke ƙara shigewa jikin Ramlat. Da sauri ta
wangale baki gami da gyaɗa kai, duk sai ta sanyasu
dariya.
Anan ne Ramlat ke ji dagasken dai su na da ƴan uwa a
garin, kwatancen da ta yi yasa nan take suka gane gidan
musamman Hajiya da Yakasai ya zama unguwar da ta ci
ƙuruciyarta a ciki. Sai dai basu taɓa shiga gidan ba don ba
wani fita suke yi ba sosai a unguwa, hakanan su ma
mutan gidan ba kowa suke shiga sabgarsa ba sai wanda
ya isa.
***
Hisham gwanin cika alƙawari sai gashinan ya zo tun ma
biyar saura. Babban abinda ya ƙara kwadaita masa zuwan
bai wuce na cewa da ta yi lamarin ya shafi Hussein ba. Ya
faka motarsa a waje, Maigadi na shirin bude gate ya
dakatar da shi gami da nuna yanzun shima zai fito. Bayan
sun kammala gaisuwar ya ƙaraso ciki, ji ya yi kansa ya
sara yayinda kirjinsa ya shiga dukan tara-tara. Ba don a
yau ɗin ya ziyarci Hussein a ofishinsa ba, ya kuma san
kalar kayan da ya sanya da ma kalolin motocin gidan
Hussein din, zai iya rantsewa ya ƙara wannan na tsayen
Hussein ne.
KARFEN KAFA Chapter 48
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


'Kenan Hussein ƴan biyu ne?' Ya jefawa kansa tambayar
da nan take ta amsamishi da eh. Tambayoyi kala-kala ke
ɗawainiya da shi. Ya ƙaraso ganin da ya yi Alhassan ya
zubamasa idanu fuska a sake, wayar da yake dannawa ya
mayar cikin aljihu gami da miƙamishi hannu. Musabaha
suka yi, hatta da muryarsu sai ya ji tana mishi
kamanceceniya. Ja ya yi ya tsaya cikin danne mamakinsa,
damuwa sosai ya mamayeshi. Ya tuna gargadin Ramlat
akan kar ya yi wata katoɓarar don haka ya daure yana jan
Alhassan da hira da zolaya kamar ya sanshi. Anan ya kara
tabbatarwa ba Hussein bane, wannan wani ne daga
Adamawa kuma sunansa Alhassan. Yana so ya tambaya
ko yana da wani dan uwan haihuwar amma ya danne.
Kafin dai Ramlat ta fito ta yiwa Alhassan iso don ya shiga
gidan, Hisham da AlHassan hira suke yi sosai, ya fahimci
kusan halayyarsu ta daya don har Alhassan ma ya fi
Hussein sakin fuska.
Ramlat na ganinsu tare ta karasa, suka hada ido da
Hisham wanda ke kallonta bakinsa cike da tarin
tambayoyi, ta gaidashi. Ta yi musu jagora zuwa falon
Hajiya.
Nan aka ƙara gaggaisawa sannan AlHassan suka koma
sitting room. Abinci da komai ta kai musu. Bayan
kammala ci, suka yi shirin tafiya.
Ya yi daidai da dawowar su Ummi daga makaranta.
"Yaranki ne?" Dada ta fadi tana kallon Fatima, murmushi
ta yi kawai ta sunkuyar da kai.
"Ai Dada daga gani ma ba tambaya, wannan yarinyar tana
kama da ita sosai." Kausar ta fadi tana mai jawo hannun
Ummi da nutsuwarta ya burgeta.
"A'a, wallahi ta fi ta kyau."
Fadin Hafsat, tana nufin Ummi ta fi Ramlatun kyau.
Nan Kausar da Hafsat aka shiga musu, su Zulaihat me
zasu yi ba dariya ba. A karshe suka yi musu sallama suka
kama hanyar tafiya zuciyoyin kowannensu cike da farin
ciki. Babu ma kamar Hafsat wacce kafin fitowarsu daga
gidan Modibbo ranta ya ɓaci da yanda Modibbo ya amsa
gaisuwarsu a wulaƙance. A hanya har rantsuwa ta dinga yi
ba za ta ƙara zuwa wata sabgarsu ba. Ba wanda ya kulata
don kowa ransa ba dadi.
A yanzun tana jin za ta iya zuwa ta yi fiye da sati ma a
Kano saboda karamci irin na Ramlat da ƴan gidansu. Ko
ba komai ta samu wasu ƴan uwa a garin.
A ɓangaren Dada ji take inama haka Modibbo da sauran
ƴan uwanta ke sonsu, da ta tabbatar ba ta da sauran
damuwa.
