Showing 21001 words to 24000 words out of 113545 words

Chapter 8 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

ɗankali. Ta haɗamata shayi sannan ta haɗa na
Umma, itama ta zubamata farfesun.
Suna ci su na taɓa hira. Ruwa na tsagaitawa Umma ta
wuce gida da zummar za ta turo kanwarta (ita Ummar),
Magajiya ta zo ta zauna da ita.
"Ya na ganki wani iri?"
Amrah ta watsowa Ramlat tambaya tana dubanta.
Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba komai."
Girgiza kai Amrah ta yi.
"Karya ne wallahi. Dama shiru nayi don Umma na wurin
amma tun da na dora idanu a kanki na gane akwai
matsala."
Shiru Ramlat ta yi kafin kuma ta soma fitar hawaye, a yau
dai zuciyarta ta motsa da kewa mai yawa na Aliyunta. Da
ace za ta rasa duk abinda ta mallaka don kawai Allah Ya
ba ta damar ganinsa su yi magana ko sau daya ne, da tuni
ta aikata hakan. Sai dai kuma ita mutuwar gaskiya ce,
barin duniya ce ta har abada da babu dawowa sai dai ka
je ka tarar.
"Lafiya kuwa?"
Cewar Amrah kusan hankali a tashe, ganin tana neman
jefa mai juna biyu cikin matsala ta yi saurin dauke
hawayenta ta hau murmushin yaƙe.
"Ke ba fa wani abun tada hankali bane."
Nan ta kromata dukkan abinda ke faruwa, murmushi
Amrah ta yi. Ta lura ba maganar kai yaran gidan
kakanninsu ne tashin hankalin ƙawarta ba sai maganar
auren da ake budemata wuta a kai.
"Yanzu don Allah Ramlat kin fi kaunar ki yi ta zama haka
ba aure? Kina zaton hatta Abba idan ace yau yana doron
ƙasa zai yi murna da zamanki haka? Ko a tunaninki Aliyu
zai yi farin ciki da zamanki haka babu aure? Wallahi kin ji
na rantsemaki cikinsu babu wanda zai so ki ƙare rayuwarki
a haka. Kema fa mace ce, a karon kanki sai dai ki ɓoye,
kinsan cewa kina bukatar auren. Kina son wanda zai kula
da ke da rayuwarki."
Amrah ta ci gaba da kwantarwa Ramlat hankali ta hanyar
nasiha da rarrashi. Tun Ramlat na jin haushin maganganun
har ta soma gane dagaske duk abinda ta fadi babu ƙarya
ko sharri a ciki.
"Batun yara kuwa kema kinsan ba ki isa hanasu zumunci
da dangin mahaifinsu ba koda su din ba sa ta su."
Murmushi kawai Ramlat ta yi a nan.
"Ke ni ina Muhibbat ne? Kwana biyu na ji ta shiru a
WhatsApp."
"Tana nan, ko juma'ar da ta wuce mun gaisa. Ta yi rashin
lafiya kwana biyunnan wai."
"Allah Ya bata lafiya." Cewar Amrah.
Zuwan Baba Magajiya kanwar Umma ne ya ba Ramlat
damar yi musu sallama ta tafi. Yayyafi-yayyafi ake yi garin
ya yi luf-luf da sanyi mai sanya nutsuwar zuci.
Tana tafe tana tauna zantukan Amrah har ta isa ga
motarta.
***
YAKASAI..
Kanta kamar ya tsage biyu, bakinta ya yi mata nauyi
yayinda ta ƙurawa Kawu Bello idanu don ji take kamar
babu sauran laka a jikinta. Ta rasa ma me za ta ce, ta
kasa fahimtar idan bayanan suka dosa. Batun dai zai bayar
da ita ga CHAIRMAN ALIYU DIKKO ya fi komai ba ta
mamaki da kuma dariya.
"Kin yi shiru kin tsuramin idanu kamar wani sa'anki?! Sarai
kin ji ai abinda na ce! Mun gaji da zubamaki idanu, ke ba
ki kawo wani kin ce kina sonsa ba, kuma ke ba ki ba masu
sonki dama ba! Toh na bayar da ke ga Chairman, zai
soma zuwa hira wurinki ku fahimci juna. Nan da sati uku
ma zan dauramaku aure."
Ya ƙarashe yana fitar da wani huci har da muzurai, bakin
ciki ya sa hawayen ma kasa zubowa. Wato Chairman
shigo-shigo ba zurfi ya yi mata kenan? Ta ya akai ma ya
san gidan kakanninta?
"Ki je ki saurari zuwansa cikin satinnan, saura kuma
wannan karon kamar yanda kika nunamana a baya, yanzun
ma ki nuna ba mu isa da ke ba. Dama ai mai hali ba ya
fasa halinsa. To mu zuba da ke."
na.
Ni Mukhtar Adam Nation


Ina cin damuwa ina son kusanya ni cikin Addu'arku Allah yayayen Damuwa na
Ameen
KARFEN KAFA Chapter 49
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Wasu zafafan hawaye suka zubomata, ta kasa duban
Kawun har ya mike ya bar mata dakin. Jiki a sanyaye ta
share hawayenta, ta mike ta koma sashen Dada. Nan ne
ta samu Dada ta shiga kwantar da hankalinta da hanyar
nasiha da nunamata muhimmancin auren a gareta. Ita dai
ji ta yi gidan duk ya isheta, sallar la'asar kawai ta gabatar
kafin ta yiwa Dada sallama ta yi ficewarta.
A zauren suka yi kiciɓus da Kamal.
"Ashe Ramlat arzikina kika raina ban sani ba, kin nunamin
ba za ki iya aurena ba saboda a gidanmu ba'a sonki,
yanzu ai gashinan da wannan maigidannaki ya fito kin
kawoshi har ya ga Kawu. Ki dai bi a hankali duniya ce, ta
fi bagaruwa iya jima!"
Yana kaiwa nan ya gifta ta ya wuce, ta bishi da kallo
sannan ta fice, a hanyar tana tafe tana hawaye sosai.
Komai ba ya mata dadi, wannan ne yasa ta zaɓi
kaɗaicewa ita ɗaya ba tare da kowa a kusa da ita ba.
Wani Rainbow Park ta je, wuri ne mai karancin hayaniya,
mutanen da ke a wurin tsilli-tsilli, ba ruwansu da harkar
kowa. Wannan ne yasa ta zaɓi can wurin da za ta je ta
samu nutsuwar zuciya.
Cikin wata rumfar kara ta nufa inda aka jera kujeru, iska
mai dadi wurin ke bayarwa. Akwai ƙarancin jama'a a Park
din adalilin ruwan da aka yi.
Tunani kawai take tana fitar da hawaye masu ɗumi.
Duniyar da abinda ke cikinta take ji sun ishe ta, an ce
bazawara nada ƴancin zaɓin wanda ta ke so, amma tana
ji kamar ba ta da wannan damar.
***
Tafe yake a hanyarsa ta zuwa wurin Gym. Tafiyarsa yake
cikin nutsuwa yana sauraron yabon Ya Habibal Qolbi na
Sabyan Gambus. Waƙar sosai yake jin dadinta, murmushi
yake. Hankalinsa ya kai ga motar da ko a mafarki,
lambarta ba za ta ɓacemasa ba. Ɗan tattara gira ya yi don
son tabbatar da abinda idanunsa suka gani, ya nemi wuri
ya yi parking.
"Me ta ke yi anan?" Ya samu kansa da furtawa a fili alhalin
ya san babu mai amsawar.
Fitowa ya yi ya kara kallon lambar don tabbatarwa. Can
kuma ya fito ya shiga Park din don son tabbatarwa kansa.
Sanye yake da wando da riga na kamfanin Adidas, farare
da layi-layin navy blue a gefen hannu da wandon. Ƙafafun
cikin farin canvas.
Gashin kansa ya kwanta luf-luf har a ƙeya, baza dara-
daran idanunsa ya shiga yi wanda gashin ido ke kokarin
rufewa duk sadda ya kyafta.
Har ya juya cikin fidda ran ganinta a wurin, idanunsa ya
kai gareta cikin rumfa. Tana zaune ta ɗora gwuiwar
hannunta saman kujera ta kama dage kanta da tafin
hannu.
Kamar tunani take yi mai zurfi, kamar kuma hawaye ne
saman fuskarta. Don so ya tantance, sai ya ƙarasa.