***
Bayan tafiyarsu Ramlat ta takowa Hisham har wurin
motarsa. Cike da damuwa ta tari numfashinsa, kaf yanda
ta haɗu da AlHassan ba ta ɓoyemishi ba. Ya jinjina kai ya
ƙara sakin ajiyar zuciya karo na ba adadi.
"Wallahi kaina ya ƙulle Ramlat, wannan lamari da ban
mamaki yake. Zargina ya tabbata na cewa Hussein
rabashi aka yi da ƴan uwansa. Koda ba rabasun aka yi ba,
toh lallai akwai wani laifi da aka aikata gareshi har ya yi
sanadin da ya fidda kowa a babin rayuwarsa. Mutane
masu mutunci da kamala, sun bani tausayi sosai na
rashin sanin inda yake."
Ranta ya sosu, sosai ta ji tausayin Hussein ya ƙara
mamayeta. Ta karyar da wuya.
"Bari kawai, ni kaina abin yana dauremin kai. Amma fa
bana son sanar da su komai, ba kuma na son su haɗu da
juna har sai mun gano bakin zaren."
Jinjina kai Hisham ya yi.
"Gaskiya ne Ramlat, don Allah ki dage, ki ƙara shawo kan
Hussein yanda za ku shaƙu. Watakila ta hanyarki mu samu
wani information din tunda na lura wallahi ya soma
damuwa da ke."
Gabanta ya fadi. Ta dubi Hisham sosai.
"Bangane ba."
Murmushi ya yi don ba ya jin dariyar dalilin damuwa da
tausayin abokinsa da ya mishi ƙatutu. Tayar da motarsa ya
yi.
"Ke dai ki yi aikinki. In Sha Allah nasarar ma da kike
tunani zamu samu fiye da ita."
Ta amsa da toh kawai ba tare da ta tanka ba, dakyar ta iya
ba shi sallahun gaida A'isha. Har ya ja motar tana juya
maganarsa ta ƙarshe, to wace irin damuwa da ita kuma?
Ta kasa fassara wannan kalamin.
***
'Addu'a, shi ne abinda ban fiye maida hankali wurin yi
ba."
Ya furta a fili cikin ba kansa amsa, shi kadai ne a mota
yana ja bayan dakyar ya samu fitowa daga takunkumin
Hajiya Zeenatu na yi mishi rakiya duk inda zai je.
Ya yi wannan maganar a sanadin wa'azin Mufti Menk da
ya gama saurara a motar, malamin na tunadar da Bawa
akan ya dinga zama yana yiwa kansa hisabi, mene ne
abinda ya san yana aikatawa kafin lokaci ya ƙuremasa.
Damuwa da ƙunci suka cika zuciyarsa, ko sallah ya yi a
gaggauce yake yinta, bai damu da zuwa Masallaci ba ya
bi jam'i ko lokutan azumi balle kuma sallar Asuba wacce
wani zubin sai rana ta fito take gabatar da ita. Idanunsa
suka kaɗa, shakka babu shi laifukansa nada yawa a wurin
Allah.
Ruwa ake yi tamkar da bakin kwarya bai fasa tuƙi ba sai
dai yana tafiyar ne kamar wanda kwai ya fashewa a ciki.
Wannan ma kadai ya isa ya jawowa bawa munanan
abubuwa, yana da matsala babba ta wannan fannin.
Da wannan tunanin ya isa gida cike da tsantsar damuwa.
Hajiya Zeenat ba ta nan wannan yasa shi kai tsaye nufar
ɗakinsa, sai da ya rage kaya ya yi wanka kafin ya sauko
ƙasa. Nan ya iske John ya jera kwanukan abinci saman
tebur. Budewa ya shiga yi kafin ya ja tsaki ya maida ya
rufe, babu ɗaya da ya burgeshi balle ya ji zai iya ci.
Wayarsa ya jawo ya shiga dannawa, kai tsaye whatsapp
ya shiga.
Shi ɗin ba ma'abocin bude Status bane, sai dai yakan
bude na mutane masu muhimmanci a wurinsa. Sunan
HEART da ya hango a jerin wadanda suka dora Status ne
yasa kansa tsaye ya bude.
Hotonta ne zaune saman kujera a falo, ta rungume wata
kyakkyawar yarinya suna dariya. Kirjinsa ya bada dam! Ya
kara zooming ya kurawa yarinyar idanu. Da ace ya taɓa
haihuwa, ba abinda zai hana ya kira yarinyar da ɗiyarsa.
Can kuma ya tuna kamanni ne kawai, murmushi sosai
yake yana kallon yarinyar da ita kanta RAMLATUN. Sun
burgeshi sosai, yarinyar ta shiga ransa ainun. Ya yi niyyar
screenshot sai ya fasa, wannan ba halayyarsa ba ce don
haka suka ya zaɓi turamata saƙo kamar haka.
"Mutane sama da dari biyu sun ga Status dinki. Hakan
daidai ne?"
Yana aikawa ya saki murmushi gami da sauka daga
whatsapp din. Wayar ya ajiye, hakanan sai ya ji wani
kwarin gwuiwar ya ci abincin. Ya kuma rasa ta ina.
Shigowarta dakin kenan bayan sun yi sallama da Hajiya.
Wani hamma ta saki tana mai rufe baki, a gajiye liƙis take
jin ta. Kakkaɓe gefen da za ta kwanta ta yi, hankalinta ya
kai ga wayarta, shaf ta mance da ita a chaji, ta cika tun
awanni biyu ma da suka wuce.
Zareta ta yi ta shiga cikin whatsapp ganin saƙonnin da
suka faɗo daga kunna Data.
Saƙon Hussein ya sanyata dariya ba kaɗan ba, ta
maidamishi amsa.
"Ba fa celebrity ba ce."
Daga haka ta yi zaman jiran amsa har gyangyaɗi ya soma
fisgarta, can dai ta hakura ganin ba ya kusa ta kashe
wayar ta yi addu'a ta kwanta.
***
Ruwan da ake kamar da bakin ƙwarya ya sa ta barin yara a
gida don sun kammala jarrabawa kusan wasa kawai ake a
makarantar yanzun, itama ba don fitar ta zama dole ba da
babu inda za ta je. Amrah ce ba lafiya, abin tsoron kuma
lokacin haihuwarta da saura don duka-duka cikin bai kai
wata shida ba.
"Ki je zuwa anjima ma leƙa. Kar dai ki manta da kiran
Kawunnaki. Ki karasa Yakasan idan ruwan ya tsagaita."
Wani ɗaci Ramlat ta ji da bayanin karshe na Hajiyarta,
tasan kiran da Kawun ke mata bai wuce akan aure ba. Ita
shikenan yanzu kowa idanunsa a kanta, an takura akan
sai ta yi aure. Dama tun da Hajiyar ta soma batun kai yara
dangin Babansu don su ci hutunsu a can, ta soma jin ba
dadi. Babban takaicinta yanda tun rasuwar Abulle babu
wanda ya kara nemansu banda Malam da ke kira lokaci
zuwa lokaci su gaisa ko kuma ita ta kira. Hakanan Justice
duk sadda zai yiwa yaran ƴan uwansa kayan sallah toh zai
haɗa da su. Kannen Aliyu ta yi musu uzurin aure, amma a
ganinta hakan bai kai dalilin da zasu dauke ƙafa da
hankalinsu daga kan yaransa ba. Ko ƙafarsu ba ta tako ba
ai akwai waya.
"Kin yimin shiru kina wani ƙunƙuni, idan ba za ki je ba sai
ki kira ki faɗamasa."
Hajiya na kaiwa nan ta mike a fusace ta yi ɗakinta. Sauke
ajiyar zuciya Ramlat ta yi, ranta har sannan babu dadi
haka ta gyara zaman mayafin abayarta maroon ta fita rike
da kwandon abinci. Idan ka ganta ba za ka ce ta haifi yara
har uku ba, Allah Ya yi mata baiwar jiki mai kyau kuma
wanda ya samu kulawar da ta dace.
Har ta iso asibitin da Amrah suke ba ta cikin walwalarta.
Ɗahiru ta soma kiciɓus da shi a barandar emergency,
suka gaisa ya fadamata lambar dakin sannan ya fita. Ta
karasa, Amrah na kwance tana bacci sai Umma a gefe. Ta
karasa suka gaisa da Umma.
"Wai, gaskiya kin yi kokari, ana wannan ruwan kika fito?"
Murmushi ta yi.
"Umma ai dole ne, ƴar uwata guda ba lafiya fa."
Ƴar dariya Umma ta yi.
"Kinga da sauki ma, likitan ya ce wai Malaria ce kuma
kinsan ba'a son Mai ciki da ita, amma yanzu
Alhamdulillah. Ba ta jima da samun baccin ba ma."
Jinjina kai Ramlat ta yi tana maida dubanta saman fuskar
Amrah, duk ta ajiye wani kumatu.
"Allah Ya bata lafiya."
Daga nan ta ajiyewa Umma kwandon suka shiga hira
kadan-kadan. Sun kai kusan mintuna sha biyar kafin
Amrah ta farka.
"Ya jikin?"
Umma ta furta tana dubanta. Gyada kai ta yi tana kokarin
miƙewa zaune.
"Alhamdulillah, kan ya sauka ma."
Yanda ta furta ma ka san ba lafiyar. Suka yi mata sannu.
Da taimakon Ramlat, ta shiga banɗaki ta yi alwala ta
wanko baki. Suka dawo ta zauna, Ramlat da kanta ta
zubamata farfesun naman ragon da ta kawo wanda ya ji
karas da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login