Sallama ya yi amma ga mamakinsa ba'a san ya yi ba. Jan
kujera ya yi da ke fuskantarta ya zauna. Wannan ƙarar ce
ta maidota hayyacinta, ta dubeshi da idanunta da suka
ƙanƙance suka yi ja. Shima zubamata nasa kwayar idanun
ya yi fuskarsa da wata kwantacciyar damuwa.
Ta yi saurin share fuskarta, sosai ta kaɗu da ganinsa a
wurin, ta kuma yi mamaki.
"Assalamu alaikum."
Ya kara maimaitawa, ta amsa a ciki-ciki. Miƙewa ta yi da
niyyar barin wajen, ya yi saurin riƙe gefen dankwalin
abayarta wanda ba shiri ta koma ta zauna.
"Lafiya?" Ta fadi murya a ƙasan maƙoshi. Murmushi ya yi.
"Ke zan tambaya, daga ganina sai ki gudu. Zauna ki ci
gaba da hawayen ni tayaki kawai na zo yi."
Ta kauda kai daga barin kallonsa, ba ta ce uffan ba,
zuciyarta ba ta cikin nutsuwar da za ta yi wani murmushi
har ta kai ga darawa. Yau an motsa mata dukkan
damuwarta. Yau ta tuna da mutane biyu masu ƙima da
daraja a wurinta kuma mafi soyuwa a zuciyarta da ta rasa.
"Kiyi hakuri, komai na duniya mai ƙarewa ne. Wannan
hawayen faɗuwa ce a wurinki ba nasara ba. Babu abinda
zai yayemaki. Kema fa kin sani. Wani abin muna ji muna
gani amma yake gagararmu tankwarawa saboda ba mu
isa ba, sai yanda aka ce da mu, sai yanda akai da mu."
Ya fadi hankalinsa na kanta. Ta dubeshi, lokacin da ta ji
saukar wasu sabbin hawayen, ba kanta kawai ta
tausayawa ba, kalamansa na karshe kamar dan tsakure ne
daga tasa matsalar a iyakar fahintarta domin kuwa ba shi
da masaniya akan nata.
"Ka san damuwata ne? Ya akai ka san ina nan?" Ta furta
kanta tsaye a sadda ta ke kokarin share hawayenta. Ya yi
murmushi.
"Gashinan rubuce saman fuskarki."
Ta kara tsuke fuska ganin ya share tambayarta ta biyu.
"Kinsan me?"
Ta dubeshi gami da girgiza kai. Ya maida hankali kan
wayarsa dake ringing, ganin sunan Hisham na yawo
saman screen ya ɗaga.
"Ba zan samu shigowa ba." Abinda ya ce kenan bayan sun
gaisa. Ramlat ta saci kallonsa, ba shiri ta kauda nata
idanun ganin irin duban da yakemata.
Tana jin muryar Hisham na tambayar dalili.
Murmushi ya yi mai sauti.
"Ina tare da Heart."
Daga nan ya katse kiran. Kalmar Heart da ya furta ta
sanya gabanta faɗuwa, ta dubeshi, ganin ya ɗagamata kira
ta kauda kai. Ya ajiye wayar saman teburin.
"Tambayarki ta biyu ce ni kaina amsarta nake nema.
Nasan dai a wautana motarki na gani, na haddace
lambarta fiye da zatonki. Sai dai na rasa ya akai jikina ya
bani ke ɗin ce ke jan ta, kuma har na zaɓi shigowa nan na
ga wanda kika zo gani. Sai kuma na ganki ke ɗaya kina
hawaye. Nan take tunanina ya bani cewar watakila faɗa ku
ka yi ya tashi ya bar ki ko kuma bai zo ba. Ma'ana, ya yi
disappointing dinki."
Murmushin takaici ta yi.
"Babu ko daya cikin hasashenka, asalima a karon kaina na
zaɓi nan matsayin wajen da zan samarwa zuciya da
kwakwalwata nutsuwa."
"Kina zuwa kenan?"
Ta ɗan taɓe ƙaramin bakinta gami da girgiza kai. Ya bi
bakin da kallo ya kauda fuska yana murmushi.
"Heart." Ya furta a hankali, sai dai ta ji shi sarai. Miƙewa ta
ƙara niyyar yi ya hanata ta hanyar rike mayafin karo na
biyu. Dole ta zauna.
"Tafiya zan yi."
Yanda ta furta kusan a fusace sai ta ba shi dariya.
"Ba ki isa ba ai, uzuri ne fa da ni kika dakatar da ni."
Ta saki baki da mamaki.
"Yaushe?"
"Yanzu mana."
"Ni na faɗa?"
Ya girgiza kai.
"Abar maganar, kawai dai shawara zan ba ki. No matter
what, ko meke damunki kar ki bari hakan ya sa ki zo irin
wuraren nan. Ki yi hakuri, babu matsalar da wani ko wata
zai magancemaki. Ki miƙa wa Allah lamuranki. Ki dage da
kai kukanki gareShi. Wannan shi ne babban kuskurena a
baya wanda a yanzun ya ke farautana."
Ya ƙarashe cike da tsantsar damuwa, ta dubeshi da
kulawa.
"Ban yi zaton kana da damuwa ba, Allah Ya maka dukkan
ni'ima. Kuma.."
"Ke Allah bai miki dukkan ni'ima ba?"
Ta kauda fuskarta daga kallonta.
"Ni kuwa Allah Ya yiwa ni'ima. Ya bani lafiya, Ya ban iyaye
da ƴan uwa masu sona, Ya ban ƴaƴa. Alhamdulillah."
Tana kaiwa nan ta saci kallonsa. Kamar ta so karantar
damuwarsa da yanda ya sauya lokaci guda. Can kuma ta
ga ya ɓige da jinjina kai.
"Yes, you are right. Alhamdulillah."
Yanda ya yi maganar a sanyaye sai ya bata tausayi.
"Gwara ki tafi, yamma ta yi."
"Kana da ƴan uwa a garinnan?"
Abinda ta ce kenan. Wani banzan kallo ya watsamata da
ya razanata.
"Ba ki damar shiga rayuwata hakan ba yana nufin har da
lasisin da za ki tambayi abinda ya shafi rayuwata bane. Ya
kamata ki san wannan."
Yana kaiwa nan ya mike a fusace ya yi gaba.
Ta bishi da kallo duk sai ta ji hankalinta ya tashi, bata taɓa
ganinsa a yanayi makamancin wannan ba. Labarin da
Hisham ya ba ta sadda magana makamanciyar haka ta
haɗa su shi ya fado ranta. Da sauri ta mike ta dauki
jakarta da zummar mara mishi baya. Wayarsa ta gani
ajiye, ta dauka ta bi bayansa. Sai dai har ya kai ƙarar fita.
Kafin ta karasa har ya shige mota ya tayar. Zagayawa ta yi
da sauri ta bude mazaunin gefe ta shiga.
Ya buga sitayari murya a kausashe ya ce
"Fita!"
Girgiza kai ta yi hawaye na zuba.
"Ka yi hakuri don Allah, wal..."
"I said get out!!"
Ya faɗi cikin tsawa hadi da buga sitayari iyakar karfinsa
har sai da ta razana. Idanunsa kamar an watsa barkono.
Yanda jikinsa ke rawa itama haka nata jikin ke yi. Ta bude
murfin motar ba shiri ta fita. Bai bari ta karasa rufewa ba
ya fisgi motar har yana kokarin buge wani mota. Mai
motar ya dakata da sauri yana duramasa ashar. Hussein
bai ma san yana yi ba. Ita dai Ramlat kirjinta je dukan
tara-tara da irin gudun gangancin da ta hangoshi yana yi,
hawaye kamar famfo take fitarwa ba ta ko damu da kallon
da jama'ar wurin ke bin ta da shi ba. Ta shiga motarta ta
bar wurin cike da jin haushi kanta, me ya kai ta wannan
gangancin?
***
MAFARIN KENAN.....
Jikin Hajiya ya yi sanyi bayan gama sauraron Ramlat. Sam
ba ta tsammaci hakan ce za ta faru ba. Ta dauka dai faɗa
akan fiddo mijin kawai za'a yi mata. Ta sauke ajiyar zuciya
tana kallon yanda Ramlat ke kuka kamar ranta zai fita.
"Ke fa na yarinya ba ce, kin kuma sani dama can ba'a yi
miki dole ballantana a kwata wannan karon. Da ace wani
ne ba shi Maigidannaki ba, toh ba lallai ya dameni ba.
Amma sam bana son wannan haɗi na Yaya Bello. Duk ke
kika jaza wa kanki ai Ramlatu, tun yaushe ake biyamaki
karatun fidda miji kin ƙi haddacewa balle ki yi aiki da shi?
Yanzu gashinan an miki shigo-shigo ba zurfi."
Ramlat ta dubeta tana sharce hawaye.
"Nima Hajiya ba wai ba zan bi umarninsa ba ne, sai dai
nasan waye Chairman tunda ni ke aiki karkashinsa. Ya sha
nunamin zai zo gidanmu ina ƙin ba shi dama don na riga
na san waye shi. Ban ɓoyemaki komai dangane da
alaƙarmu ba. Yanzu kam an zo gaɓar da zan bar
ma'aikatar Revenue, ba zan iya ci gaba da zamansa ba.
Ya kamata ace dama tun a baya na yanke wannan
hukuncin. Amma yanzun ma lokaci bai ƙuremin ba."
Kai Hajiya ta jinjina.
"Ina bayanki, ya dace yanzu kuma ki bar masa ma'aikatar
duk da ba tasa bace ta gwamnati ce, kinga kenan ba shi
da wata ƙafar da zai yi amfani da ita wajen cin zarafinki
ko yi miki bita da kulli. Ni ai tunda ki ka ce ya san waccan
matar hankalina bai kwanta ba."
Nan da nan Hussein ya fado ranta, ta dubi Hajiya. Ta ji
tana son zayyanemata komai.
"Hajiya kin tuna baƙinmu na Adamawa?"
"Ta ya zan mance su, mutane masu karamci haka
Ramlatu? Meyafaru?"
Hajiya ta tambaya cike da ƙaguwa. A zatonta, abinda ƴan
uwan Ramlat din ke zargi ne zai tabbata, wato soyayya
tsakanin Alhassan da ita. Abinda ba za ta yarda ba kenan
ko don mutunci da girmamawar da Kausar ke mata.
"Kinsan kuwa suna da alaƙa da Hussein da nake ba ki
labari mijin Hajiya Zeenatu?"
Ido waje Hajiya ke dubanta.
"Alaƙa wace iri?"
Tiryan-tiryan ta ba ta labarin duk abinda ta sani. Sai ga
Hajiya na salati har da hawayen tausayi.
"Kai duniya! Mata me muka dauketa ne? Matattarar da
za'a dauwama ko me? Zunuban kanmu kaɗai bai isa ba
sai mun zalunci wasunmu? Kaico da wannan rayuwa.
Allah Ya sakawa wannan yaro, Allah Ya karya ƙadarin
wannan mata."
Hawayen Ramlat suka ci gaba da ambaliya, sam ba ta
faɗa wa Hajiya abinda ya faru tsakaninsu a yau ba,
hankalinta ya yi kansa sosai, tana son ta ji muryarsa ko
don tabbatar da lafiyarsa.
"Amma wannan fa ba karamin aiki ba ne na wasa, addu'a
ce sosai zamu dukufa ga yi masa. Zuwa anjima zan kira
Kawunki Malam Yakubu. Na tabbatar shima zai taimaka.
Ba a banza matarnan ta bar shi ba."
Zantukan Hajiya masu dadin sauraro suka katsemata
tunani. Wani sanyin dadi ta ji, har ta mance kaso mai
yawa na damuwarta, ta yi murmushi gami da godiya. Daga
wannan ta mike ta bar mata dakin zuwanata.
Nan ta iske yaran sun yi baja-baja saman gadonta ana
game a waya. Dubansu ta yi gami da murmushi, haka
kawai ta ji har ta soma kewarsu. Maimakon ta korasu
kamar yanda ta saba, kawai sai ta zauna ta biyemusu tare
da alƙalanci.
Sai da wani tunani ya faɗomata sannan ta karɓi wayarta
ta basu umarnin zuwa falo. Agogo ta duba, ƙarfe shida da
rabi na dare, so ta ke ta kirashi amma ba ta kaunar abinda
zai je ya dawo don haka ta zaɓi aikamasa saƙo.
***
LAMIƊO CRESCENT...
Yana zaune kamar kurma yana sauraron Hajiya Zeenatu da
ke buɗewa John wuta akan ya yi girkin da mijinta ya kasa
ci. Ɗora laifi kacokan ta yi akansa, shi dai ƙara russunar
da kai ya yi yana ambaton "Sorry Ma." Hussein da abin ya
ishe shi, miƙewa tsaye ya yi gami da daukar wayarsa.
"Please ya isa haka, na fadamaki yunwar ce kawai ba na
ji, ba wai girkin ba ne."
Yana kaiwa nan ya nufi matattakala. Ta bishi da kallo kafin
ta maido dubanta ga John, harara ta watsamasa gami da
ba shi umarnin tafiya. Hankalinta ya koma ga tunanin
abinda ta shirya yi. Wato shan maganin da Gora ya ba ta
wanda ya tabbatar da zarar Hussein ya kusanceta za ta
samu ciki. Samun cikinta ne zai mantar da Hussein
tunanin kowa da komai face tattalin da zai koma ba ta.
Wannan ta sa da sauri ta jawo kofin ruwa ta daga riga ta
ciro ƙullin maganin ta zuba gami da gaurayawa ta kafa
baki, ba ta ɗago ba sai da ta shanye tas tana wani
murmushi.
Shi kuwa Hussein, zube wayoyin saman gado ya yi ya
shiga rage kayan jikinsa, wanda ya ke da niyyar shiga,
ƙarar shigowar saƙo ya ɗauki hankalinsa. Duban wayar ya
yi, kamar kada ya buɗe sai kuma ya tuna da saƙon da za'a
aikomasa na abinda ya shafi aikinsa. Madadin hakan ya ci
karo da sunan da hannunsa ya rubuta saman lambar da ya
ɗauketa da wani irin muhimmancin da bai san dalili ba.
_*Heart*_
Ya furta tamkar baya so kafin ya kai ga buɗewa.
*_"Dukkanmu ajizai ne, mukan yi kuskure da saninmu ko
kuma akasinsa. Bana fatan na yi abinda zai jefaka cikin
ɓacin rai da damuwa. Shakka babu, Ramlat mai laifi ce,
na yarda na shiga personal life dinka, na zaƙe da yawa. Ka
yi hakuri, ka yi hakuri. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba. Ka
ji?"*_
Murmushi ya yi, ya kara karantawa ya fi sau uku, ya so ya
gogeshi daga wayar amma ya ji ba zai iyaba. Wani nauyi
hakan ya yi mishi don haka sai ya fasa, ya sanyawa wayar
muƙulli ya jefa saman gado. Har ya shiga banɗaki bai bar
murmushi ba.
Fitowarsa ba jimawa ya sanya kayan bacci, shigowar
Hajiya Zeenatu ne ya sa shi dubanta. Saura kaɗan wata
dariya ta kufcemasa. Rigar bacci ce a jikinta shara-shara
kuma marar tsawo don duka tsawon iyakarsa gwuiwa.
Ƙaton tumbinta da ruguza-ruguzan mamanta wadanda
suka zube sun kwanta luf sun bayyana cikin rigar.
Damtsenta kuwa a cike sosai sai dai ba ka misalta shi da
na karfafan maza ba. Akwai bambanci.
Duba sosai ya ke mata, riga dai gatanan mai ɗan karen
kyau da daukar ido. Lumshe idanunsa ya yi yayinda wani
tunani ya bijiromasa.
'Za ta yi kyau sosai.' Ya furta ƙasa ransa, ankara da
kuskuren kalaminsa ne yasa shi jan istigfari. Sai kuma
lokacin ya tuna da bai yi sallar Isha'i ba ya ke shirin
kwanciya. Abin yana damunsa, ya rasa me ke shagaltar da
shi daga bautar UbangijinSa, ma'ana gabatar da sallah
akan lokaci. Abin yana mishi ciwo, sai dai mafi yawan
lokaci ji yake kamar wanda aka mantar. Sau tari ma wani
bacci ke zuwa ya rufe idanunsa da zarar an soma kiraye-
kirayen sallah.
Ganin ya mike yasa Hajiya Zeenatu tunkaroshi,
hannayenta biyu ta sanya saman kugunsa.
Ya yi mata murmushi mai kama da yaƙe. Duk yanda ya so
nunamata tsana ko wani abun, sai ya ji ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login